فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS

 

Allah madaukaki cikin littafin sa mai girma yana cewa:

 (وَلْتَكُنْ مِنْكُمْ اُمَّةٌ يَدْعُونَ إلَى الخَيْرِ وَيَأمُرُونَ بِالمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ المُنْكَرِ وَاُوْلَئِکَ هُمْ المُفْلِحُونَ

Wata al'umma ta kasance daga gareku tana kira zuwa ga alheri tana hani da mummuna wadannan su ne rabautattu.[1]

 

Matsarkaki ya ce:

 (كُنْتُمْ خَيْرَ اُمَّةٍ اُخْرِجَتْ لِلنَّاسِ تَأمُرُونَ بِالمَعْرُوفِ وَتَنْهَوْنَ عَنِ المُنكَرِ).

Kun kasance mafi alherin al'umma da aka fitar domin mutane kuna umarni da kyakkyawa kuna hani da mummuna.[2]

 

Azza wa Jalla ya ce:

 (وَيَأمُرُونَ بِالمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ المُنْكَرِ وَيُسَارِعُونَ فِي الخَيْرَاتِ وَاُوْلَئِکَ مِنَ الصَّالِحِينَ ).

Kuma suna umarni da kyakkyawa suna hani da mummuna suna gaggawa cikin aikin alheri wadannan daga salihai suke.[3]

 

Mafi buwaya mai fadi ya ya ce:

(وَالمُؤْمِنُونَ وَالمُؤْمِنَاتُ بَعْضُهُمْ أوْلِيَاءُ بَعْضٍ يَأمُرُونَ بِالمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ المُنكَرِ)

Muminai maza da muminai mata sashensu masoya sashensu ne suna umarni da kyakkyawa suna hani da mummuna.[4]

 

Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna resheka ne guda biyu sa rassan addinin muslunci mai karkata zuwa ga gaskiya.

Ma'anar na farko: shi ne umarni da dukkanin ayyuka nagari masu kyawu wadanda Allah matsakaki ya neme su daga mutane muminai, kamar misalin farillai da wasunsu daga wajibai na shari'a.

An ce: ma'aruf : shi ne aiki mai kyau a hankali da shari'a wanda ya tattaru kan siffa mai rinjaya da ta ke kara masa kyawu ta kebanta da shi.

Ma'ana ta biyu: shi ne ya hanu daga baki dayan ayyukan da Allah madaukaki ya hana aikata su, haka ma daga dukkanin munana halaye da ,iyagun dabi'u da siffofi ababen zargi.

Wannan kuma bai kebantu da masu da addini da ma'abota ilimi kadai ba, bai wajibi kan dukkanin musulmi da musulma, kowa gwargwadon ikonsa da yanda zai iya, saboda kamar yanda ya zo daga madaukakin hadisi:  

«كلّكم راعٍ وكلّكم مسؤول عن رعيّته ».

1-dukkaninku masu kiwo ne kuma dukkanin ababen tambaya ne kana bin da aka baku kiwo.

Umarni da kyakkyawa da hani mummuna tare da ikon yinsu farillai ne biyu na wajibi daga Allah mabuwayi madaukaki, wajibi kan bawa ya canja munkari da zuciyarsa da harshensa da hannunsa, idan bai samu iko ba da hannu to da harshensa idan bai samu da harshensa to sai ya yi da zuciya wancananka shi ne mafi raunin imani.

Allah matsarkaki hakika ya sanya alamomi ga kyakkyawan aiki, haka ma ya sanyawa munkari alamomi, ya yi alkwari kan kyakkyawan aiki da shigar da ma'abocinsa aljanna gidan ni'ima, aljannoni da koramu ke gangara karkashinsu, yayi kuma alkawarin narko kan aikata munkari da shigar da ma'abocinsa wutar jahimu, lallai ita wuta ce mai babbaka mai fisga zuwa ga gashi, shi umarni da kyakkyawa da hani da mummuna basa kusanto da ajali basa yanke arziki bari suna kawo gyara cikin jama'a suna azurta mutane.

Kadai shaidan tsinanne da mataimakansa da kungiyarsa daga aljannu da mutane suna surantawa musulmi hatsaruka da tsoro cikin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, ta yiwu mai umarni da kyakkyawa da hani da mummuna ya hadu da wahalhaluda musibu sai dai cewa. Haihata-haihata, lallai hakan na daga abubuwa da shaidani yake kimsawa da zugar yan koransa fasikai da mataimakansa fajirai, ya zama dole a yake su ayi jihadi kansu, da galaba kansu da samun nasara daga Allah mai girma da daukaka, lallai shi ne mafi alherin mai taimako da tallafawa.

وعنه :

«إنّ الله عزّ وجلّ ليبغض المؤمن الضعيف الذي لا دين له ».

2-daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata a gare shi: (lallai Allah mai girma mabuwayi tabbas yana fushi da mumini rarrauna wanda babu addini gare shi.

فقيل له : وما المؤمن الذي لا دين له ؟ قال  :

«الذي لا ينهى عن المنكر».

Sai aka ce masa: wane ne mumini wanda babu addini gare shi? Sai ya ce: wanda ba ya hana aikata munkari.

 

Wannan kenan, duk da cewa shi mumini sai dai cewa ba ya hana aikata munkari shi mai raunin imani ne, bari dai bai kammalu ba cikin addininsa, bai da kammalallen addini.

 

وقال  :

«لا ينبغي لنفس مؤمنة ترى من يعصي الله فلا تنكر عليه ».

3- amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: (bai dace ga nafsu din mumini ta ga wani mai sabon Allah sannan kuma ta kyaleshi bata inkarin aikata hakan ba gare shi.

قال أمير المؤمنين عليّ  7 :

«قوام الشريعة الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر وإقامة الحدود».

4- Sarkin muminai Ali (a.s) ya ce: tsayuwar shari'a na cikin umarnin da kyakkyawa da hani da mummuna da tsayar da haddodi.

وعنه  7 في وصيّته لمحمّد بن الحنفيّة  :

«وأمر بالمعروف تكن من أهله ، فإنّ استتمام الاُمور عند الله تبارک وتعالى الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر».

5- daga gare shi (a.s) cikin wasiyyarsa ga Muhammad bn Hanafiyya: (ka yi umarni da kyakkywa za ka kasance daga ahalinsa, lallai cikar abubuwa a wurin Allah mai albarkoki madaukaki na cikin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna.

 

وعنه: في قوله تعالى: (وَآصْبِرْ عَلَى مَا أصَابَکَ ) ، قال : «من

المشقّة والأذى في الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر».

6- daga gare shi (a.s) cikin fadinsa madaukaki: (ka yi hakuri kan abin da ya sameka).[5]

وقال  7 :

«الأمر بالمعروف أفضل أعمال الخلق ...».

7- amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: (umarni da kyakkyawa shi ne mafi falalar ayyukan halittu)

«وفرض الأمر بالمعروف مصلحةً للعوام ...».

8- ya ce: kuma sai ya farlanta umarni da kyakkyawa domin maslaha ga gama garin mutane….

«فمن أمر بالمعروف شدّ ظهور المؤمنين ...».

9- duk wanda ya yi umarni da kyakkyawa ya karfafi bayan muminai…

«فرض الله... النهي عن المنكر ردعآ للسفهاء...».

10- Allah ya farlanta hani ga munkari domin tsawatarwa ga wawaye.

«ومن نهى عن المنكر أرغم اُنوف الكافرين (المنافقين )».

11- duk wanda ya yi hani ga mummuna ya turbude hancinan kafirai (munafukai).

وقال  7 :

«إنّما هلک من كان قبلكم بحيث ما عملوا من المعاصي ولم ينههم الربّانيون والأحبار عن ذلک ـأي العلماءـ فإنّهما لمّا تمادوا في المعاصي نزلت بهم العقوبات ».

12-kadai dai wadanda suka kasance gabaninku sun halaka sakamakon idan suka aikata aikin sabo malamai basa kwabarsu su da hanasu, lallai su yayin da suka suka nutsa cikin ayyukan sabo sai ukuba ta sauka kansu.

وعنه  7 :

«فإنّ الله سبحانه لم يلعن القرون الماضية بين أيديكم إلّا لتركهم الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر، فلعن الله السفهاء لركوب المعاصي ، والحلماء لترک المناهي ».

13- daga gare shi (a.s): (Allah subhanahu wata'ala bai la'anci karnonin da suka gabata gabaninku sai sakamakon barinsu ga umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, sai ya la'anci wawaye sakamakon zakkewa ayyukan sabo. Ya kuma la'anci ma'abota hankali saboda kin kwabarsu.

وكان الإمام الحسين  7 يقول:

«لا تحلّ لعينٍ مؤمنةٍ ترى الله يُعصى فتطرف حتّى يغيّره ».

14- Imam Husaini (a.s) ya kasance yana cewa: ( bai halatsa ga ido mumini ace ta ga ana sabawa Allah ta kifta har sai idan an canja shi.

وقال  :

«اعتبروا أيّها الناس بما وعظ الله به أولياءه من سوء ثنائه على الأحبار إذ يقول : (لَوْلا يَنْهَاهُمُ الرَّبَّانِيُّونَ ) ، وقال : (لُعِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ بَنِي

إسْرَائِيلَ ) ، وإنّما عاب الله ذلک عليهم لأنّهم كانوا يرون من الظلمة الذين بين

أظهرهم المنكر والفساد فلا ينهونهم عن ذلک ، رغبةً فيما كانوا ينالون منهم ، ورهبةً ممّا يحذرون ، والله يقول : (فَلا تَخْشَوُا النَّاسَ وَاخْشَوْنِ ) ».

15-amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: ku fadaku yaku taron mutane da abin da Allah ya wa'azantar waliyyansa da shi daga munana yabonsa kan malaman yahudawa yayin da yake cewa: (bada ban malamai basu hanasu ba).[6] A wani wurin kuma ya ce: (an tsinewa wadanda suka kafirce daga Banu Isra'ila)[7] kadai Allah ya aibanta hakan kansu ne sakamakon suna kallon laifukan wadanda suke cikinsu daga munkari da barna amma kuma basa hana su hakan, sakamakon kwadayi cikin abin da suke samu daga wajensu da kuma tsoran abin da suke gujewa, Allah yana cewa: (ka da kuji tsoransu ku ji tsorona).[8]

وقال  7 :

«اعتبروا أيّها الناس بما وعظ الله به أولياءه ... وقال : (المُؤْمِنُونَ وَالمُؤْمِنَاتُ بَعْضُهُمْ أوْلِيَاءُ بَعْضٍ يَأمُرُونَ بِالمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ المُنكَرِ) ، فبدأ

الله بالأمر بالمعروف والنهي عن المنكر فريضة منه ، لعلمه بأنّها إذا اُدّيت واُقيمت استقامت الفرائض كلّها هيّنها وصعبها، وذلک أنّ الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر دعاء إلى الإسلام مع ردّ المظالم ومخالفة الظالم ، وقسمة الفيء والغنائم ، وأخذ الصدقات من مواضعها، ووضعها في حقّها».

16- ku fadaku yaku mutane da abin da Allah ya wa'azantar da waliyyansa… ya ce: (muminai maza da muminai mata sashensu masoya ne ga sashe suna umarni da kyakkyawa suna hani da mummuna) sai  Allah ya fara da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna farilla daga gare shi, sakamakon saninsa da cewa su idan aka sauke su aka tsayar da su dukkanin farilloli za su tsayu saukakansu da masu wahalarsu cikinsu. Sakamakon umarni da kyakkyawa da hani da mummuna su ne kira ne zuwa ga muslunci da mayar hakkoki da yakar sabawa azzalumi, da kasa ganima da fai'u, da karbar sadakoki daga wurarenta da ajiyeta a muhallinta.  

قال الإمام مولانا الباقر :

«الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر خلقان من خلق الله، فمن نصرهما أعزّه الله، ومن خذلهما خذله الله عزّ وجلّ » .

17-shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce: (umarni da kyakkyawa da hani da mummuna halittu biyu ne daga halittun Allah, duk wanda ya taimake su Allah zai daukaka shi, duk wanda ya tozarta su Allah Azza wa Jalla zai tozarta shi.

وفي حديث له  7 :

«إنّ الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر سبيل الأنبياء، ومنهاج الصلحاء، فريضة عظيمة ، بها تقام الفرائض ، وتأمن المذاهب ، وتحلّ المكاسب ، وتردّ المظالم ، وتعمر الأرض ، وينتصف من الأعداء، ويستقيم الاُمراء».

18- ya zo cikin hadisinsa (a.s): lallai umarni da kyakkyawa da hani da mummuna tafarkin annabawa ne, hanyar salihai ce, farilla ce mai girma, da su ne farillu suke tsayuwa, hanyoyi suke samun aminci, mu'amaloli suka halasta, ake dawo da hakkoki, kasa take rayuwa, ake adalci daga makiya, shugabanni suke daidaita sahu.

Allahu Akbar Allahu Akbar, me yafi kyawunta daga fa'idojin umarn da kyakkyawa da hani da mummuna da su ne addini yake tabbatuwa, rukunan addini suke tsayuwa, jama'a suke azurtuwa, adalci ya jagaba cikin al'umma cikin rayayyun yankuna, mutum da su yake samun kubutuwa duniya da lahira.  

قال مولانا أمير المؤمنين عليّ بن أبي طالب  7 :

«من كنّ فيه ثلاث خصال ، سلمت له الدنيا والآخرة : من أمر بالمعروف وائتمر به ، ونهى عن المنكر وانتهى عنه ، وحافظ حدود الله» .

19-shugabanu sarkin muminai Ali bn Abi dalib (a.s) ya ce: duk wanda cikinsu halaye suka tabbatu ya kubuta duniya da lahira: wanda ya yi umarni da kyakkyawa ya umartu da shi a kankin kansa, ya yi hani da mummuna ya hanu daga barinsa, ya kiyaye haddodin Allah.[9]

Shin kasan sakamakon da yake ga wanda yake barin umarni da kyakkywa da hani da mummuna?

20- karanta abin da annabi mafi girmama Muhammad (s.a.w) ya ce:

«لا يزال الناس بخيرٍ ما أمروا بمعروف ونهوا عن منكر، وتعاونوا على البرّ، فإذا لم يفعلوا ذلک نزعت منهم البركات ، وسلّط بعضهم على بعض ، ولم يكن لهم ناصر في الأرض ولا في السماء» .

Mutane ba za su gushe ba cikin alheri matukar suka yi umarni da kyakkyawa suka yi hani da mummuna, suka yi taimakekeniya kan kyautatawa, idan basu aikata haka ba za a cire albarkoki daga gare su, sashensu su yi iko kan sashe, basu da mai taimakonsu cikin kasa ko sama.[10]

 

21- ya zo cikin Nahjul Balaga, daga sarkin muminai (a.s):

«أيّها المؤمنون ، إنّه من رأى عدوانآ يعمل به ، ومنكرآ يدعى إليه ، فأنكره بقلبه فقد سلم وبرئ ، ومن أنكره بلسانه فقد اُجر وهو أفضل من صاحبه ، ومن أنكره بالسيف لتكون كلمة الله هي العليا وكلمة الظالمين هي السفلى ، فذلک الذي أصاب سبيل الهدى ، وقام على الطريق ، ونوّر في قلبه اليقين ».

Yaku muminai, lallai dukkanin wanda ya ga ana aikata wani ta'addanci, ko wani munkari ana kira zuwa gare shi, sai yayi inkarinsa da zuciyarsa hakika ya kubuta ya tsira, wanda yayi inkarinsa da harshensa hakika ya samu lada kuma yafi wand aya gabace shi da zuciya, wanda yayi inkarinsa da takobi domin Kalmar Allah ta kasance ita ce madaukakiya, wadancananka shi ne ya dace da tafarkin shiriya, ya tsayu kan hanya, yakini haskaka cikin zuciyarsa.

وفي كلام آخر له  7 يجري هذا المجرى  :

«... فمنهم المنكر للمنكر بيده ولسانه وقلبه ، فذلک المستكمل خصال الخير. ومنهم : المنكر بلسانه وقلبه ، والتارک بيده ، فذلک متسمّک بخصلتين من خصال الخير ومضيّع خصلة . ومنهم : المنكر بقلبه ، والتارک بيده ولسانه ، فذلک الذي ضيّع أشرف الخصلتين من الثلاث ، وتمسّک بواحدة . ومنهم : التارک لإنكار المنكر بلسانه وقلبه ويده ، فذلک ميّت الأحياء. وما أعمال البرّ كلّها، والجهاد في سبيل الله عند الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر إلّا كنفثة في بحرٍ لجّي ، وإنّ الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر لا يقرّبان من أجل ، ولا ينقصان من رزق ، وأفضل من ذلک كلّه ، كلمة عدل عند إمام جائر».

22- cikin wata magana da ake danganta masa (a.s) da take da irin ma'anar maganar da ta gabata: (a cikin mutane akwai mai inkarin munkari da hannunsa da zuciyarsa da harshensa, hakika wadancananka ya kammala dukkanin alheri, haka ma a cikinsu akwai mai inkarin munkari da harshensa da zuciyarsa banda hannunsa, wadancananka yayi riko da halaye biyu daga cikin halayen uku na alheri ya tozarta daya, daga cikinsu akwai mai inkari da zuciyarsa ya bar hannunsa da harshensa, wadancananka shi ne ya tozarta mafi daukakar abubuwa biyu daga uku ya zama ya riki guda daya, daga cikinsu akwai wanda yayi watsi da inkarin munkari da hannunsa da harshensa da zuciyarsa, wadancananka shi ne mataccen cikin rayayyu, baki dayan ayyukan alheri da jihadi cikin tafarkin Allah ba ya bakin komai suke ba idan aka kwatanta su da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna sai kamar misalin huri cikin zuzzurfan kogi, lallai umarni da kyakkyawa da hani da mummuna basa kusanto da ajali, basa tauye arziki, sannan mafi falala daga dukkanin wadannan abubuwa shi ne fadar Kalmar gaskiya a gaban shugaba azzalumi.

Haka ne tabbas kalamin Imam jagoran kalamai ne, kalaminsa (a.s) yana saman kalaman mutane yana kasa da kalamin mahalicci,  me yake nufi da fadinsa (kamar huri ne cikin tafki mai zurfi) ? sannan me yae nufi da (mafi falala daga dukkanin wadannan shi ne fadin kalmar adalaci a gaban sarki Ja'iri)? Me zan iya fadi gaban wadannan kalmomi masu haskaka, da wadannan haruffa masu sheki? Babu mamaki da an rubuta ta su kan fararen kunci da alkaluma daga haske sakamakon abin da kalmomin suke dauke da shi daga madaukakan ma'anoni da daukakar sama, da mafahim madaukaka da daukakar daukaka, lallai wallahi darussa ne masu kima wadanda suke cike da da rayuwa da nishadi da motsi, suna koyar da jama'a-jama'a cikin dukkanin zamanunnuka da lokuta, suna bayyana musu wazifofinsu, da nauye-nauyen da yake kan wuyansu na `yan'Adamtaka.

Wannan kenan, sannan idan mun nufi tsinkayar girman umarni da kyakkyawa da hani da munkari, ya zama wajibi kanmu mu kara mayar da kallonmu zuwa ga Ayoyin kur'ani mai girma da riwayoyi madaukaka, domin mu ga abin da ke kosar da mai kishi ya warkar da mai larura ya azutar da mutum cikin rayuwarsa.

Allah madaukaki ya ce:

 

 (يَا بُـنَيَّ أقِمِ الصَّلاةَ وَأمُرْ بِالمَعْرُوفِ وَآنْهَ عَنِ المُنكَرِ وَآصْبِرْ عَلَى مَا أصَابَکَ إنَّ ذَلِکَ مِنْ عَزْمِ الاُمُورِ).

Ya dana ka tsayar da sallah ka yi umarni da kyakkyawa ka yi hani da munkari ka yi hakuri kan abin da ya same ka lallah wancan yana daga manyan lamura.[11]

Sannan umarni da kyakkyawa da hani da munkari suna da martabobi uku: bisa la'akari da yanayin da mutum musulmi mai imani yake rayuwa ciki, haka ma suna da sharudda wanda duka an ambace su cikin litattafan fikihu da risaloli aiki, sai a koma can.

Lallai umarni da kyakkyawa shi ne doruwa kan aiki a fade, da nufar afkar da shi daga abin da aka umarci mutum da shi.

 Hani da munkari shi ne hana aikata sabo a aikace a fade da kuma kin afkuwarsa.

Kadai dai wajabinsu ya tabbatu da nakali da ijma'in ma'abota Alkibla sakamakon ayoyi da hadisai, haka ma a hankalce sakamakon kasantuwarsu ludufi, domin su suna daga abin da yake kusanta mutum zuwa ga da'a da nesanta shi daga sabo, ba tare da sun kai ga haddin tilastawa ba, sannan shi ludufi kamar yand aya tabbata cikin ilimin Kalam wajibi ne, bisa hukuntawar ka'idojin Adalci, saboda suna daga cikin abubuwa ake samun cimma manufa da su da kuma rashin wajabcinsu yana lazimta rashin cimma manufa, da haka ne umarni da kyakkyawa da hani a mummuna suka wajabtu a hankalce bukata ta biya.

Sannan wajabcinsu yana daga wajibi (Kifa'i) wanda ya faduwa kan sauran mutane idan wasu ba'ari suka dauki nauyin sauke shi, idan kuma ba a samu wadanda suka sauke nauyin nauyin ba kowa na da laifi, kadai dai wajabcinsu ya kasance kifa'i sakamakon hadafi a shari'ance shi ne afkuwar kyakkyawa da samuwar cikin jama'a, da shafewar munkari, saboda su jama'a kamar jirgine, shi mai aikata munkari kamar mai huda jirgi ne, duk wanda ya ganshi yaki hana a tsawatar masa domin dauke munkari lallai sakamako zai kasance nutsewar jirgi cikin tafkin duhhai, duhhai ba'arinsu saman ba'ari, kuma zai kasance daga sh'awe-sha'awe da lalacewar halaye da tozarta da tsiyata duniya da lahira, abin nufi da kaucewa munkari ba tare da mai aikata shi ayyananne ba, dukkaninku makiyaya ne kuma kowanne makiyayi abin tambaya ne kan abin da aka bashi kiwo, idan wajabcin dagewar ta

hakkaku, wannan shi ne ma'anar wajibi kifa'i kamar yanda mustahabbi ne umarni da aikin mustahabbi da hani da aikin makaruhi, kadai dai suna wajabta tare da ilimin mai umarni kyakkyawa da mai hani da munkari domin kada ya dinga umarni da munkari da hani da kyakkywa, kuma tare da amintuwa daga cutuwa da rashin barna kan mai yi ko kan ba'arin muminai ko dukiyarsu da mutuncinsu, tare kuma da samuwar tasiri don gudun ka da ya kasance bamai yiwu ba ne, ya dai kasance mai yiwuwa gwargwadon abin da yake bayyanuwa daga halinsa, da kuma kafewar mai aikata munkarin kan munkarin, hakika malaman fikih sun ambaci mas'alolin umarni da kyakkyawa da hani da munkari cikin litattafansu na fikihu da risalolin aiki da manyan litattfan istidlalin fikihu, Allah ya saka musu da mafi aihrin sakamako.

Ya kai mai karatu mai girma, yana girman gaske gareni in bar umarni da kyakkyawa da hani da munkari, ya zama cikin madaukakin sha'aninsu ban kawo wasu ba'arin madaukakan riwayoyi ba daga Ahlil-baiti (a.s): lallai su ne mafi sanin abin da yake cikin gida, ga wasu gajerun riwayoyi masu dauke da manyan ma'anoni, masu yan takaitattun haruffa amma tare da mafahim manya-manya, fatana gareka mai karatu ka zurfafa kallo ka lura cikin nutsuwa, ka haddace su ka yada su tsakankanin mutane, domin ka azurta jama'arka su azurtu, ka rabauta mutane su samu rabauta, ka samu lada da sakamako, madalla da ladan masu aiki, wannan kenan, dama ita zakkar ilimi shi ne yada shi.    

عن أحدهما   ـالباقر أو الصادق ـ أنّه قال  :

«لا دين لمن لا يدى الله بالأمر بالمعروف والنهي عن المنكر» .

23- daga dayansu Albakir ko Sadik (a.s) cewa ya ce: babu addini ga wanda bai bautar Allah da umarni da kyakkyawa da hani da munkari.[12]

وعن الرسول الأعظم  :

«من أمر بالمعروف ونهى عن المنكر، فهو خليفة الله في الأرض وخليفة رسوله » .

24-daga manzo mafi girma (s.a.w) : dukkanin wanda ya yi umarni da kyakkyawa yayi hani da mummuna, lallai shi halifan Allah ne cikin kasa halifan manzon sa ne.[13]

وعن عليّ أمير المؤمنين   :

«غاية الدين الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر وإقامة الحدود».

25- daga Ali sarkin muminai (a.s): tukewar manufar addini shi ne umarni da kyakkyawa da hani da mummuna da tsayar da haddodi.

 

Ya zo cikin kur'ani mai girma:

 (إنَّ اللهَ يَأمُرُ بِالعَدْلِ وَالإِحْسَانِ وَإيتَاءِ ذِي القُرْبَى وَيَنْهَى عَنِ الفَحْشَاءِ وَالمُنكَرِ وَالبَغْيِ).

Lallai Allah yana umarni da kyakkyawa da ihsani da baiwa makusannci yana hani da alfasha da munkari da zalunci.[14]

وعن مولانا الصادق  :

«إذا رأى المنكر فلم ينكره وهو يقدر عليه ، فقد أحبّ أن يعصى الله، ومن أحبّ أن يعصى الله فقد بارز الله بالعداوة » .

26-daga shugabanmu Sadik (a.s) : idan wani ya ga munkari yaki inkarinsa alhalinsa yana da iko kan hakan, to hakika yana son a sabawa Allah, dukkan wanda ya so a sabawa Allah to hakika yayi fito na fito da Allah da adawa.[15]

 

وعن أبي بصير، قال : سألت أبا عبد الله  7 عن قول الله عزّ وجلّ  : (قُوا أنفُسَكُمْ وَأهْلِيكُمْ نَارآ) ، قلت : هذه نفسي أقيها، فكيف أقي أهلي ؟

قال : «تأمرهم بما أمر الله به ، وتنهاهم عمّا نهاهم الله عنه ، فإن أطاعوک كنت وقيتهم ، وإن عصوک فكنت قد قضيت ما عليک ».

27-an karbo daga Abu Basir, ya ce: na tambayi Abu Abdullah (a.s) dangane da fadin Allah Azza wa Jalla: ( ku tseratar da kawukanku da iyalanku daga wuta)[16] n ace: wannan nafsu dina cezan tseratar da ita, ta kaka zan tseratar da iyalina? Sai ya ce: ka umarce su da abin da Allah yayi umarni da sh, ka hana su daga abin da ya hane su da shi, idan suka yi maka biyayya to ka tseratar da su idan kuma suka saba maka to ka sauke nauyin da yake kanka.[17]

وعن الرسول الأكرم  :

«إذا لم يأمروا بمعروف ولم ينهوا عن منكر، ولم يتّبعوا الأخيار من أهل بيتي ، سلّط الله عليهم شرارهم ، فيدعو عند ذلک خيارهم ، فلا يستجاب لهم » .

28-an karbo daga manzo mafi karamci (s.a.w):

(idan suka ki umarni da kyakkyawa suka ki hani da mummun, suka ki biyayya ga Ahlin gidana, Allah zai dora Ashararan cikinsu kansu).

 

ومن وصايا أمير المؤمنين  عند شهادته  :

«لا تتركوا الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر فيولّى عليكم شراركم ثمّ تدعون فلا يستجاب لكم

29-daga wasiyyoyin sarkin muminai (a.s) yayin shahadarsa:

(ka da ku sake ku bar umarni da kyakkyawa da hani da munkari sai Allah ya shugabantar Ashararan cikinku kanku, ku dinga addu'a Allah ba ya amsa muku)

وعن الإمام جعفر بن محمّد، عن أبيه ، قال  :

«قال رسول الله  : إنّ المعصية إذا عمل بها العبد سرّآ، لم تضرّ إلّا عاملها، وإذا عمل بها علانية ولم يغير عليه ، أضرّت العامّة ».

30-an karbo daga Imam Jafar bn Muhammad daga babansa, ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya ce: sh sabo idan bawa ya aikata shi a boye babu wanda yake cuturwa sai wand aikata shi, amma idan ya aikata shi a bayyane sannan bai canja kansa, ya cutar baki dayan mutane.

قال جعفر بن محمّد  :

«وذلک إنّه يذلّ بعمله دين الله، ويقتدي به أهل عداوة الله».

31-Jafar bn Muhammad (a.s) ya ce: wadancananka kadai dai yana wulakanta addinin Allah da iliminsa, makiya Allah suna kwaikwayonsa.

وعنه :

«ما أقرّ قوم بالمنكر بين أظهرهم لا يغيّرونه ، إلّا أوشک أن يعمّهم الله بعقابٍ من عنده ».

32- daga gare shi amincin Allah ya kara tabbata gare shi:

(wasu mutane basu taba tabbatar da munkari tsakankaninsu ba sa hani da shi face ya kusa Allah ya game su da ukuba daga gare shi).

وعن أمير المؤمنين :

«أيّها الناس ، إنّما يجمع الناس الرضى والسخط ، وإنّما عَقر ناقة ثمود رجل واحد، فعمّهم الله بالعذاب لمّا عمّوه بالرضا».

33- daga sarkin muminai (a.s):

(Yaku mutane, kadai yarda da fushi ke tattaro mutane, kadai mutum guda daga samudawa ya kashe taguwar annabi Salihu (a.s) sai Allah ya game su da azaba yayin da su suka yi ittifaki tare da shi cikin kashe taguwar ta hanyar nuna yardarsu da kisan)

وقال :

«من استحسن قبيحآ، كان شريكآ فيه ».

34- amincin Allahb ya tabbata gare shi (a.s) ya ce: ( duk wanda ya ga kyawun mummunan aiki, lallai ya kasance ya yi tarayya cikinsa).

 Ya mai karatu mai daraja ka da ka kasance cikin wadanda Imam Bakir (a.s) kansu yake cewa:

«يكون في آخر الزمان قوم ، يتبع فيهم قوم مراؤون ، يتقرّأون ويتنسّكون ، حدثاء، سفهاء، لا يوجبون أمرآ بمعروف ولا نهيآ عن منكر إلّا إذا أمنوا الضرر، يطلبون لأنفسهم الرخص والمعاذير».

(a karshen zamani za a samu wasu mutane cikinsu wasu `yan riya zasu biye su, suna masu matukar karatu da ibada, zaka same su matasa wawaye basa wajabtar da umarni da kyakkyawa da hani da barin mummuna sai dai idan sun tabbatar ba zasu cutu cikin aikata hakan ba, zaka same su suna nemawa kasan sauki da uzururruka.

Ka da mu kasance daga wadanda Allah yake cewa kansu:

 (أتَأمُرُونَ النَّاسَ بِالبِرِّ وَتَنسَوْنَ أنفُسَكُمْ وَأنْتُمْ تَتْلُونَ الكِتَابَ أفَلا تَعْقِلُونَ ) .

Yanzu kuna umartar mutane da kyautatawa kuna mantwa da kawukanku alhalin kuna tilawar littafi yanzu ba zaku hankalta ba[18]

 

وأمير المؤمنين  7 يقول  :

إنّي لأرفع نفسي عن أن أنهى الناس عمّا لست أنتهي عنه ، أو آمرهم بما لا أسبقهم إليه بعملي

35- daga sarkin muminai (a.s) yana cewa: lallai ni ina daukewa kaina hana abin da ni ban hanu kansa ba, ko kuma in umarce su da abin da ban gabace su zuwa gare shi ba da aikina.

وقال :

«لا تكن ممّن يرجو الآخرة بغير العمل ».

36-amincin Allah ya kara tabbata a gare shi, ya ce: ka da ka kasance daga cikin masu fatan lahira ba tare da aiki ba.

وقال :

«لعن الله الآمرين بالمعروف التاركين له ، والناهين عن المنكر العاملين به ».

37-amincin Allah ya kara tabbata a gare shi, ya ce: Allah ya tsinewa masu umarni da kyakkyawa amma kuma su a kankin kansu suna barinsa, da masu hani da munkari amma suna aikata shi.

والإمام الباقر  يقول  :

«ولو أضرّت الصلاة بسائر ما يعملون بأموالهم وأبدانهم لرفضوها، كما رفضوا أسمى الفرائض وأشرفها».

38- Imam Bakir (a.s) yana cewa:

(da sallah za ta cutar da sauran abubuwan da suke aikatawa da dukiyarsu da jikkunansu da tabbas sun yi watsi da ita, kamar yanda suka yi watsi da da farillai da mafi daukakarsu).

 

وقال الرسول الأعظم :

«غشيتكم السكرتان : سكرة حبّ العيش ، وحبّ الجهل ، فعند ذلک لا تأمرون بالمعروف ولا تنهون عن المنكر».

39- manzo mafi girma (s.a.w) ya ce: maye biyu sun zakke muku: mayen son rayuwa, da na son jahilci, a wannan lokaci sai ya zama bakwai umarni da kyakkyawa bakwa hani da munkari.

 

Allah madaukaki yana cewa:

 (المُنَافِقُونَ وَالمُنَافِقَاتُ بَعْضُهُمْ مِنْ بَعْضٍ يَأمُرُونَ بِالمُنْكَرِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ المَعْرُوفِ ).

Munafukai maza da munafukai mata sashensu daga sashe yake suna umarni da munkari suna hani da kyakkyawa.[19]

 

Wajibi kan kowanne daya daga cikinmu shi ne ka da ya ji tsoran mutane cikin mukamin hani da munkari bari dai kadai ya ji tsoran Allah matsarkaki.

Allah Azza wa Jalla ya ce:

الَّذِينَ قَالَ لَهُمُ النَّاسُ إنَّ النَّاسَ قَدْ جَمَعُوا لَكُمْ فَاخْشَوْهُمْ فَزَادَهُمْ إيمَانآ وَقَالُوا حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الوَكِيلُ

Wadanda Allah ya ce musu lallai mutane sun taru gareku sai suka ji tsoransu sai ya kara musu imani suka ce Allah ya isar mana madalla da wakili.[20]

قال رسول الله :

«لا يحقّرن أحدكم نفسه ».

40-manzon Allah (s.a.w) ya ce: ka da wani cikinku ya wulakanta kansa.

قالوا: يا رسول الله، وكيف يحقّر أحدنا نفسه ؟

Sai suka ce ya manzon Allah yaya dayanmu zai wulakanta kansa?

 قال  :

«يرى أنّ عليه مقالا، ثمّ لا يقول فيه ، فيقول الله عزّ وجلّ يوم القيامة  : ما منعک أن تقول في كذا وكذا؟ فيقول : خشية الناس ! فيقول : فإيّاي كنت أحقّ أن تخشى ».

Sai ya ce: ya fuskanci cewa kansa akwai maganar da wajabta ya fada, sannan tare da haka sai ya ki fada, sai ranar Alkiyama Allah Azza wa Jalla ya ce: mene ne ya hanaka kayi magana cikin kaza da kaza? Sai ya ce: ina tsoran mutane ne! sai Allah ya ce masa: ni kadai ne na cancanci ka ji tsorona.

وقال :

«لا يمنعنّ أحدكم هيبة الناس أن يقول الحقّ إذا رآه أو سمعه ».

41- amincin Allah ya kara tabbata a gare shi, ya ce:

(ka da kwarjinin mutane ya hana dayanku fadin gaskiya idan ya ganta ko ya ji da kunnensa).

 

Wajibi kanmu mu yaki ayyukan sabo ko da kuwa ta hanyar turbune fuska ne da kaurace musu.

 

Allah matsarkaki madaukaki ya ce:

وَإذَا رَأيْتَ الَّذِينَ يَخُوضُونَ فِي آيَاتِنَا فَأعْرِضْ عَنْهُمْ حَتَّى يَخُوضُوا فِي حَدِيثٍ غَيْرِهِ وَإمَّا يُنسِيَنَّکَ الشَّيْطَانُ فَلا تَقْعُدْ بَعْدَ الذِّكْرَى مَعَ القَوْمِ الظَّالِمِينَ.

Idan ka ga wadanda suke kutsawa cikin ayoyinmu to ka bijire musu har sai sun kutsa cikin wani batun daban idan shaidani ya mantar da kai to ka da ka zauna tare da azzalumai.[21]

قال رسول الله :

«تقرّبوا إلى الله تعالى ببغض أهل المعاصي ، والقوهم بوجوه مكفهرّة ، والتمسوا رضا الله بسخطهم ، وتقرّبوا إلى الله بالتباعد منهم ».

42- manzon Allah (s.a.w) ya ce: ku nemi kusancin Allah ta hanyar kiyaya da ma'abota aikata ayyukan sabo, idan zaku hadu da su ku hadu da halin fuskokinmu na turbune, ku nemi yardarm Allah ta hanyar fusata su, ku nemi kusanci zuwa ga Allah ta hanyar nesantuwa daga gare su.

وعنه  :

«أوحى الله إلى أيّوب  7: هل تدري ما ذنبک إليَّ حين أصابک البلاء؟ قال : لا، قال : إنّک دخلت إلى فرعون فداهنت في كلمتين ».

43- daga gare shi (a.s) : Allah yayi wahayi zuwa ga Ayyuba (a.s): shin kasan laifin da kake da shi a wurina lokacin da bala'i ya zakke maka? Sai ya ce: a'a, Allah ya ce: lallai kai kaje wurin Fir'auna sai ka lausasa cikin kalmomi biyu.

 قال أمير المؤمنين عليّ :

«أمرنا رسول الله  أن نلقى أهل المعاصي بوجوه مكفهرّة ».

44- sarkin muminai Ali (a.s): manzon Allah ya umarce mu mu hadu da ma'abota aikata sabo halin fusakenmu na turbune.

 

وعنه :

«أدنى الإنكار ان تلقى أهل المعاصي بوجوه مكفهرّة ».

45- daga gare shi (a.s) : mafi karancin inkari shi ne ka hadu da ma'abota aikata sabo halin fusake na turbune.

وقال الإمام الصادق في قوله تعالى: (كَانُوا لا يَتَنَاهَوْنَ عَنْ مُنكَرٍ فَعَلُوهُ ) : «أما إنّهم لم يكونوا يدخلون مداخلهم ، ولا يجلسون مجالسهم ، ولكن كانوا إذا لقوهم ضحكوا في وجوههم وآنسوا بهم

46- Imam Sadik (a.s) cikin fadin Allah madaukaki (sun kasance basu kwabar juna daga munkari da suka aikata)[22] ya ce: amma lallai su basu kasance suna shiga mashigarsu ba, basa zama mazaunarsu, sai dai cewa lallai yayin da suka hadu da ma'abota aikata sabo sai suyi dariya a gaban fuskokinsu su debe haso da su 

وقال  :

«إنّ الله عزّ وجلّ بعث ملكين إلى أهل مدينة ليقلبها على أهلها، فلمّا انتهيا إلى المدينة وجدا رجلا يدعو الله ويتضرّع ... فعادا إلى الله فقال : يا ربّ ، إنّي انتهيت إلى المدينة فوجدت عبدک فلانآ يدعوک ويتضرّع إليک ، فقال : امضِ لما أمرتک به ، فإنّ ذا رجل لم يتمعّر وجهه غيظآ لي قطّ

46- ya ce: lallai Allah Azza wa Jalla ya aiko mala'ku guda biyu zuwa ga mutanen wani gari domin su halakar da gari, lokacin da suka shiga garin sai suka samu wani mutum yana rokon Allah yana magiya da kankan da kansa… sai wadannan mala'iku suka dawo wurin Allah dayansu ya ce: ya Allah lallai ni na shiga wannan gari sai na samu wani bawanka wane yana kiranka yana magiya gareka, sai ya ce: kaje ka zartar da abin da na umarceka da shi, lallai wannan mutumin fuskarsa bata taba canjawa ko da sau daya don yin fushi saboda ni ba.

وعنه  :

«لو أنّكم إذا بلغكم عن الرجل شيء تمشيّتم إليه فقلتم : يا هذا، إمّا أن تعتزلنا وتجتنبنا، وإمّا أن تكفّ عن هذا، فإن فعل ، وإلّا فاجتنبوه ».

47- daga gare shi (a.s): da ace ku idan labara ya zo muku gameda mutum kun je wajensa kun ce: ya kai wannan bawan Allah, ko dai ka zobaitar da mu ka nesance mu, ko kuma ka kame kanka daga wannan, idan ya aika hakan shikenan, idan ko bai aikata ba ko kaurace masa. 

وقال  :

«لتحملنّ ذنوب سفهائكم على علمائكم ... ما يمنعكم إذا بلغكم عن الرجل منكم ما تكرهونه ـممّا يدخل به علينا الأذى والعيب عند الناس ـ أن تأتوه فتأنبوه وتعظوه ، وتقولوا له قولا بليغآ؟!».

فقلت له : إذا لا يقبل منّا ولا يطيعنا؟ قال : فقال  :

«فاهجروه عند ذلک واجتنبوا مجالسته ».

48- amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: lallai zaku dora laifukan wawayenku kan malamanku…me yake hanaku idan labari ya iso gareku dangane da mutum daga gareku da kuke kiyayya da shi daga abin da yake shigar da cutuwa da shi kanmu da aibu wurin mutane da ku je ku zargeshi ku yi masa wa'azi ku gaya masa magana mai isarwa?!

Sai na ce masa: idan ya zama bay a karba daga garemu baya yi ma’ana da’a fa? Ya ce: Sai yace: to ku kaurace masa ku nesance shi.[23]

 

هذا ولا يكون زماننا هذا كما قال الرسول الأكرم  :

«كيف بكم إذا فسدت نساؤكم وفسق شبابكم ولم تأمروا بالمعروف ولم تنهوا عن المنكر، كيف بكم إذا أمرتم بالمنكر ونهيتم عن المعروف !... كيف بكم  إذا رأيتم المعروف منكرآ والمنكر معروفآ».

Wannan kenan, sannan wannan zamanin namu bai kamata ya zama kamar yanda manzo mafi karamci (s.a.w) ya fadi ba,

(me kuke tsammani idan matayenku suka lalace matasanku cikinku suka zama fasikai kuka ki umarni da kyakkyawa kuka ki hani da mummuna, yaya gareku idan kukai umarni da kyakkyawa kuka yi hani da mummuna…. me kuke tsammani idan kuka ga kyakkyawa a matsayin mummuna, mummuna a matsayin kyakkywa.

 

Allah ya kiyashe mu daga faruwar hakan, ya shiryar da mu zuwa ga tafarkinsa siradinsa madaidaici, yayi mana damdagatar zuwa ga raya hukunce-hukuncen muslunci da haddodinsa, mu dinga umarni da kyakkywa da hani da abin kyama domin neman kusanci zuwa ga Allah madaukaki, bama damuwa da matsaloli da wahalhalu kan kiran mutane zuwa ga kyakkyawan aiki da gyara, bari muna fadi tashi da gwagwarmaya har ta kaimu zuwa ga shiga gidan kaso (prison) bayan nan kuma mu sha azabatarwa kai hatta ta kaimu ga shahada da kisa cikin tafarkin Allah, me yafi kyawu da kayatarwa daga ace musulmi da musulma sun zama shahidan umarni da kyakkywa da hani da mummuna, cikinsu alamomin izza da daukaka suna yin tajalli, ka'idojin muslunci da dokokinsa suna misaltuwa jikinsu, cikin dukkanin mumini da mumina ruhin muslunci mai girma yana jikkantuwa, domin tsare-tsaren rayuwar `yantattu ya zama shi ne abin da shugaban Shahidai  shugabanmu Husaini (a.s) ya fada a ranar Ashura lokacin da yake bayyana haduffan motsinsa da tashinsa cikin haskakan kalmomi, cikin fadinsa:    

«لم أخرج أشِرآ ولا بَطِرآ، ولا ظالمآ ولا مفسدآ، وإنّما خرجت للإصلاح في اُمّة جدّي آمر بالمعروف وأنهى عن المنكر».

ni ban fito domin nuna isa da Gadara, ba kuma mai neman zalunci da barna ba, kadai dai na fito don neman kawo gyara cikin al'ummar kakana ina umarni da kyakkyawa ina hana abin kyama.

Yaku musulmai!! Tsakaninku da Allah kunyi koyi da manzon Allah (s.a.w) kunyi koyi da tsatsonsa tsarkaka, kun yi koyi da magabata nagargaru daga iyayenmu da malamanmu rabautattu ta hanyar tsayar da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna cikin garuruwanmu da jama'armu musulmai da ahalinmu da kawukanmu?![1] Alu Imran:104

[2] Alu Imran:110

[3] Alu Imran:114

[4] Tauba:71

[5] Lukman:17

[6] Ma’ida:63

[7] Ma’ida:78

[8] Ma’ida:44

[9] Amali Mufid:77

[10] Mishkatul Anwar:51

[11] Lukman:17

[12]  Biharul-Anwar:m 97 sh 86

[13] Mustadrak Alwasa’il: m 2 sh 358

[14] Nahali:90

[15] Mustadrak Alwasa’il: m 2 sh 257

[16] Attahrim:6

[17] Biharul-Anwar:m 97 sh 74

[18] Bakara:44

[19] Tauba:67

[20] Alu Imran:173

[21] An’am:68

[22] Ma’ida:79

[23] Dukkaninsu riwayoyi ne da zaka same su cikin littafin Mizamul Hikima sai ka koma can