فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Wilaya da bara'a

 

Allah madaukaki cikin bayyanannen littafin sa mai girma ya ce:

(قُلْ لا أسْألُكُمْ عَلَيْهِ أجْرآ إلاَّ المَوَدَّةَ فِي القُرْبَى وَمَنْ يَـقْتَرِفْ حَسَنَةً نَزِدْ لَهُ فِيهَا حُسْنآ إنَّ اللهَ غَفُورٌ شَكُورٌ).

Kace bana tambayarku wani lada kansa sai kauna ga makusanta

Duk wanda ya aikata aiki na kwarai zamu kara masa kyawu cikinsa lallai Allah mai yawan gafara ne mai yawan godiya ne.[1]

 

Lokacin da annabi (s.a.w) ya tashi da isar da sakon manzancinsa sakon sama saukakka, ya tseratar da larabawa daga jahilcinsu na jahiliyya, Allah ya daukaka musulmai cikin addininsu, sun zo wajen annabi mafi karamci (s.a.w) don su bashi lada sakon da ya zo musu da shi, da nauyinta nauyayya da ya dauke shi, sai cikin gaggawa aminin Allah Mala'ika Jibrilu (as) ya sauka da wannan madaukakiyar aya  

 (قُلْ لا أسْألُكُمْ عَلَيْهِ أجْرآ إلاَّ المَوَدَّةَ فِي القُرْبَى ).

Kace bana tambayarku wani lada face nuna kauna ga makusanta.

 

Ma'anarta: shi ne ko nuna kauna ta da soyayyata cikin makusantana daga gareku, ku kiyaye ni cikinsu.

Ko kuma dai ma'anarta shi ne ku so makusantana da tsatsona ku kiyaye ni cikinsu.

1-Ya zo daga bangarori biyu daga Ibn Abbas ya ce: lokacin da aya madaukakiya ta sauka sun ce ya manzon Allah (s.a.w) su wane ne wadannan mutane da ka umarce mu da kaunarsu? Sai ya ce: Fadima da Ali da yayayensu

وفي حديث ، قال رسول الله  9 :

«إنّ الله تعالى خلق الأنبياء من أشجار شتّى ، وخلقت أنا وعليّ من شجرة واحدة ، فأنا أصلها، وعليّ فرعها، وفاطمة لقاحها، والحسن والحسين ثمارها، وأشياعنا أوراقها، فمن تعلّق بغصنٍ من أغصانها نجا، ومن زاغ هوى ، ولو أنّ عبدآ عبد الله بين الصفا والمروة ألف عام ثمّ ألف عام ثمّ ألف عام ، حتّى يصير كالشنّ البالي ، ثمّ لم يدرک محبّتنا، أكبّه الله على منخريه في النار، ثمّ تلا: (قُلْ لا أسْألُكُمْ عَلَيْهِ أجْرآ إلاَّ المَوَدَّةَ فِي القُرْبَى )».

2- ya zo cikin wani hadisi, manzon Allah (s.a.w) ya ce: lallai Allah madaukaki ya halicci annabawa daga bishiyoyi mabanbanta, an halicce ni da Ali daga bishiya daya, ni ne jijyarta, Ali kuma reshenta, Fadima kuma ita ce Allurar ta kililinta, Hassan da Husaini kayan marmarinta, yan shi'ar mu kuma su ne ganyenta, duk wanda ya ratayu da reshe daga reshenta ya kubuta ya tsira, duk wanda ya kauce musu kuma ya halaka, da wani bawa zai bautawa Allah tsakanin dutsen safa da marwa tsawon shekaru dubu sannan ya kara shekaru dubu dubu, har ya kai ya zama kamar tsohuwar gorar ruwa, sannan ya zama bai samu soyayyar mu ba, Allah zai kifa fuskarsa a wuta, sannan ya karanto wannan aya: (kace bana tambayar ku lada face soyayya cikin makusanta.

Sannan tsiwirwirar aiki na kwarai shi ne nuna kauna ga iyalan Muhammad (s.a.w) kamar yanda ya zo a cikin riwayoyi masu tarin yawa da tafsirai daga shi'a da sunna. Su ka koma ka duba.

وقال الرازي في تفسيره الكبير: روى الكلبي عن ابن عباس ، قال  : إنّ النبيّ  9 لمّا قدم المدينة كانت تنوبه نوائب وحقوق وليس في يده سعة ، فقال الأنصار، إنّ هذا الرجل قد هداكم الله على يده ، وهو ابن اُختكم ، وجاركم في بلدكم ، فاجمعوا له طائفة من أموالكم ، ففعلوا، ثمّ أتوه به فردّه عليهم ، ونزل قوله تعالى : (قُلْ لا أسْألُكُمْ عَلَيْهِ أجْرآ)، أي على الإيمان ، إلّا أن تودّوا أقاربي ، فحثّهم على مودّة أقاربه ، ثمّ قال ـأي الرازي ـ نقل صاحب الكشّاف :

3- Razi cikin tafsirinsa Alkabir ya ce: malam Kalbi daga ibn Abbas ya rawaito cewa, ya ce: lallai annabi (s.a.w) lokaicn da ya shigo madina damuwa daban daban da hakkoki su ne maye masa kuma babu yalwa a hannunsa, sai mutanen madina suka ce: lallai wannan mutumin Allah ya shiryar da ku ta karkashinsa , kuma shi dan `yar'uwarku ne, sannan makocin kune a garinku, ku dan tattara masa wani yanki daga dukiyoyinku mana, sai suka aikata haka, sai suka dauki kudin suka kai masa, sai ya mayar musu da kudadensu, sannan fadin Allah ya sauka: (kace bana tambayarku lada kansa).[2]

 ma'ana kan imani, sai dai ku kaunaci makusantana. Sai ya kwadaitar dasu kan kaunar makusantansa, sannan Razi ya ce: mai littafin Kushshafu ya nakalto:

عن النبيّ  9، أنّه قال  :

«من مات على حبّ آل محمّد مات مغفورآ له ، إلّا ومن مات على حبّ آل محمّد مات تائبآ، ألا ومن مات على حبّ آل محمّد مات مستكمل الإيمان ، ألا ومن مات على حبّ آل محمّد بشّره ملک الموت بالجنّة ثمّ منكر ونكير، ألا ومن مات على حبّ آل محمّد يزفّ إلى الجنّة كما تزفّ العروس إلى بيت زوجها، ألا ومن مات على حبّ آل محمّد  9 فتح له في قبره بابان إلى الجنّة ، ألا ومن مات على حبّ آل محمّد جعل الله قبره مزار ملائكة الرحمة ، ألا ومن مات على حبّ آل محمّد مات على السنّة والجماعة ، ألا ومن مات على بغض آل محمّد جاء يوم القيامة مكتوب بين عينيه آيس من رحمة الله، ألا ومن مات على بغض آل محمّد لم يشمّ رائحة الجنّة ».

4-daga annabi (s.a.w) cewa shi ya ce: duk wanda ya mutu kan soyayyar iyalan gidan Muhammad ya mutu yana mai kasantuwa ana gafarta masa zunubansa, duk wanda ya mutu kan soyayyar iyalan gidan annabi ya mutu yana mai tuba, duk wanda ya mutu yana kan soyayyar iyalan Muhammad yam utu yana mai cikakken imani, duk wanda yam utu kan son iyalan Muhammad ya mutu Mala'ikan mutuwa yana mai masa bushara da aljanna sanan munkir da nakiru, duk wanda ya mutu yana son iyalan Muhammad za a raka shi aljanna kamar yanda ake raka amarya dakin angonta, duk wanda ya mutu kan soyayayyar iyalan Muhammad cikin kabarinsa za a bude masa kofofi biyu na aljanna, duk wanda ya mutu kan son iyalan Muhammad Allah zai sanya kabarinsa maziyartar Mala'ikun rahama, duk wanda ya mutu kan soyayyar iyalan Muhammad ya mutu kan sunna da jama'a, duk wanda ya mutu kan kiyayyar iyalan Muhammad ranar kiyama zai zo goshinsa an rubuta cewa ya debe tsammani daga rahamar Allah, duk wanda ya mutu kan kiyayyar iyalan Muhammad ba zai taba jin kamshin aljanna ba.

5- mawallafin littafin Alkushshafu ya rawaito daga annabi (s.a.w) cewa makusantan da soyayyarsu da kaunarsu ta wajaba su ne: Ali da Fadima da yayansu.

Cikin zaman tahiyar sallah duk wanda bai yi salati kansu sallar sa bata karbu ba, wannan haka hukuncin yake wurin dukkanin mazhabobin cikin muslunci, wannan na nuni da kan cewa soyayyar iyalan Muhammad wajibi ce.

Shugaban mazhbar shafi'iyya ya ce:  

يا آل بيت رسول الله حبّكمُ         فرضٌ من الله في القرآن أنزلهُ

كفاكمُ من عظيم الشأن أنّكمُ         من لم يُصلِّ عليكم لا صلاة لهُ

Ya iyalan gidan manzon Allah soyayyarku farilla ce daga Allah da ya saukar da ita cikin kur'ani.

Ya isar muku cikin girman sha'ani cewa duk wanda bai salati gareku ba babu sallah gare shi.

 

A wani wajen kuma ya ce:

يا راكبآ قف بالمحصّب من منى         واهتف بساكنِ خيفها والناهضِ

سحرآ إذا فاض الحجيج إلى منى         فيضآ كملتطمِ الفرات الفائضِ

إن كان رفضآ حبّ آل محمّدٍ         فليشهد الثقلان أنّي رافضي

 

Ya kai mahayi ka tsaya wajen tsakwanni daga mina ka daga sautinka wanda ke zaune da mike ya jika lokacin alfijir idan mahajjata sun kwararo zuwa ga mina kwarara kamar wanda ya gwamutsu da furatu yana mai kwarara

Idan har rafilanci shi ne soyayyar iyalan Muhammad to mutane da aljannu su yi shaida da cewa ni barafile ne.

وعن النبيّ الأكرم :

«حرمت الجنّة على من ظلم أهل بيتي وآذاني في عترتي ».

6- daga annabi mafi karamci (s.a.w): an haramta aljanna ga wanda ya zalinci ahalin gidana ya cutar da ni cikin tsatsona.

Na'am. wannan kadan daga tafki, wani dan digo daga kogi cikin tafsirin wannan aya mai daraja, akwai daruruwan riwayoyi masu daraja kwatankwacinta, kuna iya komawa littafin Biharul Anwar mujalladai na – 23-24-25-26-27 dukkaninsu cikin bahasin imamanci, sannan daga mujalladi na 15-53 cikin tarihin annabi da tarihin A'imma tsarkaka, wannan littafi daya daga dubunnan litattafai cikin wannan fage.[3]

Bai buya ba cewa wajabcin kauna yana lazimta wajabcin da'a, kamar yanda hakan yake tabbatacciyar gaske wajen ma'abota tantancewa.

Da wannan ne ake banbancewa tsakanin soyayya da kauna, lallai ita kauna ma'anarta shi ne soyayya tare da kauna, son Ahil-baiti baya isarwa face idan ya kasance cudanye da da'a da imani da cewa su wajibi ne a yi musu biyayya.

 

عن الإمام الباقر، قال  :

«وصّى النبيّ  9 إلى عليّ والحسن والحسين  :، ثمّ قال في قول الله : (يَا أيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أطِيعُوا اللهَ وَأطِيعُوا الرَّسُولَ وَاُوْلِي الأمْرِ مِنْكُمْ ) ، قال  :

الأئمة من ولد عليّ وفاطمة إلى أن تقوم الساعة ».

7-daga Imam Bakir (as) ya ce: annabi (s.a.w) ya yi wasiyya ga Ali da Hassan da Husaini, sannan cikin fadin Allah (yaku wadanda kuka yi imani ku yi da'a ga Allah da manzon Allah da ma'abota al'amari)[4] ya ce: su ne A'imma daga `ya`yan Ali da Fadima har zuwa ranar tashin kiyama.

وعن مولانا أبي جعفر، قال  :

«ذروة الأمر وسنامه ومفتاحه وباب الأنبياء وباب الأشياء ورضى الرحمن : الطاعة للإمام بعد معرفته ، قال : إنّ الله يقول : (مَنْ يُطِعِ الرَّسُولَ فَقَدْ أطَاعَ اللهَ) ، أما لو أنّ رجلا قام ليله ، وصام نهاره ، وتصدّق بجميع ماله ، وحجّ دهره ، ولم يعرف ولاية وليّ الله فيواليه ، ويكون جميع أعماله بدلالة منه إليه ، ما كان له على الله حقّ في ثوابه ، ولا كان من أهل الإيمان ،

ثمّ قال : اُولئک المحسن منهم يدخله الله الجنّة بفضله ورحمته ».  

8-daga shugaban mu Abu Jafar (as) ya ce: kololuwar al'amari da tozansa da mabudinsa da kofar annabawa da kofar abubuwa da yardar Allah, biyayya ga Imami bayan saninsa, ya ce: Allah yana cewa: ( duk wanda ya yi da'a ga manzon Allah hakika yayi da'a ga Allah)[5] amma da za a ce wani mutum ya raya darensa da ibada ya kuma azumci yininsa yayi sadakar dukkanin dukiyarsa yayi hajji tsawon rayuwarsa, amma kuma tare da haka bai san wilayar waliyinsa ba da zai masa biyayya, dukkanin ayyukansa su kasance karkashin shiryarwarsa daga gare shi zuwa gare shi, to da bai da hakkin Allah ya bashi ladan ibadarsa, da ma kuma bai kasance daga ahalin imani ba, sannan ya ce: wadancananka mai kyautatawa Allah zai shigar da shi aljanna da falalarsa da rahamarsa.[6]

Hakika Allah matsarkaki madaukaki da manzon sa mafi karamci cikamakin annabawa Muhammad (s.a.w) sun yi umarni da wilayar tsatso tsarkaka, Allah da manzon sa sun yi umarni da soyayyarsu da kaunarsu, da bin dabi'unsu, da barranta daga makiyansu masu nuna musu kiyayya da masu inkarin falalolinsu, ba wani abu ne addini ba face soyayya don Allah da kiyayya don Allah.

Jibanci da nuna kauna ga masoya Allah, da barranta daga makiyansu suna daga cikin farillolin addini da wajiban Allah.

Wilaya da bara'a ma'ana soyayya da kiyayya duk da cewa suna daga ayyukan zuciya sai dai cewa ita zuciya ita ce shugaba kan gangan jiki, sannan su mutane suna kan addinin shugabanninsu ne, idan zuciya ta gyaru gabban ciki da waje sai su gyaru, mutum ya gyaru cikin tafiyarsa da sulukinsa, lallai tafiya d ahalaye na gyaru da gyaruwar zuciya, sai kufaifayin kauna da soyayya su bayyanu cikin tunanin mutum masoyi da sulukinsa, har sai ya narke saboda masoyansa rabautattu yana mai da'a da tsarkakewa, lallai masoyi na da'a ga masoyinsa yana kuma sadaukar da ai da dukiya, yana iya hawan maratayu saboda masoyinsa da kuma akidarsa da imaninsa da waliyan Allah, da shiriyarsu yake shiriya, kufaifayinsu da sawunsu yake bi, yana da abin kwaikwayo mai kyawu daga gare su, kamar yanda fushi da kiyayya ga makiyan Allah anabta da wilaya da suke tajalli kan harshensa da ayyukansa da aikinsa, baya damuwa da mutuwa ta afka kansa ko kuma shi ne ya afka kan mutuwa, hakan na kasancewa yayin da zuciya ta cika makil da kin makiya Allah da manzon sa da Ahlil-baiti da barranta daga gare su, masoyin Ahlil-baiti ma'asumai bai saba musu cikin karamin lamari da babba, yana kuma siffantuwa da siffofi alheri da adalci, yana samun mafo cikar rabo daga kamalar tsarkakar zuciya, daga imani da aiki nagari da ilimi mai amfani, lallai soyayya tsarkakka tana da alamomi da kufaifayi cikin tafiya da suluki.

9-hakika manzon Allah mafim karamci masoyin ubangijin talikai shugaban annabawa da manzanni Muhammad (s.a.w) ya ce:  

«من رزقه الله حبّ الأئمة من أهل بيتي فقد أصاب خير الدنيا والآخرة ، فلا يشكّن أحد أنّه في الجنّة ، فإنّ في حبّ أهل بيتي عشرون خصلة ، عشر منها في الدنيا، وعشر منها في الآخرة .

Duk wanda Allah ya azurta shi son A'imma daga Ahlin gidana hakika ya dandagatar da alheri a duniya da lahira, ka da wani mutum ya yi shakka cewa shi yana cikin aljanna, lallai soyayya Ahlil-baiti yanada darajoji ashirin, goma a duniya goma a lahira

أمّا التي في الدنيا: فالزهد، والحرص على العمل ، والورع في الدين ، والرغبة في العبادة ، والتوبة قبل الموت ، والنشاط في قيام الليل ، والياس ممّا في أيدي الناس ، والحفظ لأمر الله ونهيه عزّ وجلّ ، والتاسعة : بغض الدنيا، والعاشرة  : السخاء.

Amma darajojin duniya: shi ne zuhudu da kwadayi kan aiki na kwarai, da tsantseni cikin addini, da kauna cikin ibada, da tuba gabanin mutuwa, da nishadi cikin raya dare, da debe tsammani daga abin da yake hannun mutane, da kiyaye umarnin Allah da haninsa Azza wa Jalla, ta tara ita ce kin duniya, ta goma: kyauta.

وأمّا التي في الآخرة : فلا ينشر له ديوان ، ولا ينصب له ميزان ، ويعطى كتابه بيمينه ، ويكتب له براءة من النار، ويبيضّ وجهه ، ويكسى من حلل الجنّة ، ويشفع في مائة من أهل بيته ، وينظر الله عزّ وجلّ إليه بالرحمة ، ويتوّج من تيجان الجنّة ، والعاشرة : يدخل الجنّة بغير حساب .

فطوبى لمحبّي أهل بيتي ».

Amma wadanda suke lahira: babu abu de masa diwani, ba a kafa masa mizani, ana bashi littafin sa a hannun dama, ana rubuta masa barranta daga wuta, ana haskaka fuskarsa, ana tufatar da shi daga kayan adon aljanna, ana bashi ceto cikin mutum dari daga mutanen gidansa, Allah yana kallonsa da rahama, ana daura masa kan sakin da kan sarkin aljanna, ta goma: zai shiga aljanna ba tare da hisabi ba.

Daraja ta tara tana daga kasha na farko kin duniya domin shi son duniya shi ne jagaban kowanne kuskure, yaya masoyin duniya , mumini yana kuskure, ta yaya zai sabawa Allah da manzon sa da ma'abota lamari ahalin gidansa, idan ya aikata sabo cikin sauri zaka samu ya fadaka ya nemi gafara ya tuba zuwa ga makaginsa ba kuma zai kuma kara aikatawa ba karo na biyu, wannan yayyafi ne daga yayyafin kauna, haske daga hasken wilaya, baa i kira ba cikin muslunci da misalin kiran da akai cikin wilaya, kamar yanda ya zo cikin ingantaccen hadisi, lallai ita wilaya ita ce ruhin muslunci da haikakaninsa, ita wilaya cudanye take da aiki da ibada idan aka rabata da su zata zama kamar gangar jiki babu ruhi, lallai gangar jiki za ta rube ta yi wari, iskar ibada ba tare da wilaya ba tana cutar da mashakan irfani da ruhukan garai-garai na malakutiyya, da zukatan ruhaniyya, duk wanda ya sameta zai tsinkayi abin da nake fadi a bayyane.

10-Alwilaya, kadai dai ita hade take da aiki, bau wilaya idan babu aiki, haka ma babu aiki idan babu wilaya, ga wani hadisin Imam Bakirul ulum maulana Muhammad bn Ali (as) lokacin da yake magana da Jabir Ju'ufi: 

«أيكتفي من انتحل التشيّع أن يقول بحبّنا أهل البيت ؟ والله ما شيعتنا إلّا من اتّقى الله، وما كانوا يعرفون يا جابر إلّا بالتواضع والتخشّع وكثرة ذكر الله والصوم والصلاة والتعهّد للجيران من الفقراء وأهل المسكنة والغارمين والأيتام وصدق الحديث وتلاوة القرآن وكفّ الألسن عن الناس إلّا من خير، فكانوا اُمناء عشائرهم في الأشياء...».

Shin wanda ya danganta kansa da shi'anci zai iya wadatuwa da fadin cewa yana son mu Ahlil-baiti? Wallahi babu shi'ar mu face wanda yake jin tsoran Allah, ba a kasance ana saninsu ba ya Jabir face da tawali'u da kankan da kai da yawaita ambaton Allah da azumi da sallah da taimakon makota daga talakawa da  matalauta da mabarata da marayu da gaskiya cikin magana da karatun kur'ani  da kame harsuna daga barin mutane face da fadin alheri, sun kasance amintattun cikin al'ummarsu cikin abubuwa.

إلى أن قال  :

«من كان لله مطيعآ فهو لنا وليّ، ومن كان عاصيآ فهو لنا عدوّ، ولا ينال ولايتنا إلّا بالورع والعمل

    Har zuwa in da ya ce: (duk wanda ya kasance mai da'a ga Allah to masoyin mu ne, amma wanda ya kasance mai sabon Allah to makiyin mu ne, ba a samu soyayyar mu sai da tsantseni da aiki)

Mamaki ta kaka ba za mu so ahalin gidan isma ba, wadanda su ne a gidajensu akai izinin daukaka sunan Allah ana kuma aka saukar da littafin Allah, da su ne ake sanin daidai, su ne ma'aunin ayyuka, shugabannin halittu baki daya, rukunan kasa, jagororin bayi, su ne halifofin manzon Allah (s.a.w)

Ya kai wannan bawan Allah tsakaninka da Allah yanzu ta yaya zamu fifita wanda mutane suka fifita kan wanda Allah ya bashi fifiko da kansa? Yanzu wanda yake shiriyarwa zuwa ga gaskiya shi yafi cancanta a bi ko kuma wanda baya shiriyarwa sai dai shima a shiryar da shi?

Ta yaya za mu bi wanda yake fadin ku kwabe ni ku cire ni, da kuma wanda ya ce dukkanin mutane sun fi shi ilimi hatta mata masu hidima!!

Ace kuma mu ki biyayya ga wanda cikin falalarsa da mukaminsa da wilayarsa da da'arsa ayoyi dari uku suka sauka, kai daya bisa ukun kur'ani, kamar yanda bangarori biyu suka nassanta haka daga sunna da shi'a- ba kowa bane da ya wuce shugaban wasiyyai Imamin waliyyai, ubangidan masu kadaita Allah sarkin muminai zakin Allah mai galaba Aliyu bn Abi dalib (as) kamar yanda dubunnan hadisai suka gangaro, ma'ajiya ta cika makil da falalarsa da `ya`yansa ma'asumai A'imma madamaita, ta yaya alhalin hatta makiyi ya boye falalarsa saboda tsananin gaba, masoyi kuma ya boye saboda tsoro, amma tare da haka falalarsa ta cika sama da kasa, na nakashceka daga hadisin Saklaini tsarkakka shi kadai hanyoyin da aka nakalce shi sun kai hanya dari biyu da hamsin daga sunna da shi'a daga Sihahu Sitta da Kutubul Arba'a da mujalladai da sauran litattafai.

 

11-Hakika manzon Allah (s.a.w) mai ceton dukkanin mutane baki daya ya ce:

«إنّي تارکٌ فيكم الثقلين : كتاب الله وعترتي أهل بيتي ، ما إن تمسّكتم بهما لن تضلّوا بعدي أبدآ، ولن يفترقا حتّى يردا عليَّ الحوض ، فانظروا كيف تخلفوني وتحفظوني فيهما، وإنّ الله سائلي وسائلكم ، فما أنتم قائلون ...».

Lallai ni mai bar muku nauyaya guda biyu ne: littafin Allah da tsatso na Ahalin gidana, matukar kuka yi riko da su ba za ku taba bata bayana ba har abada, ba kuma zasu taba rabuwa da juna ba har sai sun gangaro tafkina, ku duba yaya zaku halifantar da ni da kiyaye ni cikinsu. Lallai Allah zai tambaye ni zai kuma tambaye ku, me zaku gaya masa…..

Daga wannan furuci na ubangiji muke samun manzo mafi girmama (s.a.w) yana maimatawa musulmi wannan haidisi a bayyane, yana kuma umartarsu da wilayar mutanen gidansa, cikin kowacce munasaba yana mai neman al'umma ta yi riko da su ta yi riko da kur'ani mai girma:

 (وَآعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللهِ جَمِيعآ وَلا تَفَرَّقُوا)

Kuyi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba.

Cikin rikonku da igiyar Allah.[7]

 

Hakika Allah da manzon sa sun nufi wannan al'umma mumina mai tsinkaya mai imani da manzanci da ta yi riko da A'imma tsarkaka, da soyayyarsu da kin makiyansu, hadisan manzon Allah (s.a.w) dangane da A'imma Isna Ashariyya mutawatirai sun da shakali mai ban mamaki, wannan shakali babu inda yake gasgatuw ada dabbakuwa face kan A'imma Isna Ashariyya daga Ahlil-baiti, nauyayya na biyu wanda manzo ya barwa al'umma shi domin shiryar da su da kuma kare shari'ar muslunci daga bata da rushewada karkacewa daga asalai.

Yayin da ya zama babu wani mutum da zai iya inkarin wannan riwaya da suka kan sanadinta sakamakon tawatirancinta da yawaitar mariwaitan ta daga malamai, sai wasu makiya suka yi kokarin kawar da wadannan hadisai daga ma'anarsu, wasu mutane kuma suka yi tawili, duk yanda makiya suka kai da fafutika wajen kawar da wadannan hadisai daga ma'anarsu, lallai ko dai adadi ya ragu ko kuma ya karu, to lallai wadanda suke kira da Hulafa'ur Rashidun basu kai adadin ba, sannan kuma sarakuna Umayyawa sun haura adadin, Abbasiyawa kuma sun ninninka adadin, wasu daga malamansu sun yi kokarin tsakuro wani adadi daga Umayyawa da Abbasiyawa domin kammala adadin don su zo da shi a cike wanda hakan ta tilata su shigar sarakunan zalunci da bata kamar misalin Mu'awiya da Yazidu da Abdul-malik bn Marwan da `ya`yansa- tare da haka basu iya cika adadin da yazo cikin hadisin ba, sunayen da suka zaba suka kunyata su ya zamanto wadanda suka kasa da adadin da manzon Allah (s.a.w) da Allah zasu nufi su kasance jagororin al'umma tsaraikun kur'ani mai girma, kamar yanda akwai wasu hadisai da suka yi bayanin sunayen A'imma a bayyane karara, ba zai yiwu wani ya kawo rudu sakamakon yawansu da tabbatarsu.

Hakika malamai masu tarin yawa sun walaffa littafi mai cin gashin kansa da suka tattaro hadisai da suka gangaro daga manzon Allah (s.a.w) kan Ai'imma goma sha biyu, kuna iya duba littafin (Kifayatul Asar fil nususi ala A'immatu Isma Ashariyya) wallafar Shaik Abu Abdullah Ahmad bn Abdullah bn Abbas, da littafin (Al'intisaru fi Nassi ala A'immatu Adhar) wallafar Muhammad bn Ali bn Usman Karraji) da littafin (Isbatul Huda) wallafar Shaik Hurrul Amili, mutumtaka cikin tarihinta mai tsayi bata shaida wasu mutane misalin A'immar mu ba goma sha biyu, wadanda Allah ya tafiyar musu da datti ya tsarkake su tsarkakewa, su ne matattarar faloli da kyawawan halaye da madaukakan misalai, duk wata rayayyiyar al'umma tana damuwa da rayuwa manyan mutanen cikinta da shugabannin ta, zaka same ta tana gina mutum mutumi na tunawa da su da girmama su, ta koyar da darasin rayuwarsu ga al'ummar da suka zo bayansu, sakamakon wayewarsu da karfafa da'awarsu tsarkakarta, yafi kamata ga al'ummar musulmai musamman ma a wannan zamanin zamanin farkawar muslunci, su karanta rayuwar A'immatu Ahlil-baiti ba tare da ta'assubanci da taklidi ba, su binciki kufaifayinsu da hadisansu, domin su bi tsarin hanyar da suka bi, su diba daga ilimansu da rayuwarsu su samu samfuri ba haikika rayayye, da zai kais u bakin gabar aminci, da kololuwar daukaka da azurta, su samu alherin da suke nema, domin tutar izzarsu ta dawo tana filfila cikin duniya karo na biyu.

(قُلْ هَذِهِ سَبِيلِي أدْعُو إلَى اللهِ عَلَى بَصِيرَةٍ أنَا وَمَنِ آتَّبَعَنِي وَسُبْحَانَ اللهِ وَمَا أنَا مِنَ المُشْرِكِينَ ).

Kace wannan ne tafarki na ina kira zuwa ga Allah a kan basira ni da wanda yake bina tsarki ya tabbata ga Allah ni bana daga masu shirka.[8]

Daga cikin abin da yake radadi cikin rai, yake kuma yanke nadin zuciya shi ne cewa wasu ba'arin mutane shaidan yayi galaba kansu, sun yi watsi da hanyar Ahlil-baiti, sun tafka kuskure cikin fifita wasu kan Ahlil-baiti, sun yi watsi da ikirari da imamancinsu saboda zalunci, da danne hakkokinsu wadanda Allah da manzon sa suka halasta musu, kamar yanda hakan yake zalunci ne ga kawukansu sakamakon jayayyarsu ga gaskiya da kaucewa hanya madaidaiciya, tare da sanin falalarsu da girman mukaminsu madaukaki

 (وَجَحَدُوا بِهَا وَآسْتَيْقَنَتْهَا أنْفُسُهُمْ ظُلْمآ وَعُلُوّآ) .

Kuma suka yi jayayya da ita saboda zalunci da gurman kai zukatansu sunyi yakini da su.[9]

Wannan hadisi ma'abocin bakin ciki kuma akan kirjin farko nauyi mai gima na afkawa daga wannan biyayya da bai'a, Allah yana da sha'ani kan halittunsa, sannan karkacewarsu daga gaskiya shi ne sababin abin da muke gani a yau daga wasan kurar da kafirai suke da dukiyoyin musulmai da mamaya da buwayar fajirai bare a kansu, da mulkin mallakarsu da daka wawa kan alheran da suke tare da sun a zahiri da badini.

Ya zama dole a raya rukunai biyu na asasi wato wilaya da bara'a- barranta daga makiya Allah cikin al'ummar musulmi, mu dawo tsatso tsarkaka da kur'ani mai girma da sunna muhammadiya tacacciya tare da dukkanin iklasi, mu komo zuwa ga jagororin shiriya, su ne hanyar zuwa ga Allah matsarkaki, su ne kofar Allah wadanda daga gare su ake zuwar masa, da su Allah ya bude da su kuma zai hattama, kadai dai ana kimanta ayyuka da wilayarsu, kamar yanda hakan ya zo cikin madaukakan hadisai mutawatirai da ayoyin kur'ani mai daraja nassantattu bayyanannu, lallai mafi falalar bigire a ban kasa shi ne tsakanin rukuni da mukam    

ويقول الرسول الأكرم  9 :

«ولو أنّ رجلا عمّر ما عمّر نوح في قومه ألف سنة إلّا خمسين ، يصوم النهار ويقوم الليل ، في ذلک الموضع ـما بين الركن والمقام ـ ثمّ لقي الله بغير ولاية أهل البيت لم ينفعه ذلک شيئآ، ومن لم يوالِ عليآ لم يشمّ رائحة الجنّة ، ولم يدخلها».

12- manzon Allah mafi karamci (s.a.w) yana cewa: da a ce wani mutum zai rayu misalin yanda Nuhu ya rayu cikin mutanensa shekaru dari tara da hamsin, ya zama ya raya darensa da ibada ya azumci yininsa, cikin wannan muhalli tsakanin rukunu da mukamu, sannan ya hadu da Allah ba tare da yana da wilayar Ahlil-baiti ba babu abin da wancan hali zai amfana masa, duk wanda bai yiwa Ali wilaya ba zai taba jin kamshin aljanna ba, ba kuma zai shiga ba. 

وقال  :

«لو أنّ رجلا صلّى وصفّ قدميه بين الركن والمقام ، ولقى الله ببغضكم أهل البيت دخل النار»

13- amincin Allah ya kara tabbata a gare shi, ya ce:

Da wani mutum zai yi sallah ya daidaita kafafunsa tsakanin rukunu da mukamu, sai ya zamanto ya hadu da Allah yana mai kiyayya da Ahlil-baiti wuta zai shiga.[10]

وقال معلّم البشرية ومنذرهم  :

«والذي بعثني بالحقّ نبيّآ، لو أنّ رجلا لقي الله بعمل سبعين نبيّآ، ثمّ لم يأتِ بولاية وليّ الأمر من أهل بيتي ، ما قبل الله منه صرفآ ولا عدلا» .

14- malamin dukkanin mutane mai gargadinsu (s.a.w) ya ce: 

Na rantse da wanda ya aiko annabi da gaskiya da ace wani mutum zai hadu da Allah da irin ibadar annabawa saba'in , sannan ace bai zo da wilayar shugaban lamari ba daga Ahalin gidana ba, da Allah bai karbi wanin aikin farilla ba ko na mustahabbi daga gare shi ba.[11]

Daga karshe Muhakkikul Faizul Kashani cikin littafin sa Minhajul Najat) yana cewa: (son waliyyan Allah wajibi ne haka ma kin makiyansu da jagororinsu musammam wadanda suka zalunci Ahlil-baiti kan hakkinsu suka kwace musu gadonsu suka jirkita sunnar annabinsu haka ma kin wadanda suka tauye bai'ar imamancinsu).

Babu laifi in jawo hankulanku zuwa ga maudu'I muhimmi, shi ne: tarihin shi'anci yana komawa zuwa ga zamanin annabi mafi karamci (s.a.w) lallai shi cikin wurare da daman gaske ya ambaci sarkin muminai Ali (as) da shi'arsa masu karamci, lallai su zababbu ne, lallai suna daga ahalin aljanna, wannan shi ne abin da bangarori guda biyu na shi'a da sunna suke ambata cikin litattafansu-kuna iya komawa cikin littafin (Asalul Shia wa Usuluha)- amma isdilahin sunna wal jama'a hakika tun farko ya zo ne cikin harsunan mabiya Mu’awiya.

Hakika musulmai sun sassaba sun juya kan bayansu bayan wafatin annabi mafi girma (s.a.w) sun karkasu zuwa kashi saba'in da uku, kamar yanda annabi ya bamu labarin faruwar hakan, sannan mai shiriya mai bushara da gargadi fitila mai haske ya nusantar damu zuwa ga kungiya ta shiriya da misalin hadisin Saklaini mutawatiri daga dukkanin bangarori biyu, haka ma da hadisin jirgin tsira    

«مثل أهل بيتي كسفينة نوح ، من ركبها نجى ، ومن تخلّف عنها غرق وهوى » ،

Misalin ahalin gidana cikinku kamar misalin jirgin annabi Nuhu ne, duk wanda ya shige shi ya tsira dukkan wanda ya juya baya ya nutse ya halaka.

Haka ma da daruruwan hadisai da madaukakan riwayoyi, kamar yanda kur'ani ya mikar da hakan.

Sai dai cewa mu imamiyya Isna Ashariyya, muna hukunci da tsarkakar kungiyoyin muslunci, duk da cewa mun saba cikin abubuwan da Asalai da reshe suka kebantu da su, muna mu'mala tare da su, auratayya da gado suna gudana tsakaninmu da su, a kowanne lokaci muna kiran dukkanin musulmi zuwa ga hadin kan muslunci, da riko da igiyar Allah baki daya cikin wannan zamani da muke ciki sakamakon kasantuwar makiyinmu guda daya ne duka mu biyun shi ne girman kan duniya da dukkanin karfin sa na yammaci (Amerika) da gabashi (Rasha)da karnukan farautarsu da yaransu.

Sai dai cewa akwai wasu kungiyoyi da muke zartar da hukuncin kafirci da najasa kansu duk da cewa suna danganta kansu da muslunci, kamar misalin Kawarijawa da Gullatu da nawasib da mujassima, sakamakon suna inkarin larurorin addini, ko kuma sakamakon nassi ya bayyana karara kan kafirtarsu da riddarsu larurorin addini, Amma Kawarijawa sun kafirta ne sakamakon inkarin jumla daga larurorin addini, kamar misalin halasta kisan sarkin muminai Ali (as) da wadanda da suke tare da shi daga musulmi da kuma, da kuma kafirta duk wanda ya sanya wani yayi hukunci, su sun fita daga addini.

15- ya zo daga annabi mafi karamci cikin siffanta su (s.a.w):

«إنّهم يمرقون من الدين كما يمرق السهم من الرامي ».

Lallai suna fita daga cikin addini kamar yanda kibiya ta ke fita daga kwari da baka.

Amma Gullatu su ne wadanda suka ketare iyaka cikin A'imma ma'asumai: har takai ga sun yi da'awar ubangijintaka cikinsu, suka yi da'awar cewa sarkin muminai Ali (a.s) wannan bawa salihi da cewa shi ne makagi mahalicci, suka yi inkarin abin da aka san gurbartarsa da larurorin addini.

 

16-ya zo cikin madaukakin hadisi daga Abu Hassan (a.s) cewa ya ce: 

«توقّوا مساورته ».

Ku kauracewa ruwan da ya sha ya rage.

 

Amma nasibawa su ne wadanda suka kafa kiyayya da Imam Ali (a.s) da `ya`yansa tsarkaka (a.s) da shi'arsa cikin zukatansu.

 

17-ya zo cikin hadisin Abu Ya'afur daga Imam Sadik (as)   

«لا يغتسل من البئر التي تجتمع فيها غسالة الحمّام ، فإنّ فيها غسالة ولد الزنا، وهو لا يطهر إلى سبعة آباء، وفيها غسالة الناصب ، وهو شرّهما، إنّ الله لم يخلق خلقآ شرّآ من الكلب ، والناصب لنا أهون على الله من الكلب ».

Ba a wanka daga ruwa rijiyar da cikinta akwai ragowar ruwankan gidan wanka, saboda cikinsa akwai ruwan dan zina, shi kuma ba ya tsarkaka har zuwa iyaye bakwai, cikinsa akwai ruwan banasibe, shi ne mafi sharri daga biyun, Allah bai halicci wata halitta ba mafi sharri daga kare, banasibe yafi wulakantuwa wurin Allah daga kare.

18- ya zo cikin wani hadisi daban:

إنّ الله تبارک وتعالى لم يخلق خلقآ أنجس من الكلب ، وإنّ الناصب لنا أهل البيت لأنجس منه.

Allah albarku sun tabbata gare shi madaukaki bai halicci wata halitta mafi najastuwa daga kare ba, makiyin mu Ahlil-baiti yafi najastuwa daga kare.

 

Amma Mujassima, su ne masu cewa Allah yanada jiki kamar sauran jikkuna, ko kuma shi jiki ne ba irin sauran jikkuna ba, sai suka tafi kan jikkantuwar Allah wacce take kore mukamin wajibul wujud ga zatinsa, wanda hakan yake lazimta masa imkani da bukatuwa, Allah ya daukaka daga haka daukaka babba.

Ma'auni cikin kafircin kungiyoyi masu sabawa daga musulmi shi ne inkarin laurorin addini ko kuma abin da ya nassantu kan kafircinsu, na'am ba a shigar da mai zagin annabi (s.a.w) da imami ma'asumi (a.s) da Zahara (a.s) daga cikinsu wadannan su masu keta alfarmar muslunci da fadi da aiki duk da cewa kashe shi wajibi ne, haka ma wanda yayi imani da sabanin gaskiya daga musulmi bai shiga karkashin ma'aunin da aka ambata a baya, kamar misalin mai musun nassi kan sarkin muminai (as) saboda a misalin wannan zamanin fatawa shi ne tsarkakarsu, duk da cewa lokacin bayyanar Sahibul Amri (as) zai musu mu'amala sabanin mu'amalar da muke musu a wannan zamani, kamar yanda Allah madaukaki yake musu mu'amala bayan rabuwar ruhinsu da gangar jikinsu, kadai dai mu na hukunci da tsarkakarsu bisa tafiyar kan abin da ya shahara tsakanakanin malamai, bari dai ta yiwu ya zaa larurar mazhaba, sakamakon yankakkiya sira daga sauran kungiya ta gaskiya, cikin sauran zamanunnuka da garuruwa, sakamakon yankewa cudanyar A'imma tsarkaka da sahabbansu hatta shugabanninsu da wadanda suka assasa mazhabarsu, saboda gamewa da tsanani da tsananta da wahala kan kaddara najasa, da kuma nassoshi masu tarin yawa, bari dai mutawatirai cikin halascin abin da yake kasuwar musulmi da tsarkaka, tare da yankewa da karancin imamiyya cikin baki dayan  zamanunnuka musammam ma zamanin gangarowar wadancan nassohi, ballantana har ace suna da kasuwa da za ta zama muhallin da maudauin wadancan hukunce-hukunce, wannan yana daga mafi karfafar dalilai kan tsarkakar wadannan mutane   sannan ya zo cikin hadisai madaukak tsakanin muslunci da imani, muslunci shi ne kalmomin shahada guda biyu.

19- ya zo cikin Usulul Kafi daga Sufyanu bn Samad ya ce; wani mutum ya tambayi Abu Abdallah (as) tsakanin muslunci da imani, mene ne abanbanci tsakanin su? Sai yaki amsawa, sannan ya kara tambayar sa, yaki amsawa, sannan mu ka hadu kan hanya a lokacin tafiya ta kusantowa mutum.

Sai Abu Abdullah (as) ya ce: kamar tafiya ta kusanto maka? Sai ya ce: na'am.

Sai ya ce: ka zo gida ka same ni.

Sai ya je ya same shi, ya tambaye shi meye banbanci tsakanin muslunci da imani?

Ya ce: muslunci shi ne zahirin da mutane suke kai shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Muhammad manzon Allah (s.a.w) da tsayar da sallaha da ba da zakka da azumn watan Ramadan da ziyartar dakin Allah.

Ya ce: (imani sanin wannan al'amari, ma'ana wilaya Ahlil-baiti:, tare da wannan idan ya ikirari da imani amma kuma bai san al'amari to ya kasance musulmi batacce).

وفي خبر سماعة ، قال : قلت لأبي عبد الله الإمام الصادق  7 : أخبرني عن الإسلام والإيمان ، أهما مختلفان ؟

فقال : «الإيمان يشارک الإسلام ، والإسلام ولا يشارک الإيمان ».

فقلت : فصفهما لي ؟

فقال : «الإسلام شهادة أن لا إله إلّا الله، والتصديق برسول الله، وبه حقنت الدماء، وعليه جرت المناكح والمواريث ، وعلى ظاهره جماعة الناس . والإيمان الهدى ، وما ثبت في قلوب من صفة الإسلام وما ظهر من العمل ».

20- ya zo cikin riwayar Samma'atu, ya ce: na cewa Abu Abdulah Imam Sadik (as) ka bani labari dangane da muslunci da imani, shin su biyun suna da banbanci da juna?

Sai ya ce: imani yana tarayya da muslunci, amma muslunci baya tarayya da imani).

Sai na ce: to siffanta mini su?

Sai ya ce: ( muslunci shi ne shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, da kuma gasgata manzon Allah,, da shi ne jinane suka samu kariya, a kansa auratayya da gado suka gudana, kan zahirinsa jama'ar mutae ke kai, amma imani da shiriya, abin da ya tabbatu cikin zukatan mutane yana daga siffar muslunci abin da kuma ya bayyana yana daga imani.

وفي خبر حمران بن أعين ، عن الباقر  7، قال : سمعته يقول  :

«الإيمان ما استقرّ في القلب ، وأفضى به إلى الله تعالى عزّ وجلّ ، وصدق العمل بالطاعة والتسليم لأمره ، والإسلام ما ظهر من قول أو فعل ، وهو الذي عليه جماعة الناس من الفرق كلّها، وبه حقنت الدماء، وعليه جرت المواريث ، وجاز النكاح ، واجتمعوا على الصلاة والزكاة والصوم والحجّ ، فخرجوا بذلک من الكفر، واُضيفوا إلى الإيمان ».

21- ya zo daga hadisin Himrana bn A'ayun, daga Bakir (as) ya ce: naji shi yana cewa: imani shi ne abin da ya samu tabbatuwa cikin zuciya, ya gangarar da shi zuwa ga Allah Azza wa Jalla, ya gasgata aiki da da'a da mika wuya zuwa ga umarnin sa, shi muslunci shi ne abin da ya bayyana daga furuci ko aiki, shi ne abin da mutane suke kai daga kungiyoyi baki dayansu, da shi ne jinane suka samu kariya, kansa gado ya gudana, auratayya ta halasta, suka hadu kan sallah da zakka da azumi da hajji, sai suka fita daga kafirci da hakan, aka jingina su zuwa ga imani.

إلى أن قال فيه : قلت : فهل للمؤمن على المسلم في شيء من الفضائل والأحكام والحدود وغير ذلک ؟

Har zuwa inda ya ce: shin mumini yana da wata falala daga falaloli da hukunce-hukunce da haddodi da wanin haka da ya fifici musulmi da ita 

فقال  :

«لا، هما يجريان في ذلک مجرى واحد، ولكنّ المؤمن فضّل على المسلم في أعمالهما، وما يتقرّبان به إلى الله عزّ وجلّ ».

Sai ya ce: ( a a a cikin wadannan suna gudana kan maguda guda daya, sai dai cewa mumini an fifita shi kan musulmi cikin ayyukan su da abin da suke neman kusanci zuwa ga Allah Azza wa Jalla da shi.

Wannan hadisi yana da tsayi sai dai zamu takaita da wannan gabar.

A takaita ce abin da yake daga cikin hadisai shi ne cewa musulmi baya fita daga muslunci zuwa kafirci face sai in yayi jayayya da inkarin abin da yake larura a muslunci, sannan yanda lamarin yake a wani lokacin akan amfani da muslunci da ma'anar abi da yake tarayya da imani akan kiran ma wanda bai gasgata wilaya ba da wannan suna bisa tsuran bayyana kalmomin shahada biyu, sannan kafirci yana kishiyantar sa cikin abubuwa guda uku, kamar yanda yake cewa mumini yana kan na farko, haka ma kan wanda ya gasgata wilaya, wilayar Ahlil-baiti A'imma goma sha biyu da imamancinsu. Wannan shi neabin da ya zo cikin littafin (Tahrirul Wasila) cikin kashe-kashen najasosi:

Na goma daga cikin najasa akwai kafiri: shi ne wanda ya dangantu zuwa ga wani addinin daban, ko kuma wanda ya dangantu da muslunci amma kuma yayi jayayya da abin da aka sani da larura daga addini ta yanda jayayyar sa za ta koma ga inkanin sakon muslunci, ko karyata annabi (s.a.w) ko tauye shari'ar sa tsarkakakkiya, ko kuma wani abu da yake hukunta kafircinsa ya gangaro daga gare shi daga furuci ba tare da banbanci ba tsakanin murtaddi da kafiri na asali na harbi da zummi

Amma nasibawa da kawarijawa Allah ta'ala ya la'ance su lallai su najasa ne ba tare da tsayuwar hakan ba kan jayayyar su ya koma ba ga inkarin manzanci, amma gullatu idan gullancin say a kasance yana lazimta inkarin Allantakar Allah, ko tauhidi ko annabta to shi kafiri ne, ida kuma ba haka ba ne to ba kafiri bane.

Wadanda ba `yan shi'a Isna Ashariyya ba ne daga kungiyoyin shi'a, idan nasibanci da kiyayya da zagin sauran Imaman da bas u yi imnai da imamancinsu ba bai bayyanu daga gare su to a nayi musu hukunci da tsarkaka, amma idan ya bayyanu daga gare su to basu da banbanci da sauran nasibawa.

 Wannan kenan, hakika na bijira kan misalin wadannan bahasosi, domin samun cikakkiyar fahimtar Usulul dini da bayani dalla-dalla sai a komawa littafin (Bidayatul Fikri fi sharh Babul Hadi Ashar) ko kuma (Alkaulul Hamid fi sharh Tajrid)

Amma cikin wannan risala da darasi na gaggawa zan takaitu da abin da na ambata domin gujewa tsawaitawa, domin a san cewa ita wilaya cikin imamanci tana daga asalan addini, wilaya da da'a ga Muhammad da iyalan gidansa tsarkaka suna daga rassansa, ita wilaya bisa laakari da nasabtawar Allah kamar annabta tana daga ayyukan Allah, sai ta shiga cikin asalan addini da ilimin kalam (Aka'id) amma bisa la'akari da kaunar cikin zuciya da da'a tana shiga cikin rassan addini sai su zamanto daga fikihu domin sun ratayu da ayyukan mukallafai, saboda wannan ne muke imani da wilaya duk da kasantuwarta daga rassa, sai dai cewa bisa la'akari da shugabanci game gari cikin addini da duniya lallai imamanci cigaban hanyar annabta ne kuma nasabta wasiyyi da waliyi na hannun Allah matsarkaki to lallai ta wannan fuskar za ta kasance daga asalan addini.

Babu laifi mu rufe wannan fasali da addu'ar shugaban mu zainul Abidin shugaban masu sujjada Aliyu bn Husaini (as)  

«اللهمّ صلّ على محمّد وآل محمّد، شجرة النبوّة ، وموضع الرسالة ، ومختلف الملائكة ، ومعدن العلم ، وأهل بيت الوحي .

Ya Allah ka salati ga Muhammad da iyalan Muhammad bishiyar annabta, muhallin sauke sako, wurin shige da ficen Mala'iku, ma'adanin ilimi, da Ahalin gidan wahayi.

اللهمّ صلّ على محمّد وآل محمّد، الفُلک الجارية في اللجج الغامرة ، يأمن من ركبها، ويغرق من تركها، المتقدّم لهم مارق ، والمتأخّر عنهم زاهق ، واللازم لهم لاحق .

اللهمّ صلّ على محمّد وآل محمّد، الكهف الحصين ، وغياث المضطرّ المستكين ، وملجأ الهاربين ، وعصمة المعتصمين .

Ya Allah kayi salati ga Muhammad da iyalan Muhammad jirgi mai gudana cikin kumfar kogi mai karo da juna, dukkanin wanda ya hau wannan jirgi yana tsira, duk wanda ya bar shi zai nutse, wanda ya gabace su ya fita daga shiriya, dukkanin wanda ya jinkirce su ya gushe, wanda ya lazimce su ya na riska.

Ya Allah kayi salati ga Muhammad da iyalan Muhammad karfaffen shinge, taimakon wanda yake cikin larura da talauci, mafakar gudaddu, kariyar masu neman kariya.

اللهمّ صلّ على محمّد وآل محمّد، صلاةً كثيرةً تكون لهم رضىً ولحقّ محمّد وآل محمّد أداءً وقضاء، بحولٍ منک وقوّة ، يا ربّ العالمين .

اللهمّ صلّ على محمّد وآل محمّد، الطيّبين الأبرار الأخيار، الذين أوجبت حقوقهم ، وفرضت طاعتهم وولايتهم .

Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da iyalan Muhammad salati mai tarin yawa da zai kasance yarda gare su ya kuma zama saukewa sauke nauyi da biyan bashi ga hakkinsu, da karfi da dabara daga gareka, ya ubangijin talikai.

Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da iyalansa tsarkakakku rabautattu mafi alherin mutane wadanda ka wajabta hakkokinsu farlanta da'arsu da wilayarsu

اللهمّ صلّ على محمّد وآل محمّد، واعمر قلبي بطاعتک ، ولا تخزني بمعصيتک ، وارزقني مواساة من قترت عليه من رزقک بما وسعت عليّ من فضلک ، ونشرت عليَّ من عدلک ، وأحييني تحت ظلّک ...» .

Ya Allah kayi salati ga Muhammad, ka raya zuciya ta da biyayyarka, ka da ka kunyata ni da sabona, ka azurtani da taimakon wand aka kuntata kansa daga arzikinka daga abin da ka yalwata kaina da falalarka da abin da ka yada daga adalcinka, ka raya ni karkashin inuwar ka…


[1] Shura:23

[2] Kushshaf Zamakshari: m 2 sh 173

[3] Na fitar da wadannan riwayoyi daga Biharul-Anwar

[4] Nisa’i:59

[5] Nisa’i:80

[6] Biharul-Anwar: m 23 sh 194

[7] Alu Imran:108

[8] Yusuf:108

[9] Namlu:14

[10] Amali Dusi:73

[11] Amali Mufid:75