ittifakin malaman muslunci daga shi'a da sunna

 

Hakika malumman shi'a da sunna sun yi ittifaki ta fuskanin hadisai da zantuttuka cikin wadannan abubuwa guda biyu da aka ambata, daga bushewar alkalami daga abin da zai kasan ce har zuwa tashin kiyama, daga lauhul mahawu da isbat.

Hakika jumlar hadisai daga bangaren sunna da shi'a sun zo da cewa lallai alkalami ya rigaya ya bushe daga abin da zai kasan ce har zuwa tashin kiyama, sai aka tambayi manzon Allah (s.a.w) cikin wanne abu kenan za mu yi aiki ya manzon Allah? sai ya ce: kuyi aiki kowanne abu an yassare shi ga abin da aka halicce shi domin shi.

Ya zo cikin Sahihul Bukari babul Kadri: alkalami ya rigaya ya bushe zuwa ga abin da duk zaka hadu da shi, haka ya zo cikin sauran litattafai dama ingantattun litattafan sh'a cikin bahasin mahawu wal isbat.

Abu Darda'i daga ya rawaito ta hanyar sunna kamar yanda malam Fakrul Razi ya nassanta abin da shi'a suka yi masa ishkali kai kan bada'au cikin tafsisrin sa mai suna Tafsirul Kabir ya nakalto daga annabi (s.a.w)

إنّ الله تعالى في ثلاث ساعات بقين من الليل ينظر في الكتاب الذي لا ينظر فيه غيره ، فيمحو ما يشاء ويثبت .

Hakika Allah madaukaki cikin yan lokuta uku na karshen dare yana kallon cikin littafi wanda wanin sa baya duba shi, sai ya goge abin da ya so ya tabbatar da da wanda ya so.

Ahlus-sunna anan basu banbanta da shi'a ba, suma sun yi imani da tasirin addu'a da sadar da zumunci da abin da yayi kama da haka cikin karuwar arziki da raya kasa da jinkirta ajali da sauransu, duka wannan yana daga bada'u da ya dace da hankali lazim ga kowanne musulmi ya fahimci haka, bawai ya kebanta da imamiya ba kadai, duk wanda bai iya fahimtar haka ba ya kasan ce mai tauyayyen imani da sanin ubangiji, kamar yanda da sannu bayanin hakan zai zo a nan gaba da yardar Allah.