Na farko: abin da abokin dauki ba dadi yake fadi kan batacciyar Bada'u

 

Na biyu: Bada'u a luggan ce da isdilhan ce.

Na uku: Bada'u a makarantar Ahlil-baiti da mabiyan su daga malamai da manya-manyan masana.

Na hudu: hujjojin imamiya kan Bada'u wanda ya dace da hankali.

Na biyar: Bada'u karkashin hasken kur'ani da Ahlil-baiti.

Na shida: natijar imani da Bada'u

Na bakwai: tambayoyi tare da amsa kan imani da Bada'u

Katima: takaice bahasi.

Ba buya ba cewa maudu'in Bada'u ana kirga shi daga mas'aloli da aka buga jayayya kansa a ilimin tauhdi, wanda kansa aka bijiro da bahasi mai fadin gaske tsakanin malaman ilimin tauhidi tun farkon karnin fark, sabanin a wancan zamani cikin mas'alolin ilimin tauhidi, ana kirga Bada'u daga larurar mazhabar imamiya isna ashariya, kamar yanda yake bayyana daga hadisai da suka kan wannan mukami, sai dai cewa ba kamar yanda abokan rigima suke tunani da suranta shi ba ko kuma mu ce yanda suke sharara karya da kage kan shi'a, lallai Bada'u idan ya kasan ce da ma'anar sauya ra'ayi wanda haka ya bubbugo daga jahilci da nadama, to lallai wannan ba zai taba yiwuwa ba har abada kan hakkin sa madaukaki matsarkaki, imamiya basu tafi kan wannan ma'ana basu yi imani da ita  ba ta kowacce irin fuska, bari imamiya sun tafi kan cewa hakan ba zai taba sabuwa ba har abada kuma hakan kafirci ne duk wanda yayi imani da wannan ma'ana kafiri ne, kuma wajibi a barranata daga gare shi domin shi lallai batace ne mai batarwa.

Idan Bada'u ya kasan ce da maanar sa wacce hanakali ya ke karba- da sannu zai bayyana-wanda wajibi imani da shi, shi ne wanda aya mai albarka ta bayyana shi:

(يَمْحُوا اللهُ ما يَشاءُ وَيُثْبِتُ وَعِنْدَهُ أُمُّ الْكِتابِ )[3] ،

Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar da abin da ya so wurin sa uwar littafi take.

Wannan da ma'anar sa ta lugga kenan daga mudalakin bayyanuw, da kuma ma'anar sa a isdilahan ce daga kebantacce bayyanuwa.

Wanan shafewa da tabbatarwa yana tajalli cikin abin da Allah yake bayyanarwa kan harshen Annabin sa ko waliyin sa da wasiyin sa cikin zahirin hali sakamakon maslaha da take hukunta bayyanar da shi, sannan ya shafe shi, sai ya zama ya sauya abin da ya bayyanar, tare da gabatar sanin sa madaukaki.

Wannan shi ne Bada'u cikin kasantattu wand ayake kama da nasaki cikin nassosin shari'a, lallai Bada'u na hankali yana kama da nasakin hukunce-hukuncen shari'a d ata gabata da sabuwar shari'ar Annabin mu Muhammad (s.a.w) ko kuma muce yana kama da nasakin ba'arin hukuncehukunce da shari'ar Annabin mu (s.a.w) ta zo da ita kamar misalin sallah ana halin karkata zuwa masallacin baitul mukaddar matsayin akibla, wanda daga baya akai nasakin sa da juyowa zuwa ga dakin Ka'aba mai daraja.

Sannan shi'a bas u yi imani da irin wannan Bada'u da nasakin ba, hakika hakan na nuna iyakan ce ikon Allah da iradar sa da basu da kaidi da dabaibaiyi, kamar yanda kur'ani mia gima yayi ishara zuwa ga haka cikin jumlar daga akidojin Yahudawa cikin fadin sa madaukaki  

 (وَقالَتِ الْيَهُودُ يَدُ اللهِ مَغْلُولَةٌ غُلَّتْ أَيْديهِمْ وَلُعِنُوا بِما قالُوا)[4]

Yahudawa suka ce hannun Allah kulle yake Allah ya daure hannayen su ya kuma tsine musu bisa abin da suka fada.

Wannan abin da ya sadada zuwa cikin akidun wasu kungiyoyin muslunci wadanda ba Imamiya ba,[1] a lura sosai

Sannan babu abin da ya rage mana face tsunduma cikin maudu'I kamar yanda muka tsara cikin mukaddima daga bayanin al'amura bakwai da Katima mda yardar Allah, daga Allah muke neman dacewa da damdagatar.

Batu na farko: abin da abokin fada yake fadi dangane da Bada'u

Muhammad bn Abdul-Karim Shaharistani wanda yayi wafati hijira na da shekaru 548, a cikin littafinsa Almilalu wan Nihal[2] ya nakalto daga Salmanu bn Harizu Azzaidi haka ma Fakrul Razi yana mai hakaitowa daga gare shi a karshen littafinsa mai Suna (Almuhassalu) ya ce: Rafilawa sun kirkiri[3] maganganu biyu ga `ya shi'arsu wadanda babu wani da zai jayayya da su yayi nasara kansu kan wadannan maganganu guda biyu:  

Ta farko: Akidar Bada'u amfani da wannan akida na kara musu karfi da karfafa, sannan al'amarin bai kasancewa kamar yanda suka fada: Allah madaukaki ya sauya ra'ayi cikin sa.

Zurara bn A'ayuni yayin da yake bada labara kan alamomin bayyanar Imamul Hujja (a.s) ya ce wadancananka wasu alamomi ne da za so zo a lokacinsu, bada ban bada'u ba da na kira su da wadanda basu subucewa….har zuwa inda yake fadin daya maganar ta biyu: Takiyya, duk sanda sukai niyyar jayayya da shi idan aka ce musu wannan kuskure ne ko kuma gurbatar sa ta bayyanars musu sai suce: an mun fadi hakan ne sakamakon takiyya, maganar sa ta kare.

Ya nakalto daga Fakrul Razi yana cewa: Rafilawa sun yi imani da Bada'u kan Allah, shi ne cewa ya kudurce wani abu ya bayyanar da wani abu daban sabanin abin da ya kudurce, suna masu riko da fadin sa madaukaki:         

 (يَمْحُوا اللهُ ما يَشاءُ وَيُثْبِتُ وَعِنْدَهُ أُمُّ الْكِتابِ )

Allah ya shefe abin da ya so ya tabbatar da wanda ya so gurinsa uwar littafi take.[4]

Wannan gurbatacce lamari ne, domin shi ilimin ubangiji yana daga abubuwa da suke damfare da zatinsa kebantacce, da duk abin da ya kasan ce haka, shigar sauyi da canji cikin sa abin da da ba zai yiwu ba. Maganar ta kare.

Cikin wannan ishkali da nuna kiyayya an samu wasu jama'a sun bishi musammam ma daga makarantar wahabiyawan wannan zamani bisa biyewa babban malamin su Ibn Taimiya, sai suka dafa cikin wahami suka yiwa shi'a sharri da cewa sun danganta jahilci kan Allah da canja iradar sa, ko kuma ace yana yin nadama.

Wannan fahimta ta su tana kan kuskure bari ma dai ya wuce kuskure tsabar sharri da kage ne kawai kan shi'a, litattafan shi'a cikin fagen ilimin taudi da jidali sun cika zaurukan nazari a fadin duniya kowa na iya samun su don yin bahasi, abu da bazai yiwu ba a hankalce da nakalan ce ka samu shi'a yana imani da irin wannan fahimta kan bada'u wanda yake tukewa zuwa ga tabbatar da jahilci da nadama kan Allah madaukaki, ko kuma ace sauya iradar sa, wannan wata magana ce da take gurbatacciya a bayyane, hakika shi'a sun barranta daga wannan tuhuma da karya da sharri da kage.

Bari dai yana daga jumlar abin da ake kafa hujja da shi kan jirkitar Attaura da Linjila daga abin da ya zo daga tabbatar da jahilci ga Allah madaukaki, alal misali cikin Attauta bugu na uku madabba'ar Bairut shekara ta 1881 cikin (Ishahul Sadisu) cikin sa ya zo cewa: (sai ubangiji yayi fushi kan cewa yayi  mutum ne a doron kasa yayi takaici cikin zuciya, sai ubangiji ya ce: shafe shi daga dora kasar mutum wanda na halicce shi, da mutum tare da kwarjinin sa da dabbobi da tsuntsayen sama sakamakon ni nayi fushi da cewar ni nayi su) wannan na nuni zuwa canja iradar ubangiji wannan a gurbace yake.

Malaman shi'a da A'immar su tsarkaka tun ranar farko zuwa wannan zamani da muke ciki da ma wanda zai zo nan gaba basu da banbanci da malaman sunna ta fuskanin ra'ayi da hadisai cikin wannan fage.

Hadisai daga Ahlus-sunna sun yi ittifaki da na shi'a cikin shiryarwa zuw al'amura guda biyu da suke ta'allaka da akida da abin da ya zo cikin kur'ani mai girma, sune cikin farko duba da kallo ta yiwu ace basu dace da juna ba basu hadu ba a zahiri, tsakanin su akwai cin karo da juna, sune: da farko idan kuka ce alkalamin kaddarawa ya rigaya ya bushe tun azal, ba zai yiwu a samu canji da sauyi cikin abubuwa da kaddarori ba har abada, (idan ajalinsu ya zo basa gabata da kankanin lokaci ba kuma sa iya jinkirtawa)

Na biyu: Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar da wanda ya so.

Bayyanannen abu yake kuma sananne cewa abin da yake hukunta bushewar alkalami shi ne rashin samuwar canji cikin kaddarorin Allah, kamar misalin Karin shekaru da tauye su, yalwar arziki da kuntatarsa, da makamantan haka.

Haka zalika mai hukunta na farko shi ne rashin tasirin addu'a cikin tunkude bala'I, da rashin tasirin ayyukan alheri kamar sadaka cikin neman yalwar arziki da jinkirt ajali da makamantan haka.

Malamam muslunci sun yi bakin kokarin su cikin tunkude wannan shubuha da kuma cewa babu cin karo da juna tsakanin al'amura guda ma'ana bushewar alkalamin kaddara da kuma tasirin addu'a da sauran ayyukan alheri kan canja kaddara.

Amsa kan wannan matsala wacce take da dangantaka da mas'alar jabaru da tafwidi da mas'alar kada'au da kadar.

Daga cikin amsa: ubangiji yana da alluna guda biyu: lauhul ummul kitab: cikin abin da yake rubutawa da alkalamin kudura, sai kuma lauhul jabahatul mulki, suranta wannan yana tabbatuwa tare da duban hasken wanda yake da ma'amar yayewa, shi rubu haske ne, cikin haske daga haske: rubutun alkalamin kudura cikin lauhul mahfuz wanda shi ne allon tabbatattun abubuwa.

Sai lauhul mahawu wal isbat: shi ne allon canje-canje kamar misalin ratayayyun ajalai, cikin allon farko ajali yana kasancewa yankakke zartacce tabbatacce, wanda cikin sa fadin sa madaukaki yazo ( basa gabatar ko da kankanin lokaci ba kuma sa iya jinkirta masa) amma na biyu lauhul mahawu wal isbat ajalai sun kasan ce cikin sa ratayayyu, duk da cewa Allah ya kaddara ajali ya zo cikin rana kaza lokaci kazaa wuri kaza, sai dai kuma ya rataye shi kan addu'a da sadar da zumunci , duk wanda ya aikata su lallai Allah zai goge masa wannan ratayayyen ajalin, jirgin rayuwar say a tsallake wannan tasha da take gabansa ta da take cikin da bama-baman mutuwa cikin aminci ya tsallaka zuwa tasha ta biyu da ta uku, haka dai yayi ta tsallakewa har ya tuke ga tabbataccen ajali yankakke, wanda shi an rubuta shi ne a lauhul ummul kitab da lauhul mahfuz.

Sannan ya zo cikin hadisai daga Ahlil-baiti da bayyana mahawu wal isbat matsayin bada'u.

Sai dai cewa tare da haka mutanen naka sun cudanya da gwamutsa tsakanin jingina bada'u zuwa ga mutum da kuma jingina zuwa ga ubangiji, lallai cikin jinginawar su zuwa ga wani mutum yana daga abin da jahilci ya gabace shi, ma'ana shi wannan mutum da ya kasan ce ya jahilci al'amarin sai ani sabon ra'ayi ya zo masa kansa,sai jahilai magauta makaga cikin danganta shi'a cikin bada'un Allah da cewa yana lazimta jahilci gare shi, sai hakan ya zama dalili batawa shi'a suna da cewa wai suna dangantawa Allah jahilci, gaskiya al'amari shi ne abin da shi'a suke fadi cikin bada'uda ake dangana shi ga Allah ya banbanta da bada'un da ake dangantawa ga su Zaidu da Amru, abin da shi'a suke fadi yana daga tsantsar tauhidi kuma magaryar tukewar ilimi da ma'arifa ne ga Allah matsarkaki, natijoji akida da tarbiya na rattabuwa kansa kamar yanda da sannu zai bayyana da izinin Allah madaukaki, lallai imani da bada'u yana lazimta da kudurar Allah mudlaka, fa'idoji akida da ilimi da tarbiya na biyo bayan hakan, ta kaka mai da'awa zai da'awa, mai gasgatawa ya gasgata , mai sadar da zumunci ya sadar ba da ban imani da bada'u ba, hakika Allah ya shafe abin da ya so ya tabbatar da wanda ya so kuma gare shi uwar littafi take.[1] Mun ciro daga littafin Aka'idul imamiya na Shaik Rida Muzaffar sh 45-46.

[2] Almilalu wan Nihal j 1 sh 141

[3] Amfani da Kalmar kirkire ta bayyanar da munafunci mai fadinda yana nuna cewa maganganu biyu ba daga Allaha suke daga aljihunsu suka fito da su, wannan karara yiwa Allah karya ne da danganta karya ga A'imma tsarkaka (a.s) wadanda Allah ya tafiyar da dukkanin dattai daga gare su ya tsarkake su tsarkakewa wannan wani abu ne da shi'a da sunna sukai ittifaki a kansa cikin daukakar darajarsu

[4] Arra'adu: 39