فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

dalilin annazamu (tsari)

 

A larurance dukkanin abin da yake da tsari, to lallai shi yana shiryarwa zuwa ga mai tsari mai tsarawa mai hikima mai iko masani, wannan duniya daga kwayar zarrar ta har zuwa manyan dunyoyinta na taurari tana da wani tsari kebantacce, da zata sabawa wannan tsari da gwargwadon silin gashi da baki dayan duniya ta kone, ya zama tilas ya kasance tana da makagi mahalicci mai hikima mai tafiyarwa gyangyadi ko bacci bai daukar sa, idan ba haka ba ta kaka ga mada daskararra wacce bata da rayuwa bata da ihsasi da riska bata da tunani bata kaga ga wannan duniya mai babba ace wai ita ce take tasiri cikinta?

 Ta kaka mafi kankantar mai tasiri zai kasance cikin mafi daukakar daraja? Wannan kammaluwa abin hankalta cikin shakalan samuwa cikin zawiyyar wannan duniya faffada lallai tabbas hujja ce da dalili yankakke kan tabbatuwar samuwar mahalicci.

Da za ka kyale kallo cikin wannan halittu kasantattu ka dawo da kallonka cikin gangar jikinka da abin da ke kunshe cikin sa daga gabbai da gaeffa da sake-sake tsararru da jijiyoyi da zaka samu yakini lallai cewa kana da makagi mahalicci mai surantawa daga wannan ne riwaya mai daraja ta gangaro             

      «من عرف نفسه فقد عرف ربّه »،

Dukkanin wanda ya san kansa hakika ya san ubangijin sa. Tabbas wannnan duniya tana da mahalicci makagi

Da dalilin dukkanin abin da ke cikin wannan duniya daga ayoyi da tsaruwa da shiryuwa.

(سَنُرِيهِمْ آيَاتِنَا فِي الآفَاقِ وَفِي أنْفُسِهِمْ حَتَّى يَـتَـبَـيَّنَ لَهُمْ أنَّهُ الحَقُّ ) .

Da sannu za mu nuna musu ayoyinmu cikin sasanni da cikin kawukansu har sai ya bayyana gare su lallai cewa shi gaskiya ne.