Koma ga farkon bayani cikin dalilai:

 

Amma jigon abin da ake kafa hujja da shi kan mazhabar imamiya cikin mas'alar bada'u dacacce da hankali to abubuwa guda uku:

Na farko: ayoyi da suke shiryarwa zuwa ga haka kamar fadin sa madaukaki: (Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar wurin sa uwar littafi take) haka ma fadin sa madaukaki:

 (يَسْئَلُهُ مَنْ فِي السَّماواتِ وَالاْرْضِ كُلَّ يَوْمٍ هُوَ في شَأْنٍ )

Wadanda suke sammai da kasa suna tambayar sa shi kowacce rana cikin sha'ani yake.

Da kuma fadin sa (Allah baya sauya abin da ke tattare da mutane har sai sun sauya shi da kansu)

Fuskar kafa hujja: hakika ya bayyana daga cikin abin da aka kawo cewa lallai Allah matsarkaki madaukaki yana da lauhul mahfuz wanda shi ne uwar littafi, cikin sa yake rubuta hukunci da kaddara yankakkiya, cikin sa an rubuta Allah yana da lauhul mahawu wal isbat, lallai Allah yana shafe abin da yaso ya tabbatar, sai ya canja halitta bawai daga rashin sani da jahilci ba gabatacce ko kuma sanadiyyar jahilci d aya gabata, bari dai yana aikata haka saboda maslaha da hikimomi da aka kaddara su cikin lauhul mahfuz, dukkanin hakan cikin ilimin Allah matsarkaki ba tare da janyo sauyi da canji cikin ilimin sa azali abadi ai sarmadi.

Na biyu: tasirin ayyuka cikin makoma da goben mutum, wannan na daga tabbatattun abubuwan da kur'ani ya tabbatar ya kuma karfafa su. Kari kan riwayoyi da suka daga Annabi (s.a.w) da iyalan sa tsarkaka daga karfafa da ya zo da tawatiri kanta.

Ma'anar wadancan dalilai na nakali daga kur'ani mai girma da madaukakan hadisai shi ne hakika ayyuka mutum daga imani da shirka da `da'a da sabo, da biyayyar iyaye da saba musu, da ciyarwa da sadaka ga talakawa, da rowa da addu'a da sadar da zumunci da yanke shi, dukkanin suna tasiri cikin arziki da yalwar sa, da albarka da dawwamar ta, da tsahon rayuwa da farin ciki da wanin haka, lallai wadannan al'amura kur'ani ya ambace su muraran kamar yanda hadisai suka kawo a lokuta masu yawn gaske.

Hakika kur'ani mai girma ya tattare su cikin fadin sa madaukaki: 

 (إِنَّ اللهَ لا يُغَيِّرُ ما بِقَوْمٍ حَتّى يُغَيِّرُوا ما بِأَنْفُسِهِمْ )[4] .

Hakika Allah baya canja halin mutane har sai sun canja da kawukansu.

Duk wanda yake inkarin bada'u yake karyatawa da wannan ma'ana, lallai inkarin da yake d asannu zai kaishi zuw aga inkarin hakikar kur'ani bayyananniya wanda daga karshe zai tuke da shi ya zuwa kafirci da ridda.

Duk wanda yayi imani da wannan hakika to hakika yayi imani da bada'u, wannan shi ne abin da imamiya suke fadi cikin bada'u

Na uku: kaman ceceniyar mas'alar da mas'alar nasaki cikin shari'a cikin kasantattu, lallai bada'u dacacce da hankali kamar nasaku yake cikin shari'a, shi bada'u nasaku ne cikin halitta, shi kuma nasaku bada'u ne cikin hukuncin shari'a.

Kamar yanda mas'alar nasaku cikin shari'a tsarkakka ya tabbata wurin musulmai baki dayansu, kamar misalin cikin canja aklibla daga masallacin Al'aksa zuwa ga Ka'aba madaukakiya, babu wani musulmi da yake da sabani cikin haka, babu wanda yayi la'akari da hakan matsayin canji da sauyi cikin ilimin Allah azali, kuma hakan bai lazimta tabbatar jahilci to haka al'amarin yake cikin bada'u cikin hukunce-hukunce halittu ba tare da lazimta sabawa ilimin Allah magabaci ko kuma jahilci magabaci.

Duk wanda yake kawo ishkali kan bada'u da wannan ma'ana lallai shi wajibi yayi ishkali kan nasaku, dukkanin biyun suna tsotsa daga nono guda daya.

Duk abin da aka kawo daga jawabi cikin ingancin nasaki da imani da shi, ana kawo shi cikin bada'u da imani da shi, babu wai banbanci tsakanin al'amuran biyu: ma'ana nasaku da bada'u.

A hakika duk mai ishkali kan bada'u daidai yake da maimaita ishkalin Yahudawa kan nasakin shari'a, lallai su sun ce hannun Allah kulle yake, hannunsu yake kulle azaba mai radadi ta tabbata a gare su.

Abin da yake kishiyantar jawabin Yahudawa daga fuskanin muslunci, da tabbatar musu da nasaki cikin shari'a ba tare da lazimta tawaya ba cikin fagen uabngijintaka tsarkakka, lallai wannan magana tana iya dabbakuwa kan amsa daga bada'u cikin duniyar halittu da gudanarwa.

Dukkanin wanda yayi inkarin haka kodai jahili ko kuma wanda ajizi ko kuma mai tsaurin kai da girman kai da kin gaskiya, ko makaryaci makagi, ko kuma makiyi mayaudari.

Zuwa ga Allah al'amura suke komawa kuma shi ne shugaba, babu tsimi babu dabara face ga Allah madaukaki mai girma