فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Kumusi

 

Allah mdaukakin sarki cikin mabayyanin littafin sa mai girma ya ce:

 

 (وَآعْلَمُوا أنَّمَا غَنِمْتُمْ مِنْ شَيْءٍ فَأنَّ للهِ خُمُسَهُ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي القُرْبَى وَاليَتَامَى وَالمَسَاكِينِ وَآبْنِ السَّبِيلِ إنْ كُنتُمْ آمَنْتُمْ بِاللهِ).

Ku sani abin da kuka samu ganima daga wani abu lallai Allah    yana da kaso daya cikin biyar da manzon sa da makusanta da marayu da matalauta da dan kan hanya idan kun kasance kuna imani da Allah.[1]

Kumusi yana daga cikin farillan muslunci da wajiban addini kan dukkanin musulmi da mumini, Allah madaukaki ya sanya shi ga annabin sa (s.a.w) da zuriyar sa maimakon zakka ya yi hakan ne don karrama su, lallai yadda lamarin yake ana karrama ido dubu albarkacin wani ido guda daya.

duk wanda ya hana dirhami daga kumusi koma kasa daga dirhami lallai ya kasance cikin masu zaluntar annabi (s.a.w) da zuriyar sa da masu kwace musu hakkokin su, bari dai mai ganin halascin yin hakan ya kasance daga kafirai ya kuma yi inkarin daya daga cikin laruran addini da haka ya wayi gari daga murtaddai kansa akwai tsinuwar Allah da mala'iku har zuwa tashin kiyama. 

1 ـ في الخبر الشريف عن أبي بصير، قال : قلت لأبي جعفر  7: ما أيسر ما يدخل به العبد النار؟ قال  7: من أكل مال اليتيم درهمآ، ونحن اليتيم.

1-ya zo cikin hadisi mai daraja daga Abu Basir ya ce: na cewa Abu Jafar (as) me yafi sauki da bawa yake shiga wuta ta hanyarsa?sai ya ce:wanda ya ci dirhami daga dukiyar marayu, sannan kuma mu ne marayun.[2]

Shaika Saduk Allah ya yi masa rahama cikin littafin sa mai daraja Ikmalud Dini yana cewa: abin da ake nufi da maraya shi ne wanda abokin cudanya ya yanke daga gare shi cikin wannan waje, an kirayi manzon Allah (s.a.w) da maraya da wannan ma'ana, haka dukkanin wani imami bayan sa shima ana kiransa maraya da wannan ma'ana, sannan ayar cin dukiyar marayu bisa zalunci kansu ta sauka, daga bayan lamarin ya cigaba da gudana cikin sauran halittu hatta marainiya zinariya an kirata ne da marainiya sakamakon yankewa daga `yar'uwarta da kwatankwacinta

قال الشيخ الصدوق عليه الرحمة في كتابه الشريف إكمال الدين : معنى

ـ وعن مولانا الصادق  7، قال  :

«إنّ الله لا إله إلّا هو، حيث حرّم علينا الصدقة أنزل لنا الخمس ، فالصدقة علينا حرام والخمس لنا فريضة ، والكرامة لنا حلال ».

2- daga shugabanmu Sadik (as) ya ce: (lallai Allah babu abin bautawa da gaskiya sai shi, ta yadda shi ya haramta sadaka kanmu sai ya saukar mana da kumusi, sadaka ta haramtu garemu shi kuma kumusi farilla ne garemu, karamci garemu halal ne.

ـ وعن أبي جعفر  7 :

«لا يحلّ لأحد أن يشري من الخمس شيئآ حتّى يصل إلينا حقّنا».

3- daga Abu Jafar (as) (bai halasta ga wani mutum ya sayi wani abu ba daga kumusi har sai ya kawo mana hakkinmu.

وعن أبي عبد الله  7 :

«لا يعذر عبد اشترى من الخمس شيئآ أن يقول يا ربّ اشتريته بمالي حتّى يأذن له أهل الخمس

4- daga Abu Abdullah (as) : (ba a yiwa bawa uzuri wanda ya sayi wani abu daga kudin kumusi da wai ya ce ya ubangiji na saye shi ne da kudina har sai idan masu kumusin sun yi izini)

وعنه  7 قال  :

«إنّي لآخذ من أحدكم الدرهم وإنّي لمن أكثر أهل المدينة مالا، ما اُريد بذلک ، إلّا أن تطهروا».

5- daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce: (lallai ni mai karbar dirhami ne daga dayanku ga wanda yafi kowa kudi a madina, bana nufin komai da hakan face ku tsarkaka)

daga cikin hikima da falsafar kumusi shi ne tsarkaka kamar yadda ya kasance cikin zakka, hakama daga cikin hikima kumusi shi ne yalwata talakawa daga zuriyar manzon Allah (s.a.w)

وعن الإمام موسى بن جعفر  7، قال عندما قرئت عليه آية الخمس  :

«ما كان لله فهو لرسوله ، وما كان لرسوله فهو لنا».

6-daga imam Musa bn Jafar (as) lokacin da aka karanta masa ayar kumusi, sai ya ce: (duk abin da ya kasance na Allah to lallai na manzon sa ne, sannan dukkanin abin da ya kasance na manzon Allah ne to namu ne)

 

ثمّ قال  :

«والله لقد يسّر الله على المؤمنين أرزاقهم بخمسة دراهم ، جعلوا لربّهم واحدآ، وأكلوا أربعة أحلّاء».

ثمّ قال  :

«هذا من حديثنا صعب مستصعب ، لا يعمل به ولا يصبر عليه إلّا ممتحن قلبه للإيمان ».

Sannan ya ce: (wallahi hakika Allah ya yassarewa muminai arzikinsu da dirhami biyar, suka sanya daya ga ubangijin su suka ci dirhami hudu halaliya).

Sannan ya ce: (wannan yana daga zancenmu wahala mai wahalartarwa, babu mai iya daukar sa sai mala'ika makusanci ko annabi aikakke ko muminai da Allah ya jarrabci zuciyarsa da imani).

7 ـ وفي الحديث المستفيض عن الأئمة  : :

«إنّ حديثنا ـفي رواية : أمرناـ صعب مستصعب ، لا يتحمّله إلّا ملک مقرّب أو نبيّ مرسل أو مؤمن امتحن الله قلبه بالإيمان ».

daga hadisi da ya kwarara daga A'imma (as):

(lallai zancenmu wahala ne mai wahalartarwa ne, babu mai iya daukarsa sai mala'ika makusanci ko annabi aikakke ko muminai da Allah ya jarrabci zuciyarsa da imani).

Abin da ake nufi da hadisi shi ne al'amarinsu wanda shi ne (wilaya) lokacin da aka bijiro da ita ga mala'iku basu dauketa ba basu karba bahakikanin karba face mala'ika makusanci, yayin da aka bijiro da ita ga annabawa basu samu ikon daukarta ba face manzo daga cikinsu, yayin da aka bijiro da ita ga mutane babu wanda ya dauka sai mumini wanda Allah ya jarraba zuciyarsa a wurare da imani.

Yana bayyana gareni cewa lallai bada kumusi na daga mabayyanun wannan jarrabawa ta Allah, duk wanda ya bada kumusi da dadin zuciya cikin farin ciki da nishadi, lallai hakan na daga alamomin imani, babu mai hakuri kansa face wanda Allah ya jarraba zuciyarsa da imani, duk wanda ya gaza bada kumusi daga dukiyar sa ta kaka zai bada ransa lokacin bayyanar imamin zamaninsa?!

ـ وعن مولانا الكاظم  7، قال  :

«قال لي هارون : أتقولون إنّ الخمس لكم ؟

قلت : نعم .

قال : إنّه لكثير.

قال : قلت : إنّ الذي أعطاناه علم أنّه لنا غير كثير».

8-daga shgabanmu Imam Kazim (as) ya ce: {Haruna ya ce mini: shin kuna cewa lallai kuna da kumusi?

Sai na ce: na'am

Sai ya ce: lallai shi mai yawa ne.

Ya ce: sai na ce: wanda ya bamu ya san cewa garemu bai da yawa}.

Misalin Haruna Rashid dagutu ai dama kumusi zia wahala da tsanani kansu zai ga abin da zai bayar daga kumusi kaso ne a wurin sa mai yawan gaske, to kaka kuma ga wanda yake inkari yake kuma hana asalin hakan?[3]

Wannan boyayye lamari bane cewa kadai Allah ya wajabta kumusi a zamanin annabi (s.a.w) cikin ganimonin yaki, sannan shuwagabanninmu tsarkaka suka bayyana ragowar wurare daga zamanin Imam Bakir (as) da Sadik (as) kamar yadda zaka samu bayaninsa filla-filla cikin Risala Amaliyya da sauran litattafan fikihu, kadai dai jinkirta bayanin ragowar wurare da kumusi ya wajabta bayan ganimonin yaki a zamanin manzon Allah (s.a.w) zuwa zamanin Imam Bakir da Sadik (as) ya kasance ne da hikima ubangiji.

Kadai kumusi kamar yadda ya zo cikin aya mai daraja yana daga sinfofi guda shida: ga Allah, manzon Allah (s.a.w) makusanta A'imma tsarkaka, abin da ya kasance na Allah ne to na manzon sa ne, sannan abin da ya kasance na manzo to na imami ma'asumi ne (as) ya zama sannan lamari tsakankanin wadanda suka yi zamani da ma'sumai akwai wani kaso a zamanin gaiba kubra wanda ake kira da kason Imami ma'asumi (as) da ake sarrafa shi cikin yada addinin muslunci da izinin marja'in taklidi wanda ya cika sharudda ko kuma wakilin sa, amma rabi na biyu daga kumusi to lallai shi ana bada shi ga sinfofi uku daban da aka ambata cikin ayat kumusi daga hashimawa mayin zakka da aka haramta cinta gare su domin ta waninsu ce ta kuma haramta kansu, ana kiran wannan kaso da sunan kason sharifai.

Kumusi yana daga farillan da aka karfafa su da nassi daga cikin kur'ani mai girma, hakika himmatuwa babba ta gangara kan sha'anin kumusi daga riwayoyi da aka rawaito daga Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata gare su wadanda cikin ba'arin su tsinuwa da azaba da tabewa suka zo kan wanda yake kin bada kumusi haka kan wanda yake cinsa ba tare da hakki da cancanta ba.

فمن كتاب لإمامنا الحجّة الثاني عشر المهدي المنتظر عليه السلام وعجّل الله فرجه الشريف قال: 

«ومن أكل من مالنا شيئآ فإنّما يأكل في بطنه نارآ».

9- daga littafin imaminmu Hujjatu na sha biyu Mahadi Muntazar amincin Allah ya kara tabbata gare shi Allah ya gaggauta bayyanar sa ya ce: (duk wanda yaci wani abu daga dukiyarmu kadai dai yana cin wuta ne a cikinsa).

وقال  7 في كتاب آخر :

«بسم الله الرحمن الرحيم ، لعنة الله والملائكة والناس أجمعين على كلّ من أكل من مالنا درهمآ حرامآ».

10-amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce: (da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Tsinuwar Allah da mala'iku da mutane baki daya ta tabbata kan dukkanin wanda ya ci dirhami daga haramun daga dukiyarmu)

وقال  7 :

«وأمّا المتلبّسون بأموالنا، فمن استحلّ منها شيئآ فأكله ، فإنّما يأكل النيران » .

11-amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: (amma masu cadanya da dukiyarmu duk wand aya halasta wani abu daga gareta sannan  yaci to kadai dai yana cin wuta)[4]

Shi wanda yake hana kumusi anya kuwa zai rayuwa cikin yalwa da ni'ima da farin ciki? Ta kaka haka zata yiwu alhalin kudubin duniyar imkani wanda shi ne Sahibul Asri waz-zaman (as) zai yi tsinuwa kan mai hana kumusi? Farin ciki ga wanda ya bada kumusi sannan kuma addu'ar shugaban sa ta tattaro da shi, ta kaka wanda ya bada kumusi ba zai farin ciki da dacewa ba cikin rayuwar sa? ta kaka ba zai rayu cikin yalwa a duniya ba?! Da aljanna fadinta kamar misalin fadin sammai da kasa ba a lahira.

Ya kai wannan bawan shin wai dukiyar daga wajen wa take ne? shin ashe ba daga Allah matsarkaki take ba? to me yasa ne mutum yake rowarta? Idan ance: kadai dai ni na sameta ne daga gumina da wahalata, sai mu ce daga wajen wa dabara da karfinsu suke?daga wajen wa lafiya take? daga wajen wa dacewa take?mene ne ya sanya ba zamu yiwa ubangijin talikai da'a ba? Mene ne ya sanya yin rowa? Wacce kima kudi suke da ita ko nawa suka kakai? Yaya kake tunani idan hana kumusin ya kasance ya jawo masa tsinuwar Sahibuz-zaman (as) kansa, da la'anar mai kin sauke hakkokin shari'a? cikin dukiya akwai hakkin mai roko da wanda ka haramtawa, wacce kima dukiya take da ita idan karshenta ya zama mai jawo azaba da tabewa da la'anar Allah da mala'iku da baki dayan mutane.

Ashe lokaci bai yi ga wadanda suka yi imani ba zuciyarsu ta kaskantar da kai ga Ambaton Allah.

Kada ka yi bakin ciki kan abin da ya tafi kada kuma ka yi farin ciki cikin mai zuwa, ka ci ganimar lokacinka da kake cikinsa, ka tuba zuwa ga ubangijinka, ka biya bashin abin da ya subuce ya fauce, ka sauke hakkokin ubangijinka da suke kanka, ka faranta ranka, ka yi taka tsantsan dukkanin taka tsantsan daga tsorace-tsoracen lahira da wuta.

Hakika ya zo cikin tafsirin kummi cikin aya mai daraja lokacin da za a tambayi `yan wuta:     

 (مَا سَلَـكَـكُمْ فِي سَقَرَ) ؟

Mene ne ya shigar da

ku cikin wutar sakar?[5]

Daga cikin amsar da za su bada shi ne:

 (وَلَمْ نَکُ نُطْعِمُ المِسْكِينَ ) ،

Bamu kasance muna ciyar da matalauci ba.[6]

Ya ce: hakkokin Alu Muhammad (s.a.w) daga kumusi ga makusanta da marayu da matalauta da dan kan hanya su ne Alu Muhammad.

Haka ya zo cikin fadinsa madaukaki: 

 (وَلا تَحَاضُّونَ عَـلَى طَعَامِ المِسْكِينِ ) ،

Kuma bakwa kwadaitarwa kan ciyar da matalauci.[7]

Ma'ana bakwai kiyaye su, wadanda su ne suka yiwa Alu Muhammad da iyalansa suka yi kwacen hakkinsu suka ci dukiyar marayu da talakawansu da `ya`yan kan hanyarsu wannan bayani yana daga tawilin ayar idan bai kasance daga tafsirin ta ba, sai ka lura, ka zurfafa gani- sha'anin muhimmancin kumusi bai kasa da na zakka daga cikin hikima da riwaya, sannan wanda ya yi inkarin sa to shi dan wuta ne tir da matabbata.

Amma batun yadda ake cire kumusi, lallai anyi bayanin kansa filla-filla dalla-dalla cikin Risalolin taklidi na maraji'anmu masu girma, duk wanda bai fitar da kumusi a baya-ma'ana daga shekarar da ya balaga- domin kumusi yana fara wajaba cikin shekarar farkon balaga kamar yadda sallah take wajaba har zuwa ranar bada shi, lallai shi zai kimanta dukkanin abin da ya mallaka sannan ya je ya daidaita tare da mujtahidi ko wakilin sa, sannan bayan ya ayyanawa kansa lokacin fitar da kumusin sa cikin kowacce shekara cikin wannan lokaci da ya ayyana sai ya fitar da kumusin dukiyar sa wanda ya karu kan bukatun sa mudlakan, babu banbanci cikin kasantuwar su tsabar kudi ko wasun su, mai ciratuwa ne koma mara ciratuwa, babu laifi cikin komawa wajen malaman garinku da duk wanda ka aminta da shi domin ya lissafa maka ya fitar maka da kumusin.

Babu laifi mu kawo abin da Allama daba'daba'i babban malamin tafsiri (rd) ya fada cikin littafin sa mai daraja (Almizan fi tafsiril kur'an)[8] cikin ayar kumusi karkashin fadin sa madaukaki:

 (وَآعْلَمُوا أنَّمَا غَنِمْتُمْ مِنْ شَيْءٍ فَأنَّ للهِ خُمُسَهُ وَلِلرَّسُولِ )

Ku sani lallai abin da kuka ci ganima daga wani abu lallai Allah yana da kaso daya cikin biyar da manzon sa[9]…..zuwa karshen ayar.

Ganimomi da ganima: samun wata fa'ida daga fuskanin kasuwanci ko wani aiki ko kuma ya dabbaku da yadda muhallin da ayar ta sauka kan ganimar yaki.

Ragib Isfahani ya ce: ganamu da wasalin fataha guda- sannan abu shi ne dabbobi daga sanuwa, da dabbobi wadanda muka haramta musu kitsensu, sannan gunumu da wasalin damma da dauri-shi ne samunsa da cimmasa da nasara kansa, sannan akai amfani da Kalmar kan dukkanin abin da akai nasara kansa aka cimmasa daga bangaren makiyi da waninsa, Allah madaukakin sarki ya ce: {ku sani kadai abin da ku samu daga wani abu} {kuci daga abin da kuka samu} jam'in Kalmar shi ne maganim, ya ce: {wajen Allah akwai ganimomi masu tarin yawa} maganarsa ta kare.

ـ ... ثمّ قال في البحث الروائي : في الكافي عن عليّ بن إبراهيم عن أبيه عن ابن أبي عمير عن الحسين بن عثمان عن سماعة قال : سألت أبا الحسن  7 عن الخمس فقال : في كلّ ما أفاد الناس من قليل أو كثير.

12…sannan ya ce cikin bahasi na riwaya cikin littafin Alkafi daga Aliyu bn Ibrahin daga babansa daga ibn Abu umairu daga Husaini Usmanu daga Samma'atu ya ce: na tambayi Abu Hassan (as) dangane da kumusi sai ya ce: dukkanin abin da mutane suka samu fa'ida daga mai yawa ko kadan.

ـ وفيه عن عليّ بن إبراهيم عن أبيه عن حماد بن عيسى عن بعض أصحابنا عن العبد الصالح الإمام موسى بن جعفر  8 قال : الخمس في خمسة أشياء من الغنائم والغوص ومن المعادن والملاحة يؤخذ من كلّ هذه الصنوف الخمس لمن جعل الله له ، ويقسم أربعة أخماس بين من قاتل عليه وولى ذلک .

13- sannan kuma cikinsa daga Aliyu bn Ibrahim daga babansa daga Hammad bn Isa daga ba'arin sahabbanmu daga bawan Allah nagari Imam Musa Alkazim bn Jafar (as) ya ce: kumusi yana cikin abubuwa guda biyar daga ganimomi da abin da aka samu daga nutso a ruwa da ma'adanai da….ana cire daga dukkaniwadannan sinfofi guda biyar ga wanda Allah ya sanya su gare shi, ana karkasa shi kashi hudu cikin biyar tsakanin wanda ya yi yaki kansa da wanda ya jibanci hakan.

Ana kasa kumusi tsakaninsu kan sahami shida, sahamin Allah, sahamin manzon Allah, sahamin ma'abota kusanci, sahamin marayu, sahamin matalauta, sahamin `ya`yan hanya. Da farko sahamin Allah da na manzon Allah (s.a.w) su na komawa ga ma'abota al'amari bayan manzon Allah magadansa, su suna da sahami uku, sannan kuma sahami guda Allah ya basu shi ne, sun tashi da rabin kumusi kenan, sannan dayan rabin kumusin yana komawa ga tsakankanin Ahlil-baiti: sahami guda ga marayunsu, sahami guda ga matalauntansu, sahami guda ga `ya`yan hanyar su, rarraba musu kan littafin Allah da sunna abin da za su wadatu da shi cikin fari da fako, idan kuma wani abu ya ragu daga gare su to yna komawa ga waliyi, idan suka kasa ya kuma zamanto ya tawaya daga wadatar dasu to wajibi kan waliyi ya ciyar da su abin da zai wadatar da su daga abin da yake daga gare shi abin da zai, kadai dai Allah ya sanya kumusi gare su kebance, koma bayan matalautan sauran mutanen wanda basu da `ya`yan hanya don ya zama mayi da maimako gare su daga zakka da sadakar mutane don tsarkake kusancin su daga manzon Allah (s.a.w) da karamci daga Allah gare su daga kazantar mutane, sai Allah ya kebance su da kumusi daga gare shi da abin da zai wadatar da su don gudun kada ta kai ga gangara wurin kaskanta da wulakanta, amma babu laifi su yi sadaka ga junansu. Wadannan su ne wadanda Allah ya kebance su da kumusi wadanda su ne makusantan annabi (s.a.w) wadanda Allah ya ambace su ya ce:

  (وَأنذِرْ عَشِيرَتَکَ الأقْرَبِينَ )

Ka gargadi danginka mafi kusanci.[10]

Su ne banu Abdul-muddalib, mazaje daga cikinsu, mata basa cikin su daga cikin ma'abota gidajen kuraishawa babu wani mutum guda daga larabawa da yake daga gare su ya yi tarayya da su cikin wannan kumusi daga majibantan su, sadaka na iya halasta ga mutane daga masoyan su, su basu da banbanci da sauaran mutane cikin sadaka.

Sannan ya ce: hadisai daga A'immatu Ahlil-baiti (as) sun zo da tawatiri cikin kebantuwar kumusi ga Allah da manzon sa da Imami daga Ahlil-baitin sa da marayu da matalauta da makusanta da `ya`yan hanyarsu bai tsallake ya zuwa waninsu ba, lallai shi kumusi ana kasa shi gida shida kamar yadda ya gabata cikin riwayoyi, lallai bai kebanta da ganimomin yaki ba kawai bari dai yana gamewa da dukkanin abin da ake kira da ganima a luggance daga ribar kasuwanci da taskoki da abin da akai nutso ruwa aka tsamo shi da ma'adanai, a cikin riwayarsu kamar yadda ya gabata lallai hakan kyauta daga Allah ga Ahlil-baiti bisa abin da Allah ya haramta musu daga zakka da sadakoki.

Wannan kenan sannan mu muna karbar addininmu daga Ahlil-baiti mutanen gidan annabta, cikin gidanjen su kur'ani ya sauka su ne Ahlin wahayi, muna kiran kumusi kan dukkanin abin yake amsa sunan ganima a luggance, duk da cewa masu sabani da mu daga sauran musulmai suna kebantar da kumusi cikin ganimar yaki kawai, sabanin abin da riwayoyi daga hanyar Ahlil-baiti suke kansa.

Kamar yadda zahirin aya mai daraja lallai ita tattara kan shar'antawa na har abada kamar yadda ya kasance wannan shi ne zahirin shari'o'i kur'ani, lallai shi hukuncin da ya ratayu da abin da ake kira ganimar yaki wacce aka kwato daga hannun kafirai da wasunsu da kuma abin da ake kira da ganima a luggance daga ribar kasuwanci da abin da akai nutso aka fito da shi da abin da aka fito da shi da taskoki da ma'adanai, duk da cewa abin da ita ayar ta sauka kansa shi ne ganimar yaki, muhallin ba a kebantar da shi.

Hakama zahiri abin da aka kirga daga wurare da ake sarrafa kumusi da fadinsa madaukaki:     

(للهِ خُمُسَهُ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي القُرْبَى وَاليَتَامَى وَالمَسَاكِينِ وَآبْنِ السَّبِيلِ )

Ga Allah daya bisa biyar dinsa yake komawa da manzon sa da makusanta da marayu da matalauta da dan hanya.[11]

Togacewar wurare cikin wadanndan sinfofi, lallai kowanne daya daga gare su yana da wani sahami da ma'anar cin gashin kansa cikin karba kamar yadda ake amfanuwa cikin misalinsa daga ayar zakka ba tare da ambaton sinfofi da za a baiwa ba.

Wannan dukkaninsa yana daga abin da babu kokwanto cikinsa bisa kallon abin da zahirin ayar take nuni zuwa gare shi, sannan kari kansa akwai riwayoyi da suka zo daga hanyoyin Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata a gare su.[12]

Magana kan abin da riwayoyi ke kunshe da su kadai ya rage, lallai Allah matsarkaki ya nufi shar'anta kumusi domin karrama Ahlil-baitin annabi (s.a.w) da dangin sa da daukaka su daga barin karbar kazantar mutane cikin dukiyar su, zahirin magana shi ne wannan magana an cirota daga fadinsa madaukaki cikin ayar zakka a maganar sa ga annabinsa amincin Allah ya kara tabbata a gare shi da mutanen gidansa: 

 (خُذْ مِنْ أمْوَالِهِمْ صَدَقَةً تُطَهِّرُهُمْ وَتُزَكِّيهِمْ بِهَا وَصَلِّ عَلَيْهِمْ إنَّ صَلاتَکَ سَكَنٌ لَهُمْ ).

Ka cira daga dukiyarsu sadaka da zaka tsarkakesu da ita kuma kayi musu addu'a lallai addu'arka nutsuwa ce gare su.[13]

Lallai tsarkakewa da tsaftacewa kadai dai yana rataya ne daga abin da bai wofinta daga datti da kazanta ba da makamancinsu, sannan cikin ayar kumusi wani abu mai nuna haka bai faru ba.

Abin da ke ta'allakuwa da ayar daga natijar da take samuwa daga bahasin tafsiri shi ne wannan abin da muka gabatar, sannan akwai wasu bahasosin daban daga bahasin kalam da fikihu da suke wajen hadafinmu, haka akwai bahasin shari'a da hakkoki da zamantakewa cikin abin da yake da tasiri cikin kumusi daga tasirin zamantakewar muslunci da sannu zai gangaro gareka cikin magana kan zakka.[14]

A hakika lallai shi kumusi ana kirga shi daga mafi tsarkakar dukiyar mai bada kumusi, saboda shi an cudanya shi da Allah matsarkaki

 (للهِ خُمُسَهُ ) ،

Ga Allah.[15]

Duk abin da ake dangane shi da Allah zai kasance madaukaki da girmama da tsarkaka da tsarkakewa kamar misalin dakin Allah da haraminsa da masallatansa da makamantan haka masu yawa, sai a lura.[1] Anfal:41

[2] Wasa'ilul shi'a: m 6 sh 337, haka zalika wasu riwayoyin daban

[3] Biharul-Anwar: m 93 sh 188

[4] Wadannan riwayoyi da misalansu ana iya samunsu cikin wasa'il shi'a mu 6 sh 383

[5] Mudassir:42

[6] Mudassir:44

[7] Alfajar:18

[8] Almizan: m 9 sh 89

[9] Anfal:41

[10] Shu'ara:214

[11] Anfal:41

[12] Tafsiurl Mizan:m 9 sh 91

[13] 03Tauba:1

[14] Tauba:103

[15] Hakika nay i bahasin kan wannan maudu'I da bayani filla-filla cikin littafin{ Ma'amul FI Takrimul zuriyatul Rasul}