Batu na uku: bada'u daga fahimtar makarantar Ahlil-baiti da mabiyan su

 

 Daga bayyanannen abu sananne shi ne cewa hakika mutanen garin Makka sune mafi sanin lokunan Makka, mutanen gida sune mafi sanin gida, abin da ya kamata ga duk mai son hukunta wani kan akidunsa to ya zama ya tanadi kwararan dalilai na ilimi, hakan na tabbatuwa cikin kasantuwar shi ma'abocin akidar da kansa ya bada labarin meye akidar sa, bawai dogaro da zato da kirdado ba wadanda dukkansu basu gamsar da komai daga gaskiya, da kuma samun sa yana karba daga abokin gaba kamar yanda haka shi ne galibi wurin mutane marsasa adalci da suke yi wa shi'a kage da sharri da karya kan akidun su, zaka same su suna karba hujjoji daga wurin abokin rigima makiyinsu, a bayyanae yake makiyi bai fadin gaskiya da hakika kan wanda yake gaba da shi, kadai dai zaka same shi yana bakin kokarin sa cikin fassara akidar makiyin sa ta yadda bukatar sa zata biya, yana rikar su matsayin makamai da zai bugi wanda yake kiyayya da shi, da kuma rusa akidar sa ta gaskiya, ta hanyar shigo da shubuhohi da shakku wadanda asalinsu daga munafuncin Shaidan yake kamar yanda ya zo cikin riwaya, hakika Iblis la'ananne shi ne farkon wanda ya fara wurgo da shubuhohi bakwai kan Mala'iku bayan da aka kore shi daga aljanna, da saukowar sa zuwa kasa, sai Allah ya bada labarin karyarsa da riyar sa da munafincinsa.

Idan muna son sanin hakikar bada'u wurin shi'a imamiyya to wajibi mu koma ga manyan malamansu wanda akai ittifaki da ijma'i kan jagorancinsu ga addini da ilimi, daga nan ne za mu koma zuwa ga mabubbugar maganganunsu da inda suka samo asali da kafa hujja da dalilai na nakali bayan na hankali, ta hanyar komawa zuwa ga ayoyin kur'ani mai girma sannan ingantattun hadisai da suka dogara da su wadanda aka rawaito su daga Manzon Allah (s.a.w) da iyalan sa tsarkaka A'imma ma'asumai.

Wannan shi ne zai zama adalci duk wani abu koma bayansa zai zama takaitawa da takaitar da kai, da kage da sharri da yunkurin kafirtarwa ba tare da dalili da hujja ba, (ku dagatar da su lallai su ababen tambaya ne).

Da wannan tunanin ne muke nuni zuwa ga jumla daga kalmomin manyan malaman mu magabata da wadanda suka zo bayan su, sannan zuw aga abin da ake kafa hujja da shi kan bada'u dacacce da hankali, sannan zamu kawo misalsalai da samfuri daga riwayoyi cikin wannan mukami.