Amsoshi na hankali da nakali

 

da Allah matsarkaki ya kasance yana da

 sama da ya kasance yana zaune kan ala'arshin sa, yana saukowa daga ita kamar yadda mutum ke ke sauka daga kan mimbarin sa, lallai al'amarin yadda yake shi ne ana nufin wannan sama ta waje mai bigire, domin shi Allah mai girma da daukaka yan sama da halittunsa, sannan yana kasancewa sama da mutane, zahiri dai taken samaniya dangane dasu  da kuma ita al'amarin da ya danganta, lallai shi yana sassabwa da sassabawar zamani da wuri, wanda yana lazimta haddi iyaka da karewa a wannan lokaci sai ya zamanto murakkabi shi kuwa dukkanin abu murakkabi mabukaci ne matalauci ne yana kuma lazimta masa yiwuwa, sai sakamakon haka ya kasance wajibul wujud cikin zatin sa mai yiwuwa ne wanda ba zata taba sabuwa ba har abada.

Na biyu: tare da kasantuwar kasa kewayayya kamar kwallon kafa kamar yadda hakan ya tabbata a ilimin zamani. Yaa lazimta masa cewa sama ta kasance ba tare da karshe ba, sai ya lazimta Allah ya kasance iyakantacce da iyakancewar jazibiya kasa (fizgarta) , lallai yadda al'amarin yake kowanne na da saman sa da ya kebantu da shi bisa abin da ke tare da shi daga kebantacce bigire, wannan na daga abin da ke cin karo da dayantar Allah da dayantuwarsa shi daya ne da bai da na biyu bai da tarkibi cikin sa, lallai shi babu wani abu kwatankwacin sa.

Na uku: abin da aka fadi daga sama da bata da karshe itace mafarar sama ubangijintaka, sai ya lazimta msa iayakantuwa da karshe da mafara da karshe.

Na hudu: idan ya kasance ana nufin saman Allah ba tare da jazibiyar kasa ba bari dai da abin da ke bayan jazibiyar kasa da sama wadda ta danganta, to a wannan lokaci zai zamanto ya lazimta saman zata rasa ma'anarta, sai ya kasance mafhumi ba tare da misdak ba(ma'ana ba tare da abin da ta gasgatu kan sa ba) a wannan lokaci ta kaka za ai suranta cewa al'arshi Allah tana saman kasa ko kuma ace tana saman duniya.

Na biyar: da ya kasance yana cikin kowanne dare yana saukowa daga al'arshin sa da ya lazimta al'arshin sa ya wofinta daga shi har abada, saboda shi dare yana lazimta kewayarwa kasa a kowanne lokaci ba yankewa cikin daya rabin da ke kishiyanta wanda yake kasancewa cikin yini?

Wannan kadan kenan daga abin da ke garemu daga gaskiya ta hakika.