فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Azumi

 

Allah madaukaki matsarkaki cikin bayannannen littafin sa mai daraja ya ce:

 (يَا أيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ ) .

Yaku wadanda suka yi imani an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi kan wadanda suka gabaceku tsammaninku kuji tsoran Allah.[1]

Azumin watan Ramadan mai albarka yana daga cikin mafi muhimmancin wajibai a muslunci bayan sallah, kuma shi daya daga cikin rukunai biyar ne wadanda aka gina muslunci kansu, kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja daga shugabanmu Sadik (as)

«بني الإسلام على خمس دعائم ، على الصلاة ، والزكاة ، والصوم ، والحجّ ، وولاية أمير المؤمنين والأئمة من ولده ، وما نودي بمثل ما نودي بالولاية » .

1-an gina muslunci kan ginshikai guda biyar, kan sallah, da zakka, da azumi, da hajji, da wilayar sarkin muminai da imamai daga `ya`yansa, sannan ba ai kira ba da misalin abin da kai kira kan wilaya.[2]

A cikin shari'ar muslunci mabayyaniya ana la'akari da wajabcin azumin watan ramadana daga cikin larurar addini, duk wanda yayi inkarinsa yayi tawaye da tsaurin kai zai kasance kafiri, kamar yadda da zai bayyanar da cin abinci da ranar tsaka cikin garuruwan muslunci to da za ai masa ta'aziri da haddi, idan kuma kwata-kwata ya yi inkarin azumin to shi murtaddi ne ya yi ridda ko dai murtaddi milli ko fidiri kowanne daga cikin su yana da kebantaccen hukuncin a shari'ar muslunci.

Shi azumin watan ramadana reshe ne na biyu daga rassan adini, shi reshe na biyu daga rassan bishiyar muslunci mai albarka, wajibi ne kan dukkanin musulmi kamili baligi mai hankali da lafiya jiki ya azumci azumin watan Ramadan, bawai kadai kan musulmi a ka farlanta azumi ba kadai, bari dai da nassin kur'ani mai girma hakika Allah ya farlanta shi ga wadanda suka gabace mu, sai dai cewa hakika ya gangaro daga hadisi mai daraja:   

ـ عن الإمام الصادق  7 :

«إنّ شهر رمضان لم يفرض الله صيامه على أحد من الاُمم قبلنا».

فقلت له : فقول الله عزّ وجلّ (يَا أيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ ...) ؟! قال  :

«إنّما فرض الله صيام شهر رمضان على الأنبياء دون الاُمم ، ففضّل الله به هذه الاُمّة ، وجعل صيامه فرضآ على رسول الله  9 وعلى اُمّته ».

2- daga Imam sadik (as) lallai watan Ramadan Allah bai farlanta azumin sa ba kan al'ummun da suka gabacemu ba. Sai na ce masa: me zaka ce kan fadin Allah mai girma mabuwayi (yaku wadanda suka yi imani an farlanta muku….)? sai ya ce: kadai dai Allah ya farlanta shi kan annabawa ne kadai koma bayan al'ummu, sai Allah ya fifita wannan al'umma da shi, ya sanya azumin sa farilla kan manzon Allah (s.a.w) da kan al'ummarsa

ـ وعن مولانا الإمام زين العابدين  7 من دعائه في وداع شهر رمضان  :

«ثمّ آثرتنا به على سائر الاُمم ، واصطفيتنا بفضله دون أهل الملل ، فصمنا بأمرک نهاره ، وقمنا بعونک ليله ...».

 3- daga shugabanmu imam Zainul Abidin (as) daga cikin addu'ar sa ta bankwana da watan Ramadan: (sannan ka fifita mu da shi kan sauran al'ummu, ka zabemu da falalar sa koma bayan ahlin akidu, sai cikin umarninka muka azumci yinin sa, cikin taimakonka muka raya daren sa)[1] Bakara:183

[2] Biharul-anwar: m 93