فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja

 

Ya zo daga cikin hadisin da zindiki ya tambayi Imam Sadik (as) dangane da wasu mas'aloli cikin su yake cewa:

أخبرني عن السراج إذا انطفأ أين يذهب نوره ؟

قال : «يذهب فلا يعود».

قال : فما أنكرت أن يكون الإنسان مثل ذلک ، إذا مات وفارق الروح البدن لم يرجع إليه أبدآ كما لا يرجع ضوء السراج إليه إذا انطفأ؟

قال : قال : «لم تصب القياس ، إنّ النار في الأجسام كامنة قائمة بأعيانها، كالحجر والحديد، فإذا ضرب أحدهما بآخر سطعت من بينهما نار يقتبس منها سراج له ضوء، فالنار ثابتة في أجسامها، والضوء ذاهب ، والروح جسم رقيق ، قد اُلبس قالبآ كثيفآ ليس بمنزلة السراج الذي ذكرت ، إنّ الذي خلق في الرحم جنينآ من ماء صافٍ وركّب فيه ضروبآ مختلفة من عروق وعصب وأسنان وشعر وعظام وغير ذلک هو يحييه بعد موته ويعيده بعد فنائه »

Ka bani labari dangane da fitila idan aka kasheta ina haskenta yake tafiya?

Sai ya ce: yana tafiya ne ba kuma ya dawo.

Sai ya ce: yanzu baka inkarin mutum ya kasance misalin wannan fitila, idan ya mutu gangar jikin sa ta rabu da ruhin sa ba zai komo zuwa gare shi ba har abada kamar yadda hasken fitila idan aka kashe ya tafi kenan ba zai dawo gareta ba?

Sai ya ce: baka dace da kiyasi ba, lallai ita wuta cikin jikkuna boye take tsaye take da kanta, kamar misalin dutse da karfe, idan aka buga daya jikin dayan sai tsakankaninsu wuta ta hudo wacce fitila mai haskaka ke tsonowa daga gareta, saboda haka ita wuta tabbtacciya ce cikin jikkunanta, shi ko haske tafiya yake, shi kuma ruhi jiki ne siriri, hakika ya tufatatantu da wani kalibi babba ba daidai da yake da matsayin fitila ba wacce ka ambata, lallai wanda ya halicci jariri cikin mahaifa daga tacaccen ruwa sannan ya harhada abubuwa daban-daban cikinsa daga jijiyoyi da hakora da kasusuwa da makamantan haka shi ne wanda zai raya shi bayan yam utu ya kuma dawo da shi bayan karewar sa.[1]

ــ وسئل الحسن بن عليّ بن أبي طالب  :: ما الموت الذي جهلوه ؟

قال : «أعظم سرور يرد على المؤمنين إذا نقلوا عن دار النكد إلى نعيم الأبد، وأعظم بثور يرد على الكافرين إذا نقلوا عن جنّتهم إلى نار لا تنفذ» .

an tambayi Hassan bn Ali bn Abu dalib (as) shi ne mece ce mutuwar da suka jahilta?

Sai ya ce: (mafi girman farin ciki da yake gangara kan muminai idan sun ciratu daga gidan wahala ya zuwa ni'ima madawammiya. Ita ce mafi girman ciwo da zai gangara kan kafirai idan suka ciratu daga jahannama zuwa ga wata wuta da bata zartuwa.

 وقال عليّ بن الحسين   :

«لمّا اشتدّ الأمر على الحسين بن عليّ بن أبي طالب  :، نظر إليه من كان معه فإذا هو بخلافهم ، لأنّهم كلّما اشتدّ الأمر تغيّرت ألوانهم وارتعدت فرائصهم ووجلت قلوبهم ، وكان الحسين صلوات الله عليه وبعض من معه من خصائصه تشرق ألوانهم وتهدأ جوارحهم وتسكن نفوسهم ، فقال بعضهم لبعض : انظروا لا يبالي بالموت ؟ فقال لهم الحسين  7: صبرآ بني الكرام ، فما الموت إلّا قنطرة يعبر بكم عن البؤس والضرّاء إلى الجنان الواسعة والنعيم الدائمة ، فأيّكم يكره أن ينتقل من سجن إلى قصر؟ وما هو لأعدائكم إلّا كمن ينتقل من قصر إلى سجن وعذاب ، إنّ أبي حدّثني عن رسول الله  9: إنّ الدنيا سجن المؤمن وجنّة الكافر، والموت جسر هؤلاء إلى جنانهم وجسر هؤلاء إلى جحيمهم ، ما كُذبت ولا كَذبت » .

Aliyu bn Husaini ya ce: sa'ilin da lamari ya tsananta ga Husaini bn Ali bn Abu dalib (as) sai ya kalli wadanda suke tare da shi sai ga shi ya kasance sabanin su, sakamakon su duk sanda lamari ya tsananta kansu sai launinsu ya sauya kafadun su su girgizu zukatan su, su tsorata, Husaini bn Ali (as) ya kasance daga cikin falolin da ya kebantu dasu ba'arin gabban ba'arin wadanda yake tare da su ke haskaka zukatan su ke samun nutsuwa, sai ba'arin wadanda suke tare suka cewa ba'arinsu ku duba shi bai damuwa da mutuwa? Sai Husaini (as) ya ce musu: kuyi hakuri ya `ya`yan masu daraja, mutuwa ba komai bace face gada da zata tsallakar da ku daga barin tsanani da wahala zuwa ga aljannoni masu fadi da ni'ima madawwamiya, wane ne daga cikinku bai kaunar ya ciratu daga gidan fursun gidan kaso zuwa fada? Ita mutuwa ba komai bace ga makiyanku face kamar misalin wanda zai ciratu daga fada zuwa  fursun da zaba, lallai babana ya zantar dani daga manzon Allah (s.a.w) : cewa lallai ita duniya fursun din mumini ce kuma aljannar kafiri ce, sannan ita mutuwa gada wadannan ce zuwa ga aljannonin su haka gadar wadan can ce zuwa ga jahimin su ba a karya taka ba, ba kuma ka taba yin karya ba.[2]

ــ وقيل لمحمّد بن عليّ  : ما الموت ؟

قال : «هو النوم الذي يأتيكم كلّ ليلة إلّا أنّه طويل مدّته ، لا ينتبه منه إلّا يوم القيامة ، فمن رأى في نومه من أصناف الفرح ما لا يقادر قدره ، ومن أصناف الأهوال ما لا يقادر قدره ، فكيف حال فرح في النوم ووجل فيه ؟ هذا هو الموت فاستعدّوا له » .

An cewa Muhammad bn Ali (as): mece ce mutuwa?

Sai ya ce: ita ce baccin da yake zuwar muku cikin kowanne dare sai dai kawai ita mutuwa baccinta yana da tsawon lokaci, mutum bai farkwa sai ranar kiyama, duk wanda cikin barcin sa ya ga sinfofi farin ciki daga wanda da ba a kaddara girman su, hakama daga sinfofi tsorace-tsorace da ba a kaddara girman su, ta kaka farin ciki ya shiga tsakanin barci wanda cikin sa akwai tsoro? Wannan ita ce mutuwa ku yi mata tanadi.[3]

ــ وعن عليّ بن الحسين  8 في رواية نفخ الصور :

«... فعند ذلک ينادي الجبّار جلّ جلاله مجيبآ لنفسه في قوله تعالى  : لمن الملک : لله الواحد القهّار، وأنا قهرت الخلائق كلّهم وأمتّهم ، إنّي أنا الله لا إله

إلّا أنا، وحدي لا شريک لي ولا وزير، وأنا خلقت بيدي وأنا أمتّهم بمشيّتي وأنا اُحييهم بقدرتي ، قال : فنفخ الجبّار نفخة في الصور يخرج الصوت من أحد الطرفين الذي يلي السماوات ، فلا يبقى في السماوات أحد إلّا حي وقام كما كان ، ويعود حملة العرش ويحضر الجنّة والنار ويحشر الخلائق للحساب ، قال : فرأيت عليّ بن الحسين صلوات الله عليهما يبكي عند ذلک بكاءً شديدآ».

An karbo daga Aliyu bn Husaini (as) cikin riwayar busa cikin kaho: a wannan lokaci mai girma girman sa ya girmama zai yi shela yana mai amsawa kansa cikin fadin sa madaukaki: yau mulki ga wa yake: ga Allah daya mabuwayi, ni ne na buwayi bayi baki dayan su na matar da su, lallai ni ne Allah babu abin bauta da gaskiya sai ni, ni kadai babu abokin tarayya gareni babu waziri, ni na yi halitta da hannuna ni ne wanda ya karbi rayukan su da mashi'ata ni ne nake raya su da iko na, ya ce: sai mai tilastawa ya busa kaha busa daya sauti na fitowa dayan bangarori biyu wadanda yake biyo sammai, babu abin da zai wanzu a sama face rayayye ya tsaya kamar yadda ya kasance, ya dawo da madaukan al'arshi, ya halarto da aljanna da wuta ya tashi halittu domin yi musu hisabi, ya ce: sai na ga Ali bn Husaini amincin Allah ya kara tabbata gare su yana kuka a wannan lokaci kuka mai tsanani.[4]

ــ وقال أمير المؤمنين  7 في خطبته  :

«فإنّ الغاية أمامكم ، وإنّ وراءكم الساعة تحدوكم ، تخفّفوا تلحقوا، فإنّما ينتظر بأوّلكم آخركم »

Sarkin muminai Ali (as) cikin wata huduba tasa yana ya ce:

Lallai magaryar tukewa na gabanku, lallai bayanku lokaci na koraku, ku rarraurawa zaku riska, lallai kadai ana jiran na farkonku dana karshenku.[5]

ــ وقال أمير المؤمنين   :

«واتّقوا الله عباد الله، وبادروا آجالكم بأعمالكم ، وابتاعوا ما يبقى لكم بما يزول عنكم ، وترحّلوا فقد جدّ بكم ، واستعدّوا للموت فقد أظلّكم ، وكونوا قومآ صيح بهم فانتبهوا، وعلموا أنّ الدنيا ليست لهم بدار فاستبدلوا، فإنّ الله سبحانه لم يخلقكم عبثآ ولم يترككم سدىً ، وما بين أحدكم وبين الجنّة أو النار إلّا الموت أن ينزل به ... فيا لها حسرة على ذي غفلة أن يكون عمره عليه حجّة ، وأن تؤدّيه أيامه إلى شقوة ، نسأل الله سبحانه أن يجعلنا وإيّاكم ممّن لا تبطره نعمة ولا تقصر به عن طاعة ربّه غاية ، ولا تحلّ به بعد الموت ندامة ولا كآبة ».

Sarkin muminai (as) ya ce: kuji tsoran Allah ya bayin Allah, ku gaggauci gabaci ajalinku da ayyukanku, ku sayo abin da ya rage gareku da abin da zai gushe ga barinku, ku shirya tafiya lallai ta tabbata daku, ku shirya ga mutuwa hakika ta yi lullubeku da inuwarta, ku zama mutanen akai musu tsawo sai suka fadaku, suka kasan cewa lallai duniya ba wajen zaman su bane sai suka sauya da waninta, lallai Allah tsarki ya tabbatar masa bai haliceku don wargi ba hakama bai barku haka sakaka ba kara zube, babu abin da ke tsakanin dayanku da aljanna ko wuta face mutuwa da zata sauka kansa… ya hasara gareta kan ma'abocin gafala da rayuwar sa zata kasance hujja kansa, kwanakin sa su sauke shi ga tsiyata, muna rokon Allah matsarkaki ya sanya mu da ku daga cikin wadanda ni'ima ba ta sanya musu Gadara, magaryar tukewa ba ta takaita su daga barin da'ar ubangijin su, bayan mutuwa bakin ciki ko nadama bai sauka kansu.[6]

ــ وقال  7 :

«وجاء من أمر الله ما يريده من تجديد خلقه أماد السماء وفطرها، وأرج الأرض وأرجفها، وقلع جبالها ونسفها، ودلّ بعضها بعضآ من هيبة جلالته ومخوف سطوته ، وأخرج من فيها فجدّدهم بعد أخلاقهم ، وجمعهم بعد تفريقهم ، ثمّ ميّزهم لما يريد من مسألتهم عن خفايا الأعمال وخبايا الأفعال ، وجعلهم فريقين أنعم على هؤلاء وانتقم من هؤلاء، فأمّا أهل طاعته فأثابهم بجواره ، وخلّدهم في داره » .

Sarkin muminai (as) ya ce: sannan ya zo daga al'amarin Allah abin da yake nufar sabunta halittar sa da ya motsa sama ya kuma tsagota ya girgizata, da tunbuke duwatsu da yin rugu-rugu da su, da shiryar da shashen su zuwa ga sashe daga haibar girmamar sa da tsoratarwar tumben sa, ya fit abin da wadanda ke rayuwa cikinta sai ya sabunta su bayanda ya tsofaitar dasu, ya tattaro bayan rarrabuwarsu, sannan ya banbance su zuwa ga abin da yake nufi daga tambayar su boyayyun ayyuka, sannan ya sanyu kungiyoyi biyu ya ni'imta wadannan ya azabtar da wadancan, amma wadanda suka yi masa da'a da biyayya sai ya yi musu sakayya da basu mafaka kusa da kuma dawammar dasu cikin gidansa.

 Wannan wani dan kankani tsonowa daga haskayen shiriya daga littafin Allah da sunnar annabi da tsatsonsa tsarkaka cikin asalan addini. Muna rokon Allah hakul yakini da ilimi da aiki nagari amin rabull alamin.

Muna son mu tunatar kan (Du'a'ul Adila) daga littafin (Mafatihul Jinan) na hatimun masana ilimin hadisi shaik Abbas Kummi Allah ya jikan rai wacce ta tattaro asalai biyar, mafi falala shi ne karanta ta lokaci zuwa lokaci, musammam ma cikin wadannan kwanaki masu albarka da wurare masu daraja, bari dai da wurin A'imma tsarkaka, kamar yadda shugabanmu Sayyid Abdul Azim shah Hasani ya yi, wanda yake da wurin ziyara cikin garin Rayyu cikin babban birnin kasar Iran Tehran, lokacin da aka bijiro da addinin sa ga imam zamanin sa Imam Hadi (as) sai Imam ya yi masa addu'a, lallai mu muna imani cikin imamanmu (as) kamar yadda ya zo cikin ziyarar imam Rida (as)

«أشهد أنّک ترى مكاني وتسمع كلامي وتردّ سلامي ».

Ni ina shaida cewa lallai kai kana ganin inda na ke kana kuma jin maganata kana kuma amsa tambayata.

Imami ma'asumi ya na ji kuma ya na gani.

Na kwadaitar da ku da ku riki wannan addu'a ta Adila da zan kawo ta yanzu da sannu cikinta zan fitar da asalan addini guda biyar tsakankanin baka biyu domin kara cika fa'ida.[1] Biharul-anwar: m 6 sh 216

[2] Biharul-anwar: m 6 sh 216

[3] Bihraul-anwar: m 6 sh 154-155

[4] Bihraul-anwar: m 6 sh 324

[5] Biharaul-anwar: m 6 sh 135

[6] Nahjul balaga:165