Daga maganganun manya-manyan malamai

 

1- shaik Saduk cikin littafinsa (Attauhid) ya ce: bada'au ba kamar yanda jahilai suke rayawa ba yake da cewa wai daga nadama yake, Allah ya daukaka daga haka daukaka mai girma, sai dai cewa wajibi mu tabbatarwa ga Allah Azza wa Jalla da cewa shi ba da ma'anar sa shi ne ubangiji yana da iko ya farar da wani abu cikin halittar sa, sai ya halicce shi gabanin wani abu, sannan ya batar da wannan abu ya farar da wani wata halittar koma bayan sa, ko kuma yayi umarni da da wani abu sannan yayi hani daga misalin sa, ko kuma yayi hani ga wani abu sannan yayi umarni da misalin abin da da ya hana, misalin nasaki da yake yi cikin shari'a, da misalin sauya kibila daga Aksa zuwa Ka'aba da yayi, da sauya iddar macen da mijinta ya mutu da ya farar a cikin shari'a.

Allah bait aba umartar bayinsa a wani lokaci ba face ya san maslahar su cikin wannan lokaci, ya umarce su ne da abin da yake gyara gare su, duk wanda ya tabbatarwa da Allah cewa yana da ikon kan aikata abin da ya so, ya kuma jinkirta wand aya so ya halicci abin da ya so ma gurbinsa, ya gabatar da abin da ya so, ya jinkirta wanda ya so, yayi umarni da abin da yake so, yadda ya so, to tabbas yayi ikirari da bada'u, ba a taba girmama Allah Azza wa Jalla da wani mafi falala daga ikirari da cewa al'amari da halitta na hannunsa ba, jinkirtawa da gabatarwa, tabbbtar da abin da bai kasan ce ba, shafe abin da ya kasan ce.

Shi bada'u raddi ne da martani kan Yahudawa bayan da suka ce: hakika Allah ya rigaya ya gama al'amari, sai muka ce: shi Allah a kowacce rana shi yana cikin sha'ani yana rayawa ya matarwa, yana azurtawa yana aikata abin da ya so, kuma shi bada baya daga nadama, kadai bayyana al'amari ne.

Larabawa suna cewa: (bada li shaksun fi dariki) wani mutum ya bayyana gareni a kan hanyata, Allah Azza wa Jalla ya ce:

 (وَبَدا لَهُمْ مِنَ اللهِ ما لَمْ يَكُونُوا يَحْتَسِبُونَ )[1]

Abin da basu kasan ce suna tsammanin sa ba ya bayyana gare su.

Ma'ana ya bayyana gare su, yaushe ya bayyana ga Allaha matsarkaki madaukaki daga bawa sadar da zumunci sai ya kara tsahon rayuwarsa, sannan duk sanda yanke zumunci ya bayyana sai ya rage masa tsahon rayuwa, duk sanda aikata zina ta bayyana ga bawa sai ya tauye azrikinsa da rayuwar sa, duk sanda kame kai daga aikata zina ya bayyana sai ya kara masa cikin arzikin sa da tsahon rayuwar sa, daga wannan bayani ne fadin Imam Sadik (a.s)  

«ما بدا لله بداء كما بدا له في إسماعيل إبني ».

Bada'I bai taba tabbata ga Allah kamar yadda ya bayyana cikin `dana Isma'il.

Yana cewa: wani abu bai taba bayyana bag a Allah kamar bayyanar ga Isma'il `dana yayin da ya kashe shi gabani na domin da haka ya san cewa shi ba Imami bane bayana- sai dai cewa tare da haka wasu mutane sun bacewa hanya sai suka kafe kan imamancin Isma'il sune wanda a wannan zamani ake kiransu da Isma'iliya wanda suke da kashe-kashe da kungiyoyi.

2- Shaik Mufid ya ce: (maganar imamiyya cikin bada'u, hanya ce ta jib a ta hankali ba… cikin ba a nufin bibiyar ra'ayi, da bayyanar abin da a da ya kasan ce boye daga gare shi, dukkanin ayyukan sa madaukaki bayyane suke cikin halittunsa bayan ba su kasan ce ba, su sannannu ne cikin abin da bai abin da bait aba gushewa).

3- Shaikkul Da'ifa Shaik Dusi ya ce: (bada'u a luggan ce yan nufin bayyana, saboda haka ne ma ake cewa: bada lana suwarul madina, ganuwar garin ta bayyana garemu, fuskar ara'ayin ta bayyana garemu, amma idan aka jingina wannan lafazi ga Allah madaukaki to cikin akwai abin da yake halasta da wanda baya halasta, amma wanda yake halasta daga lafazin shi ne abin da nasakin hukuncin yake fa'idantarwa ba tare da wani banbanci ba, idalakin hakan yana kasantuwa kan yalwatar misali daga majazin lugga, kan wannan fuska ne ake dora baki dayan hadisan da suka zo daga Imam Sadik da Bakir (a.s) da suka kunshi jingina bada'u ga Allah madaukaki, koma bayan abin da baya halasta kansa daga samuwar ilimi da a da babu shi, fuskar idlakin hakan ga Allah madaukaki na kasancewa tashbihi, shi ne idan ya kasan ce yana shiryarwa kamar yanda nasakin aya ke shiryarwa sai ya bayyanar da shi ga mukallafai abin da a da bai kasan ce bayyane gare su ba, su samu saninsa baya da basu sani ba, kan wannan ne aka dora lafazin bada'u.   

 4- daga Alamul Huda Assayid Murtada an samu wata fuskar daban cikin haka shi ya ce: (Albada'u) a hakikarsa bawai majazi ba kamar yanda yake wurin Shaik Dusi bari dai ana dora shi kan hakikanin sa sai ace: (bada lillahi) da ma'anar zuhuri da bayyana gare shi daga umarni a da bai kasan ce bayyane ba, ya bayyana gare shi da hani daga abin da bai kasan ce bayyane gare shi ba, saboda gabani samuwar umarni da hani basu kasan ce bayyane ba riskakku kadai dai ya san cewa yana bada umarni ko kuma yana hani a cikin nan gaba, amma kasantuwar sa mai umarni mai hani, bai inganta ya san shi face bayan samuwar umarni da hanin, magudanar dayan wadannan fuskoki da aka ambata ya gudana cikin fadin sa madaukaki:

 (وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ حَتَّى نَعْلَمَ الْمُجَاهِدِينَ مِنكُمْ )

Tabbas zamu jarrabeku har sai mun san mujahidai daga cikinku.

Mu dora shi kan muradi har sai mun sani da sanin aiki a aikace- jihadinku, saboda gabanin samuwar jihadin ba a iya sanin cewa akwai jihadi kadai dai a na sani baya faruwar sa, to haka lamarin yake cikin bada'u, wannan fuskar tana da kyau matuka, maganar sa ta zo karshe.

5- shugaban masana hikima Mirdamad cikin littafin (Alkabasat: sh 84) ya ce: hakika ya inganta ta hanyar tawatiri da istifadar nakali daga shugaban dukkanin halittu (s.a.w) da cewa lallai alkalami ya rigaya ya bushe an nade takardu, ya ce: farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne alkalami, sai ya ce masa: rubuta sai alkalami ya ce me zan rubuta ? sai ya ce: kaddara abin da ya kasan ce da wanda zai kasan ce da abin da yake kasantacce har zuwa tashin kiyama.

Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa ya ce: babu daga wata mai numfashi kasantacciya har zuwa tashin kiyama nface ita kasantacciya ce.

Ya ce: alkalamin ya bushe daga abin da yake kasancewa, sai aka ce masa meye abin yi kenan ya manzon Allah? Sai ya ce: kuyi aiki kowanne an yassare shi ga abind aka halicce shi don shi.

Tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iylansa ya ce: babu wani mutum daga cikinku face an rubuta matsugunar sa a wuta da matsugunar sa a aljanna, sai suka ce ya manzon Allah yanzu ba zamu dogara da abin da aka rigaya aka rubuta a littafin mu ba mu yi watsi da yin aiki? Sai ya ce: kuyi aiki kowanne an yassare shi ga abin da aka halicce shi, ko da ya kasan ce daga ma'abota farin ciki da sannu za mu yassare shi ga aikin ma'abota farin ciki da azurta, idan kuma ya kasan ce daga matsiyata, da sannu zamu yassare masa aikin matsiya, sannan ya karanta

 (فَأَمَّا مَن أَعْطَى وَاتَّقَى * وَصَدَّقَ بِالْحُسْنَى)[5] .

 Amma wanda ya bayar da kyauta ya ji tsoran Allah* ya gasgata kalma mai kyau.

An tambayeshi (a.s) shin mu ma muna cikin wadanda aka riga aka gama da su, ko kuma za a sake sabunta al'amarin? Sai ya ce: kuna cikin wadanda aka gama da su kuma kuna cikin wadanda za a sake sabunta al'amari.

Sai Mirdamad ya karkata kan maganar Fakrul Razi da bashi amsa kan ishkalin da yayi ya ce: shugaban masu shakku jagoransu cikin Tafsirul Kabir ya ce: idan mai magana ya ce: ashe ba kune kuke raya cewa kaddarori sun riga sun gabata ba, kuma alkalami ya rigaya ya bushe, lamarin bai karbar sabuntawa, ta kaka maganarku zata daidaita da wannan ma'ana ta mahawu wal isbat? Sai mu ce: mahawu wal isbat din ma suna daga cikin abubuwan da alkalami ya rigaya ya bushe kansu, bai shafe wani abu face abin da shafe shi ya gabata cikin ilimin sa da hukuncin sa.

Sannan larabawa sun ce: ana kiran duk abin da yake gudana magudanar asalin abu uwa gare shi, daga cikin misalin haka akwai fadin su kan kwakwalwa: (uwar kai)  da uwar alkaryu ga Makka, haka ma uwar littafi, wanda shi myake kasancewa asali ga dukkanin litattafai, cikin sa akwai magana biyu:

Magana ta farko: hakika uwar litattafai wanda shi ne lauhul mahfuz, da dukkanin abubuwan da suke faruwa madaukakiyar duniya da makaskanciya tabbace yake cikin sa  

عن النبي  6 إنّه قال : كان الله ولا شيء، ثمّ خلق اللوح المحفوظ ، وأثبت فيه أحوال جميع الخلق إلى قيام القيامة ، وعليها التقدير، فعند الله كتابان  : أحدهما: الكتاب الذي يكتبه الملائكة على الخلق ، وذلک الكتاب محل المحو والاثبات ، والكتاب الثاني هو اللوح المحفوظ ، وهو كتاب مشتمل على نقش جميع الاحوال العلوية والسفلية ، وهو الباقي .

An karbo daga Annabi (s.a.w) ya ce: Allah ya kasan ce lokacin da babu komai, sannan ya halicci lauhul mahfuz, ya tabbatar halaeyn dukkanin halittu a cikin sa har zuwa tashin kiyama, cikinsu akwai kaddara, wurin Allah litattafai biyu, dayansu shi ne littafin da Mala'iku suke rubuta ayyukan halittu, wannan littafi shi ne mahallin mahawu wal isbat, shi littafi ne da ya tattaru kan rubuta baki dayan halayen madaukakiyar duniya da makaskanciya, shi wanzazze ne.

روى ابو الدرداء عن النبي  6: إنّ الله تعالى في ثلاث ساعات بقين من الليل ينظر في الكتاب الذي لا ينظر فيه غيره ، فيمحو ما يشاء ويثبت ما يشاء.

Abu Darda'u ya rawaito daga Annabi (s.a.w): hakika Allah madaukaki cikin sa'o'I uku na karshen dare yana duba littafin da waninsa baya duba shi, sai ya goge abin da ya so ya tabbatar da abin da ya so.

Masana falsafa suna da wani bayani kan wadannan litattafai guda biyu cikin bayani akwai kalmomi na ban mamaki da boyayyun sirrika.

Magana ta biyu: shi uwar littafi shi ne ilimin Allah ka baki dayan abubuwa daga samammu da rasassu, lallai shi duk da cewa ya sauya sai dai cewa kuma ilimin Allah madaukaki wanzazze ne tsarkakakke ne daga canjawa, abin da ake nufi da uwar littafi shi ne wadancananka. Abin da Razi ya fada ya zo karshe.

Muhakkik Mirdamad ya ce: saboda haka shi lauhul mahfuz zai zama kenan  wani littafi na tsara samuwa tun daga kirji har zuwa kwauri, shi littafin Allah ne mabayyani wanda bai bar wani danye ko busheshshe daga duniyoyin samuwa face ya tattaro shi, shi zamani ne babu mai kewaya da shi face makaginsa  mahaliccinsa , shi ne Allah matsarkaki.

Hakika na ji dadin Kalmar da babban malaminsu Abu Hamidul Gazzali ya fada cikin littafinsa (Ihya'u ulum): hakika duniya wacce ita ce tsari system din samuwa baki dayanta halittar Allah madaukaki ce, mene ne yafi dadi daga wannan kalami me yafi zakaka, system na jumla ga duniyoyin samuwa shi ne littafin Allah mabayyani wanda bai barin daga abin da ya yalwata kabiliyarsa dabba'uwa da imkani da kuma daukowa daga gare shi cancantuwar mahiyat da tanadi madda da duk wani kararta bai bar karama ko babba daga gare su face ya kidaice ya kidaya su, Allah matsarkaki shi ne makagin wannan littafi mai girma mai sanya shi makirkirinsa mahaliccinsa.

Sannan Muhakkik Mirdamad ya kara karkata kan maganar Razi da kageta kan shi'a cikin akidar su kan bada'u, yana mai basda amsa kan ishkalin ya ce: sannan wannan jagoran masu shakka Allama ya shiga mashigar ta'addanci da kage da karya da sharri, sai ya ce: Rafilawa sun ce bada'u ya halasta ga Allah madaukaki, shi ne yana kudurce wani abu, wani abu daban ya bayyana gare shi, lallai al'amarin sabanin abin da ya kudurce, sannan sunyi riko da fadin sa  madaukaki (yana shafe abin da ya so ya tabbatar) wannan gurbace yake, saboda ilimin sa yana daga laziman zatinsa kebantacce, da abin da ya kasan ce misalin haka, hakika shiga canji da sauyi cikin sa abu ne wand abai yiwuwa.

Wannan shi ne lafazin da Razi ya fada.

Sai Mirdamad ya bashi amsa yana mai cewa: sai na cewa masa jagoran mutanenka, Allaman gayyarka: yanzu ashe baka san abin da ya bijiro ga bibiyarka da karatunka ba, hakika mas'alar bada'u bata kebantu da Rafilawa ba da kuma iya hadisan Imaman su tsarkaka ba, bari dai mas'alar ta zo cikin hadisin Manzon Allah (s.a.w) ta maimaitu fiye da karo guda, ta zo cikin Sahihul Bukari da Muslim da sauran ingantattun litattafanku da Asalanku da kuka yi ittifaki kan riwayoyin su da abin da suka tabbatar.

Sannan wurin Rafilawa ma'anar sa bai nufin nadama da bayyanar sabanin kudurcewa, bari dai kololuwar abin da ya kunsa shi ne tabbatar da jingina canje-canje da sauye-sauye cikin daurorin samarwa da hukunce-hukunce halitta ya zuwa makagi madaukaki, sannan afkuwa sauyi bawai cikin hukunci da zamani, bari dia cikin lokaci, cikin ba'arin kaddara ba tare da lazimtar canji da sauyi ba, da riskar juna da wasa da juna da kiyasi zuwa mai samarwa da kasantarwa mulkinsa ya girmama, da kuma karyata maganar Yahudawa da cewa an rigaya an gama al'amari daga samarwa da kasantarwa. Maganar sa ta zo karshe an gama da ita

6- Maula Muhsin Faizul Kashani cikin littafin sa (Alwafi) cikin babin Bada'u ya ce: idan akace ta kaka danganta bada'u zai inganta ga Allah madaukaki tare da kewayar ilimin sag a baki dayan komai tun azal kuma Abadan kan abin da yake kai cikin hakika al'amari, da tsarkakar sa daga dukkanin abin da yake kawo canji da da bijirowa da makamantansu?

Sai muce: ka sani hakika maganar masana ilimin taurari basu iya kewaya da dukkanin abin da zai afku daga al'amura karo day aba sakamakon rashin tukewa wadancan al'amura, bari dai kadai dai abubuwa suna suranta cikin sa a sannu-sannu a hankali, jumla da jumla tare da sabubban su da illolin su kan tsarin mai mikewa da tabbataccen system, lallai abin da yake faruwa cikin duniya da barna kadai dai yana daga laziman motsin taurari hararru ga Allah madaukaki, da natijojin albarkar su, su sun san lallai duk sanda abu kaza ya kasan ce, duk yanda ilimin ya kai ga samuwa gare su daga sabubba faruwar al'amari cikin wannan duniya sai tayi hukunci da faruwar sa cikinta, hukunci ya surantu sakamakon hakan, ta yiwu ba'arin asu sabubba masu jawo afkuwa suyi jinkiri sabanin abin da ke jawo sauarn sabubban ba da ban wannan sababi ba ilimi da sanin hakan ba zai samu, sakamakon rashin tsinkaya kan sababin hakan, sannan abin da ya zo ko kuma lallai yand aal'amarin yake da ta tsinkaya kansa sai tayi hukunci da sabanin hukuncin farko, sai ya shafe hukuncin farko ya tabbatar da wani hukuncin daban.

Sannan ya ce: amma dangana baki dayan hakan zuwa ga Allah madaukaki, ya kasan ce ne sakamakon abin da yake gudana cikin wannan duniya ta malukutiya ta mala'ikanta kadai dai yana gudana cikin iradar Allah madaukaki, bari dai ayyukansu a ainahin sa aikin Allah ne matsarkaki, ta yanda su basa saba masa abin da ya umarce su kuma suna aikata abin da ya yayi umarni da su aikata, babu abin da ya sanya aiki face iradar Allah Jalla wa Azza, sakamakon su sun rigaya sun narkar da iradar su cikin iradar Allah madaukaki, misalin su kamar misalin mariskan mutum ne duk sa'ilin da ya himmatu da wani lamari riskakke sai daya daga mariskansa ta zartar da abin da yayi niyya kai tsaye, dukkanin wani rubutu da yake kasancewa cikin wannan allunan da takardu suna karkashin rubutattun Allah Azza wa Jalla bayan hukuncinsa magabaci rubutacce da alkalamin san a farko, sabida sai ya zama ya inganta a siffanta Allah Azza wa Jalla da misalsalan hakan bisa wannan la'akari, duk da cewa misalin wadannan al'amura za a canji da bijirowa sabon abu, gashi kuma shi Allah ya tsarkaka daga hakan, lallai duk wani samamme da wanda zai samu nan gaba to shi ya fito ne daga duniyar ubangijintaka. Anan maganar Faizul Kashani ta zo karshe.

7-domin kara samun bayani da haske cikin mas'alar bada'u dacacce da hankali wanda kansa shi'a imamiya suka tafi daga makarantar Ahlil-baiti (a.s) zamu kawo abin da Muhakkikul Isfahani ya fada cikin ta'alikin sa kan littafin (Kifayatul Usul) na Muhakkikul Kurasani: takaice abin da ya fada:  (Allah matsarkaki yana da wasu duniyoyi cikin kausul nuzuli da su'ud wadannan duniyoyi suna da tartibi na farkon duniyoyi shi ne duniyar dabi'a, ita mazhari da mabayyanar duniyar masal ce, tana kasan ce matsayin  inuwa gareta.

Duniyar masal wacce take ta buya ga dabi'a wacce ake mata hukunci barzahu  da take tsakanin dabi'a da duniyar hankali mujarradi, cikinta tana suranta surori abin da yake gudana a cikin duniyar dabi'a daga abubuwa da suke afkuwa filla-filla, sai ta kasan ce da hukuncin madubi da surori da hotunan abubuwa suke bayyana cikin sa ba tare da gangan jikin su ba kwatankwacin abin da ake hiyalin sa daga surori hiyali cikin duniyar hiyali, shi ne abin da ake kira da mahawu wal isbat, domin surantuwa mai sabunata tana da tanadin karbar canji da sauyi, sabanin abin da yake sama da shi daga wata duniyar, shi ne tabbatacacciyar duniya daga duniyoyi, shi ne duniyar lauhul mahfuz, cikinta akwai surori da dandakakkun ma'anoni filla-filla ba tare da cudanya da canji da yankewa ba, ana kiran ta da duniyar lauhul mahfuz sakamakon kubutar ta daga gwamutsa da kurar juzu'iyya da sabunta da yankewa, sai ta kasan ce ma'abociyar tabbatattun surori, sannan sama da wannan duniya akwai duniyar Akalul kulli, mukaminta mukanin hankali na farko, cikin sa surorin hankali suke kasancewa samammu a dunkule, da wannan ta ffifita daga sauran duniyoyin wadanda cikin akwai faifaice koma filla-filla, wannan duniya sai ta kasan ce da ma'ana tattarar hankali.

Wadannan dunyoyi hudu: duniyar dabi'a da masal (lauhul mahawu wal isbat) da duniyar hankali (lauhul mahfuz) da Akalul kulli mujarrad.

Sakamakon duniyar dabi'a ta kasan ce mazharin masal kuma inuwar ta, idan ta wani nafsu daga tsarkakan nufus suka sadu da duniyar masal sai ya zamnto an samu abin da yake hukunta mutuwar Zaidu yayin saduwar nafsin sa da ita, za a bada labarin cewa yam utu, tare da rashin tsinkaya kan tabbatuwar abin da yake hukunta rayuwa daga baya sakamakon kasantuwar sa sannu-sannu, sabanin idan ya sadu da duniyar lauhul mahfuz, ita wannan duniya ce ta surorin hankali, babu sabunta da sannu-sannu cikin duniyoyin hankali, lallai su tabbatattu ne ainahin take ne, babu makawa zai tsinkaya kan abin da yak e tabbatacce, bawai abin da ake hukunta yiwuwar afkuwar abin da zai zame masa shamaki da hanau ba.

Sannan bayan haka tsakanin manufa daga jinginar da bada'u da dangana shi ga Allah matsarkaki madaukaki da cewa abubuwa na waje cikin duniyoyin su da jabarutinsu da malakutinsu da nasut daga martabobin ilimin Allah madaukaki bisa bijira ba bisa zati ba, ta yanda shi ilimi ma'anar sa shi ne hallara, babu wata hallara mafi karfafa daga hallarar ma'alumin illa, zamu iya cewa abin da yake hukunta mutuwar Zaidu sakamakon samuwar sa a waje ma'ana cikin duniya daga duniyoyi, hakika a wannan lokaci an samu mai hukuntawa kenan ta hanyar tabbatuwar mai hukuntawar da ta dace da shi, babu wata tabbatuwa da take da cewa da kansa, wannan shi ne ilimi da ma'alumi a farkonce.

Sannan aka samu illar rayuwar Zaidu d ata hana mai hukunta mutuwar sa tasiri, shi ma'aluli bai tabbatuwa a waje face da samuwar mai hukunta shi da kuma rashin samun mai hana shi tasiri, sai aka samu rayuwa mai yiwa mutuwar sa shinge da hanata tasiri, iata rayuwa ilimi ce da ma'alumi a karo na biyu sabanin  na farko.

Sai wannan al'amari ya bayyana- ma'ana rayuwa bayan da an hukunta mutuwa, ya bayyana cikin martaba daga martabobin ilimin sa madaukaki, abin da sabanin sa ya bayyana da farko bisa wannan martaba, maganar sa ta kare Allah ya daukaka mukamin sa.

Da wannan magana mun samu damar sanin wata fuskar daga bada'u dacacce da hankali, da ma'anar lauhul mahawu wal isbat da lauhul mahfuz, da dunyiyoyin nasutiya da malukutiya da jabarutiya da lahutiya.

8- Assayid Abdullahi Shubbar cikin littafin sa mai kima (Almasabihul Anwar fil hallil mushkilatil Akbar) juz 1 sh 33 ya ce: bada'u yana wasu ma'anoni ba'arin su yana halasta kan Allah matsarkaki madaukaki wasu ba'arin kuma baya halasta kansa, akasarin amfani da ake da shi a luggan ce shi ne bayyanar wani abu bayan buyan sa, da kuma sanin sa bayan jahiltar sa, al'umma tayi ittifaki kan rashin halascin wannan ma'ana ta lugga kan Allah matsarkaki face wadanda ba a la'akari da maganar s, duk wanda ya danganta haka zuwa ga imamiya to hakika ya kagi karya kansu yayi musu sharri sannan imamiya sun barranta daga gare shi.

9- Assayid Abdul Husaini Sharafuddini Musawi cikin littafin mai kima (Ajwiba Masa'ili Jarullahi) sh 101-103 ya ce: natijar abin da shi'a suke fadi anan shi ne lallai Allah yak an tauye arziki kuma yak an kara shi, haka ajali da lafiya da rashin lafiya da farin ciki da tsiya da jarrabawa da musibu da imani da kafirci da sauran abubuwa, kamar yanda fadin sa madaukaki yake hukuntawa: (Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar) wannan shi ne abin da Umar bn Khaddab da Ibn Mas'udu da Abu Wa'ILU DA Katada suka tafi akai, hakika Jabir ya rawaito daga Manzon Allah (s.a.w) ya kasan ce da yawa-yawan magabata suna rokan Allah suna magiya da ya sanya su cikin masu farin ciki azurtattu kada ya sanya cikin matsiyata marasa arziki, hakika wannan ma'ana ta zo da tawatiri daga imaman mu (a.s) cikin addu'o'in su da aka samu daga gare su, ya zo cikin sunnoni masu yawa cewa sadaka da biyayyar iyaye da yin kyakkyawan aiki yana sauya tsiya zuwa farin ciki da arziki, yana kuma kara tsahon rayuwa, sai dai cewa Allah yana shafe abin da ya so daga kaddara ta hanyar yin addu'a, wannan shi ne bada'u wanda shi'a suka tafi kan sa majazan ba hakika ba-cikin idlaki da amfani da bada'u  sakamakon kaman ceceniya… rigima da jayayyar da ke tsakanin mu da Ahlus-sunna tana cikin banbancin lafazi ne kawai, abin da shi'a suka tafi kai kan bada'u sauran musulmi duka sun yi imani da hakan.

10- Shail Aga Buzurgi Tehrani cikin littafin sa mai kima (Azzari'a ila Tasniful Shi'a) juz 3 sh 513 ya kawo cewa: bada'u ma'anar sa cikin lugga shi ne bayyanar wani ra'ayi da a da bai kasan ce ba, ko kuma gani wani abu da aka sani bayan da ba a san shi ba, wannan ma'ana tana faruwa ga dukkanin daidaikun mutane, sai dai cewa mustahili ne bazai taba yiwuwa ga Allah sha'anin say a daukaka, sakamakon lazimtar sabon ra'ayi da a da bai kasan ce ba sakamakon jahiltar sa da fari, ko kuma gazawa daga gare shi shi Allah ya daukaka ya tsarkaka daga wannan ma'ana.

Bada'u wanda shi'a imamiya suke imani da shi yana cikin ma'anar da wajibi dukkanin wani musulmi yayi imani da shi kishiyar Yahudawa Nasara da suke fadin cewa Allah ya rigaya y agama al'amari , babu kuma wani abu da zai kara zuwa daga gare shi (yadullahi maglula) hannun Allah kulle yake, ma'ana duk wand aya biyewa maganar Yahudawa yana mai raya cewa Allah Allah madaukaki ya rigaya ya samar da dukkanin samammu ya afakar da su karo guda, babu wani abu da zai samu face wanda ya rigaya ya samu da farko, ko kuma wanda kasan ce ya na imani da ukul da nufusul falakiya tasirin ilimin taurari yana mai cewa: Allah ya samar da hankali na farko wanda yake wajen mulkin sa da ikon sa yana tasarrufi cikin sa sauran hankula, ya kamata duk wani musulmi ya karyata wannan maganganu, yayi imani da cewa shi madaukaki cikin kowacce rana yana cikin sha'ani, maganar sa ta zo karshe Allah ya daukaka matsayin sa.

Wadannan sune jumla daga maganganun manyan malaman mu daga magabata da wadanda suka zo bayan su da na wannan zamani, karkashen wadannan bayanai ya fito fili cewa bada'un da shi'a suka tafi kai ya saba da wand akai musu sharri aka lika shi kansu.

Babu mamaki ta yiwu sun kagi wannan sharri ga shi'a domin hana yaduwa da habbaka da fantsamar shi'a cikin su da garuruwan su da sakafar sa ta asali daga makarantar Ahlil-baiti tsarkakka cikin tauhidi da annbata da imamanci  da ma'ad, hakama cikin furu'a rassan addini da Akhlak, lallai shi'anci tare da mazajen sa da alamansa cikin zamanin Annabi (s.a.w) da bayan wafatin sa, da bayan fashin mulki da juyawar mutane da komawa zuwa ga abin da suka baro a jahiliya, shi'anci ya fara da tsirarun mutane da basu wuce adadin yatsun hannu ba, sai dai cewa kuma a yau muna samun yan shi'a suna gogayya da mazhabobi da addini da al'ummu cikin ilimummukan su da ma'arifofi da sakafa da wayewa, bari dai mutane gayya gayya jama'a-jama'a suna shiga shi'anci dare da ran aba kakkautawa, kamar yanda tasoshin tauran dan Adam suke nakalto mana abin da yake gudana daga cancantuwar wannan mazhaba mai daraja, da abin da yake wurin wannan kungiya ta tsira daga kamaloli da arziki na har abada, da ga katangaggen tunani nda dacacciyar magana wacce take dacewa da halittar dan Adam dayantatta, da lafiyayyen hankali da saukakken wahayi.