فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Hajji

 

Allah madaukaki cikin mabayyanin littafin sa yankakken zancen sa ya ce:

 (وَللهِ عَلَى النَّاسِ حِجُّ البَيْتِ مَنِ اسْتَطَاعَ إلَيْهِ سَبِيلا وَمَنْ كَفَرَ فَإنَّ اللهَ غَنِيٌّ عَنِ العَالَمِينَ ).

Kuma Allah yana da hakkin ziyartar dakinsa kan mutane gawanda ya samu iko zuwa gare shi duk wanda ya kafirce lallai Allah mawadaci ne daga barin talikai.[1]

 

 Matsarkaki ya ce:

 (وَأذِّنْ فِي النَّاسِ بِالحَجِّ يَأتُوکَ رِجَالا وَعَلَى كُلِّ ضَامِرٍ يَأتِينَ مِنْ كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٍ ) .

yi shelar wajabcin hajji cikin mutane za su zo maka da kafafuwansu kuma kan dukkanin danwararren rakumi za su daga dukkanin rango mai zurfi.[2]

Shi hajji ibada ce ta zamantakewa da siyasa cikin muslunci ma'abociya jahadi Mai girma na ruhi da gangar jiki, cikin daidaiku da jama'a cikin dukkanin fagagen rayuwa daga ibada da siyasa da tattalin arziki da sakafa da cigaba da habbaka da yan'uwantakar muslunci da makamancin haka.

Hajji wani ayari ne na zamantakewa da jamhur suke fuskantar cikinta, jamhur din musulmai mukallafai da sauke wannan farali, ko kuma muce masu tadawwa’i don taruwa da hallara cikin wannan waje guda daya mai tsarki, wanda shi ne mafi daukakar bigirea ban kasa, a cikin zamani guda cikin wata mai alfarma na zul hijja mai albarka, wannan ayari suna aikata ibadoji da suka hadasu suka dayantu cikinsu, wadanda cikinsu mutum ke fita daga duniyar mada ta zahiri ya filfila fukafukansa zuwa ga madaukakin masoyi zuwa ga duniyar mala'ikanta da ruhu ba tare da karshe ba, zuwa ga hallarar Allah matsarkaki, yana mai tattara siffofin kamala da yanayin saki babu kaidi.

Ya isar cikin girmamar hajji kasantuwarsa daya daga rukunan da muslunci ya ginu kansu, shi hajji asasi ne da ginin muslunci madaukaki ya doru kansa, ruhin kauna da yan'uwantaka da tacewa da hakimantar ma'anawiyya kan madiyat yana tajalli cikinsa, lallai muslunci yana daukaka babu abin da yake daukaka kansa, dole ne wata rana zata zo da tutar muslunci zata filfila kan baki dayan duniya, dukkanin wanda ya halarci Makka mai karamci da birnin Madina dayyiba zai fahimci hakan a bayyane

Lallai wannan addini mai kima da ma'abotansa za su yi riko da shi su dabbaka shi cikin fagen rayuwarsu da wannan addini ya shugabanci duniya ko da mushrikai basa so, domin mutum da al'umma da suka bace suka shiga cikin rudewa za su samun abin da suke cigiya da nema cikin wannan addini, addini mai girma shi ne wanda ya dauki nauyin azurtar mutum cikin gida biyu gidan duniya da gidan lahira  

عن مولانا الباقر، قال  :

«بني الإسلام على خمس : إقام الصلاة ، وإيتاء الزكاة ، وحجّ البيت ، وصوم شهر رمضان ، والولاية لنا أهل البيت ، وما نودي بمثل ما نودي بالولاية ».

1- daga shugabanmu Bakir (a.s)

{an gina muslunci kan abubuwa biyar: tsayar da sallah da bada zakka da ziyartar dakin Allah da azumtar watan Ramadan da wilayarmu ba ai kira misalin kiran da akai kan wilaya ba.[3]

 

Shi hajji yana bayyana izzar muslunci da wanzuwarsa da ikonsa, babu wata al'umma daga al'ummu da take da wannan babban taro na duniya baki daya da ya tattaro alherai da albarkoki, musulmi daga gabashin duniya da yammacinta suna taruwa cikinsa tare da banbancin mazhabobinsu da kungiyoyinsu da launukansu da shakalinsu mabanbanta da kuma mabanbanta yarukansu da tsarinsu, ba a banbance mawadacinsu daga talakansu bawa da mai gidansa, kowanne ya daura harami suna amsa kiran Allah wanda sautinsa ya fallatsa cikin al'ummu tsawon karnoni da zamanunnuka tun daga shugaban annabawa Ibrahim masoyin Allah (as) yana mai fada masa:

(وَأذِّنْ فِي النَّاسِ بِالحَجِّ يَأتُوکَ رِجَالا وَعَلَى كُلِّ ضَامِرٍ يَأتِينَ مِنْ كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٍ ).

Kayin shela da wajabcin hajji cikin mutane za su zo maka da kafafunsu kan dukkanin madankwarin rakumi zaso zo daga dukkanin rango mai zurfi.[4]

 

Wadancananka su ne wadanda kasuwanci da saye da sayarwa baya shagaltar da su daga barin Ambaton Allah, suna begen tsarkaka, su ne wadanda suka gasgatar da abin da suka daukarwa Allah alkawari kansa.

Kai kace shi matsarkaki madaukaki cikin matsayar ihrami ya nufi wasu matsayoyin daban daga ibadun hajji, da cewa mutane su tuna tsayuwar ranar da kuma yin tanadin don tsayuwar lahirar ta hanyar neman guzuri, lallai mafi alherin guzuri shi ne guzurin tsoran Allah, a wannan zamani matsiyaci nawa ne ya nufi wannan daki mai albarka sai ya dawo azurtacce, mai sabo nawa ne ya nufi sai ya dawo yana mai da'a, fajiri nawa ne ya mai shi mai tsoran Allah, gafallalle nawa ne ya zama mai fadaka, ba komai ya kawo hakan ba face daga albarkar wadancan wurare masu girma da matsayu madaukaka.

Shi hajji rabauta ne, hakika dukkanin wanda ya tsayar da shi yadda aka nema daga gare shi to ya rabautu, kadai manzon Allah (s.a.w) da A'imma tsarkaka sun himmatu kan hajji saboda sanin muhimmancinsa, da kuma cewa shi lallai ya tattaru kan da yawan ibadoji da falaloli da alheri na zamantakewa da kuma ladan lahira

2- manzon Allah (s.a.w) ya ce: mahajjaci idan ya dauka cikin tarkacensa ba zai daga wani abu ko ajiye shi ba face Allah ya rubuta masa lada goma, ya kuma goge masa zunubai goma, ya daukaka darajoji goma don shi…idan ya yi dawafi daura da dakin Ka'aba sai ya fita daga cikin zunubansa, idan ya yi sa'ayi tsakanin safa da marwa zai fita daga zunubansa, idan ya tsaya a Arafat zai fita daga cikin zunubansa.

ـ وفي بعض الروايات  :

«خرج من ذنوبه كيوم ولدته اُمّه ».

3- ya zo cikin ba'arin wasu riwayoyin: (zai fita daga cikin zunubansa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi)

عن أمير المؤمنين عليّ ، قال عند شهادته في وصيّة لأولاده  :

«الله الله في بيت ربّكم ، لا تخلّوه ما بقيتم ، فإنّه إن ترک لم تناصروا».

4- daga sarkin muminai Ali (as) lakocin da zai yi shahada ya fadawa `ya`yansa cikin wasiyyarsa gare su:

(Ina hadaku da Allah ina hadaku da Allah da cikin dakin ubangijinku, kada ko wofintar da shi matukar kuna raye, lallai yadda al'amarin yake idan aka wofintar da dakin Allah ba za a taimake ku ba)

وقال   :

«الحجّ جهاد كلّ ضعيف ».

5- amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: (Hajji jihadin dukkanin wani rarrauna ne)

وعنه  :

«نفقة درهم في الحجّ تعدل ألف درهم ».

6- daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata gare shi:

(dirhamin da aka ciyar cikin hajji tana daidai da dirhami dubu)

وقال   :

«الحاجّ والمعتمر وفد الله، ويحبوه بالمغفرة ».

7- amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce:

(mahajjaci da mai umara bakin Allah ne, zai masa kyauta da gafara)

ـ عن الإمام الباقر أو الإمام الصادق   :

«إنّ إبراهيم أذّن في الناس بالحجّ ، فقال : أيّها الناس ، إنّي إبراهيم خليل الله، إنّ الله أمركم أن تحجّوا هذا البيت فحجّوه ، فأجابه من يحجّ إلى يوم القيامة ، وكان أوّل من أجابه من أهل اليمن ».

8- daga Imam Bakir ko Sadik (as):

(lallai Ibrahim ya yi yekuwar wajabcin hajji cikin mutane sai ya ce: yaku mutane, lallai ni Ibrahim masoyin Allah, lallai Allah ya umarceku da ku ziyarci wannan daki, sai wanda zai hajji ranar kiyama ya amsa kiransa, farkon wanda ya amsa masa ya kasance wani mutum daga mutanen kasar yaman).

 

وقال الإمام الصادق   :

«من حجّ حجّتين لم يزل في خير حتّى يموت ، ومن حجّ ثلاث حجج لم يصبه فقر أبدآ».

9- daga Imam Sadik (as) (duk wanda ya ziyarci dakin Allah ba zai gushe ba cikin alheri har zuwa mutuwarsa, duk wanda ya ziyarci dakin Allah sau uku talauci ba zai taba shafar shi ba).

وعنه   :

«ما رأيت أسرع غنىً ولا أنفى للفقر من إدمان حجّ البيت ».

10- daga gare shi amincin Alah ya kara tabbata gare shi:

(banga wani abu da yake saurin kawo wadata ba da saurin korar talauci ba daga dawwamar ziyartar dakin Allah).

ولمّا سأله إسحاق بن عمّار وقال : إنّي قد وطّنت نفسي على لزوم الحجّ كلّ عام بنفسي أو برجل من أهل بيتي بمالي ، فقال الإمام الصادق   : «وقد عزمت على ذلک ؟»، قال إسحاق : نعم . فقال  : «فإن فعلت ذلک فأيقن بكثرة المال ، وأبشر بكثرة المال ».

11- lokacin da Isha'k bn Ammar ya tambaye shi ya ce: lallai ni na taskace kaina kan lazimtar zuwa dakin Allah kowacce shekara da kaina ko kuma da wani mutum daga mutanen gidana da dukiyata, sai Imam Sadik (as) ya ce: hakika ka yi azama kan hakan? Sai Is'hak ya ce: na'am.

Sai Imam (as) ya ce: idan ka aikata haka to ka samu yakini kan yawaitar dukiya, ka yi bushara da yawaitar dukiya.

 

وعن مولانا زين العابدين  7 :

«حقّ الحجّ أن تعلم أنّه وفادة إلى ربّک ، وفرار إليه من ذنوبک ، وبه قبول توبتک وقضاء الفرض الذي أوجبه الله عليک ».

12- daga shugabanmu Zainul Abidin (as):

(hakkin hajji shi ne ka sani cewa lallai shi hajji ziyara ce zuwa ga ubangijinka, guduwa ne daga zunubanka zuwa gare shi, da shi ne ake karbar tubanka da sauke farilla da Allah ya wajabta kanka.

 

وقال أمير المؤمنين عليّ  7 :

«وحجّ البيت والعمرة ، فإنّهما ينفيان الفقر، ويكفّران الذنب ، ويوجبان الجنّة ».

13- sarkin muminai Ali (as) ya ce:

(ku ziyarci dakin Allah da umara, lallai su biyun suna korar talauci, sun kankare zunubi, suna wajabta aljanna).

 

وعن الإمام الصادق   لمّا قال له عبد الرحمن : إنّ اُناسآ من هؤلاء القصّاص يقولون : إذا حجّ رجل حجّة ثمّ تصدّق ووصل كان خيرآ له ، فقال   :

«كذبوا، لو فعل هذا الناس لعطّل هذا البيت ، إنّ الله عزّ وجلّ جعل هذا البيت قيامآ للناس ».

14- daga shugabanmu Sadik (as) lokacin Abdur-Rahman ya ce  masa: lallai wasu mutane daga wadannan masu kissoshi suna cewa: idan mutum ya je hajji sau daya sannan yi sadaka ya sadar da zumunci ya kasance alheri gare shi, sai Imam ya ce: karya suke da mutane za su aikata haka da wannan gida ya tozarta an daina ziyartarsa, lallai Allah mai girma mabuwayi ya sanya wannan gida ma'aunin ingancin adddini ga mutane).

وقال   :

«لو عطّل الناس الحجّ لوجب على الإمام أن يجبرهم على الحجّ إن شاؤوا وإن أبوا، لأنّ هذا البيت إنّما وضع للحجّ ».

15- amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce:

(da mutane za su yi watsi da zuwa hajji da ya zama wajibi kan Imami ya tilasta su kan hajji ko sun ki ko sun so, lallai wannan daki kadai an sanya shi ne ga mutane).

وقال رسول الله  :

«يا عليّ، كفر بالله العظيم من هذه الاُمّة عشرة : ... ومن وجد سعة فمات ولم يحجّ ».

16- manzon Allah (s.a.w) ya ce: (ya Ali mutane goma daga cikin wannan al'umma sun kafircewa Allai mai girma……da wanda ya samu yalwa sai ya mutu bai je hajji ba).

 

A wannan waje abin da ake nufi da kafirci kamar yadda Allah madaukaki ya zo a wannan ayar tab hajji:

(وَمَنْ كَفَرَ فَإنَّ اللهَ غَنِيٌّ عَنِ العَالَمِينَ ) ،

Duk wanda ya kafirce lallai Allah mawadaci ne daga talikai.[5]

 

Shi ne kafirci na aiki wanda ke wajabta fasikantar mutum.

وعنه  :

sai ya dinga jinkirta zuwa hajji har ya mutu Allah zai tashe shi ranar kiyama bayahude ko banasare)

وقال الإمام الصادق  :

«من مات ولم يحجّ حجّة الإسلام ، ولم تمنعه من ذلک حاجة تجحف به ، أو مرض لا يطيق الحجّ من أجله ، أو سلطان يمنعه ، فليمت إن شاء يهوديآ وإن شاء نصرانيآ».

18- Imam Sadik (as) ya ce: (duk wanda ya mutum bai je hajjin wajibi ba, sannan ba wani uzuri da ya hanashi zuwa, ko kuma ciwo da ba zai iya samun damar zuwa ba sakamakonsa, ko wani sarki da ya hana shi, to in ya so ya mutu bayahude ko banasare)

وعن الصادق ، عن أبيه  ، قال  :

«قال رسول الله  9: للحاجّ والمعتمر إحدى ثلاث خصال : إمّا أن يقال له : قد غفر لک ما مضى وما بقي . وإمّا أن يقال له : قد غفر لک ما مضى ، فاستأنف العمل . وإمّا أن يقال له : قد حفظت في أهلک ووولدک ، وهي أحسنهن ».

19- daga Sadik (as) daga babansa (as) ya ce:

(manzon Allah {s.a.w} ya ce: mahajjaci da mai umara suna da abubuwa uku: ko dai ace masa: an yafe maka abin da ya gabata da wanda ya wanzu, ko kuma ce masa, an yafe maka wanda ya gabata, yanzu ka niyyaci sabon aiki, hakika an kiyaye ka cikin iyalanka da `ya`yanka ita ce mafi kyawunsu.

 

Shin kuwa ka san abin da barin zuwa aikin hajji ke haifarwa ga wanda yake da ikon zuwa?

 

قال أبو عبد الله الصادق  ، في قوله تعالى : (وَمَنْ كَانَ فِي هَذِهِ أعْمَى فَهُوَ فِي الآخِرَةِ أعْمَى وَأضَلُّ سَبِيلا) ، قال  :

«نزلت في مَن يسوّف الحجّ حتّى مات ولم يحجّ ، فعمي عن فريضة من فرائض الله».

 

20- Abu Abudllah Sadik (as) yana cewa cikin fadinsa madaukaki: {duk wanda ya kasance makaho cikin wannan duniya to shi lahira zai tashi makaho da mafi batan hanya}[6]

Ya ce: wannan aya ta sauka ne kan wanda yake jinkirta zuwa aikin hajji har sai da takai ga ya mutu bai je ba, sai ya makanta daga barin farilla daga farillan Allah.

Sannan ma'anar (yasuwwuful hajji) jinkirta hajji kamar yadda ya zo cikin wata riwayar daban ma'anar hajjin wajibi, yana mai fadin da sannu zanje hajji shekara mai zuwa ya yi ta jinkirtawa har sai mutuwa ta riskeshi.

 

وعن مولانا الصادق  ، قال  :

«من أراد الحجّ فتهيّأ له فحرمه ، فبذنبٍ حُرِمه ».

21- daga shugabanmu Sadik (as) ya ce: (duk wanda ya nufi zuwa hajji sannan ya yi tanadi don hajjin sai kuma ya zama ya haramtu daga hajjin, to sakamakon wani zunubi ya sanya ya haramtu daga hajji.

Wannan fa kenan ga wanda ya yi tanadi ya shirya domin hajji kenan, ya kuma ga wanda ya gafala daga hajjin kwata-kwata, zuciyarsa ta raya masa barin hajji da jinkirta zuwa da burace burace?

Sannan abin da ake nufi daga kariya cikin iyalansa kamar yadda ya zo ckin riwaya Kulaibu bn Mu'awiyatu.

قال : «قلت لأبي عبد الله : شيعتک تقول : الحاجّ أهله وماله في ضمان الله، ويخلف أهله ، وقد أراه يخرج فيحدث على أهله الأحداث ؟ فقال : إنّما يخلفه فيهم بما كان يقوم به ، فأمّا ما كان حاضرآ لم يستطع دفعه فلا».

22- ya ce: na cewa Abu Abdullah (as) `yan shi'arka suna cewa: mahajjaci dukiyarsa da iyalansa suna cikin laminin Allah, zai bar iyalansa, hakika ina ganin yana fita sai wasu abubuwa su faru kan iyalansa? Sai ya ce: hakika cikinsu ya halifantar da wanda zai kasance zai tsayu da shi, amma abin da ya kasance halarce bai iya tunkude shi ba to babu matsala.

Na'am…su riwayoyin Ahlil-baiti sashensu yana fassara sashe, kamar misalin kur'ani mai girma da ba'arinsa ke bayanin ba'ari, su zantukansu haske ne wasiyyarsu takawa ce, aikinsu alheri, dabi'arsu karamci, al'adarsu Ihsani, da iyalan Muhammad ake sanin daidai, a gidajensu wahayi ya sauka.

Zamu kara komawa kan maudu'inmu mu ce: ibada cikin shari'a saukakakkiya ta kasu zuwa kashi biyu:

1-ibadar aiki: kamar misalin sallah da azumi.

2-ibadar madiya: kamar kumusi da zakka.

Shi hajji shi ibada ne kwaya daya wacce ta tattaro kaso biyun tare da juna, shi hajji iabada ce ta aiki, sakamakon abin da yake tattare cikinsa daga ayyuka kamar dawafi da sa'ayi, kuma hajji ibada ce madiyya: sakamakon abin da ya tattaro daga guzurin ciyarwa tafiya da dawowa da hadaya da makamantan haka. mamaki, shin wane ne yake da wannan babban taro na duk duniya na shekara-shekara? Ya zama wajibi ga kowanne musulmi wanda ya yi imani da shari'ar muhammadiya tsantsa ya kamata ya ji wannan nauyi a kansa dangane da wannan babban taro fitacce, sai ya yi amfani da wannan dama domin yada addinin muslunci mai karkata ga shiriya da kuma tabbatar da haduffansa tsarkaka cikin duniya don samar da fahimta kan matsalolin musulmai da warware su, lallai wannan babban taro yana da rahama babba ga musulmai, cikinsa akwai amfanunnuka ga mutane, lallai shi ne mafi alheri dalili kan girmamar muslunci da hukumrsa, da kasantuwarsa mafi falalar shari'o'I shi ne mai shafe sauran addinai da mazhabobi mai galaba kan hukumomi da bana muslunci ba, hakika yan mulkin mallaka sun fahimci haka da dukkanin rundunoninsu na gabas da yamma cikin wannan hakika ta babban taron hajji na shekara-shekara, shi ya sanya ma zaka samesu dare da rana suna shirya makirce-makirce suna dasa guba mai halakarwa, suna yada wayewarsu mara tushe da halayensu lalatattu tsakankanin musulmai domin raba aikin hajji da abin da ya kunsa na asali, domin musulmai su tsaya iya zahirin muslunci da zahirin hajji, sai su yan mulkin mallaka su samu damar yin iko kan ma'anonin hajji da hakikarsa ta hanyar munafukan karnukan farautarsu maciya amanar musulmai, ta yanda sace dukiyar musulmai ta dabi'a kamar fetur da sauransu zasu saukaka gare su, domin idanunsu su yi bacci cikin kwanciyar hankali da ni'ima ta hanyar amfani da musulmai gama gari wanda basu san abin da suke ba, sai dai cewa haihata haihata faufau, lallai farkawar duniyar da ruhin muslunci ya riga ya yadu cikin gangar jikin musulmai, muslunci ya dawo kamar yadda ya kasance tun farkon da'awarsa, hakika Allah ya yiwa musulmai bushara da cewa zai gadar da kasa ga bayinsa nagargaru, sai suka kwabe barci daga kwarmin idanuwan yan mulkin mallaka da girman kan duniya, dole kaddara ta amsa kira, dole ne kaidi da sasari su karye, dole duhu ya yaye, dole ne gaskiya tai nasara, ashe asubahi ba kusa take ba? Na'am wallahi lallai asubahi kusa take.

Wannan kenan, ta yiwu mu tsinkayi hikima da falsafar hajji a takaice karkashin ayoyin hajji cikin kur'ani mai girma, lallai shi Allah matsarkaki madaukaki ya ce:

 (لِيَشْهَدُوا مَنَافِعَ لَهُمْ ) .

Domin su halarci alfanu gare su.[7]

Bai zai yiwu a iyakance wannan amfanoni ba a kewaye da dukkaninsu, shin amfanonin tattalin arziki ne ko sakafa da siyasa dukkanin abin da taken unwanin amfanonin duniya kai hatta na nafsu  da na ruhi da lahira yake dabbakuwa a kansa, hakika a wasu lokuta amfanonin madaukaka wadanda suke bijira kan bukatu mahajjaci na yawaita alhalin shi yana shiri domin mafi falalar tafiya cikin rayuwa, saika gan shi yana kwadayi kan bahasi cikin ma'anonin shari'ar muslunci ga dukkanin abin da yake giftawa ta gefansa, zai tsinkayi tasirin da muslunci ke sanyawa cikin zukata daga sihiri mai daukar hankali da `yan'uwantaka ta gaskiya, wannan amfani ne daga amfanonin cikin aikin hajji, lallai mahajjaci yana riskar ma'anar fadinsa madaukaki:   

 (إنَّمَا المُؤْمِنُونَ إخْوَةٌ ).

Kadai dai muminai `yan'uwan juna ne.[8]

Ma'anar `yan'uwantakar muslunci na yayewa gare shi a lokacin aikin hajji yayin da a mahallin aikin hajji al'ummu da jinsi daban-daban da launukan fata mabanbanta da yaruka masu sabani da juna da mabanbantan halaye suke cudanya da juna, sai dai cewa mahajjaci na ganin `yan'uwantakar muslunci daga dukkanin daya daga cikinsu duk yanda yarensa yakai da banbanta da nesantar garinsa, a wannan lokaci sai ya riski abin da ake bari cikin zukata daga sabo da juna da kauna da soyayya da `yan'uwantaka ta gaskiya, muslunci ya hada tsakanin zukatansu, Akida ta `yan'uwantu tsakanin zukatansu, riko da igiyar hadin kan muslunci ya bayyana da mafi kyawun sura, lallai hadin kan da yake dawwamuwa da dawwamar rayuwa kai har bayan mutuwa, shi ne hadin kai na addini, hadin kai na akida zurfaffa, babu wata akida da tafi akidar muslunci zurfafa.

 (لَوْ أنفَقْتَ مَا فِي الأرْضِ جَمِيعآ مَا ألَّفْتَ بَيْنَ قُلُوبِهِمْ وَلَكِنَّ اللهَ ألَّفَ بَيْنَهُمْ )

Da zaka ciyar da baki dayan abin da ke cikin kasa da baka hada tsakanin zukatansu ba sai dai cewa Allah ya hada tsakaninsu.[9]

Haka ne, lallai hajji yana daga cikin rukunan muslunci, hakika sura guda daga kur'ani ta kebanta da sunansa, hakika an ambaci hajji cikin kur'ani a wurare goma, wuri tara ya zo da lafazin (Hajji) da wasalin fataha ga harafin hakarami daya kuma ya zo da lafazin (Hijju baitulllahi) dukkan biyun daga asali daya suke.

Hajji da fataha-yana da ma'anar ziyara, sannan da wasalin kasara yana da ma'anar sakamakon ziyara da akai niyya, da wani bayanin kuma lafazin farko masdari ne na (Hijaju) na biyu sunan masdari ne.

Abin da yake wajibi kan mutane shi ne hijju baitullah ai ziyara abar nufa da kudurcewa, gundarin niyya ziyara kadai bai isarwa, hajji da fataha sharen fagen hijju da kasara ce, lallai ita niyya da kuduri na zuci share fage ne ga aiki da ibadoji.

Hajji a cikin lugga yana zuwa kan ma'anoni da zai yiwu a nufe su cikin hajji da isdilahin da yake zuwa da ma'anar ziyartar dakin Allah mai alfarma, hajji yana zuwa da ma'anar: 

  1-nufar ziyara ko yawaitata zuw aga wanda ya nufi girmama sh, mutane cikin ziyartarsu ga dakin Allah suna nufar ubangijin dakin ne domin girmama ibadojin sa, lallai girmama ibadojin Allah yana daga takwar zukata.

2-kamewa, mai kudurin ziyara zuwa ga Allah cikin tafiyarsa ta malakutiyya ya zama wajibi kansa ya kame daga dukkanin koma bayan Allah ya yi watsi da dukkanin abin da bai da dangantaka tare da Allah matsarkaki, hatta nafsu dinsa da take tsakanin geffansa, har ya samu ya kaiwa ga mukamin fana'i cikin Allah, ya cika samuwarsa da shauki da soyayya da kaunar ga Allah Azza wa Jalla.

3- gabata, sai ya gabata zuwa ga dakin Allah kuma dakin mutane da tsarkakakkiyar niyya da imani da takwa da iklasi.

4- galaba da hujja, duk wanda ya sanya kafarsa cikin tafarki madaidaici zai galaba kan nafsu mai umarni da mummuna, zai galaba kan shaidanun aljannu da na mutane, zai galaba kan duniya mai rudarwa da hujja mai rusa karya da dalili yankakke.

5- yawaitar shige da ficen mutane kan dakin Allah, domin mutane ya taru tare da mutane cikin kidaitattun kwanaki cikin taro na duk duniya, domin ya nemi tsari daga wurin Allah daga sharrrin mai waswasi mai buya, domin ya kai ga mukami ceto wurin sarki mai ikon yi.

Mafi alherin dalili da hujjar muslunci da dacewarsa, shi ne (Hajjin muslunci) wanda ya wajaba kan dukkanin wanda ya samu ikon zuwa cikin tsawon rayuwa sau daya.

Kamar yanda (Umratu islam) ita take matsayin ziyara wacce cikinta akwai raya kauna da soyayya da tacewa, ita ma share fage ne domin kammala hajji da kamalarsa.

Daki mai alfarma ka'abar musulmai ne alkibilarsu ne wurin dawafinsu ne, hakika an ambace shi cikin kur'ani mai girma har wuri goma sha shida. A wurare biyu ubangijinmu yana danganta shi ga kansa cikin fadinsa madaukaki ga lokacin da yake magana da Ibrahim badadin Allah (a.s)   

 (وَطَهِّرْ بَـيْتِي ).

Ka tsarkake dakina.[10]

Kuma yana magana da shi tare da Isma'il hadayar Allah:

(أنْ طَهِّرَا بَيْتِي ).

Ku tsarkake dakina.[11]

A wani wurin kuma Ibrahim badadin Allah ya danganta dakin zuwa ga ubangijin sa, cikin fadinsa:

(رَبَّـنَا إنِّي أسْكَـنتُ مِنْ ذُرِّيَّتِي بِوَادٍ غَيْرِ ذِي زَرْعٍ عِنْدَ بَيْتِکَ المُحَرَّمِ ) .

Ya ubangijina lallai ni na tsugunar da zuriya ta cikin wani kwazazzabo wanda ba ma'abocin shuka ba wurin dakin mai alfarma.[12]

A wurare uku kuma ya danganta shi zuwa ga mutane:

 (إنَّ أوَّلَ بَيْتٍ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكآ وَهُدىً لِلْعَالَمِينَ ) .

1-Lallai daki na farko da aka sanya don mutane shi ne wanda yake a bakkatu mai albarka da shiriya ga mutane.[13]

 (جَعَلَ اللهُ الكَعْبَةَ البَيْتَ الحَرَامَ قِيَامآ لِلنَّاسِ ) .

2- Allah ya sanya ka'aba dakin mai alfarma ma'aunin addini ga mutane.[14]

 (وَإذْ جَعَلْنَا البَيْتَ مَثَابَةً لِلنَّاسِ وَأمْنآ) .

3-Yayin da muka sanya dakin mafaka ga mutane da aminci.[15]

 

Kalmar (Masabatu) a luggance tana da ma'anonin: mafaka,wurin tuba, wurin fadakuwa, makoma, matsaya, mashaya, dukkanin wadannan ma'anoni suna tajalli cikin hajji cikin dakin Allah mai alfarma.

Ita Kalmar (Baitu) tana nufin wurin hutawar gangar jiki, sannan a wani lokaci ta kan kasancewa wurin hutun ruhi, su mutane cikin dakin Allah suna cikin hutu ruhi dana badini.

Amma dangane da ragowar wuraren hakika an ambaci Kalmar Baitu domin ishara zuwa ga dakin shi ne dakin Allah dakin mutane, kamar yanda ya zo cikin fadinsa madaukaki:

 (فَـلْـيَـعْـبُدُوا رَبَّ هَذَا الـبَـيْتِ ).

Su bautawa ubangijin wannan dakin.[16]

Sannan shi danganta dakin zuwa ga Allah dangantawa don a daukaka dakin.

Shi ruhi a aikin hajji yana cikin ni'ima da hutu, cikin yunkuri mutumtaka na motsin yan adamtaka da tsayuwar mutane ruhi yana tsarkaka daga damfaruwa da duniya. Shi ruhi yana cikin hajjin rayayyen dakin Allah, yantaccen daki domin bautar ubangijin daki, yana komawa zuwa ga ubangijinsa cikin rayuwar mutumtaka ta ubangiji, cikin taro na shekara-shekara ruhi na tsaya farfajiyar ubangijin sa, domin tsara al'amarinsa na kai da jama'a, da na siyasa da sakafa da tattalin aziki da tsari, yana komawa makomar gaskiya na Allah daga hatsarurrukan shirka da bata da son kai, yana shan ruwa domin kishitwarsa domin kosar kishinsa na ma'arifofi da Asraran halitta da ilimummukan Allah, ruhi yana mai tuba daga zunuban da ya aikata da laifuka da sabo,da fadaka da farkawa daga gafala da rafkana, domin Allah ya sanya wannan daki mafaka ga mutane da aminci da shiriya da rahama da albarka.

Kamar yanda aka gina ka'aba kan kafafuwa hudu haka ma ta miku cikin littafin Allah kan asasi guda hudu:

1-domin su halarci amfanoni gare su.

2-mafaka domin mutane.

-ma'aunin addini ga mutane.     3

4-shiriya kuma albarka.

Bayan hallara da halarta, da mafaka da ma'anoninta, mutane za su tsaya domin Allah, wannan wa'azi e na kur'ani:

 (إنَّمَا أعِظُكُمْ بِوَاحِدَةٍ أنْ تَقُومُوا للهِ مَثْنَى وَفُرَادَى ) .

Kadai ina muku wa'azi da kalma guda daya ku tsaya domin Allah biyu-biyu da daidaiku.[17]

Ma'ana tsayuwa daidaiku da jama'a-jama'a, wannan tsayuwa don Allah tana tajalli cikin ayyukan hajji, cikinta akwai shiriyar shari'a da halitta, cikinta akwai albarkokin sammai da kasa, cikin misalin wannan taro, izza muslunci tana bayyana da karfin musulmi da girmamarsu, da zamu koma ga asalin hajji cikin addinin muslunci madidaici.

Hajji tsayuwa ce ga mutane domin neman kubuta daga sharrin mai buya wanda yake wasiwasi cikin kirazan mutane daga aljannu da mutane, hajji shi ne tsantsar muslunci, ayyukansa kuma tunani da motsi da tashi fadi da gwagwarmaya da tsayuwa domin mutane domin assasa daular muslunci ta duk duniya, mafaka da mutane aminci da shiriya da albarka gare su domin su halarci amfanoni gare su, su ambaci sunan Allah, domin su koyi kaka za su sadu zuwa ga Allah matsarkaki, yaya rayuwa yaya mutuwa.

Ya kamata mahajjaci ya tsinkayi sirrikan hajji ya tsaya kan ma'anonin motsi da zama cikin hajji ya kuma san hakikar Ihrami da dawafi hadaya da saisaye da kwas da sallah da sa'ayi cikin Arafat da mash'arul haram da bacci a mina da jifan shaidan, ya kuma kai ga mukamin bauta da `yanci, ya kasance bawan Allah yantacce daga wanin Allah, yantacce daga son kai da nafsul ammara da dawagitai da mutane da shaidanu da dukkanin koa bayan Allah matsarkak-ya zama dole ayi hijira daga wanin Allah zuwa ga Alla Azza wa Ala cikin sairi da suluki zuwa ga Allah cikin ziyartar dakin Allah mai alfarma, ku taho ku taho zuwa ga ziyarar dakin Allah, Allah da manzon sa da Ahlin gidan manzon sa su yarda su karba hakama sahabbansa masu karamci.

Babu laifin idan mun kawo wasu ba'arin sabubba da illoli da hikimomi da suka zo cikin hadisai da riwayoyi madaukaka:   

 

قال أمير المؤمنين عليّ بن أبي طالب  7 في نهج البلاغة  :

«وفرض عليكم حجّ بيته الحرام الذي جعله قبلةً للأنام ، يردونه ورود الأنعام ، ويألهون الله ولوه الحمام ، جعله سبحانه علامة لتواضعهم لعظمته ، وإذعانهم لعزّته ، واختار من خلقه سماعآ أجابوا إليه دعوته ، وصدّقوا كلمته ، ووقفوا مواقف أنبيائه ، وتشبّهوا بملائكته المطيفين بعرشه ، يحرزون الأرباح في متجر عبادته ، ويتبادرون عنده موعد مغفرته ، جعله سبحانه وتعالى للإسلام علمآ وللعائذين حرمآ...».

23- sarkin muminai Ali bn Abi dalib (a.s) cikin Nahjul Balaga yana cewa: kuma Allah ya farlanta ziyartar dakinsa kanku wanda ya sanya shi Alkibla ga mutane suna gangarowa gare shi gangarowar dabbobin ni'ima, suna dimauta dimautar irin dimautar tattabara, kuma Allah ya sanya shi alama ga tawali'unsu mika wuya ga buwayarsa, cikin halittunsa ya zabi masu gaza kunnuwa da suka amsa kiransa, suka kuma gasgata kalmarsa, suka tsaya matsayun annabawansa, suka kamantu da Mala'iku masu dawafi daura da Al'arshinsa, suna kwasa riba cikin kasuwancin bautarsa, suna gaggawa wurin samun gafararsa, Allah matsarkaki ya sanya shi Alami ga muslunci ya kuma sanya shi mafakar masu neman kariyarsa. 

وعن مولانا الإمام الرضا  كما في بحار الأنوار :

«علّة الحجّ : الوفادة إلى الله عزّ وجلّ ، وطلب الزيادة والخروج من كلّ ما اقترف ، وليكون تائبآ ممّا مضى ، مستأنفآ لما يستقبل . وما فيه من استخراج الأموال ، وتعب الأبدان ، وحظرها عن الشهوات واللذّات ، والتقرّب في العبادة إلى الله عزّ وجلّ ، والخضوع والاستكانة والذلّ ، شاخصآ في الحرّ والبرد والأمن والخوف ، ثابتآ في ذلک دائمآ، وما في ذلک لجميع الخلق من المنافع والرغبة والرهبة إلى الله عزّ وجلّ ، ومنه ترک قساوة القلب وخساسة الأنفس ونسيان الذكر وانقطاع الرجاء والأمل ، وتجديد الحقوق وحظر الأنفس عن الفساد ومنفعة من في المشرق والمغرب ومن في البرّ والبحر، وممّن لا يحجّ ، من تاجر وجالب وبائع ومشترٍ وكاتب ومسكين ، وقضاء حوائج أهل الأطراف والمواضع الممكن لهم الاجتماع فيها، كذلک ليشهدوا منافع لهم ».

24-daga maulana Rida (a.s) kamar yanda ya zo a cikin littafin Biharul-Anwar: dalilin Hajji, bakunta zuwa ga Allah Azza wa Jalla, da kuma neman dadi da kari da fitar daga dukkanin abin da mutum ya aikata, domin ya kasance mai tuba daga abin da ya gabata, mai sake lale ga abin da zai zo nan gaba, tare da abin da yake cikinsa daga fitar da dukiya da wahalhalu na jiki da haramta jiki sha'awe-sha'awe da dadi, da neman kusanci da ibada zuwa ga Allah Azza wa Jalla, da kankan da kai da mika wuya da kaskantar da kai, yana mai bayyanuwa cikin zafin rana da sanyi da aminci da tsoro, yana mai tabbatuwa cikin haka kowanne lokaci, tare da abin da ke cikin hakan ga dukkanin mutane daga amfanoni da kwadayi tsoro zuwa ga Allah Azza wa Jalla, daga cikinsu akwai barin kekashewar zuciyar da lalacewar rayuka da mantawa da zikiri da yanke fata da sa rai, da sabunta hakkoki da hana rayuka barna da amfani da wanda ke gabas da yamma da doran kasa da tafki, da kuma wanda bai yin hajji daga attajiri da mai jalabi da mai sayarwa da mai saya da matalauci, da biyan bukatu ma'abota geffa da wurare wadanda za su iya haduwa cikinsa domin su shaida amfanoni gare su.

وعن الفضل بن يونس ، قال : «أتى ابن أبي العوجاء ـالزنديق ـ مولانا الإمام الصادق  ، فجلس إليه في جماعة من نظرائه ، ثمّ قال له  : يا أبا عبد الله، إنّ المجالس أمانات ، ولا بدّ لكلّ من كان به سعال أن يسعل ، فتأذن لي في الكلام ؟

An karbo daga Falalu bn Yunus, ya ce: Ibn Abul Auja'I zindiki ya zo wurin-maulana Imam Sadik (a.s) sai ya zauna wurinsa cikin wasu jama'a daga misalansa, sannan ya ce: ya baban Abdullah, lallai majalisai amanoni ne, ya zama dole ga wanda yake san yin tari ya yi tarinsa, shin ka yi mini izinin yin magana? 

فقال الصادق  : تكلّم بما شئت .

Sai Imam Sadik (a.s) ya ce fadi abin da kake son fadi.

فقال ابن أبي العوجاء: إلى كم تدوسون هذا البيدر، وتلوذون بهذا الحجر، وتعبدون هذا البيت المرفوع بالطوب والمدر، وتهرولون حوله هرولة البعير إذا نفر، من فكّر في هذا أو قدّر، علم أنّ هذا فعلٌ أسّسه غير حكيم ولا ذي نظر، فقل ، فإنّک رأس هذا الأمر وسنامه ، وأبوک اُسّه ونظامه ؟

Sai Ibn Abul Auja'i ya ce: har zuwa yau she zaku cigaba da tattake wannan masussuka, kuna fakewa da wannan dutsen, kuna bautawa wannan daki da aka daga ginin da dafaffen yunbu da kasa, kuna sassarfa daura da shi irin sassarfar rakumi idan ya gudu, duk wanda ya yi tunani cikin wannan ko ya kaddara zai san cewa wannan aiki harsashinsa babu hikima babu zurfin tunani, kace, kai jagaban wannan lamari kuma tozansa, mahaifinka shi ne asasinsa da tsarinsa?

فقال الصادق  7: إنّ من أضلّه الله وأعمى قلبه استوخم الحقّ فلم يستعذ به ، وصار الشيطان وليّه ، يورده مناهل الهلكة ثمّ لا يصدره ، وهذا بيت استعبد الله به خلقه ، ليختبر طاعتهم في إتيانه ، فحثّهم على تعظيمه وزيارته ، وقد جعله محلّ الأنبياء وقبلة المصلّين له ، فهو شعبة من رضوانه ، وطريق تؤدّي إلى غفرانه ، منصوب على استواء الكمال ، ومجتمع العظمة والجلال ، خلقه الله قبل دحو الأرض بألفي عام ، وأحقّ من اُطيع فيما أمر وانتهى عمّا نهى عنه ، وزجر الله المنشئ للأرواح والصور».

Sai Sadik (a.s) ya ce: lallai wanda Allah ya batar ya makantar da zuciyarsa zai ga munin gaskiya ba zai nemi tsari da shi ba, shaidan zai zama waliyinsa, zai gangarar da shi mashayun halaka sannan ba zai fitar da shi, wannan daki Allah ya bautar da bayinsa da shi, domin ya jarraba da'arsu cikin zuwar masu, sai ya kwadaitar da su kan girmama shi da ziyartarsa, hakika ya sanya shi mahallin annabawa kuma Alkiblar masallata gare shi, shi yanki daga yardarsa, hanya ce da zata kai ga samun gafararsa, an kafa shi kan daidaitar kamala, matattarar girma da jalal, Allah ya halicce shi gabanin shimfidar kasa da shekara dubu, mafi dacewar wanda akaiwa da'a cikin abin da ya yi umarni ya hanu daga barin abin da aka hane shi, Allah ya tsawatarwa mafarar ga ruhai da surori.

Wannan kenan, hakika na ambaci alamomin hajji da hikimar ibadun cikinsa, kamar yanda na ambaci tarihin Makka da Madina masu daraja cikin littafi da na sanya masa suna (Ma'alimul Makka wal Madina)

Ga hikimomin a takaice.

1-Ka'aba Alkiblar dukkanin mutane.

2-Alamar tawali'u ga mutane ga girmamarsa.

3-Gasgata matsayan annabawa.

4-Kamantuwa da Mala'iku masu dawafi.

5-Ilimin muslunci.

6-Haramin masu neman tsari.

7-Allah ya bautar da bayinsa da wannan daki domin jarraba su.

8-Mahallin annabawa.

9-Wani yanki daga yardar Allah.

10- Hanya da ta ke sadarwa zuwa ga gafarar Allah.

11- Bakunci zuwa ga Allah da neman kari

12- Fitar bawa daga dukkanin abin da ya aikata daga zunubai.

13-Cikin hajji akwai amfanoni ga dukkanin halittu daga wadanda suke aikin hajji da ma wadanda basa yi.

14- Cikinsa ya sanya haduwar mutane daga gabashi da yammaci.

15-Domin su san hadisan manzon Allah (s.a.w) da kufaifayinsa a ambace su ka da a mana da su.

16-Ahil-baiti (a.s) suna sanin wilyarsa.

17-Allah ya umarci Adamu da ya yi aikin hajji domin ya karbi tubansa.

18-Domin jarrabawa ga mutanen farko da na karshe.

19-Domin fitar da girman kai daga cikin zukata.

20-Ma'aunin ingancin addini ga mutane.

Ya zama tilas a tsarkake dukkanin niyya da aiki haka zalika aikin hajji.

عن الإمام الصادق  7 :

«الحجّ حجّان : حجّ لله وحجّ للناس ، فمن حجّ لله كان ثوابه على الله الجنّة ، ومن حجّ للناس كان ثوابه على الناس يوم القيامة ».

26-daga Imam Sadik (a.s) : hajji guda biyu ne: hajjin Allah da hajjin mutane, dukkan wanda ya yi hajji don Allah ladansa ya kasance kan Allah aljanna. Dukkan wanda ya yi hajji domin mutane ladansa ya kasance kan mutane ranar Alkiyama.

وعنه  :

«من حجّ يريد الله عزّ وجلّ لا يريد به رياءً ولا سمعة ، غفر الله له البتّة ».

27- daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata a gare shi: dukkan wanda yake nufin Allah Azza wa Jalla bai nufin riya da neman suna, Allah zai gafarta masa yanke.

وقال  في علامات ظهور الإمام المهدي :

«ورأيت طلب الحجّ والجهاد لغير الله... فكن على حذر، واطلب من الله النجاة ».

واعلم أنّ من تمام الحجّ معرفة الولاية ولقاء الإمام  7: (وَأتِمُّوا الحَجَّ

وَالعُمْرَةَ للهِ) .

28-Amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: cikin alamomin bayyanar Mahadi: (kuma ka ga neman hajji da jihadi ga wanin…ka kasance cikin taka tsantsan, ka nemi tsira daga Allah).

Kuma ka sani cewa daga cikar da kammalar hajji akwai sanin wilayarsa da haduwa da Imam (a.s) ku cika hajji da umara don Allah.[18]

عن الإمام الباقر  7 :

«تمام الحجّ لقاء الإمام ».

29- daga Imam Bakir (a.s) : cikar hajji na tare da haduwa da Imam.

وعن الإمام الصادق   في قوله : (لِيَقْضُوا تَفَثَهُمْ ) : «لقاء

الإمام ».

30-daga Imam Sadik (a.s) cikin fadinsa: {kuma su kare ibadarsu}[19]: ma'ana haduwa da Imam.

وقال  :

«إذا حجّ أحدكم فليختم حجّه بزيارتنا، لأنّ ذلک من تمام الحجّ ».

31-idan dayanku yaje hajji to ya hattama hajjin sa da ziyartarmu, domin hakan yana daga cikar hajji.

وقال أمير المؤمنين عليّ  :

«أتمّوا برسول الله  9 حجّكم إذا خرجتم إلى بيت الله، فإنّ تركه جفاء، وبذلک اُمرتم ، وأتمّوا بالقبور التي ألزمكم الله عزّ وجلّ حقّها وزيارتها، واطلبوا الرزق عندها».

32- sarkin muminai Ali (a.s) ya ce: ku cika hajjinku da manzon Allah idan kun fito zuwa ga dakin Allah, lallai barin hakan jafa'i ne, da hakan aka umarce ku, ku cika hajjinku da ziyartar kaburbura wadanda Allah Azza wa Jalla ya lazimta muku ziyartarsu, ku nemi arziki a wurin. 

وقال الإمام الباقر :

«إنّما اُمر الناس أن يأتوا هذه الأحجار فيطوفوا بها، ثمّ يأتوننا فيخبرونا بولايتهم ، ويعرضوا علينا نصرهم ».

33- Imam Bakir (a.s) ya ce: kadai dai an umarci mutane da su zo wajen wadannan duwatsu su kekkewaya su da dawafi, sannan su zo wurinmu su bamu labarin wilayarsu, su bijiro da taimakonsu kanmu.

Sannan kowanne abu yana ladubba-ma'ana kyawunta mu'amala aiki, haka ma hajji da ihrami da mahajjaci suna da ladubba.

قال الإمام الباقر :

«ما يُعبا بمن يؤمّ هذا البيت إذا لم يكن فيه ثلاث خصال : ورع يحجزه عن معاصي الله، وحلم يملک به غضبه ، وحسن الصحابة لمن صحبه ».

34-Imam Bakir (a.s) ya ce: ba a damu da wanda yake nufo wannan daki idan ba ya tare da abubuwa guda uku: tsantseni da yake hijabance shi daga sabon Allah, hakuri da yake mallakar fushinsa da shi, kyawun abokantaka ga wanda ya abokantake shi.

قال الإمام الصادق :

«إذا أحرمت فعليک بتقوى الله وذكر الله كثيرآ، وقلّة الكلام إلّا بخير، فإنّ من تمام الحجّ والعمرة أن يحفظ المرء في لسانه إلّا من خير، كما قال الله تعالى ، فإنّ الله عزّ وجلّ يقول : (فَمَنْ فَرَضَ فِيهِنَّ الحَجَّ فَلا رَفَثَ ) ».

35- Imam Sadik (a.s) ya ce: idan ka daura harami to ka kiyaye tsoran Allah da yawaita ambaton Allah, da karanta magana sai in alheri zaka fadi, lallai daga cikin cika hajji da umara mutum ya kiyaye harshensa face daga alheri, kamar yanda Allah madaukaki ya fadi, lallai Allah Azza wa Jalla yana cewa: {duk wanda cikinsu ya yi niyyar hajji to babu jima'i}.[20]

 

عن مالک بن أنس قال : حججت مع الصادق  7 سنة ، فلمّا استوت به راحلته عند الإحرام كان كلّما همّ بالتلبية انقطع الصوت في حلقه ، وكاد أن يخرّ من راحلته ، فقلت : يا بن رسول الله، ولا بدّ لک من أن تقول ؟ فقال  7 :

«يا ابن أبي عامر، كيف أجسر أن أقول : لبّيک اللّهم لبّيک ، وأخشى أن يقول عزّ وجلّ لي : لا لبّيک ولا سعديک »!!

36- daga Malik bn Anas ya ce: na yi aikin hajji tare da Sadik (a.s) a wata shekara yayin da ya daidaita kan abin hawansa yayin ihrami ya kasance duk sanda ya himmatu da fadin talbiya sai murya ta yanke cikin makogaronsa, ya kusa fadowa daga abin hawansa, sai na ce: ya dan manzon Allah shin ya zama dole gare ka sai ka fadi talbiya? sai ya ce: ya dan Abu Amir ta kaka zan yi tsaurin idon fadin: labbaika lahumma labbaika alhalin ina tsoran ka da Allah Azza wa Jalla ya ce mini: la labbaika wa la sa'adaika!!

 

Idan halin Ma'sumi ya kasance haka ya maganarmu da sauran mutane kuma?!!    

قال الإمام الصادق  7 :

«إذا اكتسب الرجل مالا من غير حلّه ثمّ حجّ فلبّى ، نودي : لا لبّيک ولا سعديک ، وإن كان من حِلّه فلبّى نودي : لبّيک وسعديک ».

37- Imam Sadik (a.s) ya ce: idan wani mutum ya tsiwirwiri kudi ya same su ba daga mahallinsu ba sannan ya je haddinsu da su ya fadi talbiya, za ayi kira: la labbaika wa la sa'adaika: idan kuma sun ksance na halal za ai kira: labbaika wa sa'adaika.

وعن رسول الله  ، قال  :

«من حجّ بمال حرام فقال : لبّيک اللهمّ لبّيک ، قال الله له : لا لبّيک ولا سعديک ، حجّک مردود عليک ».

38- daga manzon Allah (s.a.w) ya ce: duk wanda ya je aikin hajji da dukiyar haramun sannan ya fadi: labbaika, Allah zai ce masa: la labbaika wa la sa'adaika, an wurgo maka hajjinka kanka. 

وعن مولانا الإمام الرضا  :

«إنّما اُمروا بالإحرام ليخشعوا قبل دخولهم حرم الله وأمنه ، ولئلّا يلهوا ويشتغلوا بشيء من اُمور الدنيا وزينتها ولذّاتها، ويكونو جادّين فيما هم فيه ، قاصدين نحوه ، مقبلين عليه بكلّيتهم ».

39- daga maulana Imam Rida (a.s): kadai an umarce su da daura ihrami domin su samu tsoran Allah gabanin shigarsu haramin Allah da amincinsa, domin gudun ka da su yi wargi su shagaltu da wani abu daga lamurran duniya da adonta da dadinta, su kasance da gaske suke cikin abin da suke ciki, suna masu nufarsa da fuskanta kansa da dukkanin samuwarsu.

وعن مولانا الإمام الصادق   :

«إذا أردت الحجّ فجرّد قلبک لله تعالى من قبل عزمک من كلّ شاغل ، وحجاب كلّ حاجب ، وفوّض اُمورک كلّها إلى خالقک ، وتوكّل عليه في جميع ما يظهر من حركاتک وسكناتک ، وسلّم لقضائه وحكمه وقدره ، وودّع الدنيا والراحة والخلق ، وأخرج من حقوق تلزمک من جهة المخلوقين ، ولا تعتمد على زادک وراحلتک وأصحابک وقوّتک وشبابک ومالک ، مخافة أن يصير ذلک عدوّآ ووبالا، فإنّ من ادّعى رضا الله واعتمد على شيء صيّره عليه عدوّآ ووبالا، ليعلم أنّه ليس له قوّة ولا حيلة ولا لأحدٍ إلّا بعصمة الله وتوفيقه ، واستعدّ استعداد من لا يرجو الرجوع ، وأحسن الصحبة ، وراعِ أوقات فرائض الله وسنن نبيّه  9، وما يجب عليک من الأدب والاحتمال والصبر والشكر والشفقة والسخاء وإيثار الزاد على دوام الأوقات ، ثمّ اغسل بماء التوبة الخالصة ذنوبک ، والبس كسوة الصدق والصفاء والخضوع والخشوع ، وأحرم من كلّ شيء يمنعک من ذكر الله ويحجبک عن طاعته ، ولبّ بمعنى إجابة صافية زاكية لله عزّ وجلّ في دعوتک له متمسّكآ بالعروة الوثقى ، وطُف بقلبک مع الملائكة حول العرش كطوافک مع المسلمين بنفسک حول البيت ، وهرول هرولة من هواک ، وتبرّيآ من جميع حولک وقوّتک ، فاخرج من غفلتک وزلّاتک بخروجک إلى منى ، ولا تتمنّ ما لا يحلّ لک ولا تستحقّه ، واعترف بالخطايا بعرفات وجدّد عهدک عند الله بوحدانيّته ، وتقرّب إلى الله ذا ثقة بمزدلفة ، واصعد بروحک إلى الملأ الأعلى بصعودک إلى الجبل ، واذبح حنجرتي الهوى والطمع عند الذبيحة ، وارمِ الشهوات والخساسة والدناءة والأفعال الذميمة عند رمي الجمرات ، واحلق العيوب الظاهرة والباطنة بحلق رأسک ، وادخل في أمان الله وكنفه وستره وكلاءته من متابعة مرادک بدخولک الحرم ، وزر البيت متحقّقآ لتعظيم صاحبه ومعرفة جلاله وسلطانه ، واستلم الحجر رضآ بقسمته وخضوعآ لعزّته ، وودّع ما سواه بطواف الوداع ، وصَفِّ روحک وسرّک للقاء الله يوم تلقاه بوقوفک على الصفا، وكن ذا مروّة من الله تقيّآ أوصافک عند المروة ، واستقم على شرط حجّک هذا ووفاء عهدک الذي عاهدت به مع ربّک ، وأوجبته إلى يوم القيامة ».

40-an karbo daga shugabanmu Imam sadik (a.s) :

(idan ka yi niyya zuwa aikin hajji to ka karkade zuciyarka daga dukkanin abin da zai shagaltar dakai ta fuskanin azamarka domin Allah, hakama daga dukkanin hijabin mai hijabantarwa, ka fawwala baki dayan al'amuranka zuwa ga mahaliccinka, ka yi tawakkali da shi cikin baki dayan abin da yake bayyana daga motsinka da shirunka, ka mika wuya ga hukuncinsa da kaddararsa, ka yi bankwana da duniya da jin dadi da halittu, ka fitar daga hakkoki wadanda suke lazimtarka daga bangaren halittu, ka da ka dogara kan guzurinka da abin hawanka da sahabbanka da karfinka da samartakarka da dukiyarka domin gudun ka su zama makiyanka da azaba kanka, lallai wanda duk yayi da'awar yardar Allah ya dogara kan wani abu daban ba Allah ba zai mayar da shi makiyi da azaba, domin ya san lallai cewa babu tsimi babu dabara babu wani mutum face kariyar Allah da datarwarsa, ka yi tanadi tanadin wanda bai fatan komawa, ka kyawunta abokantaka, ka kiyaye lokutan farillan Allah da sunnonin annabinsa (s.a.w) da abin da ya wajaba kanka daga ladubba juriya da hakuri da godiya da tausayi da kyauta da fifita waninka cikin guzuri a tsawon lokuta, sannan ka wanke zunubanka da tatataccen ruwan tuba, ka tufata da tufafin gaskiya da tacewa da kankan da kai da kushu'i, ka haramtu daga dukkanin abin da zai hanaka ambaton Allah da kuma abin da yake  hijabanceka daga da'ar Allah, kayi talbiya da ma'anar tatacacciyar amsa kira tsarkakka domin Allah Azza wa Jalla cikin kiranka gare shi kana mai riko da karfaffiyar igiya, kayi dawafi da zuciyarka tare da Mala'iku daura da Al'arshi kamar dawafinka tare da musulmai daura da dakin Allah, ka yi sassarfa sassarfa daga gujewa son ranka, ka fita daga gafalarka da zamewar kafarka da fitarka zuwa Mina, ka da kai fatan abin da bai halasta gareka ba da abin da baka cancance shi ba, ka yi ikirari da kurakurai a Arafat ka sabunta alkawarinka wurin Allah da dayantuwarsa, ka nemi kusanci zuwa ga Allah kana ma'abocin yarduwa a Muzdalifa , ka hau da ruhinka wurin madaukakan halitta da hawanka zuwa ga dutse, ka yanka makogaron son rai da kwadayi yayin da kake yanka hadaya, ka yi jifa da sha'awe-sha'awe da kazanta da ayyuka munana yayin da kake jifan shaidan, ka aske aibobin zahiri da na badini da aske gashin kanka, ka shiga cikin amincin Allah da shingensa da labulensa da kiyayewarsa daga bibiyar muradanka da shigarka harami, ka ziyarci dakin ka'aba ka na mai tabbatarwa domin girmama ma'abocin dakin da sanin girmansa da mulkinsa, ka sumbaci dutsen yarda da kasonsa da mika wuya ga izzarsa, ka yi bankwana da koma bayansa da yin dawafin bankwana, ka tace ruhinka da badininka domin haduwa da Allah ranar da zaka hadu da shi da tsayuwarka a dutsen Safa, ka zama ma'abocin muru'a daga Allah kana mai takawa a wurin dutsen Marwa, ka daidaita kan sharadin hajjinka da cika alkawarinka wanda ka yi wa ubangijinka Alkawari da shi, ka wajabtu da shi har zuwa ranar kiyama.

Daga karshe wannan digo daga kogi cikin girman hajji, na nakashceka da wannan rukuni madaidaici da wannan haduwa mai girma, wacce musulman da suke da iko ke halartarsa duk shekara, domin shu shaida amfanoni gare su, domin su yi dawafi daura da daki mai alfarma, shin ya buya ga wani daga cikinsa daga daukaka da girmama? Shin yanzu ba za su dinga lura ba?

Tsarki ya tabbata gareka ya ubangijin talikai muna maka godiya ya Allah kan abin da kai ma'ana ni'ima daga ni'imar imani, kai kadai muke bautawa kuma kai kadai muke neman taimako daga gareka, ka shiryar damu tafarki madaidaici, kai mana gafara ranar addini, ka tashe mu cikin gayyar masu takawa tare da Muhammad da iyalansa tsarkaka.

Madalla mu nemi zuwa ziyarar daki mai alfarma daga Allah matsarkaki.

       Ga wata addu'a daga addu'o'in neman zuwa hajji

«اللهمّ ارزقني الحجّ الذي فرضته على من استطاع إليه سبيلا، واجعل لي فيه هاديآ، وإليه دليلا، وقرّب لي بُعد المسالک ، وأعنّي على تأدية المناسک ...».

Ya Allah ka azurtani hajji wanda ka farlanta shi kan wanda ya samu dma da iko zuwa gare shi, cikinsa ka sanya mini mai shiriyarwa, ka kuma sanya mini dalili zuwa gare shi, ka kusanto da nesantar hanyoyi gareni, ka taimake ni kan sauke ibadoji….[21]

 
[1]Alu imran:97

[2] Hajji:27

[3] Kisal : 253

[4] Hajji:27

[5] Alu Imran:97

[6] Isra'i:72

[7] Hajji:28

[8] Hujrat:10

[9] Anfal: 63

[10] Hajji:26

[11] Bakara:125

[12] Ibrahim:37

[13] Alu Imran:96

[14] Ma'ida:97

[15] Bakara:125

[16] Kuraish:3

[17] Saba'i:46

[18] Bakara:196

[19] Hajji:29

[20] Bakara:197

[21] Mafatihul jinan:461, munajatil dalabul hajji