فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta

 

ورد عن الإمام الرضا  7 :

«علّة الزكاة من أجل قوت الفقراء، وتحصين أموال الأغنياء، لأنّ الله تعالى كلّف أهل الصحّة القيام بشأن أهل الزمانة من البلوى ، كما قال عزّ وجلّ : (لَتُبْلَوُنَّ فِي أمْوَالِكُمْ وَأنْفُسِكُمْ ) في أموال إخراج الزكاة وفي أنفسكم توطين النفس

على الصبر، مع ما في ذلک من أداء شكر نِعَم الله عزّ وجلّ ، والطمع في الزيادة ، مع ما فيه من الزيادة والرأفة والرحمة لأهل الضعف ، والعطف على أهل المسكنة ، والحثّ لهم على المساواة ، وتقوية الفقراء، والمعونة لهم على أمر الدين ، وهي عظة لأهلى الغنى وعبرة لهم ليستدلّوا على فقر الآخرة بهم ».

Ya zo daga shugabanmu imam Rida (as):

(illar zakka wajabta zakka ya kasance saboda abin da talakawa za su samu suci, da kuma katange dukiyoyin mawadata, saboda lallai shi Allah madaukaki ya kallafawa ma'abota lafiya lura da al'amuran mutanen da suke cikin ciwo mai daukar lokaci daga bala'o'i, kamar yadda ya fada cikin fadinsa: {lallai za a jarrabaku cikin dukiyoyinku da kawukanku}[1] cikin dukiyoyi da fitar da zakka cikin kawukanku da tilastawa rai yin hakuri tare da abin da ke cikin hakan daga sauke godiya ga ni'imomin Allah mai girma mabuwayi da kwadayi cikin neman karin ni'ima, tare da abin da ke tattare da ita daga kari da tausayi da jin kai ga raunana, da tausasawa matalauta, da kwadautarwa gare su zuwa ga daidaito, da karfafa talakawa da taimaka musu kan al'amarin addini hakan wa'azi ne da fadaka ga ma'abota wadata domin su dauki dalili kan talaucin lahira da su.

عن الإمام الصادق  7 :

«إنّ الله عزّ وجلّ فرض للفقراء في أموال الأغنياء ممّا يكتفون به ولو علم الله أنّ الذي فرض لهم لم يكفهم لزادهم ، فإنّما يؤتى الفقراء فيما اُوتوا من منع من منعهم حقوقهم لا من الفريضة ».

19- daga Imam Sadik (as) :

(lallai Allah mai girma ya farlanta talakawa wani abu daga dukiyar mawadata da za su isu da shi da Allah ya sanya cewa abin da ya farlata gare su ba zai ishe su ba da lallai ya kara musu, kadai dai ana baiwa talakawa daga hanin wanda ya hana su hakkokinsu bawai daga farilla ba)

وعن أمير المؤمنين عليّ  7، قال  :

«إنّ الله فرض على أغنياء الناس في أموالهم قدر الذي يسع فقراءهم ، فإن ضاع فقير أو اُجهد أو عُري ، فيما يمنع الغني ، وإنّ الله عزّ وجلّ محاسب الأغنياء في ذلک يوم القيامة ومعذّبهم عذابآ أليمآ».

20-daga Sarkin muminai Ali (as) ya ce: (lallai Allah ya farlanta masu wadatar cikin mutane cikin dukiyoyin su gwargwadon abin da zai wadatar da talakawa, idan wani talaka ya tozarta ko kuma ya wahaltu ko ya tsaraita daga abin da mawadaci ya hana to lallai Allah zai hukunta mawadata ranar kiyama cikin hakan zai kuma yi musu azaba mai radadi.

21 ـ وقال الإمام الكاظم  7 :

«إنّما وضعت الزكاة قوتآ للفقراء، وتوفيرآ لأموال الأغنياء».

21- Imam Kazim (as) ya ce: (kadai dai an sanya zakka abinci ga talakawa, da kuma cika dukiyoyin mawadata)

قال الإمام الباقر  7 :

«الزكاة تزيد في الرزق ».

22-Imam Bakir (as) ya ce: (zakka tana kara arziki)

قال رسول الله  9 :

«إذا أردت أن يثري الله مالک فزكّه ».

23-manzon Allah (s.a.w) ya ce: (idan kana son Allah ya habbaka dukiyarka to ka tsarkaketa da zakka)

قال الإمام الحسن  7 :

«ما نقصت زكاة من مالٍ قطّ ».

24-Imam Hassan (as) ya ce: (wata dukiya bata taba tawaya da zakka ba)

قال الإمام الصادق  7 :

«يا مفضّل ، قل لأصحابک يضعون الزكاة في أهلها، وإنّي ضامن لما ذهب لهم ».

25-Imam Sadik (as) ya ce: (ya mufaddal ka gayawa sahabbanka su ajiye zakka cikin ahalinta, lallai ni ina lamini abin da ya tafi daga gare su)

قال الإماما الباقر  ، في قوله تعالى : (فَأمَّا مَنْ أعْطَى وَآتَّـقَى5وَصَدَّقَ بِالحُسْنَى: وإنّ الله يعطي بالواحدة عشرة إلى مائة ألف فما زاد،

(فَسَنُـيَسِّرُهُ لِلْيُسْرَى ): لا يريد شيئآ من الخير إلّا يسّره الله له .

26-Imam Bakir (as) ya ce: cikin fadin Allah madaukaki: {amma wanda ya bayar yaji tsoran Allah*ya gasgata kyakkyawar kalma},[2] lallai Allah cikin kowacce kyakkyawa ya bada lada goma har zuwa dari zuwa dubu da abin da ya haura, {da sannu zamu saukaka shi zuwa ga yalwa}[3] bazai kara wani abu ba daga alheri fae Allah ya yassare masa.

 

قال الإمام الصادق   :

«ما ضاع مال في برّ ولا بحر إلّا بتضييع الزكاة ، فحصّنوا أموالكم بالزكاة ».

27-Imam Sadik (as) ya ce: (wata dukiya bata tozarta ba cikin doran kasa da tafki face da tozarta zakka, ku shinge dukiyoyinku da bada zakka)

قال الإمام الباقر   :

«ما نقصت زكاة من مال قطّ ، ولا هلک مال في برّ أو بحر اُدّيت زكاته ».

28-Imam Bakir (as) ya ce: (wata dukiya bata tawaya ba daga bada zakka, wata dukiya bata halaka a kan kasa ko tafki da aka fitar da zakka cikinta)

عنه  7 :

«وجدنا في كتاب رسول الله : إذا منعوا الزكاة منعت الأرض بركتها من الزرع والثمار والمعادن كلّها».

29-daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata gaershi: (mun samu cikin littafin manzon Allah (s.a.w) : idan suka hana zakka sai kasa ta hana albarkatunta daga shuka sa `yay`an itaciya da ma'adanai baki dayansu).

قال الإمام الرضا  7 :

«إذا حُبست الزكاة ماتت المواشي ».

30- Imam Rida (as) ya ce: (idan aka tsare zakka dabbobi sai su mutu).

قال أمير المؤمنين  7 :

«حصّنوا أموالكم بالزكاة ».

31-sarkin muminai (as) ya ce: (ku katange dukiyoyinku da bada zakka)

عن الإمام الصادق  7 :

«إذا قام القائم  7 أخذ مانع الزكاة فضرب عنقه ».

32-daga imam Sadik (as) idan k'aim ya tsaya (as) zai kama mai hana zakka ya sa rai wuyansa)

وعنه  7 :

«من منع الزكاة سأل الرجعة عند الموت وهو قول الله عزّ وجلّ: (حَتَّى إذَا جَاءَ أحَدَهُمُ المَوْتُ قَالَ رَبِّ آرْجِعُونِلَعَلِّي أعْمَلُ صَالِحآ فِيمَا تَرَكْتُ ) ».

33-daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata gare shi: (duk wanda ya hana zakka zai roki raja'a lokacin mutuwarsa shi ne fadinsa mai girma da buwaya: {har idan mutuwa ta zo dayansu sai ya ce ya ubangiji ka dawo dani* tsammanina na yi aiki nagari cikin abin da na bari a baya})[4]

وقال  7 :

«السرّاق ثلاثة : مانع الزكاة ، ومستحلّ مهور النساء، وكذلک من استدان ولم ينوِ قضاءه ».

35 ـ قال رسول الله  9 :

«والذي نفس محمّدٍ بيده ما خان الله أحد شيئآ من زكاة ماله إلّا مشرک بالله».

34-amincin Allah ya tabbata ghareshi ya ce: (barayi mutane uku ne:mai hana bada zakka, mai cinye sadakokin mata, hakama wanda yayi ranci ba tare da niyyar biya ba).

وعنه  9 :

«يا عليّ، كفر بالله العظيم من هذه الاُمّة عشرة ... ومانع الزكاة ».

35-daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata gare shi:

(ya Ali mutane goma sun kafirta da Allah daga cikin wannan al'umma……..da mai hana zakka).

وقال  9 :

«من منع قيراطآ من زكاة ماله فليس هو بمؤمن ولا مسلم ولا كرامة ».

36-amnicin Allah ya kara tabbata gare shi: (duk wanda ya hana kiradi daga zakkar kudinsa shi ba mumini bane ba kuma musulmi bane babu kuma karamci).

قال الإمام الصادق  7 :

«من منع قيراطآ من الزكاة فليمت إن شاء يهوديآ وإن شاء نصرانيآ».

38-Imam Sadik (as) ya ce: (duk wanda ya hana kiradi daga zakka idan ya so ya mutu bayahude ko banasare)

قال رسول الله  9 :

«مانع الزكاة يجرّ قصبه في النار ـيعني أمعاءه في النارـ ومُثّل له ماله في النار في صورة شجاع ـثعبان ـ أقرع له زبيبان أو زبيبتان يفرّ الإنسان منه ، وهو يتبعه حتّى يقضمه كما يقضم الفجل ويقول : أنا مالک الذي بخلت به ».

39-manzon Allah (s.a.w) ya ce: mai hana zakka za a jawo hanjin sa cikin wuta za ai masa musla a cikin wuta cikin surar maciji ya buwaye shi yana da digon baki biyu akan idanunsa mutum yana gudu daga gare shi shi kuma yana binsa har sai ya yi kaca-kaca da shi kamar yadda yakewa ganyen fajalu kaca-kaca ya ce masa ni ne dukiyarka da ka yi rowarta.

عن الإمام الباقر  7، قال  :

«الذي يمنع الزكاة يحوّل الله ماله يوم القيامة شجاعآ من نار له ريمتان فيطوّقه إيّاه ثمّ يقول : الزمه كما لزمک في الدنيا، وهو قول الله: (سَيُطَوَّقُونَ مَا

بَخِلُوا بِهِ ) ».

40-daga Imam Bakir (as) ya ce: (wanda yake hana zakkaAllah zai mayar da dukiyarsa katon maciji daga wuta ya nada digon baki biyu cikin idanunsa sai ya yi masa sakandami sannan ya ce: lazimce shi kamar yadda ya lazimceka a duniya shi ne fadinsa Allah: {da sannu za ai musu sakandami da abin da suka yi rowa da shi}[5]

وقال  7 :

«إنّ الله عزّ وجلّ يبعث يوم القيامة ناسآ من قبورهم مشدودة أيديهم إلى أعناقهم ، لا يستطيعون أن يتناولوا بها قيس أنملة ، معهم ملائكة يعيّرونهم تعييرآ شديدآ، يقولون : هؤلاء الذين منعوا خيرآ قليلا من خيرٍ كثير، هؤلاء الذين أعطاهم الله عزّ وجلّ فمنعوا حقّ الله عزّ وجلّ في أموالهم

41-amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce:

(lallai Allah mai girma da buwaya ranar kiyama zai tashi wasu mutane daga kaburburan su hannayen su daddaure ya zuwa wuyansu, basu iya daukar wani abu da ita gwargwadon kan yatsu tare da akwai mala'iku suna wulakanta su wulakantawa mai tsanani, suna cewa wadannan wanda suka hana alheri kankani daga alheri mai tarin yawa, wadannan su ne wanda Allah mai girma mabuwayi ya basu kyauta sai su kuma suka hana hakkin Allah mai girma mabuwayi cikin dukiyoyinsu.

قال أمير المؤمنين عليّ  7 :

«إنّ الزكاة جعلت مع الصلاة قربانآ لأهل الإسلام ، فمن أعطاها طيّب النفس بها، فإنّها تجعل له كفّارة ، ومن النار حجازآ (حجابآ) ووقاية ، فلا يتبعنّها أحد نفسه ، ولا يكثرنّ عليها لهفه ، فإنّ من أعطاها غير طيّب النفس بها يرجو بها ما هو أفضل منها فهو جاهل بالسنّة ، مغبون الأجر، ضالّ العمل ، طويل الندم ».

42- Sarkin muminai Ali (as): (lallai zakka an sanyata tare da sallah ibadar kusanci ga ma'abota muslunci, duk wanda ya bayar da ita ransa yana mai jin dadi da bayarwar lallai za a sanya masa ita matsayin kaffara, daga wuta kuma hijabi da kariya, kada wani  mutum ya biyewa son ransa, kada ya yawaita damuwarsa kanta, lallai dukkanin wanda ya bayar da ita alhalin ransa bai so yana kuma fata da ita abin da yafi falala daga gareta lallai shi ya jahilci sunna, ya tawaye cikin lada, aikinsa ya bata, ya kasance mai tsayin nadama).

Sannan ita zakka ko dai ta zahiri ko ta badini:

ورد عن الإمام الصادق  7 لمّا سأله رجل في كم تجب الزكاة من المال ؟ قال  7: «الزكاة الظاهرة أم الباطنة تريد؟» قال : اُريدهما جميعآ، فقال : «أمّا الظاهرة ففي كلّ ألف خمسة وعشرون درهمآ، وأمّا الباطنة فلا تستأثر على أخيک بما هو أحوج إليک منه ».

ثمّ لكلّ شيء زكاة .

43- ya zo daga Imam Sadik (as) lokacin da wani mutum ya tambaye shi nawa zakka take wajabta cikin dukiya? Sai ya ce: zakkar zahiri kake nufi ko ta badini? Sai mutumin ya ce ina nufin dukkaninsu, sai ya ce:amma zakkar zahiri cikin dukkanin dubu akwai dirhami ashirin da biyar, amma ta badini shi ne cewa kada ka fifita kanka kan dan'uwanka da abin da kasan ya fika bukatuwa daga gare shi.

Sannan ga kowanne abu akwai zakka.

قال أمير المؤمنين  :

«زكاة القدرة الإنصاف ».

«زكاة الجمال العفاف ».

«زكاة الظفر الإحسان ».

«العفو زكاة الظفر».

«زكاة اليسار برّ الجيران وصلة الأرحام ».

«زكاة الصحّة السعي في طاعة الله».

«زكاة الشجاعة الجهاد في سبيل الله».

«زكاة النعم اصطناع المعروف ».

«زكاة العلم بذله لمستحقّه وإجهاد النفس في العمل به ».

«زكاة العقل احتمال الجهّال ».

«إنّ الله فرض عليكم زكاة جاهكم كما فرض عليكم زكاة ما ملكت أيمانكم ».

«زكاة البدن الصوم والجهاد».

 

44- Sarkin muminai (as) ya ce:

(zakkar iko adalci)

(zakkar kyau kamewa)

(zakkar nasara ihsani)

(zakkar yalwata kyautatawa makota da sadar da zumunci)

(zakkar lafiya sa'ayi cikin da'ar Allah)

(zakkar jarumta jihadi cikin tafarkin Allah)

(zakkar ni'ima aikata ma'arufi)

(zakkar ilimi sadaukar da shi ga wadanda suka cancance shi da wahalar da kai cikin aiki)

(zakkar hankali hakuri da jahilai)

(lallai Allah ya farlanta zakkar alfarmarku kamar yadda ya farlanta zakar abin da damanku ta mallaka).

(zakkar gangar jiki azumi da jihadi)

قال الإمام الصادق  7 :

«المعروف زكاة النعم ، والشفاعة زكاة الجاه ، والعلل زكاة الأبدان ، والعفو زكاة الظفر، وما أدّيت زكاته فهو مأمون السلب ».

45-imam Sadik (as) ya ce: (ma'arufi shi ne zakkar ni'imomi, ceto zakkar alfarma, illoli zakkar jikkuna, afuwa zakkar nasara, abin da ka bada zakkarsa ya aminta daga kwace)

وقال  7 :

«على كلّ جزء من أجزائک زكاة واجبة لله عزّ وجلّ ، بل على كلّ شعرة ، بل على كلّ لحظة ، فزكاة العين النظر بالعبرة والغضّ عن الشهوات وما يضاهيها، وزكاة الاُذن استماع العلم والحكمة والقرآن ».

46-amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: (kan dukkanin wani juzu'i daga yankunan jikinka akwai zakkar Allah mai girma mabuwayi ta wajibi, bari dai kan dukkanin wani silin gashi, bari kan dukkanin kiftawar ido, zakkar ido shi ne yin kallo tare da fadakuwa da kau da gani daga sha'awe-sha'awe da abin da suka yi kama da ita, zakkar kunne sauraren ilimi da kur'ani da hikima).

 

Shin ya kai dan'uwa ka sauke zakka tare da dukkanin kashe-kashenta da ma'anoninta?


 

 

 [1] Alu imran:186

[2] Lailu:5-6

[3] Lailu:7

[4] Muminun:99-100

[5] Alu Imran:180