Mukaddima

 

 

 Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah wanda yake shafe abin da ya so ya kuma tabbatar da abin da ya so kuma gurin sa uwar littafi take, tsira da aminci su kara tabbata ga mafi daukakar halittun sa shugaban manzanni Muhammad da iyalan sa ma'asumai, dawwamammiyar tsinuwa ta tabbata kan makiyan su har zuwa tashin kiyama.

Ya ubangiji ka buda bakina da fadin shiriya ka kuma kimsa mini tsoran ka.

Bayan haka; hakika matsarkaki madaukaki ya ce: 

 (وَلا تَقْفُ ما لَيْسَ لَکَ بِهِ عِلْمٌ إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُوادَ كُلُّ أُولئِکَ كانَ عَنْهُ مَسْوُلاً)[2] .

Ka da ka bibiyi abin da baka da sani kansa hakika ji da gani da zuciya dukkanin su ababen tambaya ne.

Lallai daga ciki kage da tuhume-tuhume da ake likawa kan shi'a da shi'anci daga fuskanin makiyan su, musammam ma mabiya makarantar Umayyawa yaran Ibn Taimiya, cewa shi'a sun yi imani da Bada'u ma'anar sa shi ne danganta jahilci ga Allah, lallai Allah ya tsarkaka daga haka, abin da `yan shi'a suke fadi yana lazimta kafirci da da bata.

Batun yaran Ibn Taimiya a takaice shi ne komar da Bada'au zuwa ga jahilci da nadama wanda hakan ya koru ga barin sa matsarkaki, sannan takaitacciyar amsa: lallai Bada'u da wannan ma'ana da suke bashi babu shakka yana kasancewa daga kafirci da bata, sai dai kuma shi Bada'u a fahimtar makarantar Ahlil-baiti (a.s) yana da ma'anar kebantacciyar bayyanuwa, abin da abokan rigima ke fadi yana komawa ne ga kuskurarriyar fahimtar su, hakan na kasancewa idan mun yi nufin kyautata musu zato, idan ba haka to lallai batun sun a daga karya da kage wanda ya samo asali daga binnanniyar kiyayya da take zukatan su tun lokacin da suka sunnan ta zagin Sarkin muminai (a.s) kan mimbarorin su da kashe shugaban shahidai da iyalan sa a ranar Ashura, (babu wani mutum daga garemu face kasashshe ko kuma wanda aka shayar da shi guba)hakan ba komai bane face matsananciyar kiyayya da yaudara da munafunci da tsabar neman rigima da kafirci, da zaluntar Ahlil-baiti da kwace hakkokin su bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w)

Amma bayani filla-filla da sanin tambaya da amsa lallai yana lazimta fara bayyana wasu ala'amura: