فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Ma'ad

 

«وأشهد أنّ الموت حقّ ، ومسائلة القبر حقّ ، والبعث حقّ ، والنشور والصراط حقّ ، والميزان حقّ ، والحساب والكتاب حقّ ، والجنّة حقّ ، والنار حقّ ، وأنّ الساعة آتية لا ريب فيها، وأنّ الله يبعث من في القبور».

Ina shaidawa lallai mutuwa gaskiya ce, tambayar kabari gaskiya ce, tashi gaskiya ne, tashi daga kabari gaskiya ne siradi gaskiya ne, mizani gaskiya ne, hisabi da littafi gaskiya ne, aljanna gaskiya ce, wuta gaskiya ce, lallai tashin kiyama mai zuwa ne babu kokwanto cikin sa, lallai Allah yana taso da wadanda suke cikin kabari.

«اللهمّ فضلک رجائي ، وكرمک ورحمتک أملي ، لا عمل لي أستحقّ به الجنّة ، ولا طاعة لي أستوجب بها الرضوان ، إلّا أنّي اعتقدت توحيدک وعدلک ، وارتجيت إحسانک وفضلک ، وتشفّعت إليک بالنبيّ وآله من أحبّتک ، وأنت أكرم الأكرمين وأرحم الراحمين ، وصلّى الله على نبيّنا محمّد وآله أجمعين الطيّبين الطاهرين ، وسلّم تسليمآ كثيرآ كثيرآ، ولا حول ولا قوّة إلّا بالله العليّ العظيم ».

Ya Allah falalarka ita ce fatana, karamcinka da rahamarka burina, bani da wani aiki da nayi dana cancanci samun aljanna da shi,babu wata da'a gareni da da zata jawo mini samun yardarka, sai dai cewa lallai ni na kudurce tauhidinka da adalcinka, nayi fatan ihsaninka da falalarka, na nemi ceto zuwa gareka da annabi da iyalan sa daga masoyanka, kai ne mafi karamcin masu karamci kai ne mafi jin kan masu jin kai,tsira da aminci Allah su kara tabbata ga Muhammad da baki dayan iyalan sa zababbu tsarkaka, da sallamawa mai tarin yawa, babu tsimi babu dabara face ga Allah madaukaki mai girma.

«اللهمّ يا أرحم الراحمين ، إنّي أودعتک يقيني هذا وثبات ديني ، وأنت خير مستودع ، وقد أمرتنا بحفظ الودائع ، فردّه عليّ وقت حضور موتي برحمتک يا أرحم الراحمين ».

 Ya Allah ya mafi jin kan masu jin kai, lallai ni na ajiye yakini na wannan da tabbatuwar addini a hannunka, lallai kai ne mafi alherin wurin ajiya, hakika ka umarce mu da kiyaye ajiya, ka dawo mini abin da na baka ajiya lokacin hallarowar mutuwa ta don alfarmar rahamarka ya mafi jin kan masu jin kai.

Sannan mawallafin wannan littafi mafatihul jinan shaik Abbas Kummi (rd) ya ce: hakika ya zo cikin wannan addu'a da akai tuntube da ita daga gare su tsarkaka:

«اللهمّ إنّي أعوذ بک من العديلة عند الموت »،

Ya Allah lallai ni ina neman tsarinka daga Adila lokacin mutuwa.

Ma'anar Adila shi ne barin gaskiya da komawa zuwa ga bata lokacin mutuwa, wanda shi ne shaidan ya hallara wurin mai kakakin mutuwa yayi masa wasiwasi cikin kirjin sa ya sanya shi yin shakka cikin addnin sa, sai ya cire imani daga zuciyar sa, sakamakon wannan wasu addu'o'in neman tsari suka zo cikin litattafan addu'a.

Fakrul muhakkikin ibn Allama hilli ya ce: duk wanda ke son ya kubuta daga Adila to ya hallarar da imani da hujjoji kansa, da Asalai biyar da yankakkun hujjoji kan su, tsarkin niyya da tsaftace zuciya domin ya baiwa Allah madaukaki ajiyar su shi kuma Allah ya dawo masa da su lokacin kakakin mutuwa, ma'ana ya furta akidojin gaskiya lokacin da yake kakakin mutuwa.

«اللهمّ يا أرحم الراحمين ، إنّي قد أودعتک يقيني هذا وثبات ديني ، وأنت خير مستودع ، وقد أمرتنا بحفظ الودائع ، فردّه عليَّ وقت حضور موتي ».

Ya Allah ya mafi jin kan masu jin kai, hakika ni na ajiye yakini na wurinka wannan da tabbatuwar addini na, kai mafi alherin wurin ajiya, hakika ka umarce mu da kiyaye ajiya, ka dawo mini da ajiyata lokacin kakakin mutuwa ta.

Hakika karanta wannan addu'a mai daraja da halarto da abin da ta kunsa cikin zuciya tana baiwa mutum aminci daga hatsarin Adila lokaicn kakakin mutuwa.

Amma dangane da wannan addu'a, shin daga ma'asumi (as) ta gangaro ko kuma tana daga kagar ba'arin wasu malamai? Cikin wannan batu kwararren malamin hadisi da matattarar hadisan A'imma malami tafkin ilmi masanin hadisi mai warware zare da abawa maulana Alhahi mirza Nuri (Allah ya haskaka makwancin sa) yana cewa ama addu'ar Adila sananniya, lallai ita tana daga wallafar ba'arin wasu ma'abota ilimi ba daga A'imma ba, ba       ta kuma zo cikin madaukan litattafan hadisai na masu banbance aya da tsakuwa ba.

Ka sani lallai Dusi Allah ya jikan rai ya rawaito daga Muhammad bin Sulaimanu Dailami cewa:

قال للصادق  7: إنّ شيعتک تقول : إنّ الإيمان قسمين : فمستقرّ ثابت ، ومستودع يزول ، فعلّمني دعاءً يكمل به إيماني إذا دعوت به فلا يزول . قال  7 : «قل عقيب كلّ صلاة مكتوبة : (رضيت بالله ربّآ، وبمحمّد  9 نبيّآ، وبالإسلام دينآ، وبالقرآن كتابآ، وبالكعبة قبلة ، وبعليّ وليآ وإمامآ، وبالحسن والحسين وعليّ بن الحسين ومحمّد بن عليّ وجعفر بن محمّد وموسى بن جعفر وعليّ بن موسى ومحمّد بن عليّ وعليّ بن محمّد والحسن بن عليّ والحجّة بن الحسن صلوات الله عليهم أئمة ، اللهمّ إنّي رضيت لهم أئمة فارضني بهم ، إنّک على كلّ شيءٍ قدير)،

Ya cewa Sadik (as) `yan shi'arka suna cewa: lallai imani ya kasu zuwa kashi biyu: zaunanne tabbatacce, da kuma na ajiya da yake gushewa, saboda haka ka koyar dani wata addu'a da imani zai kammalu idan na kirayi Allah da ita imani ba zai gushe ba. sai ya ce: cikin bayan kowacce sallah ta farilla ka ce: (na yarda da Allah matsayin ubangiji, na yarda da Muhammad (s.a.w) matsayin annabi, na yarda da muslunci matsayin addini, yarda da kur'ani matsayin littafi, na yarda da ka'aba matsayin Alkibla, na yarda da Ali matsayin magaji da imami, na yarda da Hassan da Husaini da Ali bn Husaini da Muhammad bn Ali da Jafar bn Muhammad da Musa bn Jafar da Ali bn Musa da Muhammad bn Ali da Ali bn Muhammad da Hassan bn Ali da hujjatu bn Hassan amincin Allah ya kara tabbata gare su, ya Allah lallai ni na yarda dasu matsayin jagorori ka yardar dani dasu, lallai kai kan komai mai iko ne).

Ya zo cikin wata addu'ar daga littafin Kaf'ami bayan dukkanin salloli zaka karanta: 

(رضيت بالله ربّآ، وبالإسلام دينآ، وبمحمّد  9 نبيّآ، وبعليّ إمامآ، وبالحسن والحسين وعليّ ومحمّد وجعفر وموسى وعليّ ومحمّد وعليّ والحسن والخلف الصالح  : أئمة وسادة وقادة ، بهم أتولّى ، ومن أعدائهم أتبرّأ)»،

Na yarda Allah ubangiji ne, na yarda muslunci shi ne addini na yarda da Muhammad (s.a.w) annabi ne, na yarda Ali imami ne, na yarda Hassan da Husaini da Ali da Muhammad da Jafar da Musa da Ali da Muhammad da Ali da Hassan da magaji salihi su A'imma ne shugabanni jagorori da su na *ke karkata daga makiyansu na ke barranta.

Sannan sai ka fadi wannan sau uku:

«اللهمّ إنّي أسألک العفو والعافية والمعافاة في الدنيا والآخرة ».

Ya Allah lallai ni ina rokonka afuwa da lafiya duniya da lahira.

Wannan wani dan yanki daga abin da muka so bayani daga asalan addini wanda yake da matsayin jijiya da tushe bishiyar muslunci zurfaffa cikin zuciyar muminai.

Daga karshe zanyi maka hadaya da munajatin muminai marufin sa almiski, cikin wancan masu rigengeniya suke rigengeniya: