فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Cikin falalar mai sallah

 

ـ يقول أمير المؤمنين عليّ  7 :

«لو يعلم المصلّي ما يغشاه من جلال الله ما سرّه أن يرفع رأسه من سجوده ».

8-Da mai sallah ya san abin da ke lullube shi daga girman Allah da lallai ba zai faranta masa ya dago kansa daga sujjada ba.

ـ «إنّ الإنسان إذا كان في الصلاة فإنّ جسده وثيابه وكلّ شيء حوله يسبّح ».

9-Lallai mutum lokacin da yake shagaltuwa da yin sallah lallai jikin sa da tufafin sa da dukkanin abin da yake kewaye da shi ya na yin tasbihi.

«إذا قام الرجل إلى الصلاة أقبل إبليس ينظر إليه حسدآ لما يرى من رحمة الله التي تغشاه ».

10-Idan mutum ya tashi zuwa ga sallah sai iblis yana dinga fuskantowa yana kallon sa saboda hassada daga abin da yake gani daga rahamar Allah wacce ke lullube wannan mutumin

«وما دمت في الصلاة فإنّک تقرع باب الملک الجبّار، ومن يكثر قرع باب الملک يفتح له ».

11-Matukar kana cikin shagaltuwa da yin sallah lallai kai kana kwankwasa kofar sarki mai tilastawa, duk wanda ya yawaita kwankwasar kofar sarki za a bude masa.

ـ عن رسول الله  9 :

«ما من مؤمن يقوم إلى الصلاة إلّا تناثر عليه البرّ ما بينه وبين العرش ، ووكّل به ملک ينادي : يا ابن آدم ، لو تعلم ما لک في صلاتک ومن تناجي ما سئمت وما التفت » .

12-Daga manzon Allah (s.a.w) : babu wani daga mumini da zai tashi zuwa ga sallah face alheri ya daidaitu ya zuba kansa tsakaninsa da al'arshi, sannan an wakilta wani mala'ika yana shela yan cewa: ya bil adama, da kasan abin da ke gareka cikin sallarka da kuma daga munajati da baka kosa ba da baka waiwayo ba.[1]

Sallah tana kaiwa ga girmama da kololuwarta daga muhimmanci mai tukewa shi ne cewa abin da shugabanmu jagoranmu Sadik (as) yayi wasicci da shi:

ـ فعن أبي بصير، قال : دخلت على اُمّ حميدة اُعزّيها بأبي عبد الله  7، فبكت وبكيت لبكائها، قالت : يا أبا محمّد، لو رأيت أبا عبد الله عند الموت لرأيت عجبآ، فتح عينه ثمّ قال  :

«اجمعوا كلّ من بيني وبينه قرابة ».

قالت : فما تركنا أحدآ إلّا جمعناه ، فنظر إليهم ثمّ قال  :

«إنّ شفاعتنا لا تنال مستخفّآ بالصلاة ».

13-Daga Abu Basir ya ce: na shiga wajen ummu hamida ina yi mata ta'aziyya da Abu Abdullah (as) sai ta fashe da kuka ni ma na fashe da kuka sakamakon kukanta, sai tace: ya Abu Muhammad da ka ga Abu Abdullah lokacin da zai bar duniya da kaga abin ban mamaki, ya bude idon sa sannan ya ce: ku tattaro dukkanin dangina.

Sai tace: bamu bar wani wanda yake da dangantaka da ba shi face mun tattaro su, sai ya kalle su sannan ya ce: lallai cetona baya hadowa da mai sako-sako da sallah.

Ceton Ahlil-baiti bai samun mai wasa da sallah to kaka kuma ga wanda yake barinta baki daya?!

Kamar yadda ya zo cikin ingantaccen hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (as)

«ما أعلم شيئآ بعد المعرفة أفضل من هذه الصلاة ، ألا ترى إلى العبد الصالح عيسى بن مريم قال : وأوصاني بالصلاة والزكاة ما دمت حيّآ» .

14-Ni ban san wani mafi falala ba bayan ma'arifa daga sallah, ashe baka ga bawa nagari Isa dan Maryamu ya ce: ya yi mini wasiyya da sallah da zakka matukar ina raye.[2]

Hakika riwayoyi masu tarin yawa sun kwarara cikin kwadaitarwa kan kiyaye sallah cikin farkon lokacin shigarta, da kuma cewa lallai ma sakaci da ita ana hukunci kansa da mai barin sallah.

16-Hakika manzon Allah (s.aw.) mai tseratar duniyar mutane daga jahilci zuwa ga kwazazzabon ilimi da fari ciki da ni'ima ya ce:

«ليس منّي من استخفّ بصلاته ، لا يرد على الحوض ، لا والله».

Ba ya tare da ni duk wanda yake sakaci da sallah, ba kuma zai gangaro tafkina ba wallahi.

ـ وقال  :

«لا تضيّعوا صلاتكم ، فإنّ من ضيّع صلاته حُشر مع قارون وفرعون وهامان ، وكان حقّآ على الله أن يدخله النار مع المنافقين ، فالويل لمن لم يحافظ على صلاته »

16-A wani wurin ya ce: kada ku tozartar da sallarku, lallai duk wanda ya tozarta sallah za a tashe shi tare da karuna da fir'auna da hamana, sannan ya kasance wajibi kan Allah ya shigar da shi wuta tare da munafukai, azaba ga wanda bai kiyaye sallar sa.[3]

كما ورد في الخبر الشريف : بينما رسول الله  9 جالس في المسجد إذ دخل رجل فقام فصلّى فلم يتمّ ركوعه ولا سجوده ، فقال  7 :

«نقر كنقر الغراب ، لئن مات هذا وهكذا صلاته ليموتنّ على غير ديني ».

وبالجملة ، فما ورد من الآيات الشريفة أكثر من أن يحصى ، تدلّ بوضوح وترشدنا إلى عظمة الصلاة في الإسلام ، ولله درّ صاحب الدرّة ،
17-kamar yadda ya zo cikin madaukakin hadisi; yayin da manzon Allah (s.a.w) yake zaune cikin masallaci sai kwatsam wani mutum ya shigo ya mike ya yi sallah bai cika ruku'un sa ba, bai cika sujjadar sa ba, sai manzon Allah (s.a.w) ya ce: ya yi caccake kamar caccaken hankaka, lallai idan wannan mutumin yam utu alhalin sallarsa tana irin wannan yanayi lallai zai mutu ba a kan addinina ba[4]

A jumlace dai abin da ya zo daga ayoyi masu daraja ya wuce kidaicewa, suna nuni a bayyane suna kuma shiryar damu zuwa ga girmamar sallah cikin muslunci, mamakin basira da ilimin mawalaffin littafin durratu[5]yana cewa:

تنهى عن المنكرِ والفحشاء         أقصر فهذا منتهى الثناء

Ita sallah tana hani ga barin munkari da alfasha* mafi wannan shi ne magaryar tukewar yabo ga sallah.

Daga Sikatul Islam Shaik Dabarasi cikin tafsirin sa majma'ul bayan cikin fadin Allah madaukaki:

 (lallai sallah tana hani ga barin alfasha da munkari)

 sai ya ce: cikin wannan akwai shiryarwa zuwa ga cewa lallai yin sallah ludufi ne ga mukallafi cikin barin mummuna da ayyukan sabo wadanda hankali yake tabbatar da su da shari'a. lallai barin aikata mummuna yana kasancewa taufiki.

ـ وروي أنّ فتىً من الأنصار كان يصلّي الصلاة مع رسول الله  9 ويرتكب الفواحش ، فوصف ذلک لرسول الله  9 فقال  :

«إنّ صلاته تنهاه يومآ ما».

فلم يلبث أن تاب .

18-An rawaito cewa wani matashi daga Ansar ya kasance yana yin wata sallah tare da manzon Allah (s.a.w) sannan kuma tare da da haka ya aikata alfasha, sai aka baiwa manzon Allah (s.a.w) labari sai ya ce: lallai sallar da yake yi wata rana zata hane shi aikata abin da yake aikatawa.

Aiko bai dau dogon lokaci ba sai gashi ya tuba[6]

ـ روى أصحابنا عن أبي عبد الله  7، قال  :

«من أحبّ أن يعلم أقُبِلَت صلاته أم لم تُقبل ؟ فلينظر هل منعته صلاته عن الفحشاء والمنكر؟ فبقدر ما منعته قبلت منه ».

19-An rawaito daga sahabbanmu daga Abu Abdullah (as) ya ce: duk wanda yake son ya san cewa shin sallar sa ta karbu ko bata karbu ba to ya duba ya gani shin ta hana shi aikata alfasha da munkari? gwargwadon yadda ta hana shi aikata alfasha ta karbu.

ـ قال رسول الله  9 :

«من لم تنهه صلاته عن الفحشاء والمنكر، لم يزدد من الله إلّا بُعدآ».

20-Manzon Allah (s.a.w) ya ce: duk wanda sallar sa bata hana shi aikata alfasha da munkari ba babu da abin da zai karu daga Allah face nisanta.

«لا صلاة لمن لم يطع الصلاة ، وطاعة الصلاة أن تنهى عن الفحشاء والمنكر».

21-babu sallah ga wanda bai yi da'a ga sallah ba, da'a ga sallah shi ne ta zamanto ta hani ga barin alfasha da munkari.

وقال في رجل يصلّي بالنهار ويسرق بالليل  :

«إنّ صلاته لتردعه ».

فالويل كلّ الويل لمن تركها متعمّدآ، فإنّما يُسئل أهل النار: (مَا سَلَـكَـكُمْ فِي سَقَرَقَالُوا لَمْ نَکُ مِنَ المُصَلِّينَ ).

22- cikin wani mutum da yake sallah yake kuma yin sata da daddare ance:

Lallai sallar sa tabbas zata hane shi sata.

Azaba dukkanin azaba ga wanda ga wanda ya bar yin sallah da gangan, lallai kadai za a tambayi `yan wuta:

 (me ya shigar da ku cikin wuta sakar* sai sukace bamu kasance daga masu yin sallah ba)[7]

ويقول رسول الله  9 :

«في جهنّم وادٍ، فيه حيّات ، كلّ حيّة ثخن رقبة البعير، تلسع تارک الصلاة ، فيغلي سمّها جسمه سبعين سنة ، ثمّ يتهرّى لحمه ».

23-manzon Allah (s.a.w) yana cewa: cikin jahannama akwai wani kwazazzabo cikin sa akwai macizai, kowanne maciji kwaya daya yakai kaurin wuyan rakumi suna saran mai barin sallah, sai gubar saran su ta tafasa cikin jikinsa tsawon shekaru saba'in sannan naman sa ya dahu.

ـ وقال  9 :

«ما بين المسلم والكافر إلّا أن يترک الصلاة الفريضة متعمّدآ أو يتهاون بها فلا يصلّيها».

24- tsira da amincin Allah ya kara tabbata gare shi da iyalan sa ya ce: babu abin da yake tsakanin musulmi da kafiri face barin sallar farilla da ganganci ko kuma ya dinga yin sakaci da ita ba ya sallatarta.[8]

وقال  9 :

«لا ينال شفاعتي غدآ من أخّر المفروضة بعد وقتها».

25-a wani wajen ya ce: bazai samu cetona ba gobe wanda ya jinkirta sallar farilla zuwa bayan lokacinta.

Ina hadaku da Allah ina hadaku da Allah cikin sallolinku, hakika jagororin addini sun himmatu kanta magaryar himmatuwa, kada ka bari sallah cikin kowanne hali kai hatta yayin da kake neman nutsewa cikin tafki, da mai nutsewa cikin ruwa zai ji muryar mai kiran sallah da lallai shi zai iya yin sallar sa ko da fadin kabbarar harama ne.[9]

ـ عن مولانا أبي الحسن العسكري  ، قال  :

«كلّم الله عزّ وجلّ موسى بن عمران ، قال موسى : إلهي ، ما جزاء من صلّى الصلوات لوقتها؟ قال : أعطيته سؤله واُبيحه جنّتي ».

26-daga shugabanmu Abu Hassan Askari, amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: (Allah mai girma mabuwayi ya yi magana da Musa bn Imran, sai Musa ya ce: ya ubangijina, mene ne sakamakon wanda ya sauke salloli a kan lokacin su? sai Allah ya ce: zan bashi abin da ya tambayeni zan kuma halasta masa aljannata.

Babu alheri cikin duk wani aiki da ya gabata kan sallah kamar yadda ya zo cikin hadisi, wajibi kanmu mu cewa ayyukanmu mufa wajibi kanmu mu fara sauke sallah gabanin komai, bawai mu cewa sallah ba muna da wani aiki a gabanmu gabaninta baya zamanto mun jinkirta ta zuwa karshen lokacin ayyukanmu, kamar yadda wasu keyi cikin ban takaici mai tsananin gaske.

عن الصادق ، عن آبائه  :، قال  :

«قال النبيّ  9: ما من صلاة يحضر وقتها إلّا نادى ملک بين يدي الناس ]أيّها الناس [ قوموا إلى نيرانكم التي أوقدتموها على ظهوركم فاطفئوها بصلاتكم » . والمراد من النيران الذنوب ، وإنّما شُبّهت بالنار إذ تهلک من وقع فيها.

27- daga Sadik (as) daga babannin sa, ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya ce: babu wata sallah da lokacinta zai halarto face mala'ika a gaban mutane ya yi shela yana mai cewa yaku mutane ku tashi zuwa ga wutarku wacce kuka rurata kan bayanku to ku kasheta da sallolinku)[10] abin da ake nufi da wuta a nan shi ne zunubai kadai dai an kamanta zunubai da wuta domin suna halakar da duk wanda ya fada cikin su.

ـ وعن أمير المؤمنين  7 أنّه قال في كلام يوصي أصحابه  :

«تعاهدوا الصلاة وحافظوا عليها واستكثروا منها وتقرّبوا بها، فإنّها كانت على المؤمنين كتابآ موقوتآ».

28-Daga sarkin muminai (as) lallai shi cikin wata magana da yakewa sahabban sa wasiyya ya ce: (kuyi alkawari da sallah cikin junanku ku kiyaye ta ku yawaita daga gareta ku nemi kusancin Allah da ita, lallai ita sallah ta kasance wajibi mai kayyadadden lokaci.[11]

Ita sallah tana daga shari'o'in addini ita ce minhajin annabawa da kusancin dukkanin mumini mai tsoran Allah.

ـ قال رسول الله  9 :

«الصلاة من شرايع الدين ، وفيها مرضاة الربّ عزّ وجلّ ، وهي منهاج الأنبياء».

29- manzon Allah (s.a.w) ya ce: sallah tana daga cikin shari'o'in addini, cikinta yardar Allah mai girma mabuwayi take, ita ce minhajin annabawa.[12]

ـ وقال  9 :

«ليكن أكثر همّک الصلاة ، فإنّها رأس الإسلام بعد الإقرار بالدين ».

30- amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: ya zamanto abin da ka himmatuwa kansa shi ne sallah, lallai ita ce jagaban muslunci bayan ikirari da addini.[13]

 ـ وقال  9 :

«لكلّ شيء وجه ، ووجه دينكم الصلاة » .

31-Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: (kowanne abu yanada fuska. fuskar addininku sallah).[14]

وقال أمير المؤمنين عليّ  7 :

«الصلاة حصن من سطوات الشيطان ».

32-Sarkin muminai Ali (as) ya ce: (sallah ita garkuwar ce daga hare-haren shaidan)

وقال  7 :

«الصلاة تستنزل الرحمة ، الصلاة ميزان ، فمن وفّى استوفى ».

33- amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce: sallah na sauko da rahama, sallah mizani ce, dukkanin wanda ya cikata za a cika masa.

ـ قال رسول الله  9 :

«جعل الله جلّ ثناؤه قرّة عيني في الصلاة ، وحبّب إليّ الصلاة كما حبّب إلى الجائع الطعام ، وإلى الظمآن الماء، وإنّ الجائع إذا أكل شبع ، وإنّ الظمآن إذا شرب روي ، وأنا لا أشبع من الصلاة ».

34-manzon Allah (s.a.w) ya ce: (Allah yabon sa ya girmama ya sanya sanyin idona cikin sallah, ya soyar da sallah gareni kamar yadda aka soyantar da abinci ga mai jin yunwa, aka soyantar da ruwa ga mai jin kishirwa, lallai mai jin yunwa idan yaci abinci yana koshi, lallai mai jin kishi idan ya sha ruwa yana iya koshi, amma ni bana koshi daga sallah).[15]

ـ قال أمير المؤمنين عليّ  7 :

«كان رسول الله لا يؤثر على الصلاة عشاءً ولا غيره ، وكان إذا دخل وقتها كأنّه لا يعرف أهلا ولا حميمآ».

35-Sarkin muminai Ali (as) ya ce: (manzon Allah ya kasance baya fifita cin abinci farkon dare ko wanin sa kan yin sallah, ya kasance idan lokacin sallah ya shiga sai ka ganshi kamar san Ahalin sa ba ko wani masoyi.[16] 

وقال  7 :

«الصلاة قربان كلّ تقيّ».

«الصلاة أفضل القربتين ».

36-Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: (sallah kusancin dukkanin wani mai tsoran Allah) (sallah ita ce mafi falalar kusanci biyu).

Ina yi musu wasicci da sallah da kiyayeta, lallai ita ce mafi alherin aiki ita ce amudin addininku.

وعن الإمام الكاظم  7 :

«صلوات النوافل قربات كلّ مؤمن ».

37- daga imam Kazim (as): (sallolin nafila kusancin dukkanin mumini ne.

«مثل الصلاة مثل عمود الفسطاط ، إذا ثبت العمود نفعت الأطناب والأوتاد والغشاء، وإذا انكسر العمود لم ينفع طنب ولا وتد ولا غشاء».

38-manzon Allah (s.a.w) ya ce: (misalin sallah misalin amudin ginin hasumiyar fusdadu ne idan ya tabbatu sai igiyoyi da turaku da rufi su amfana, idan kuma ya karye ba zai amfanar da turakun ba da igiyoyi da rufin.[17]

«الصلاة عماد الدين ».

Sallah ita ce ginshikin addini.

ـ وقال  9 :

«إذا قمت إلى الصلاة وتوجّهت وقرأت اُمّ الكتاب وما تيسّر من السور، ثمّ ركعت فأتممت ركوعها وسجودها، وتشهّدت وسلّمت غفر لک كلّ ذنب فيما بينک وبين الصلاة التي قدّمتها إلى الصلاة المؤخّرة ».

39-amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce: idan ka tashi yin sallah ka nufeta ka karanta fatiha da abin da ya saukaka daga surori, sannan kayi ruku'u ka cika ruku'in da ka yi sujjada, ka yi zaman tahiya ka sallame Allah zai gafarta maka dukkanin zunubin da yake tsakaninka da sallar da ka gabatar har zuwa wacce zata zo daga bayanta.

وقال لأصحابه لمّا أخذ غصنآ من شجرة كانوا في ظلّه ، فنفضه فتساقط ورقه وأخبرهم عمّا صنع  

«إنّ العبد المسلم إذا قام إلى الصلاة تحاتت عنه خطاياه كما تحاتت ورق هذه الشجرة ».

40-amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya cewa sahabban sa lokacin da ya rike wani reshe cikin wata bishiya da suka kasance cikin inuwarta, sai ya girgiza reshen bishiyar sai ganyenta ya zubo kasa ya basu labarin abind aya aikata: (lallai bawa mumini idan ya yunkura yin sallah zunuban sa suna karkadewa kamar yadda ganyen wannan bishiya ya karkade.

وقال  9 :

«تحترقون ـأي بالذنوب ـ فإذا صلّيتم الفجر غسلتها، ثمّ تحترقون فإذا صلّيتم الظهر غسلتها، ثمّ تحترقون فإذا صلّيتم المغرب غسلتها، ثمّ تحترقون تحترقون فإذا صلّيتم العشاء غسلتها، ثمّ تنامون فلا يكتب عليكم حتّى تغتسلوا».

41- amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce: (kuna konuwa da aikata zunubai, sai idan ku kai sallar alfijir sai ta wanke su, idan kukai sallar azuhur sai ta wanke su, sannan kuka kara konuwa amma idan kukai sallar magariba sai ta wanke su, sannan kuka kara konuwa ku kara konuwa idan ku kai sallar isha'i sai ta wanke su, sannan kuka kwanta ba za a kara rubuta muku komai kanku har sai kun yi wanka.[18]

وقال  9 :

«سمعت مناديآ عند حضرة كلّ صلاة فيقول : يا بني آدم ، قوموا فأطفئوا عنكم ما أوقدتموه على أنفسكم ، فيقومون فيتطهّرون فتسقط خطاياهم من أعينهم ، ويضلّون فيغفر لهم ما بينهما...».

42-amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce: (naji mai shela yana shela lokacin halartowar kowacce sallah yan cewa: ya `yan adam,ku tashi ku kashewa kawunkanku abin da kuka rura a kan kawukanku, sai su tashi su tsarkaka laifukan su su karkade su zube daga idanuwan su, su bata a yafe musu abin da ke tsakankanin su.

ـ قال أمير المؤمنين عليّ  7 في وصيّته بالصلاة  :

«وإنّها لتحتّ الذنوب حتّ الورق ، وتطلقها إطلاق الريق ».

«الصلوات الخمس كفّارة لما بينهنّ ما اجتنبت من الكبائر، وهي التي قال الله: (إنَّ الحَسَنَاتِ يُذْهِبْنَ السَّيِّـئَاتِ ) ».

43- Sarkin muminai Ali (as) ya ce: cikin wasiyyar sa da sallah (lallai ita tana zubar da zunubai kamar zubar ganye, tana tofar da su tofarwar yawun baki).

Salloli biyar kaffara ne ga abin da ke tsakanin su matukar bawa ya kauracewa manyan laifuka, ita ce kanta Allah yake cewa: (lallai kyawawan ayyuka suna tafiyar da munana).[19][1] Biharul-anwar: m 82 sh 234

[2] Biharul-anwar: m 82 sh 225

[3] Biharul-anwar: m 82 sh 201

 

 

[5] Aldurratul najafiyya: ta sayyid mahadi baharul ulum taba'taba'i.

[6] Biharul anwar: m 82 sh 285

[7] Mudassir:42-43

[8] Ikabul a'amal:231

[9] Amali shaik dusi:281

[10] Amali saduk:297

[11] Biharul-anwar: m 82 sh 244. daga Nahjul balaga

[12] Kisal: m 3 sh 522

[13] Biharul-anwar: m 77 sh 127

[14] Da'a'imul islam: m 1 sh 133

[15] Makarimul akhlak: m 2 sh 366

[16] Tanbihul kawadir: m 2 sh 78

[17] Alkafi:  3 sh 263

[18] Biharul-anwar: m 82 sh 232

[19] Hudu:114