فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

SALLAH

 

 

Allah mabuwayi mai girma cikin littafin sa mai girma ya na cewa:

 (ذَلِکَ الكِتَابُ لا رَيْبَ فِيهِ هُدىً لِلْمُتَّقِينَ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالغَيْبِ وَيُقِيمُونَ الصَّلاةَ ).

Wancan littafi babu kokwanto cikinsa shiriya ga masu takawa*wadanda suke imani da gaibu suke tsayar da sallah.[1]

A wasu wuraren kuma cikin littafin sa mai girma tsarki ya tabbatar masa ya ce:

(وَأقِيمُوا الصَّلاةَ ) .

Ku tsayar da sallah.[2]

 Mai girma da daukaka ya ce:

 (وَأمُرْ أهْلَکَ بِالصَّلاةِ وَآصْطَبِرْ عَلَيْهَا لا نَسْألُکَ رِزْقآ نَحْنُ نَرْزُقُکَ وَالعَاقِبَةُ لِلتَّقْوَى ).

Ka umarci Ahlinka da sallah sallah kayi hakuri kanta ba zamu tambayeka arziki ba mu ne muke azurtaka kyakkyawan karshe yana ga masu takawa.[3]

Madaukaki ya ce:

 (وَأقِمِ الصَّلاةَ إنَّ الصَّلاةَ تَنْهَى عَنِ الفَحْشَاءِ وَالمُنْكَرِ وَلَذِكْرُ اللهِ أكْبَرُ) .

Ka tsayar da sallah lallai sallah tana hani da alfasha da munkari tabbas ambaton Allah shi ne mafi girma.[4]

Mafi daukakar mai magana ya ce:

(يَا بُـنَيَّ أقِمِ الصَّلاةَ ).

Ya dan dana ka tsayar da sallah.[5]

(حَافِظُوا عَلَى الصَّلَوَاتِ وَالصَّلاةِ الوُسْطَى وَقُومُوا للهِ قَانِتِينَ ).

Ku kiyaya salloli da sallar tsakiya ku tashi don Allah kuna masu kana'a.[6]

(فَإذَا قَضَيْتُمُ الصَّلاةَ فَاذْكُرُوا اللهَ قِيَامآ وَقُعُودآ وَعَلَى جُنُوبِكُمْ فَإذَا اطْمَأنَنتُمْ فَأقِيمُوا الصَّلاةَ إنَّ الصَّلاةَ كَانَتْ عَلَى المُؤْمِنِينَ كِتَابآ مَوْقُوتآ) .

Idan kuka kammala ibadojinku ku ambaci Allah a tsaitsaye da zazzaune da kuma kan geffanku idan kun samu nutsuwa ku tsayar da sallah lallai sallah ta kasance kan mumini wajibi mai kayyadadden lokaci[7]

(وَكَانَ يَأمُرُ أهْلَهُ بِالصَّلاةِ وَالزَّكَاةِ وَكَانَ عِنْدَ رَبِّهِ مَرْضِيّآ) .

Ya kasance yana umartar iyalan sa da sallah da zakkaya kuma kasance yardajje wurin ubangijin sa.[8]

(رَبِّ آجْعَلْنِي مُقِيمَ الصَّلاةِ وَمِنْ ذُرِّيَّتِي رَبَّـنَا وَتَقَبَّلْ دُعَاءِ) .

Ya ubangiji ka sanya ni mai tsayar da salla hakama da zuriyata ya ya ubangijinmu ka karbi addu'a.[9]

Lallai Allah tsarki ya tabbatar masa mai tausasawa ga bayin sa, yana nufin farin ciki gare su na har abada, daga cikin ludufin sa yana shiryar dasu da litattfan sa da manzannin sa zuwa ga tafarki madaidaici, kadai dai ya kallafa musu taklifan hukunce-hukuncen shari'a domin ludufi da samun farin ciki madawwami, ya sanya hukunce-hukunce daga wajibai da muharramai da wasun su bisa maslahohin bayin sa cikin kankin kan ayyukan su, dukkanin abin da cikinsa akwai maslaha lazima cikakkiya sai ya sanya shi wajibai da muharramai (abubuwan da aka haramta) ya kuma yi umarni da shi, sannan dukkanin abin da a cikinsa akwai barna da fasadi mai tsanani sai ya sanya shi haramun ya kuma yi hani kan aikata shi, abin da kuma cikinsa akwai maslaha mai rinjaye amma tare da halascin barin sa sai ya sanya shi mustahabbi ya kwadaitar zuwa gare shi, sannan abin da cikinsa akwai barna mai rinjaye amma tare da halascin aikata shi sai yayi hani kansa hani tanzihi (don tsarkake kai) sai ya sanya shi makaruhi, sannan cikin daidaitar geffa biyu to hukunci yana kasancewa halal.

Wadannan hukunce-hukuncen taklifin shari'a –wajibi haramun mustahabbi makaruhi da mubahi (halal) ba wani abu bane face adalcin sa da tausayinsa ga bayinsa domin bijirar dasu zuwa ga samun lada, daga nan ne kuma za su samu farin cikin duniya da lahira, da gidajen aljannoni da karkashin koramu ke gudana cikinsu akwai abin da idanu basu taba gani ba kunnuwa basu taba ji, wannan falala ce daga Allah da ladan sa.

Sannan ya zama tilas ya kasance akwai hukunci gare shi madaukaki cikin dukkanin wani abu dake faruwa da afkuwa da jahili da masani suke tarayya cikin wannan hukunci, babu wani abu da zai wofuntu daga hukuncin waki'i cikin ilimin Allah, ko da kuwa kofar sanin al'amarin ta toshe garemu, lallai mu zamu yi aiki da zato wanda ake la'akari da shi a shari'ance kamar misalin khabarul wahid na sika zahirin littafin Allah, wadancananka ya na kasancewa cikin rassan addini da hukunce-hukuncen su, bawai cikin asalan addini ba, lallai cikin rassa Allah ya sanya zato a matsayin yakini lokacin kofar zuwa ga ilimi da yakini ta toshe garemu.

Daga cikin muhimman rassa wajibai na Allah cikin addinin muslunci mai karkata zuwa ga shiriya shi ne sallah, me ya sanar da kai mece ce sallah? Lallai saloli na wajibai na yau da gobe guda biyar tabbas su ne mafi falalar ayyuka addini da mafi soyuwarsu zuwa ga Allah tsarki ya tabbatar masa, ita sallar ita wasiyyar karshe ta dukkanin annabwa da waliyyai, ita ce tsayuwar muslunci da amudinsa, idan ta karbu a lahira cikin mizanin Allah to sauran ayyuka koma bayanta ma sun karbu, idan kuma akai wurgi da ita to ragowar ayyuka za ai wurgi da su, ita ce farko abin da za a fara dubawa daga aikin bil adama, idan ta inganta ta karbu to ba za duba sauran ayyukan ba, idan kuma bata inganta ba baa za a tsaya bata lokacin duba sauran ayyukansa ba, kamar yadda ya zo cikin riwaya daga manzon Allah (s.a.w) da tsatson sa tsarkaka da mafi alherin sahaban sa

Hakika ya zo cikin madaukakin hadisi:  

«مثل الصلاة كمثل النهر الجاري ، فكما أنّ من اغتسل فيه كلّ يوم خمس مرّات لم يبقَ في بدنه شيء من الدرن والأوساخ ، فكذلک كلّما صلّى صلاة فقد كفّر ما بينهما من الذنوب والمعاصي

Misalin sallah kamar misalin korama ce mai gudana, kamar yadda duk wanda ya yi wanka daga cikin wannan korama kowacce rana sau biyar babu wata datti da kazanta da zata wanzu cikin jikin sa, to haka al'amarin yake duk sanya ya yi wata to sallah hakika to an kankare masa abin da ya ke tsakankanin su daga zunubai da ayyukan sabo.[10]

Sannan ya isar maka cikin girmamar sallah kasantuwar ita ce mai banbance musulmi daga kafiri, kuma ita ce farkon abin da za a tambayi bawa ranar kiyama, idan ya zo da ita cikakka shikenan idan kuma bai zo da ita cikakka ba sai a wurga shi cikin wuta.[11]

قال رسول الله  9 :

«حافظوا على الصلوات الخمس ، فإنّ الله تبارک وتعالى إذا كان يوم القيامة يدعو بالعبد، فأوّل شيء يسأل عنه الصلاة ، فإن جاء بها تامّآ وإلّا زخ في النار».

2-Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ku kiyaye salloli biyar, lallai Allah albarku sun tabbata gare shi madaukaki idan ranar kiyama ta kasance zai sa a kira bawan sa, abu na farko da za fara tambayar sa ita ce sallah, idan bawa ya zo da ita cikakka shikenan idan kuma bai zo da ita cikakka ba sai a wurga shi cikin wuta.

ـ «أوّل ما ينظر في عمل العبد في يوم القيامة في صلاته ، فإن قبلت نظر في غيرها، وإن لم تقبل لم ينظر في عمله شيء».

3-Abu na farko da za a fara dubawa cikin aikin bawa a ranar kiyama shi ne cikin sallar sa, idan ta samu karbuwa sai aduba sauran ayyuka, idan kuma bata samu karbuwa ba, ba za ma a duba sauran ayyukan sa ba.

Hikimar sallah shi ne tsarkaka da tawali'u ga Allah matsarkaki sannan lallai ita sallah akida ce.

قال أمير المؤمنين عليّ  7 :

«عباد الله، إنّ أفضل ما توسّل به المتوسّلون إلى الله جلّ ذكره : الإيمان بالله وبرسله وما جاءت به من عند الله... وإقامة الصلاة فإنّها الملّة ».

4- Sarkin muminai (as) ya ce: (yaku bayin Allah lallai mafi falalar abin da masu tawassuli suka tsanantu da shi zuwa ga Allah ambaton sa ya girmama shi ne imani da Allah da manzannin sa da abin da suka zo da shi daga wurin Allah…da tsayar da sallah lallai ita sallah akida ce.

«فرض الله الصلاة تنزيهآ عن الكبر».

-Allah ya farlanta sallah domin tsarkake bayinsa daga girman kai5

وقال الإمام الباقر  7 :

«الصلاة تثبيت للإخلاص وتنزيه عن الكبر».

6- Imam Bakir (as) ya ce: sallah tana tabbatar da iklasi da tsarkakewa daga girman kai.

7 ـ عن الإمام الرضا  7 فيما كتب عن علّة الصلاة ، قال  :

«إنّها إقرار بالربوبيّة لله عزّ وجلّ ، وخلع الأنداد، وقيام بين يدي الجبّار جلّ جلاله بالذلّ والمسكنة والخضوع والاعتراف ، والطلب للإقالة من سالف الذنوب ، ووضع الوجه على الأرض كلّ يوم خمس مرّات إعظامآ لله عزّ وجلّ ، وأن يكون ذاكرآ غير ناسٍ ولا بطر، ويكون خاشعآ متذلّلا راغبآ طالبآ للزيادة في الدين والدنيا، مع ما فيه من الانزجار والمداومة على ذكر الله عزّ وجلّ بالليل والنهار، لئلّا ينسى العبد سيّده ومدبّره وخالقه فيبطر ويطغى ، ويكون في ذكره لربّه وقيامه بين يديه زاجرآ له عن المعاصي وماعآ من أنواع الفساد».

           7-An karbo daga Imam Rida (as) cikin abin da ya rubuta kan illa da dalilin sallah, ya ce: lallai ita sallah ikirari ce                                                                ubangijintakar Allah mai girma mabuwayi, da kwabe masa kishiyoyi, da tsayuwa girma mabuwayi, da kwabe masa kishiyoyi, da tsayuwa tsakankanin gaban mai tilastawa girmansa ya girmama cikin kankan da kai da talauci da mika wuya da furuci, da neman zobaita daga abin da ya gabata daga zunubai, da sanya fuska kan kasa a cikin kwacce sau biyar domin girmama Allah mai girma mabauwayi, sannan mutum ya kasance mai tunawa ba mai mantuwa ba, ba kuma mai Gadara ba, ya kasance mai kushu'i mai kaskantar da kansa mai kwadayi mai neman kari ckin addini da duniya, tare da abin da ke cikinsa daga kwabuwa da kuma dawwamuwa kan tunawa da Allah mai girma mabuwayi dare da rana, don kada bawa ya manta da shugabansa mai tafiyar da shi mahaliccinsa da gudun kada ya zamanto yana Gadara da dagawa, ya kasance cikin tunawar sa ga ubangijin sa da tsayuwar sa gabansa yana mai tsawatuwa kan barin aikata ayyukan sabo da nau'ukan fasadi.[1] Bakara:2-3

[2] Bakara:43.83.110.nisa'i:77. 103 da kuma wasu surorin

[3] Daha:132

[4] Ankabut:45

[5] Lukman:17

[6] Bkara:238

[7] Nisa'i:103

[8] Maryam:55

[9] Ibrahim:5

[10] Biharul-anwar: m 82 sh 220

[11] Biharul anwar: m 82 sh 201 daga jami'ul Akbar