فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Zakka

 

 

 

Allah madaukakin sarki cikin littafin sa mabayanni yana cewa:

 

 (فَأقِيمُوا الصَّلاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ ).

Ku tsayar da sallah ku bada zakka.[1]

Matsarkaki ya ce:

 (وَوَيْلٌ لِلْمُشْرِكِينَالَّذِينَ لا يُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُمْ بِالآخِرَةِ هُمْ كَافِرُونَ)

Azaba ga mushrikai* wadanda basa bada zakka sannan su gameda lahira suna kafircewa.[2]

 (فَإنْ تَابُوا وَأقَامُوا الصَّلاةَ وَآتَوْا الزَّكَاةَ ).

Idan suka tuba suka tsayar da sallah suka bada zakka.[3]

Mai girma madaukaki ya ce:

 (وَالَّذِينَ يَكْنِزُونَ الذَّهَبَ وَالفِضَّةَ وَلا يُنفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ اللهِ فَبَشِّرْهُمْ بِعَذَابٍ ألِيمٍيَوْمَ يُحْمَى عَلَيْهَا فِي نَارِ جَهَنَّمَ فَتُكْوَى بِهَا جِبَاهُهُمْ وَجُنُوبُهُمْ وَظُهُورُهُمْ هَذَا مَا كَنَزْتُمْ لأنفُسِكُمْ فَذُوقُوا مَا كُنتُمْ تَكْنِزُونَ)

Wadanda suke taskace zinariya da azurfa basa ciyar da su cikin tafarkin Allah ka yi musu bushara da azaba mai radadi* ranar da za a gasu a kan su cikin wuta sai fusaken su suyi lallai da bayayyakin su wannan ne abin da kuka taskacewa kawukanku ku dandani abin da kuka kasance kuna taskacewa.[4]

(خُذْ مِنْ أمْوَالِهِمْ صَدَقَةً تُطَهِّرُهُمْ وَتُزَكِّيهِمْ بِهَا وَصَلِّ عَلَيْهِمْ إنَّ صَلاتَکَ سَكَنٌ لَهُمْ وَاللهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Daga dukiyoyin su ka ciri sadaka zaka tsarkake su da tsaftacesu da ita ka yi musu addu’a lallai addu’arka nutsuwa ce gare su Allah mai ji ne mai gani.[5]

Bai buya ba ga ma'abota hankula, cewa banbanci bayi cikin wadata da talauci kadai ya kasance bisa hikimar ubangiji, daga cikin sirrikan Allah cikin halittunsa, lallai Allah matsarkaki ya sanya talauci da wadata tsakankanin mutane domin saukaka al'amura da tafiyar da maslahohin su da motsar da tayar tafiyar da al'umma cikin tsarin tattalin arziki, kadai dai Allah ya sanya talauci da wadata domin jarraba bayinsa don ya san wane ne cikinsu yafi kyawun aiki da tsarkakar aiki.

Hakika Allah mai girma mabuwayi ya farlanta wani kaso ga talaka daga dukiyar mawadaci da zai ishe sh, kamar yadda yayi alkawarin gwaggwaban lada ga mawadaci bisa bada wannan kaso ga talaka, haka yayi alkawarin azaba mai radadi kansa idan ya hana talaka ya haramta masa wannan kaso da Allah ya farlanta masa cikin dukiyarsa, sai Allah ya sanya talakawa iyalansa ya kuma sanya mawadata wakilansa.

Zakka cikin addinin muslunci mai karkata ga shiriya daga wajibai take, kadai dai Allah matsarkaki ya shar'anta zakka domn tsayar da adalci cikin al'umma da zamantakewa, domin mutane su tashi kan aminci da nutsuwa cikin birnin mai daraja da falala.

Zakka a luggance tana da ma'anar habbaka da karuwa amma cikin isdilahin shari'a shi ne karbar wani kaso daga dukiya mawadaci, kadai dai an kirayeta da sunan zakka domin kulawa da habbakuwar dukiya da tumbatsarta da karuwarta da bata kariya mai makon tauyeta, zakka tana daga habbakar shuka idan ta girma, lallai cire zakka yana kawo albarka cikin dukiya yana kuma jawowa nafsu falala da karamci da kyauta, kokuma dai zakka ta zo da ma'anar tsarkakewa, lallai ita tana tsarkake dukiya daga dukkanin kazanta da nafsu da rowa.

Azaba ga dukkanin mai hana zakka, lallai shi zai ciyar da fiye kason da ya hana daga zakka cikin sabo da sabawa mahaliccinsa mai azurta shi, wani lokacin ma azzalumai kan salladuwa kansa, kamar yadda yana iya fuskantar sata da kwace da wawashe dukiyar tasa, kamar yadda tarihi ke shaida haka.

Ya isar maka cikin muhimmancin azakka da girmanta shene kasantuwar cudanyata da sallah cikin ayoyin masu daraja daga fadin sa madaukaki:  

 (وَكَانَ يَأمُرُ أهْلَهُ بِالصَّلاةِ وَالزَّكَاةِ وَكَانَ عِنْدَ رَبِّهِ مَرْضِيّآ) .

Ya kasance yana umartar iyalinsa da sallah da zakka ya kasance wurin ubangijin sa yardajje.[6]

(الَّذِينَ يُـقِيمُونَ الصَّلاةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُمْ بِالآخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ ) .

Wadanda suke tsayar da sallah suke bada zakka alhalin su dangane da lahira masu tabbatarwa ne.[7]

(وَمَا اُمِرُوا إلاَّ لِـيَـعْـبُدُوا اللهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُـنَـفَاءَ وَيُـقِـيمُوا الصَّلاةَ وَيُـؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِکَ دِينُ القَـيِّمَةِ ) .

Ba a umarce su face su bautawa Allah suna masu tsarkake niyya gare shi addini suna masu karkata ga shiriya suna tsayar da sallah da bada zakka wadancananka addini ne mai kima.[8]

Mu tsaya kan girmamar zakka da tasirinta mai isarwa cikin jama'a karkashin fagen sarrafata zuwa ga wanda zata kai gare shi daga wadanda suka cancanta, hakan ya kasance cikin fadinsa madaukaki:

(إنَّمَا الصَّدَقَاتُ لِلْفُقَرَاءِ وَالمَسَاكِينِ وَالعَامِلِينَ عَلَيْهَا وَالمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمْ وَفِي الرِّقَابِ وَالغَارِمِينَ وَفِي سَبِيلِ اللهِ وَآبْنِ السَّبِيلِ فَرِيضَةً مِنَ اللهِ وَاللهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ ) .

Kadai dai zakka tana ga talaka da matalauta da masu aiki kanta da wadanda ake janyo zukatan su da cikin yantar da wuya da masu basuka da cikin tafarkin Allah da dan kan hanya farilla ce daga Allah kuma Allah masani mai hikima.[9]

 

ـ وعن مولانا أبي عبد الله الصادق  7، في حديث ، قال 

«إنّ الله عزّ وجلّ فرض للفقراء في مال الأغنياء ما يسعهم ، ولو علم أنّ ذلک لا يسعهم لزادهم ، إنّهم لم يؤتوا من قبل فريضة الله عزّ وجلّ ، ولكن اُوتوا من منع

من منعهم حقّهم لأنّما فرض الله لهم ، ولو أنّ الناس أدّوا حقوقهم لكانوا عايشين بخير» .

1-daga shugabanmu Abu Abdullah Sadik (as) cikin wani hadisi ya ce: (lallai Allah mai girma mabuwayi ya farlanta ga talakawa wasu kudade daga dukiyoyin mawadata da za su ishe su, da ya san cewa hakan ba zai ishe su ba da ya kara musu, lallai su ba a basu daga farilla Allah mai girma da daukaka ba, sai dai cewa an basu daga hanawa daga wanda ya hana su hakkinsu, da ace mutane suna sauke hakkokinsu da sun rayu cikin alheri).[10]

 

وعنه أيضآ  ، قال  :

«إنّما وضعت الزكاة اختبارآ للأغنياء ومعونةً للفقراء، ولو أنّ الناس أدّوا زكاة أموالهم ما بقي مسلم فقيرآ محتاجآ، ولاستغنى بما فرض الله له ، وإنّ الناس ما افتقروا ولا احتاجوا ولا جاعوا ولا عروا إلّا بذنوب الأغنياء، وحقيق على الله تبارک وتعالى أن يمنع رحمته ممّن منع حقّ الله في ماله ، وأقسم بالذي خلق الخلق وبسط الرزق ، أنّه ما ضاع مال في برّ ولا بحر إلّا بترک الزكاة ».

2-daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce:( kadai dai an sanya zakka ne domin jarraba mawadata da jarraba talakawa, da ace mutane sun bada zakkar dukiyoyinsu da babu wani musulmi talaka mabukaci da zai ragu, da talaka ya wadatu da barin abin da Allah ya farlanta saboda shi, lallai mutane basu talautu ba da basu bukatu ba da basu yunwatu bada basu tsaraitu ba face sakamakon zunuban mawadata, wajibi kan Allah ya hana rahamar sa daga wanda ya hana su ka ya ki bada hakkin Allah cikin dukiyar sa.ina rantsuwa da wanda ya halicce halittu ya shimfida arziki lallai dukiya ba ta taba tozarta ba cikin tafki da kan kasa face da kin bada zakka)[11]  

ـ وعن معمر بن يحيى ، أنّه سمع أبا جعفر   يقول  :

«لا يسأل الله عبدآ عن صلاة بعد الفريضة ، ولا عن صدقة بعد الزكاة ».

3- daga mu'ammar bn Yahaya lallai shi ya ji Abu Jafar (as) yana cewa: (Allah ba ya tambayar bawa kan sallah bayan ta farilla, hakama ba ya tambayar sa sadaka bayan ta zakka.

ـ وفي حديث نبوي ، قال  9 :

«داووا مرضاكم بالصدقة ، وحصّنوا أموالكم بالزكاة ».

4-cikin hadisin annabi (s.a.w) ya ce: (ku yiwa marasa lafiyarku magani da sadaka, ku katange dukiyoyinku da zakka)

وقال  :

«ملعون ملعون مالٌ لا يزكّى ».

5-amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce: (tsinanniya ce tsinanniya ce dukiyar da ba a cire mata zakka).

وعن أبي الحسن الرضا  7 :

«وإذا حبست الزكاة ماتت المواشي ».

6-daga Abu Hassan Rida (as) (idan aka rike zakka dabbobi sai su mutu)

وعن أبي عبد الله  7 :

«إنّ الزكاة ليس يحمد بها صاحبها، إنّما هو شيء ظاهر، إنّما حقن الله بها دمه وسمّي بها مسلمآ».

7-daga Abu Abdullah (as) (lallai zakka ba a yabawa ma'abocinta, kadai wani abu ne na zahiri, kadai dai Allah ya kare jininsa da ita an kuma kiraye shi musulmi da ita).

ـ وعنه  7 :

«من منع الزكاة فليمت إن شاء يهوديآ أو نصرانيآ» .

8-daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata gare shi:

(duk wanda ya hana zaka idan ya so to ya mutu bayahude ko banasare)[12]

وقال مولانا الرضا  7 :

«إنّ الله أمر بثلاثة مقرونة بها ثلاثة : أمر بالصلاة والزكاة ، فمن صلّى ولم يزکِّ لم تقبل صلاته »

9-shugabanmu Rida (as) ya ce:

(lallai Allah ya yi umarni da abubuwa guda uku da suke cudanye da wasu abubuwa guda uku: yayi umarni da sallah tare da zakka, duk wanda ya yi sallah bai cire zakka ba Allah bazai karbi sallar sa.[13]

Zakka tana kare dukiya da kiyayeta daga bacewa da lalacewa, kai kace ita zakka wani kamfani na(inshura) wanda ya dauki nauyin bada lamuni shi ne Allah matsarkaki madaukaki, kamar yadda zakka tana azurtar da al'ummar musulmai ta yadda wani cikin su ba zai wanzu talaka ba, kowanne mutum ya rayu cikin alheri da yalwa da nutsuwa da kwanciyar hankali, a wannan lokaci tanadi da karfi da nuna da suke boye cikin zukata sai su bayyana, al'umma su daga su samu habbaka da cigaba su dinga kammaluwa ta kowanne janibi da bangarori, wasu al'ummun ma daban su yi kwadayin koyi dasu, su zama ababen buga misali, kamar yadda ya kasance a farkon muslunci.

Kamar yadda dukiya ke tsarkaka da bada zakka idan ta kasance halal da kantar hannu da gumin goshi, domin shi mutum cikin kowanne aiki daga ayyukansa daga kasuwanci da sana'a da noma da makamantan haka yana bukatuwa zuwa ga `ya`yan wannan al'umma daga nau'insa domin bada ban su ba da tsarin rayuwa ya samu matsala ya susuce, a bayyane yake cewa al'ummar mutane sun bada taimako cikin masana'antunsu da abubuwan da suke samarwa, a wannan lokaci mutum zai fara jin cewa zuciyarsa na raye, himmarsa na waye, zai ga cewa lallai shi ya takaita cikin bada gudummawa cikin jama'arsa, ya zama dole ya tsarkake kansa da dukiyarsa ta hanyar maida ishsani da ishsani kyakkyawan aiki da kyakkyawa a wannan lokacin zai ga cewa zakka da sadaka amsa kiran badinin sa ne ta hanyar bada wani kaso daga dukiyar sa wanda shari'a mabayyaniya ta iyankace shi ta ayyana shi zuwa ga jama'arsa zuwa ga talakawa da matalauta da `ya`yan kan hanya cikin tafarkin Allah, daga gina masallatai da makarantu da gina gidaje ga talakawa da samar da gadoji da husainiyyoyi da asibitoci da makamantansu daga wuraren da ake sarrafa zakka.

Musulmai muminai basu fahimci wajabcin zakka da tsinkayar tasirinta mai girma mai amfani cikin jama'a, sai bayan da suka bada sadaka su ciyar daga abin da Allah ya azurta su suka sauke hakkoki ga ahalinsu, suka bada rance suka bada tallafi ga mabukata suka kama hannun raunana suka tseratar da su daga halakoki    

وقد قال رسول الله:

«من أدّى الزكاة إلى مستحقّها وأقام الصلاة على حدودها ولم يلحق بهما من الموبقات ما يبطلهما جاء يوم القيامة يغبطه كلّ من في تلک العرصات حتّى يرفعه نسيم الجنّة إلى غرفها وعاليها بحضرة من كان يواليه من محمّد وآله الطيّبين » .

10-hakika manzon Allah (s.a.w) ya ce:

(duk wanda ya sauke zakka zuwa ga wanda ya cancanceta ya tsayar da sallah akan haddodinta bai riskar da abubuwa masu halakarwa ba cikinta da suke bata ta ranar kiyama zai zo dukkanin wanda ke wannan fili zai dinga kwadayin sa har sai sanyayayyar iskar janna ya daukaka shi zuwa falonta da daukakarta da hallarar wanda ya kasance yana jebanta daga Muhammad da iyalansa tsarkaka.   

وقال   :

«آتوا الزكاة من أموالكم المستحقّين لها من الضعفاء، لا تبخسوهم ولا توكسوهم ولا تيمّموا الخبيث أن تعطوهم ، فإنّ من أعطى زكاته طيّبةً بها نفسه أعطاه الله بكلّ حبّةٍ منها قصرآ من فضّة وقصرآ من لؤلؤ وقصرآ من زبرجد وقصرآ من زمرّد وقصرآ من نور ربّ العالمين ، وإن قصّر في الزكاة قال الله تعالى  : يا عبدي ، أتبخلني أم تتّهمني أم تظنّ أنّي عاجز غير قادر على إثابتک ؟ سوف
يرد عليک يوم تكون أحوج المحتاجين إليها، إن أدّيتها كما اُمرت ، وسوف يرد عليک إن بخلت يوم تكون فيه أخسر الخاسرين ، قال : فسمع ذلک المسلمون فقالوا: سمعنا وأطعنا يا رسول الله

11- manzon Allah (s.a.w) ya ce: (ku bawa wadanda suka cancanta daga raunana zakka daga dukiyoyinku, kada ku tauye musu kada ku nakasta musu kada kuyi nufin mummuna da basu ita, lallai dukkanin wanda ya bada zakkarsa ransa na farin ciki da ita Allah zai bashi fada daga azurfa a fada daga lu'ulu'u daga dukkanin kwayar da ya bayar daga ita da fada daga zubarjad d afada daga hasken Allah uabangijin talikai, idan kuma ya takaita cikin zakka Allah madaukaki zai ce: ya bawana, shin kana yi mini rowa neko kuma kana tuhuma tane ko kana zargin cewa lallai ni na gaza banda ikon saka maka? Da sannau zata dawo gareka ranar da kake mafi bukatar mabukata zuwa gareta, idan ka sauketa kamar yadda aka bada umarni zata gangaro kanka, idan kuma kai rowa to wannan rana zaka kasance mafi hasara masu hasara, ya ce, sai musulmi suka ji haka sai suka ce: mun ji mun bi ya manzon Allah (s.a.w)   

وقال الصادق  7 :

«من منع قيراطآ من الزكاة فليس هو بمؤمن ولا مسلم ، ولا كرامة ».

12- Sadik (as) ya ce:

Duk wanda ya hana kiradi daga zakka shi ba mumini bane ba kuma musulmi bane, babu karamci)

وعن أمير المؤمنين عليّ  7 :

«إنّ رسول الله  9 قال : يدفع بالصدقة الدبيلة والغرق والحرق والهدم والجنون ، حتّى عدّ  9 سبعين نوعآ من البلاء».

13-daga sarkin muminai Ali (as) (lallai manzon Allah {s.a.w} yana tunkude ciwon maruru da nutsewa aruwa da gobara da rusau da hauka ta hanyar bada sadaka, har sai a kidaya nau'in bala'o'i saba'in da sadaka ke tunkudewa.

ـ وعن مولانا الصادق  7، قال  :

«ما من ذي مال ذهب أو فضّة يمنع زكاة ماله إلّا حبسه الله عزّ وجلّ يوم القيامة بقاع قرقر، وسلّط عليه شجاعآ (أي ثعبانآ) أقرع يريده وهو يحيد عنه ، فإذا رأى أنّه لا يتخلّص منه أمكنه من يده فيقضمها كما يقضم الفجل ، ثمّ يصير طوقآ في عنقه وذلک قوله عزّ وجلّ : (سَيُطَوَّقُونَ مَا بَخِلُوا بِهِ يَوْمَ القِيَامَةِ )[14] ،

وما من ذي مال إبل أو بقر أو غنم يمنع زكاة ماله إلّا حبسه الله عزّ وجلّ يوم القيامة بقاع قرقر، تطؤه كلّ ذات ظلف بظلفها وتنهشه كلّ ذات ناب بنابها، وما من ذي مال نخل أو كرم أو زرع يمنع زكاتها، إلّا طوّقه الله ربعة أرضه إلى سبع أرضين إلى يوم القيامة ».

14- daga shugabanmu Sadik (as) ya ce: (babu wani ma'abocin dukiya daga zinariya ko azurfa da zai ki bada zakka face Allah mai girma mabuwayi ranar kiyama ya tsare shi a bigiren kurkur, sannan ya sallada maciji kansa yana nufar sa yana kaucewa, idan ya ga cewa shi ba zai kubuta daga gare shi sai ya kamo shi da hannunsa sai keta shi kamar yadda yake keta tsirra, sannan sai ya zama sarka a wuyan sa hakan ya kasance cikin fadin Allah mai girma mabuwayi: {da sannu za ai musu sarka da abin da suka yi rowarsa ranar kiyama}, babu wani mai dukiya daga rakuma ko shanu ko busaye tumakai da zai hana zakkar dukiyarsa face Allah mai girma mabuwayi ya tsare shi ranar kiyama a bigiren kurkur, duk wata dabbba mai farata zata dinga taka shih aka duk wata dabba mai fika zata dinga saran sa da fikarta, babu wani ma'abcin dukiya daga bishiyoyin dabino da inibi da shuka da zai hana zakkarsu face Allah yayi masa sarka tsakankanin kasarsa zuwa kasan bakwai har zuwa tashin kiyama.

Akwai kuma wasu tarin riwayoyin daban da aka ambace su cikin litattafan hadisai cikin falalar mai bada zakka da ladanta da bayanin ukubar mai hanata.

Sannan kadai zakka tana wajaba cikin zinare da azurfa daga kudade da kuma rakumi da shanu da busaye tumakai daga dabbobi sai kuma gallatul arba'a daga kayan gona, da sharuddansu kebantattu kamar yadda aka ambace su cikin litattafan fikihu, ita dangane da zakkar kudade tana da mafi kebantar ma'ana, sannan cikin riwayarmu da litattafan Akhlak ana ambatar zakka da ma'ana game gari.

Na kwadaitar da kai wadannan riwayoyin masu daraja daga shugabanmu Sadik (as) kamar yadda suka zo cikin littafin Misbahul shari'a:  

ـ قال  7 :

«على كلّ جزء من أجزائک زكاة واجبة لله عزّ وجلّ ، بل على كلّ شعرة ، بل على كلّ لحظة ، فزكاة العين : النظر بالعبرة ، والغضّ عن الشهوات وما يضاهيها، وزكاة الاُذن : استماع العلم والحكمة والقرآن وفوائد الدين من الحكمة والموعظة والنصيحة وما فيه نجاتک بالإعراض عمّا هو ضدّه من الكذب والغيبة وأشباهها، وزكاة اللسان : النصح للمسلمين والتيقّظ للغافلين ، وكثرة التسبيح والذكر وغيره ، وزكاة اليد: البذل والعطاء والسخاء بما أنعم الله عليک به وتحريكها بكنبة العلوم ، ومنافع ينتفع بها المسلمون في طاعة الله تعالى والقبض عن الشرور، وزكاة الرجل : السعي في حقوق الله تعالى من زيارة الصالحين ، ومجالس الذكر وإصلاح الناس وصلة الرحم والجهاد وما فيه صلاح قلبک وسلامة دينک .

15- amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce:

(kan dukkanin wani yanki daga yankunan jikinka akwai zakka ta wajibi ga Allah mai girma mabuwayi: bari dai kan dukkanin silin gashi akwai zakka, bari dai kan dukkanin wata kiftawar fatar idaniya akwai zakka, zakkar ido shi ne yin kallo tare da fadaka, da kamewa daga barin sha'awe-sha'awe da duk abin da ya yi kama da su, zakkar kunne: sauraren ilimi da hikima da kur'ani da fa'idojin addini daga hikima da wa'azi da nasiha da dukkanin abin da cikinsa tsiranka yake da kauracewa kishiyar sa daga karya da gulma da makamantanta, zakkar harshe: yin nasiha ga musulmi da farkar da gafalallu, da yawan tasbihi da makamancinsa, zakkar hannu: shi ne bada kyauta daga abin da Allah ya ni'imtaka da shi da motsar da hannun da karagar ilimai, da alfanoni da masulmai za su amfanu da su cikin da'ar Allah madaukaki da damkewa daga barin aikata sharruka, zakkar kafa: sa'ayi da kaikawo cikin hakkokin Allah madaukaki daga ziyartar saliha, da zuw amajalisan ambaton Allah da gyaran mutane da sadar da zumunci da jihadi da dukkanin abin da cikinsa akwai gyaruwar zuciyarka da kubutar addininka.

Wannan shi ne abin da ake tsammanin zukata su fahimce shi, rayuka su yi aiki da shi, sai dai kuma babu masu kusantarsa face bayin Allah makusanta tsarkakakku fiye daga a kidaita su su ne jagororin sa shi ne taken su koma bayan su.[15]

Kadai dai ana sanin girman zakka karkashin ayoyi da riwayoyi masu daraja, ga Dukkanin wanda ya kasance yana zuciya ka gaza jin sa yana mai shaidawa.

Wajibi kan mai karatu ya zurfafa dubansa cikin su ya dandake cikin dukkanin wani hukunci na muslunci, ya kara dawo da ganinsa karo na biyu domin daga cikinsu ya fito da tabbatattun abubuwa masu haskaka da ilimai masu tattarowa, da za su amfanar da jama'ar sa musulmai su rayuwa cikin ni'ima da farin ciki da yalwa da imani, muslunci ya daukaka shi dama ba a daukaka a kansa.  

قال رسول الله   :

«الزكاة قنطرة الإسلام ، فمن أدّاها جاز القنطرة ، ومن منعها احتبس دونها، وهي تطفئ غضب الربّ ».

16- zakka gadar muslunci, duk wanda ya sauketa zai shallake wannan gada, duk wanda ya ki bayar da ita sai a tsare shi koma bayanta, ita zakka tana kashe fushin ubangiji.

قال الإمام الصادق  7 :

«ما فرض الله على هذه الاُمّة شيئآ أشدّ عليهم من الزكاة ، وما تهلک عامّتهم إلّا فيها».

 17-Imam Sadik (as) ya ce: (Allah bai farlanta komai kan wannan al'umma ba mafi tsanani daga zakka, babu abin da yake halaka galibinsu face cikin zakka)[1] Hajji:78

[2] Fussilat:6-7

[3] Tauba:5

[4] Tauba:34-35

[5] Tauba:103

[6] Maryam:55

[7] Namlu:3

[8] Bayyina:5

[9] Tuaba:60

[10] Wasa'ilul shi'a: m 4 sh 3 babi 1 h 2

[11]  Sh 44 m Wasa'ilul shi'a:

[12] Biharul-anwar: m 4 sh 16 m 14 sh 17

[13] Kisal: m 1 sh 70

[14] ()  آل عمران : 186.

[15] Biharul-anawar: m 93 sh 7

 

في حديث المعراج  :

«قال النبيّ: يا ربّ ، وما ميراث الصوم ؟ قال : الصوم يورث الحكمة ، والحكمة تورث المعرفة ، والمعرفة تورث اليقين ، فإذا استيقن العبد لا يبالي كيف أصبح بعسرٍ أم يسر».

51-ya zo cikin hadisin mi'iraji:

(annabi ya ce: ya ubangiji mene ne gadon azumi? Sai ya ce: azumi yana gadar da hikima, sannan ita hikima tana gadar da ma'arifa, ita kuma ma'arifa tana gadar da yakini, idan bawa ya samu yakini bai damuwa da yaya ya wayi gari shin cikin tsanani ne ko yalwa).

Shi azumi yana kashe sinadaran son rai da sha'awe-sha'awe na dabi'ar dabbantaka, sannan yana gadar da hikima da ma'arifa da yakini, sannan cikinsa akwai tsaftatar zuciya da tsarkakar gabbai da gina zahiri da badini, da godiya kan mai ni'imtawa da ihsani zuwa ga talakawa da karin kankan da kai da kushu'i da kuka da riki igiyar fakewa da Allah, da sababin raunana munan ayyuka da ninninka kyawawa.

Cikin azumi akwai fa'idoji da baza su kirgu ba, abin da muka kawo ya isarwa wanda yake da hankali ya kuma samu dacewa da aikata su, ya sanya kunne alhalin yana mai shaida.

Bai buya ba lallai cewa wajibi daga azumi shi ne azumin watan Ramadan mai albarkaga wadanda suke kasance daga mukallafaidaga maza da mata, sai dai cewa lallai shi yana kasancewa mustahabbi bisa tadawwu'I cikin wasu kwananin daban, musammam ma kwanaki kebanatattu daga ranakun Allah, kamar ranar sha takwas ga watan zul hijja ranar (gadir) da ranar ashirin da biyar ga watan rajab ranar (mab'as) da wasunsu.

 

Hakika hadisi ya zo daga manzon Allah (s.a.w) ya ce:

«من صام يومآ تطوّغآ فلو اُعطي ملء الأرض ذهبآ، ما وُفّي اجره دون يوم الحساب ».

52-daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata gare shi:

(duk wanda ya azumci wata rana nafila da za a bashi cikin duniya da zinariya da ba a cika masa ladansa ba, koma bayan ranar hisabi.

وعنه  9 :

«من صام يومآ تطوّعآ ابتغاء ثواب الله وجبت له المغفرة ».

52-(Duk wanda ya azumci wata rana don neman lada daga Allah gafara ta wajaba gare shi)

وعنه  9 :

«من صام يومآ تطوّعآ ابتغاء ثواب الله وجبت له المغفرة ».

عن أمير المؤمنين عليّ  :

«إنّ الله تبارک وتعالى أتمّ صلاة الفريضة بصلاة النافلة ، وأتمّ صيام الفريضة بصيام النافلة ».

54-daga sarkin muminai Ali (as) (lallai Allah albarku sun tabbatar masa madaukaki ya cika sallar farilla da sallar nafila, hakama ya cika sallar nafila da azumin nafila)

وعن الإمام الصادق  7 :

«إيّاكم والكسل ، إنّ ربّكم رحيم يشكر القليل ، إنّ الرجل ليصوم اليوم تطوّعآ يريد به وجه الله تعالى فيدخله الله به الجنّة».

55-daga Imam Sadik (as): na haneku kasala, lallai ubangijinku mai jin kai yana godewa kadan, lallai mutum yana azumtar yini don nafila yana nufin neman yardar Allah madaukaki da shi sai Allah ya shigar da shi aljanna da shi).

ـ وعن رسول الله  9 :

«من صام ثلاثة أيام من كلّ شهر، كان كمن صام الدهر، لأنّ الله عزّ وجلّ يقول : (مَنْ جَاءَ بِالحَسَنَةِ فَلَهُ عَشْرُ أمْثَالِهَا) ».

56- daga manzon Allah (s.a.w) :

(duk wanda ya azumci kwanaki uku a cikin kowanne wata, zai kasance kamar wanda ya azumci baki dayan zamani, saboda Allah mai girma mabuwayi yana cewa:{duk wanda ya zo da kyakkyawa guda to yana da goma misalinsa}).[1]

وعنه  9 :

«صوم ثلاثة أيام في كلّ شهر، ورمضان إلى رمضان ، صوم الدهر وإفطاره ».

57- daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata gare shi: azumtar kwanaki uku cikin kowanne wata tun daga Ramadan zuwa wani ramada din daidai yake da azumtar zamani da bude bakin sa)

وقال  9 :

«من سرّه أن يذهب كثير من وحر صدره فليصم شهر الصبر، وثلاثة أيام من كلّ شهر».

58-duk wanda ya faranta masa da ya tafiyar da yawancin kiyayyar da take kirjin sa to ya azumci watan hakuri, da kwanakin uku cikin kowanne wata

عن أمير المؤمنين عليّ  7 :

«صوم ثلاثة أيام من كلّ شهر، أربعاء بين خميسين ، وصوم شعبان ، يذهب بوساوس الصدر وبلابل القلب ».

59- daga Sarkin muminai Ali (as): (azumtar kwanaki uku cikin kowacce wata laraba da take tsakanin ranakun alhamis biyu, da azumtar watan sha'aban yana tafiyar da wasiwasin cikin kirji da bala'o'oin zuciya)

عن الإمام الصادق  7 :

«كان رسول الله  9 أوّل ما بُعث يصوم حتّى يقال : ما يفطر، ويفطر حتّى يقال : ما يصوم ، ثمّ ترک ذلک وصام يومآ وأفطر يومآ، وهو صوم داود، ثمّ ترک ذلک وفرّقها في كلّ عشرة أيام يومآ خميسين بينهما أربعاء، فقبض ، عليه وآله السلام ، وهو يعمل ذلک ».

60- daga Imam Sadik (as) (manzon Allah {s.a.w} ya kasance farkon lokacin da aka aiko shi yana azumi har sai aka ce masa ba ya yini ba tare da azumi a bakinsa ba, sannan yayi ta karyawa har sai da aka ce masa baya azumi, sannan ya bar haka sai ya dinga yin azumi yau gobe kuma ya karya, wannan shi ne azumin Dauda, sannan ya bar yin haka sai ya rarraba shi cikin dukkanin kwanaki goma sai ya azumci ranakun alhamis biyu da laraba daya tsakaninsu, har Allah ya karbi rayuwa shi yana aikata hakan)

Ya kai musulmi mai daraja, gareka manzon Allah abin koyi da kwaikwayo mai kyawu nagari…

Shin kayi aiki da sunnarsa mai albarka cikin azumi, ko da cikin shekara guda daya ne? kayi kokarin gwada hakan koda sau daya ne a shekara, lallai kai da sannu zaka albarkunsa da tasirinsa na zahiri da na badini da ruhi a kebance, kada ka bar aikatawa tsawon rayuwarka… Allah abin neman taimako.
[1] An'am:160