Batu na hudu: dalilai da hujjojin imamiya kan bada'u dacacce da hankali

 

Bayani cikin jigon dalilai da hujjojin imamiya cikin mas'alar bada'u dacacce da hankali, gabanin fara bayyana su babu laifi mu yi ishara zuwa ga wasu al'amura:

Na farko: kadai muna kudurce shi cikin makarantar Ahlil-baiti da cewa hakika ilimin Allah madaukaki matsarkaki yana daga siffofin san a zati, lallai su ainahin zatinsa ne, bawai kari bane kan zatin da har zai lazimta adadantuwar kudama'au, kamar yanda yake a fahimtar makarantar Asha'ira `yan sunna. Ilimin sa azali ne abadi sarmadi wanda jahilci bai gabace shi ba.

Na biyu: hakika ma'anar bada'u a luggan ce shi ne bayyana mudlak ba tare da wani dabaibayi ba bbisa dangane da amfani da shi cikin mhawarorin mutane yana rakkabuwa daga asasai guda biyu:

Na farko: gabataccen jahilci da ilimi da ya mai riska.

Na biyu: canjawa ra'ayi da manufofi kadai dai yana biye da ilimi mai riska.

Idan akai amfani da lafazin (bada'u) cikin Allah cikin fadin mu (bada lillahi subhanahu kaza) to wanne ne daga sinadaran ya ci karo da tauhidi? Na farko ne ko kuma na biyu ko dukkan su?

Sannan shin zai yiwu a raba tsakanin su? Da yanayin da zamu yi imani da wani nau'I daga canji da sauyi da bai kasan ce ya bubbugo daga jahilci da ilimin d aya zo daga baya mai riska?

Babu shakka sinadari na farko yana cikin karo da tauhidi da imani da ilimin Allah matsarkaki na zatinsa, lallai yana daga larurori da sallamammun abubuwa a wurin musulmi, babu wani musulmi ko musulma da zasu yarda su danganta jahilci ga Allah matsarkaki, tsarki ya tabbata gare shi daga abin da suke siffantawa.

Amma sinadari na biyu, bai gushe ba tsakanin kasancewa sauyi na daga lazaiman zati da a ce ya kasan ce lazimi na zati sakamakon samuwar gabataccen jahilci da ilimi da ya zo daga baya ya riska, shi cikin wannan hali ma yana cin karo da tauhidi.

Idan jahilci ya ci karo tare da tauhidi da ma'arifar Allah matsarkaki, haka zalika yana cin karo tare da shi dukkanin wani sauyi da suke kasancewa da sanadiyyar jahilci.

Amma kasancewar sauyi da canji daga laziman bijira bai kasantu daga jahilci ba, bari dai ya bubbugo daga wasu dalilan daban, lallai a cikin wannan hali a asali al'amari baya cin karo da tauhidi.

Bada'u cikin Allah matsarkaki idan ya kasan ce daga jahilci ko sauyi da canji sanadiyar jahilci daga fuskarsa laziminsa na zati, to wannan mustahili ne bai yiwuwa cikin Allah matsarkaki kuma yana cin karo da tauhidin Allah, kuma duk wanda yayi imani da wanna ma'ana shi kafiri ne batacce mai batarwa.

Amma idan sauyi da canji suka kasan ce da wani dalili koma bayan jahilci, to wannan yana daga abin da bai cin karo da tauhidi, a wannan lokaci da zamu leka tushen sha'ariar muslunci masadir dinsa da sakafarmu da cikin akidunmu da ayyuka da sulukai, ma'ana kur'ani mai girma da sunna mai darajada ta misaltu cikin Manzon Allah (s.a.w) da hanyar Ahlil-baiti tsarkaka kamar yanda hadisul Saklaini ya nassanta (littafin Allah da zuriyata) lallai da mun ga al'amari a sarari kan ikirari da bada'u cikin Allah matsarkaki bai cin karo da tauhidi-ma'ana ta uku kamar yanda muka yi ishara zuwa gare shi, kamar yand ayake bayyane, lallai hakika ta kur'ani ana daukota daga dukkanin kur'ani da ayoyinsa masu daraja, hakika kur'ani sashen sa yana fassara sashi.

Ba a cewa: shi kur'ani ya kore dukkanin sauyi da canji daga Allah matsarkaki madaukaki

(وَلَنْ تَجِدَ لِسُنَّتِ اللهِ تَحْويلاً)[1] .

 Ba zaku taba samun sauyi cikin sunnar Allah ba.

 (وَلَنْ تَجِدَ لِسُنَّةِ اللهِ تَبْديلاً)[2] ،

Ba zakat aba samun canji cikin sunnar Allah.

Wannan ba shi ne dukkanin hakikar kur'ani ba, bari dai shi rabin hakikar sa ne, domin an fa'idantu shi ne daga wani bangare da yanki na kur'ani, sai dai cewa kuma akwai wani yankin da danganta sauyi da canji ga Allah kamar yand aya zo cikin fadin sa madaukaki 

 (يَمْحُوا اللهُ ما يَشاءُ وَيُثْبِتُ وَعِنْدَهُ أُمُّ الْكِتابِ )[3] .

 Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar wurin sa uwar littafi take.

Da fadin sa:

 (إِنَّ اللهَ لا يُغَيِّرُ ما بِقَوْمٍ حَتّى يُغَيِّرُوا ما بِأَنْفُسِهِمْ )[4

  Hakika Allah baya canja abin da ke ga mutane har sai sun canja da kawukansu.

Ayar farko tana shiryarwa kan cewa Allah yana shafe abin da yaso ya tabbatar da wanda yaso, cikinta kinaya ce daga sauyi da canji, amma aya ta biyu ita ta zo a sarari kan cewa Allah baya canja halin da mutane suke ciki matukar basu canja da kansu ba, al'umma da daidaikun mutane sun eke rike da ragamar canja makomarsu da gobensu, kowanne dayansu mun lazimta masa tsuntsunsa a wuyan sa, hakikar siyasa da ta tattalin arziki ga mutane bayani daga kaddarorin ubangiji da suke da tanadin karbar canji, idan fa mutane sun yanke hukunci canja hakikaninsu a jama'an ce da daidaiku da sakafa da kankin kai, daga shirka zuwa imani, daga bata zuwa shiriya, daga jahilci zuwa ilimi, daga duhu zuwa haske.

Wannan na shiryarwa zuwa ga cewa Allah yana kaddara biyu:

1-kaddarar ubangijintaka da halin mutane cikin da'a, idan suka yi da`da sai Allah ya azurta su ya kuma shiryar da su.

2- kaddarar ubangiji da halayen su cikin sabo idna suka saba masa sai kaskantar da su ya tsiyata su da ya batar da su.

Idan suka zabi da`a sai ya gudanar musu da kaddarar farko, idan kuma suka zabi sabo sai ya gudanar musu da ta biyu, Allah ba zai taba bsauya halin da mutane suke ciki matukar basu sauya da kansu ba daga `da'a ko sabo.

Daga wannan fuska ne abin da ya ayoyi da riwayoyi suka shiryar kan tasirin ba'arin wasu ayyuka cikin arziki da ajali da ibtila'I, wannan shi ne ma'anar kur'ani da muslunci daga cikin abin da dukkanin musulmai suka yi ittifaki akai, ba ka iya samun mutum daya da yake da sabani a ciki.

Kadai dai sabani ya bubbugo cikin ma'anar bada'u sakamakon daukar ma'anar lugga, kamar yanda yake shi ne abin da mutane suke muhawara cikin sa, lallai wannan ma'ana tana cin karo da tauhidi, kamar yanda muka kawo dangantakarsa da jahilci ko kuma da abin da zai komo zuwa ga jahilci, dukkanin biyun mustahili ne kan Allah baitaba sabuwa kansa.

Sai dai cewa yayin Ankara da lura zuwa ga ma'ana isdilahi jahilci bai lazimtuwa zuwa gare shi matsarkaki wannan yana daga abin da babu ishkali cikin sa.

Tace magana: abin nufi daga bada'u daga fahimtar makarantar Ahlil-baiti shi ne Allah yana kaddarawa bawan sa wata kaddara bisa ayyanannen abin da yake hukunci kan hakan, sannan ya sauya kaddarar bisa abin da yake hukuntawa sabo cikin bawan sa ya bayyanar da natijar ayyanannen aiki da ya tashi kansa, tare da gabataccen ilimi cikin dukkanin al'amuran biyu da halayen biyu.

Da wannan bayani za a san jayayya da rigimar da take tsakanin sunna da shi'a cikin bada'u, kadai dai rigima ce kan lafazi bawai rigima ta tushe ba da har zata lazimta bata da kafirta, bari dai bai da banbanci da rigima tsakanin balarabe da bafarise cikin sayen (Inibi) da (Angur) balarabe yana cewa ina son inibi shi kuma bafarise sai ya ce a bani Angur, sai suka samu rigima cikin lafazi, domin ma'anar abin da suke son siya a waje dai kwaya day arak, wanda yake fahimat harshen larabaci da farisanci zai ji zai fahimce su biyun zai kuma tsinkayar da su zuwa ga hakika da take guda daya a waje.

Daga wannan tunani ne Allama Assayid muhakkik Abdul Husaini Sharafuddini yayi ishara da fadin sa: rigima cikin wannan mas'ala tsakaninmu da Ahlus-sunna, sannan ya ce idna wanin mu ya kafe kan wannan rigima ta lafazi yaki karbar majazanci ma'ana ta aro ya kafe sai yayi idlaki kan abin da muka fada daga tafsiri dacacce da hankali- to mun mika wuya ga hukuncinsa da fadin sa, yaje ya canja Kalmar bada'u yand aya so kamar yanda yake kiransa mahawu wal isbat- amma fa yaji tsoran Allah cikin dan'uwansa mumini, kada ya kafirta shi ka da ya yake shi kada yayi masa kage da sharri da tuhumarsa da bata da kafirci bisa imaninsa da bada'u.

Shaik Mufid shima yayi ishara zuwa ga haka da cewar rigima ta lafazi da fadin sa: (amma idlakin lafazin bada'u kadai dai na kai gare shi da dalilin nakali daga ayoyi da riwayoyi d asuka zo daga tsanuka tsakanin Allah da bayin sa sune Muhammad da iyalansa (s.a.w) lallai su sunyi imani da bada'u, wani dalili nakali bai zo kansa mafi sanin ingancin sa, ban zo gareni cewa shi yana fushi yana kuma yana wajabtawa yana kuma mamaki bisa abin da akai idlaki kansa matsarkaki, sai dia cewa yayin da dalili ya zo mini sai na kasan ce na tafi kansa kan ma'anar da bata sabawa hankali ba, a wannan ma'ana ni da dukkanin sauran musulmi babu wani banabnci, kadai dai sabanin cikin lafazi ne koma bayan wanin sa, ma'ana rigimar na kasancewa ta lafazi ba ma'ana ba da har zai kai ga bata da tsiyata, hakika nayi Karin bayani kan dalilin idlakin sa da abin da magana zata gaza cikin sa, wannan shi ne mazhabar imamiya baki dayanta, duk wanda ya saba mata zai inkarinsa kan abin da na siffa daga suna koma bayan ma'ana  ba za a yarda da shi.

Zuwa ga wannan ma'ana ta hankali cikin bada'u da yake danganta ga Allah matsarkaki Imam Sadik (a.s) yayi ishara lallai cikin tafsirin fadin sa madaukaki: (Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar wurin sa uwar littafi take) ya ce: duk wani al'amari d aAllah yake nufin sa lallai syan cikin iliminsa gabanin kagarsa bawai wani abu bako da yake bayyana gare shi ba, idan ko ba haka to lallai hakika ya kasan ce cikin ilimin sa cewa Allah babu wani abu da yake bayyana gare shi daga jahilci. Ya ce:  

من زعم إنّ الله عزوجل يبدو له في شيء لم يعلمه أمس ، فابرؤا منه )[8] .

Duk wanda ya raya cewa Allah Azza wa Jalla wani abu ya bayyana gare shi da a jiya bai sani shi ba, ku barranta daga wannan mutumin.

Cikin wannan filin sukuwa cikin wannan babi akwai wasu riwayoyin da suke kosar da mai kishi suke warkar da mai larura, kamar yanda da sannu zamu kawo su insha Allahu ta'ala.