فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

dalilin illa da ma'aluli

 

Daga cikin abin da yake larura shi ne cewa dukkanin wani ma'aluli yana da illa, cikin wannan duniya muna samun tsari da dokar illa da ma'aluli da dukkanin bayyanuwa, ya zama tilas ga dukkanin ma'alulat ya zama suna da illa ta fari da take kwararar da samuwa kan ma'alulat daga wujudul mudlak mudlakul wujud (tsantsar samuwa) wanda shi ne Allah matsarkaki madaukaki.

 

«سئل أعرابي : ما الدليل على وجود الله تعالى ؟ فقال : البعرة تدلّ على البعير، والأثر يدلّ على المسير، فكيف بسماوات ذات أبراج وأرض فجاج لا تدلّان على اللطيف الخبير؟».

An tambayi balaraben kauye: mene ne dalili kan samuwar Allah madaukaki? Sai ya ce: kashin rakumi na shiryarwa kan cewa akwai rakumi, sawu na shiryarwa kan tafiya da cewa kuma an taka wajen, ta kaka ga sammai ma'abociyar burujai da kasa ma'abociyar hanyoyi ba za su shiryar zuwa ga mai tausasawa masani ba?.

Sannan akwai daruruwan dalilai da hujjojin hankali kamar dalili hisabin tsammani yankakka kan tabbatar mahalicci makagi girman sa ya girmama, amma dalilan nakali wadanda suka cika fal daga dalilan hankali to ka zantar babu laifi daga ayoyi bayyanannu da riwayoyi masu daraja, domin farkon da'awar annabawa da wasiyyan su kadai dai ta kasance daga kira zuwa ga dayanta Allah da imani da shi matsarkaki madaukaki da watsi da gumaka da ubangijan boge.

Sannan imani da Allah matsarkaki da bubbugar rayuwa daga gare shi bata kasance mas'ala wofintatta ba da bata da ba ta da alaka da rayuwa, bari dai ita mas'ala ce da ta alakantu da zuciya da rayuwar baki dayan mutane.

Sannan imani da Allah bai kasance natijar rigimgimu da tufka da warwarar dabaka bako kuma daga kirkira azzalumai masu cin galla, saboda wannan imani ya gabata cikin tarihin dan Adam ma'ana ya gabaci rigimgimu da tufka da warwarar dabaka daga wannan fuskar.

Wannan imani baI kasance daga natija da sakamakon tsoro dangane da annobar dabi'a ba, da addini ya kasance ya samu sakamakon tsoro da mun sami ma'abota riko da addini su ne sukafi kowa tsananin tsoro, tare da cewa wadanda suke dauke da hasken addini a tsawon tarihi zamu same su su ne mafi tsananin dakiya da karfi, su dangane da Allah zargin mai zargi bai damun su . Bari dai wannan imani yana bayyana daga fizga ta asali cikin dan Adam ya zuwa ratayuwa da mahaliccin sa da yakini zurfaffa da yake riska da fidirarsa da tsarin halittar sa zuwa ga alakar mutum da ubangijin sa da duniyar sa.