Batu na biyu: Bada'u a luggan ce da isdilahan ce

 

Albada'u a larabce da ya zo da aliful mamdud kan wazanin (sama'u) suna ne na masdari daga bada yabdu  badawan, daga babin dalab, shi yana da ma'anar bayyana, malaman lugga sun kawo banban ce-banban ce ciki tsakanin masdari wanda yake shiryarwa zuwa ga afkuwa wani abu ba tare da kayyaduwa da daya daga cikin zamani ba ma'ana zamanin da ya wuce da wanda ake ciki da wanda zai zo nan gaba, da kuma tsakanin sunasa, daga ciki akwai ismul masdar wanda shi yana samuwa daga masdari, kamar misalin saumu (azumi) da siyam da gasalu da fataha- da kuma gusulu da damma, ana amfani da bada'u kan ra'ayi da yake bayyanuwa ga mutum cikin wani al'amari da hakikarsa take bayyanar masa ciki, ba a amfani da fi'ili daga gare shi ba tare da lamul jarra ba, alal misali sai ace  

فيقال بدا لزيد كذا.

Abu kaza ya bayyana ga Zaidu.

Haka ma akan ce abdaituhu ma'ana na bayyanar da shi, bada'atu shai'I na nufin farkon abin da yake bayyanuwa daga gare shi, badiyar ra'ayi ma'ana zahirinsa, wa bada lahu fil amri wani abu ya bayyana gare shi.

Ya zo cikin littafin lugga Assihahu na malam Jauhari: bada amru badawan misalin ka'ada ku'udan ma'ana ya bayyana, wa abdaituhu na bayyanar da shi… har zuwa inda yake cewa: wa bada lahu fi hazal ibda'I ma'ana wani sabon ra'ayi ya bayyana gare shi.

Haka ya zo cikin littafin Asasul Balaga na Jahiz: zu badawan da nun, ma'ana bai gushe ba sabon ra'ayi yana kara bayyana gare shi al'amari yana bayyana gare shi.

Shaik Dusi yana cewa: amma bada'u hakikaninsa cikin lugga shi ne bayyanuwa, saboda haka ne ma ake cewa (bada lana suwarul madina) ganuwar garin ta bayyana garemu, haka ana cewa (bada lana ra'ayu) wani sabon ra'ayi ya bayyana garemu.

Allah madaukaki ya ce:

 (وَبَدا لَهُمْ سَيِّئاتُ مَا عَمِلُوا)[1]  (وَبَدا لَهُمْ سَيِّئاتُ ما كَسَبُوا)[2]

 Munin abin da suka aikata ya bayyana gare su. Munanan abubuwan da suka tsiwirwira sun bayyanar musu.

Abin da ake daga dukkanin ayoyin shi ne bayyanuwa, ana amfani da haka cikin sanin wani abu sabo bayan da an jahilce shi haka zalika cikin zato.

Amru bn Abdul-Aziz ko Rabi'atu ya ce:

بدا لي منها معصم حين جمّرت         وكفّ خضيب زُيّنت ببنان

Tsintsiyar hannunta ta bayyana gareni lokacin da ruru* da tafin hannunta wanda ya sha lalle aka kayata shi da yatsu.

Ta yiwu ayi amfani da shi cikin wasu ma'anonin daban da suke lazimta bayyanuwa, da amfani na jeka nayi ka ta fuska, sai ya zamanto daga gare shi an nufi abin da yake lazimtar ma’anar sa, ya zama cikin alakar lazimi da malzumi, kamar misalin (kuruj, wujud, hudus, mujaharatu) sai ace: bada kaumun ma'ana sun fito, badiya fulan bil badawa, ma'ana wane ya bayyanar da kauyancin sa, ana amfani da Kalmar amma sai a nufi faruwa azaba take da zuwanta ba zato ba tsammani, kamar fadin sa madaukaki:

 (وَبَدا لَهُمْ مِنَ اللهِ ما لَمْ يَكُونُوا يَحْتَسِبُونَ )[3]  (وَبَدا لَهُمْ سَيِّئاتُ ما كَسَبُوا)[4]

Kuma ya bayyanar musu daga Allah abin da ba su kasan ce suna tsammaninsa ba.

Munanan ayyukan da suka tsiwirwira sai suka bayyana gare su.

(وَبَدا لَهُمْ سَيِّئاتُ مَا عَمِلُوا)[5] .

 Munanan ayyukan da suka aikata sai suka bayyana gare su.

Daga cikin abin da aka ambata za a san cewa nukudar da aka tarayya da juna cikin amfani da Kalmar bada cikin abin da aiki ya fada kansa a dukkanin mahallan shi ne amfani da Kalmar cikin ma'ana guda daya wato bayyanuwa a hakika, bawai bayyanar ra'ayi kadai sakamakon ingancin amfani da kamlar cikin bayyana ta daban ba ta ra'ayi ba.

Anan ya kamata mu yi ishara zuwa ga wata muhimmiyar gaba, ita ce: lallai cikin muhallin da akai amfani da Kalmar aka nufi bayyanar ra'ayi sannan aikatau cikin ya kasan ce kebantacce majazi, a wannan wuri lafazi bai daukar nauyin tabbatar da dalilin wannan bayyanuwa cikin ra'ayi, da cewar sakamakon jahilci ne, da ma'anar cewa wani sabon ra'ayi ya bayyanar masa, sabida da ya jahilci ingantaccen ra'ayi, da kuma cewa sakamakon nadama cikin ra'ayin da ya gabata, ko kuma da wani dalili dai na daban, sababin bayyanar ba a iya fahimtar sa daga lafazin cikin bada'u da yake da ma'anar mudlakin bayyana, bari dole ne a samu wata karina wata shaida da zata shiryar zuwa ga wadancan dalilai kan amfani da shi a matsayin majazi.

Sannan bai buya ba bayan tabbatuwar wada'in lugga ga bada'u da ma'anar bayyanuwa tsantsa ba tare da wani kaidi da lafazin bada'u zai afku mufradi cikin julma tarkibiyya lallai ma'anar sa ta farko ba zata sauya ba, abubuwan da lafuzza ke shiryawa zuwa gare su mufradai ne basa canjawa idan sun fada cikin jumloli na tarkibi.

Idan muka ce: (bada lillahi kaza) a zahiri daga wancan ma'ana mudlaka yake, shi kuma zahiri a duk inda yake hujja ne, ma'ana ya bayyana gare shi, wannan duka idna anyi la'akari da abin da yake shiryarwa kenan bisa wada'in lugga, amma bayyanar wani ra'ayi gare shi ko kuma wani abu daban koma bayan ra'ayi lallai bisa madogarar wada'in lugga babu wani dalili kan haka a hakikan ce.

Idan kace: ana fahimta wani ra'ayi daban daga lafazin (bada) daga harafin lamul jarra cikin lafazin jalala (lillahi) sai ya lazimta yawaitar ma'ana.

Sai in baka amsa da cewa ma'anar lamu bata wuce samar dangantaka da tsani sannan amfanarwa, a wannan lokaci sai ya zama nufar bayyanar wani abu ya dangantu da Allah madaukaki daga wannan jumla ta (bada lillahi) bai fita daga ka'idodjin tattaunawa a al'adan ce.

Kamar yanda yake daga ladubban muhawara ana amfani da lafazin (bada) cikin zuhuri na kinaya, da ma'anar tabbatuwar wani abu da a da babu shi.

Da ma'anar rataya irada jiddiya da labartar da fauwar abin da bai faru ba, ma'anar (bada lillahi kaza) ai abu kaza ya bayyana zuwa duniyar samuwa da a da babu shi, ya kuma kasan ce yana da dangantaka da Allah madaukaki, hakan ya kasantu da la'akari da kudurar Allah, ma'ana daga fuskar shiryarwar danganta da Allah kan cikakkiyar kudurarsa, da mashi'arsa madawwamiya kan zirin abubuwa da ake tsammanin faruwarsu, idan akwai abubuwan da suke hukunta samuwar su.

A wani lokacin canjawa na tabbatuwa ta hanyar samar da shingayen da suke hana faruwar wadancan abubuwa, ko da kuwa abubuwa da suke hukunta samuwarsu suna nan, wani lokacin kuma ta hanyar kawar da abubuwan da suke hukunta samuwarsu gabanin tabbatuwar tasirinsu cikinsu.

Misalin kan haka: abin da ya zo daga hadisai madaukaka da cewa shi'a a zamanin Imam Sadik (a.s) sun kasan ce suna imani da cewa babban `dan Imam Sadik (a.s) Isma'il shi ne zai gaji Imamanci, sai dai cewa Allah ya bayyanar da wani abu, ma'ana ya bayyanar da abin da ya buya gare su, ko kuma ya sanya shinge ya hana faruwar hakan, ko kuma ya cire abin da zai hukunta faruwar imamancinsa ta hanyar mutuwarsa a zamanin babansa, wannan ya kasan ce babin sanarwa da cewa kowanne irin abu a hannun Allah ayke Azza wa Jalla karkashin ikonsa yake , wannan yana daga burhanul inni, ma'ana kaiwa ga illa ta hanyar ma'aluli, ta hanyar mutuwar Isma'il zamu kai ga gano dawwamar mulkin Allah da shimfidar ikonsa cikin kowanne zamani da bigire, dangane da kowanne abu, da shaidar wannan wasiwasi ai gushe daga wurin masu shakka, hakama akidar masu cewa an riga ann gama al'amari kamar yanda Yahudawa suke fadi, fa'idar wannan bada'u dacacce da hankali da lugga ta komo zuwa ga bayi, saboda yana tukewa da akidarsu da cewa makagi mahalicci madaukaki hannunsa al'amari yake da farko da kuma karshe, shi kowacce rana cikin sha'ani yake, hannun Allah ba daure damke yake ba, kamar yanda Yahudawa suke fadi Allah ya tozarta su.

Tacewar magana: da farko: shi (bada) ismul masdar ne daga bada yabdu, am'anarsa ta lugga shi ne bayyana.

Na biyu: shi fi'ili ne lazimi da yake wadatuwa da iya fa'ili kadai, wani lokacin ana nakalto shi ta babin af'alul ta'adiya da yi masa shadda ko kuma ta hanyar damfara masa harafin jarra, misalin na farko fadin sa madaukaki:

ان تبدو الصدقات)

Idan kuka bayyanar da sadakoki.

وان‌تبدوا شيئاً أو تخفوه).

idan kuka bayyanar da wanu abu ko kuka boye shi.

Na uku: ana jingina bada da ga ma'abota hankali, kamar yanda ake cewa (bada kaumu) ma'ana sun fito fili, haka wani lokacin ana jingina da ga abin da ba ma'abota hankula misalin abubuwa da ake riska, kamar yanda ya zo cikin fadin wani mawaki: (bada li minha mi'isamu) tsintsiyar hannunta ya bayyana gareni, haka ma (bada lana suwarul baladi) ganuwar garin ta bayyana garemu.

kamar yanda ake jingina shi zuwa ga siffofin nafsu kamar yanda ya zo cikin fadin sa madaukaki

 (قَدْ بَدَتِ الْبَغْضاءُ مِنْ أَفْواهِهِمْ )[6]

Kiyayya ta bayyana daga bakunansu.

 (وَبَدا بَيْنَنا وَبَيْنَكُمُ الْعَداوَةُ وَالْبَغْضاءُ)[7]

Tsakaninmu kiyayya da gaba ta bayyana.

 (ثُمَّ بَدا لَهُمْ مِنْ بَعْدِ ما رَأَوُا الآْياتِ لَيَسْجُنُنَّهُ حَتّى حيüنٍ )[8] .

 Sannan ya bayyana gare su bayan sun ga ayoyi lallai su daure shi har zuwa wani lokaci.

Na hudu: nukdar da tattarar wadannan ma'anoni masu tarayya da juna wacce ake kira da jami'il ishtiraki tsakanin wuraren da akai amfani da Kalmar (bayyana) da (bayyanarwa) amma abin da aka cewa zuhur ta fuskanin lazimtawa da lazimai to shi wannan yana banbanta bisa wuraren da akai aiki da lafazi, lallai yand aal'amarin yake duk da cewa ana sanin abubuwa ta hnayar kishiyoyinta sai dai cewa kuma shi kishiyar bayyana yana sassabawa da sassabawar aikin da akai niyyar yi da shi.

Wani lokacin zuhuri bayyana na kishiyantar buya, a wani wurin kuma yana kishiyantar (rashi) wani karaon kuma ya kan kasancewa kishiyar (jahilci) cikin misalin (bada lana suwarul baladi) da

 (بَدَتْ لَهُما سَوْآتُهُما)[9]

Tsaraicinsu ya bayyana gare su.

Abin da yake kishinyantar bada'au da zuhur shi ne buya, ma'ana bayan ganuwar garin ta kasan ce a da boye gare su sai ta bayyana alamominta suka fito fili. Cikin misalin (bada lahu fi amri kaza) yana kishiyantar jahilci, ma'ana da ya kasan ce ya jahilce sai yanzu ya zamana ya san shi ya bayyanar gare shi, misalin fadin sa:

 (ثُمَّ بَدا لَهُمْ مِنْ بَعْدِ ما رَأَوُا الآْياتِ )[10]

Sannan ya bayyyana gare su bayan sun ga ayoyi.

Abin da yake kishiyantar kokwanto, sun kasan ce suna cikin kokwanto sai abin da yake yanke kokwantonsu ya bayyana gare su.

Cikin misalin (bada salahus samaratu) cikin abin da yake kishiyantar rashin nunar kayan marmarin, saboda ma'anar sa shi ne bayyanar nunar sa bayan da bai kasan ce nunanne ba, cikin misalin (bada kaumu) yana kishiyantar cirata daga wani wuri zuwa wani wuni, saboda ma'anar sa shi ne fitowar mutanen.

Bada'u cikin baki dayan wuraren da akai amfani da shi ya zo da ma'anar bayyana, wanda ma'ana ce ta lugga ta farko, kadai dai sabanin ya kasan ce ta fuskar abin da yake kishiyantar sa da lazimtarwa, yana sassabawa da sassabawar wurin da akai aiki da shi. Sai ka lura sosai.