Komawa kan bayanin jumlar maganganun manyan malaman mu

 

Hakika a baya mun kawo julmar maganganun malaman mu daga magabata da wadanda suka zo a bayan su d ama na wannan zamani, daga cikin abin da yake nuni zuwa ga ingancin bada'au dacacce da hankali, da kuma inkarin bataccen bada'u matukar inkari, da bayanin matsayar ba'arin wasu da muke da sabani da su kamar wahabiyawan wannan zamanin da kiyayyar su kan shi'anci da `yan shi'a, domin kara tabbatar da al'amari da karfafa shi da bayanin sababbin abubuwa za mu dora maganar mu kan abin da ya gabata, hakika mun yi ishara zuwa ga manyan malamai guda goma, ga wasu jumlar ta biyu daga gare su kan tsarin silsilar da ta gabata.

11- ya zo cikin hashiyar Biharul-Anwar na Allama Majalisi wanda Assayid Taba'taba'I ya sannafa: bada'u da wasalin fataha da madda- a luggan ce yana nufin bayyanar wani abu bayan da ya kasan ce a boye, da kuma samun ilimi kansa bayan da an jahilce shi, al'umma sun yi ittifaki kan rashin halascin wannan ma'ana kan Allah matsarkaki face wand aba a la'akari da maganar sa, da kuma wanda ya kagi karya kan kan imamiya hakika ya kagi karya mai girma `yan imamiyya sun barranta daga gare shi. A al'adan ce daga abin da aka fa'idantu da shi daga maganganun malamai da jagororin hadisi-ana amfani da ingantattun ma'anonin sa baki dayansu cikin hakkin sa madaukaki.

Daga cikin ma'anar sa akwai: farar da abu da hukunci kan samuwar sa da kaddara fararre da ta'allakuwa da irada mai faruwa bisa sharudda da maslahohi, daga wannan fuska akwai samar da abubuwa da suka faruwa yau da gobe, maganar Ibn Asir tayi kusa da shi cikin hadisin Akra'u da Abrasu da A'ama, gurgu da kuturu da makaho, ya bayyana ga Allah Azza wa Jalla ya jarrabe su, ma'ana ya hukunta yin hakan, shi ne ma'anar bada'u a nan, saboda gabataccen hukunci da bada'u ganin dai abu da aka sani bayan da ba a san shi ba, haka ba zai aba yiwu ba ga Allah madaukaki mustahili ne, magana ta kare. Ta yiwu abin da yake nufi da kaddara shi ne hukunta shi da samuwa, abin da kuma yake nufi da kasantuwar sa magabaci shi ne ya san samuwar sa bayan ta'allakar iarda da su ta'allaka wacce take ba tabbatacciya ba, sakamakon rinjayar maslahar sa da sharuddan sa kan wata maslahar daban da sharudda, daga wannan fuska akwai misalin amsa addu'a, da tabbatar masa da bukatun sa da tsawaita rayuwa sakamakon sadar da zumunci, da nufin wanzar da wasu mutane bayan da ya rigaya ya nufi halakar da su.  Daga cikin akwai: shafe abin da samuwar sa ta rigaya ta tabbata cikin iyakantaccen lokaci da sanannun sharudda da kebantacciyar maslaha, da yanke cigaban sa bayan karewa wannan iyakantaccen lokaci da sharudda da maslahohi, babu banbancin cikin tabbatuwar mayin sa domin tabbatar da sharudda da maslahohi cikin tabbatar da shi da farko, daga wannan fuska akwai misalin rayawa da matarwa da  da damka da shimfidawa cikin al'amarin halitta, da shafe hukunce-hukunce ba tare da sanya mayinsu ba ko kuma tare da shi cikin al'amarin taklifi, sannan shi nasaki yana cikin bada'u kamar yanda Shaik Saduk ya fada cikin Attauhid da cikin Al'itikad.

Daga cikin malaman mu akwai wanda ya keban ce bada'u da al'amarin halitta da fitar da nasaku daga cikin sa, wannan keban cewa tsa babu wani dalili da ta dogara da shi, kadai an kirawa wadannan ma'anoni da bada'u sakamakon lazimtar bayyanar abu kan halittu bayan da ya kasan ce boye gare su, sannan wasu muatne sun yi bayani bada'u da cewa wani kufai ne da wani mutum gabanin bayyanar sa bai san da shi ba kuma bai san zai bayyana ba.

Yahudawa sun yi inkarin bada'u da fadinsu: (hannjun kulle yake) hannun su kulle Allah ya tsine musu sakamakon abin da suka fada- da fadin hakan suna nufin Allah ta'ala ya gama komai, babu wani abu da zai kara faruwa, haka nan an nakalto daga gare su cewa wai Allah baya hukunta komai ranar asabar, wannan magana tasu tayi kama da maganar mu'utazilawa: Allah ta'ala ya halicci dukkanin samammu karo guda bisa abin da yake a yanzu: daga ma'adanai da dabbobi da mutane, bai gabatar da halittar Adam (a.s) ba kan halittar `ya`yansa, gabata da jinkirta kadai yana afkuwa cikin bayyanar su daga matsugunan su koma bayan afkuwar su da samuwar su, kai kace ya riki haka daga halitta da bayyana daga mazhabar Falasifa masana falsafa.

Mai littafin Kushshaf ya nakalto daga Husain bn Fadalu abin da yake komawa zuwa ga wannan mazhabar cewa Abdullahi Dahir ya kira Husaini bn Fadalu ya ambaci cewa daga ayoyin da suka shige msa duhu akwai fadin sa madaukaki:     

 (كُلُّ يَوْمٍ هُوَ في شأن )[1]  

Kowacce rana shi yana cikin sha'ani.

Gashi kuma Hakika ya inganta cewa alkalami ya rigaya ya bushe daga dukkanin abin da ya kasan ce da wanda zai cigaba da kasancewa har zuwa ranar kiyama?!

Sai Husaini ya ce: amma fadin sa (shi kowacce rana yana cikin sha'ani) lallai su sha'aninka ne da yake bayyanar da su, bawai sha'anunnuka ne da yake kagar sub a, wadannan mazhabobi a wajen mu gurbatattu ne, saboda shi Allah ya daukaka yana afkar da abin da ya so daga baya cikin kowanne lokaci bisa hikima da maslaha kamar yanda riwayoyi suka yi nuni kan haka a wannan babi, kan wannan ma'ana fadin sarkin muminai (a.s)

«الحمد لله الذي لا يموت ولا ينقض عجائبه ، لأنه كل يوم في شان من إحداث بديع لم يكن

Godiya tabbata ga Allah wanda baya mutuwa baya tauye ababen mamakinsa, saboda shi kowacce rana cikin sha'ani yake daga kagar da kirkirar abin da bai kasan ce ba.

Wannan bayani karara cikin cewa shi Allah ta'ala yana afkar da abin da ya nufa daga mutane da halaye cikin kowanne lokaci.

Ta yiwu Husaini shima bai da banbanci da mai tambaya shima ya fahimci kaga da afkawar suna cin karo da abin da ya inganta daga bushewar alkalami, kai kasancewa babu cin karo da juna tsakanin al'amuran biyu, saboda shi bushewar alkalami ya shiryar kan cewa dukkanin kasantace da mai cigaba da kasancewa har zuwa ranar kiyama shi rubuce yake cikin lauhu mahfuz ko kuma cikin kaddarawa, sananne ne gare shi da yanayin da bai zai canja da sauyawa ba, daga cikin rubutacce sa sananne gare shi madaukaki da ya kaddara abu kaza a lokaci kaza, ya kaga da samar da shi da afkar da shi kan hikima da maslaha, kaga da samarwa wanda su ake kira da bada'u wanda anan ake nufi da cewa yana daga rubutattu. Ka lura sosai.

Wasu ba'arin manyan mutane sun fadi haka cikin sharhin su kan Alkafi. Ina cewa nan gaba dandake magana da tahkiki zai zo dangane da bada'u daga mawallafi da waninsa, maganar sa ta zo karshe Allah ya daukaka shi.

12- Allama Majalisi cikin Biharul-Anwar juz 4 sh 92 babi na 3 daga babukan tawilin ayoyi, babin bada'u da nasaku, cikin babi na 70, a karshen magana ya ce sanin hakikan bada'u kan hasken hadisai masu daraja da suka zo daga makarantar Ahlil-baiti (a.s) sai ya ce: (shimfida magana domin kautar da shakku da wahami) : ka sani hakika shi bada'u yana daga cikin akai zaton cewa imamiya kadai suka kadaita da shi, hakika da yawan wadanda suke da sabani da su sun bata musu suna sun yi musu sharri, sannan hadisai da suka kan tabbatar da bada'u suna da matukar yawa daga dukkanin bangarorin biyu sunna da shi'a kamar yanda ka sani, bara muyi ishara zuwa ga ba'arin abin da aka fada cikin tabbatar da hakan, sannan zuwa ga abin da ya bayyana gareni daga hadisai daga abin da shi ne gaskiya a wannan mukami.

Ka sani lallai sakamakon kasantuwar Kalmar bada'u da madda a luggan ce tana nufin bayyana ra'ayin da a da bai kasan ce ba-alal misali ana cewa (bada amru buduwwan) ma'ana ya bayyana a sarari, ko kuma (bada lahu hazal amru ) ma'ana wani ra'ayi sabo ya zo masa, kamar yanda malam Jauhari ya ambata, da wannan ake ishkali kan danganta shi ga Allah ta'ala sakamakon yana lazimta faruwar ilimin sa madaukaki ga wani abu bayan ya jahilce shi wanda hakan mustahili bai yiwuwa, da wannan ne da yawa-yawan masu sabani da shi'a suka bacen suna da sharri kan imamiya bisa dogaro da kallon lafazi ba tare da dogoin bincike ba kan yanda su shi'a din suka fassara shi, har ta kai ga zaka samu banasibe mai tsananin ta'asubbanci misalin Fakrul Razi cikin karshen littafin sa Almussal yana mai hakaitowa daga Sulaimanu bn Jarir cewa wai Imamiya Rafilawa sun kirkiri akidar bada'u ga `yan shi'ar su, idan suka fadi wannan akida to suna samun karfafa cikin muwara da mujadala kan abokan jayayy, sannan ak'amarin bai kasan ce kan yadda suka labartar suka ce: wani abu ya bayyana ga Allah cikin sa.

Mafi ban mamaki daga gare shi shi ne Muhakkikul Dusi ya bashi amsa kan haka cikin nakadin sa kan Almuhassal sakamakon rashin cikakkiyar kewayar sa ga hadisai da ya ce: wai imamiya basu fadin bada'u face wuri guda kadai dai inda suka tafi kansa shi ne abin da ya kasan ce cikin riwaya guda daya da akai rawaito ta daga Jafar Assadik (a.s) lallai shi ya sanya Isma'il mai tsayuwa kan matsayin sa bayan sa, sai wani abu bai ji dadin sa bay a bayyana daga Isma'il, sai ya sanya Musa Alkazim (a.s) nya tsayu kan matsayinsa bayan sa, wannan riwaya ce guda daya kuma a wurin su riwaya guda daya bata fa'idantar yakini ba kuma a yin aiki da ita, magana ta kare.

Kalli wannan mai tsaurin kai ta kaka ta'assubancin sa makantar da shi ta yanda ya nasabta karya da kage da yaudara zuwa ga jagororin addini wadanda mai sabani da su da masoyinsu basu da sabani cikin falalar su da ilimin su da tsantsenin su, da kasantuwar su mafi takawar cikin mutane mafi daukakar matsayi da daukaka, da ya san misalin wadannan lafuzza na majazi masu sanya wahami zuwa ga ba'arin wasu ma'anoni gurbatattu hakika ya zo cikin kur'ani mai girma da ma hadisai daga bangarori biyu kamar misalin fadin sa ta'ala (Allah yana yi musu isgilanci) (Allah yayi makirci) (hannun Allah) (fuskar Allah) (gefan Allah) da makamantan su daga abubuwa da ba zasu kirgu ba.

Hakika ma'anar da shi'a suka tafi akai kan bada'u ya zo cikin hadisai daga Ahlus-sunna fiye da adadin da yazo cikin hadisan mu, kamar misalin hadisin addu'ar annabi (s.a.w) kan wani bayahude, da hadisai Isa amincin Allah ya tabbata ga Annabin mu da shi, da cewa sadaka da addu'a suna canja kaddara, da wasun su.

Ibn Asir cikin Annihayatu cikin hadisin Akra'u da Abrasu da A'ama, ya ce: ya bayyana ga Allah Azza wa Jalla yayi hukunci da haka wannan shi ne ma'ana bada a nan, saboda shi gabataccen hukunci da bada'u ganin daidan abu ne da aka san shi bayan da ba a san shi, wannnan bai halasta kan Allah ba, maganar sa ta zo karshe.

Hakika aya ta shiryar kan ajalai guda biyu kuma a karshe ya fassara su da abin da ka sani, hakika madaukaki ya ce: (Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar) banasibe cikin tafsirin su ya ce: cikin tafsirin wannan aya akwai magana guda biyu:

Na farko: lallai ita gamamma ce cikin komai kamar yand zahirin lafazi yake hukuntawa, suka ce: Allaha yana shafe arziki yana kuma kara shi, haka ma maganar take cikin ajali da farin ciki da tsiyata da imani da kafirci, wannan ita ce mazhabar Amru bn Mas'udu da Jabir ya rawaito shi daga Manzon Allah (s.a.w).

Na biyu: kebantacciya ce cikin ba'arin wasu abubuwa koma bayan ba'arin wasu saboda haka cikinta akwai fuskoki:

Ta farko: abin da ake nufi da mahawu da isbat shi ne nasakin hukunci d aya gabata da tabbatar da wani hukuncin maimakon na farko.

Ta biyu: Allah ta'ala yana shafewa daga kundin diwanin makiyaya abin da yake baya daga kyakkyawa da mummuna, saboda su makiyaya an umarce su da rubuta duk wani furuci da duk wani aiki, sai ya tabbatar da wanin sa.

Ta uku: lallai shi madaukaki abin da ya nufa da mahawu shafewa shi ne cewa duk wanda ya aikata zunubi sai a tabbatar da haka cikin diwaninsa, idan ya tuba sai a shafe wannan zunubi daga diwanin sa.

Ta hudu: Allah yana shafe abin da ya so shi ne wanda ajalinsa ya zo, ya kyale wanda nasa ajalin bai zo ba ya tabbatar da shi.

Ta biyar: Allah ta'ala cikin farkon shekara yana tabbatarwa idan ta wuce sai ya shafe, ya tabbatar a wani littafin kuma ga gobe nan gaba.

Ta shida: yana shafe hasken wata ya tabbatar da hasken rana.

Ta bakwai: yana shafe duniya ya tabbatar da lahira

Ta takwas: lallai shi cikin arziki da jarrabawa da musibu yana tabbatar da su cikin littafi sannan ya gusar da su da addu'a da sadaka, cikin hakan akwai kwadaitarwa kan yankewa zuwa ga Allah da mika al'amari gare shi.

Ta tara: canjuwa halayen bawa abin da ya gabata daga gare su shi shafewa ne, abin da ya hallara ya samu shi isbat ne tabbatarwa ne.

Ta goma: yana gusar da abin da ya so daga hukuncinsa babu mai tsinkaya kan gaibun sa shi ne ya dayantu da hukunci yanda ya so, shi ne mai cin gashin kansa cikin samarwa da batarwa da rayawa da kashewa da wadatawa da talautarwa, da yanayin da babu wani daga halittun sa da zai tsinkaya kan wadancan gaibun.

Ka sani wannan babi cikin akwai babban fage, idan magana ya ce: ashe ba kune kuke raya gabatattun kaddarori ba kuma alkalami ya rigaya ya bushe, ta kaka wannan ma'ana za ta daidaita da mahawu da isbat shafewa da tabbatarwa?

Sai muce: wannan mahawun da isbat din shima yana daga abin da alkalami ya bushe kansa, baya shafe wani abu face abin da shafe shi ya gabata cikin ilimin sa da hukuncin sa.

Sannan ya ce: Rafilawa sun ce: bada'u ya halasta kan Allah ta'ala, shi ne ya kudurce wani abu sannan wani abu ya bayyana gare shi sabanin abin da ya kudurce, suna masu riko da fadin Allah ta'ala (Allah yana shafe abin da ya so yana tabbatarwa) maganar sa ta zo karshe.

Bamu san daga inda ya samo wannan magana da yayi kage kan imamiya tare da cewa litattafan malaman imamiya suka gabace cike suke da barranta daga wannan magana, shi kamar misalin Saduk da Mufid da Shaik Murtada da sauransu Allah ya kara yarda da su, babu abin da suke fadi face ba'arin abin da shi da kansa ya fada a bayaninsa da ya gabata kai da ma abin da yafi kyawunta daga bayanin da yayi kan bada'u kamar yanda da zaka san haka.    abin ban mamaki masu sabani da imamiya shi ne cewa su cikn mafi yawancin wurare suna dangantawa Allah abubuwan da basu dace da shi ba-kamar misalin saukowarsa daga sama a kan jaki daren juma'a ko kuma zamansa kan al'arshi da sanya kafarsa cikin wuta- imamiya Allah ya tsarkake sirrikan su, su sun kai makura cikin tsarkake Allah suna kafa musu dalilai da karfafan hujjoji, yayin suka gaza samun nasara kansu cikin akidun su daga abin da zai kawo nakasu da zasu alfahari da shi kansu su kagar musu misalin wancan gurbatattun maganganu , bari tsantsar sharri d akage kamar yanda yake dabi'ar wanda ya gaza, da za a kaddara cewa ba'arin wasu jahilai da suke danganta kansu ga shi'a sun fadi haka to lallai imamiya ta barranta daga gare su, daga fadin sa kamar yanda suke barranta daga misalin wannan banasibaen daga gurbatattun tatsuniyoyin sa.

Amma abin da aka fadi cikin bayani kan bada'u hakika ka rigaya ka san abin da Saduk ya kawo da Shaik cikin hakan kamar yanda bayani filla-filla ya gabata, kuma amma fadi wasu fuskokin daban:

Na farko: shi ne abin da Assayid Damad (ks) ya fada cikin Nibrasul Diya'u- hakika maganar sa ta gabata ta yanda ya ce: ana ajiye bada cikin halitta kamar yanda ake sauke nasaku cikin hukunce-hukuncen shar'ia, abin da yake cikin al'amarin shar'a da hukunce-hukuncen taklifi daga nasaki, shi ne dai bada'u cikin al'amuran halitta da zamani da kasantattu, nasaki kai kace shi ne bada'un cikin shari'a, bada'u kai kace shi ne nasakin kasantuwa.

Na biyu: shi ne abin da ba'arin wasu malamai masu daraja suka kawo cikin sharhin su kan littafin Alkafi wasun su suka tafi kao daga malamai wannan zamanin namu, shi ne cewa karfi dabbakakke na tauraro bai iya kewaya da cikakken sanin abin da zai afku daga al'amura karo guda ba sakamakon rashin tukewa wadancan al'amura, bari dai kadai yana zane da suranta abubuwa cikinsu a sannu-sannu. Jumla da jumla, tare da sabubban su da illolin su kan tsarin tabbatacce zaunanne, har zuwa karshen maganarsa.

Na uku: abin da ba'arin wasu muhakkikai suka fada misalin Mirza Rafi'a ta yanda ya ce: tabbatar da magana cikin bada'u baki dayan al'amura gamammun su da kebantattun su mudlakan su da kayyadaddun su, nasik da mansuk din su, mufrad da murakkabin su, Akbar da insha'I in su, da yanayin da babu wani abu da ya iya ratsewa daga gare shi zanannu ne cikin lauhul mahfuz, ya kwarara daga gare shi zuwa ga Mala'iku da madaukakan nufus, da makaskanta, sannan al'amari na iya kasancewa ammi ko mudlaki  ko mansuk bisa abin da hikima take hukuntawa daga kwarara a wannan lokaci, yana kuma iya jinkirta zuwa wani lokaci da hikimar kwararar sa take hukuntawa cikin sa, wadannan madaukakan nufus da abin da yayi kama da su sune ake kira da littafin mahawu wal isbat (littafin shafewa da tabbatarwa) shi bada'u bayani kan wannan shafewar da tabbatarwar.

Na hudu: abin da Assayid Murtada (rd) ya fada: cikin amsar tambayoyin garin Rayyu, yana cewa: abin da ake nufi da bada'u shi ne nasaku, yayi da'awar bai banbanta da ma’anar sa ta lugga ba.

Takaice magana: shidai bada'u shi ne kasantuwar dangantawa da ta samu ga wani abi zuwa ga tauyayyun illolin sa, da hukuncin dangantawa ya zuwa ga cikakkiyar illar sa.

Allama Majalisi yana cewa: bara mu kawo abin da ya gabata daga ayoyi da hadisai da yanayin da bayyanannun nassoshi za su shiryar kansa, lafiyayyun kwakwale zasu ki karbar sa.

Sai muce-dacewa daga Allah take-lallai su sun zurfafa cikin bada'u cikin raddi kan Yahudawa wadanda suke cewa: Allah y agama al'amari, da kuma raddi kan jagoran Mu'utazilawa Annazamu da ba'arin wasu mu'utazilawa da uyske cewa: Allah ya halicci dukkanin samammu karu guda kan abin da ma'adanai da tsirrai da dabbobi da mutane ke kai, bai gabatar da halittar Adamiu (a.s) kan halittar `ya`yansa, kadai dai gabata da jinkirta yana faruwa ne cikin bayyanar sub a cikin kagar su da samuwar sub a, kadai dai sun riki wannan mas'ala daga ma'abota buya da bayyana daga masana falsafa, da kuma raddi kan `yan falsafa masu fadin Ukul da nufusul kulliya, da cewa Allah ta'ala bai tasiri a hakika sai cikin hankali farko (Aklul Awwal) suna kwabe Allah ta'ala daga mulkinsa, suna danganta abubuwa da suke faruwa ya zuwa wadannan , sai suka kore wadannan maganganu, suka tabbatar da cewa Allah ta'ala shi kowacce rana cikin sha'ani yake, daga batar da abu da kagar wani, da kashewa wani mutumin da raya wani ya zuwa wanin haka, domin kada su bar bayi suyi koma ga Allah su roke shi suyi masa magiya da `da'a da neman kusancin sa da cikin gyaran al'amuran duniyar su da lahira, domin suyi fata yayin sadaka ga talakawa da sadar da zumunci da biyayyar iyaye da kyautatawa da ihsani da abin da aka yi musu alkawari daga tsahon rayuwa da Karin arziki da makamancin haka.

Sannan ka sani lallai ayoyi da hadisai sun shiryar kan cewa Allah ya halicci alluna guda biyu-sune fuskar mulki- cikin su ya tabbatar da abin da zai faru daga halittu:

 Na farko: lauhul mahfuz wanda shi baya canjawa baya kuma sauyawa shi ne ya daidaituwa da ilimin sa madaukaki.

Dayan kuma shi ne lauhul mahawu wal isbat, cikin sa yana tabbbatar da abu sannan yana iya goge shi sakamakon hikimomi masu tarin yawa da basu buya ga ma’abota hankula, alal misali cikin sa ana rubuta cewa tsahon shekarun Zaidu shi ne shekaru hamsin, ma’ana abin da hikima ta hukunta Kenan kansa idan bai aikata wani abu da zai hukunta tsawaitar shekaeunsa ba ko tawayar su, alal misali idan ya sadar da zumuncin dan’uwansa Yahaya to sai ya rayu shekaru sittin idan kuma ya yanke zumuncin sais u ragu zuwa arba’in, amma cikin lauhul mahfuz to rubuce yake zai kai shekaru sittin, kamar yanda hazikin likita idna ya tsinkayi yanayin mutum zai yi hukunci da cewa wannan zai kai shekaru sittin bisa wannan yanayi da yake da shi, amma idan ya sha guba ya mutum ko kuma wani mutum ya kashe shi sai shekarun suka ragu ko kuma yayi amfani da wani magani sai yanani yinsa ya karfafa shekarunsa za su karu, duk hakan bai nuna cewa ya sabawa maganar likita, canji da ya afku cikin wannan allo shi ake kira da bada’u, ko dai sakamakon cewa yayi kama da shi, kamar yanda yake cikin sauran abin da ake dorawa kan Allah daga ibtila’i da isgilanci da misalsalansu, ko kuma dai yana bayyana ga Mala’iku da mutane idan an basu labari da na farko sabanin abin da suka sani a farko, me yake nuna nesanta daga tabbatuwar wadannan alluna biyu, ina rashin yiwuwar yake cikin wannan mahawu wal isbat din da har zamu bukacin yin tawili da kallafa kan mu bayani da Allah bai kallafa mana ba, idan bamu iya gano hikimar sa sakamakon gazawar kwakwalen mu daga kewaya da ita tare da cewa hikima bayyane take cikin sa…. Sai Allama ya kawo wasu jumla daga hikimomi na bayyane kamar misalin bayyanar da ludufin sag a bayin sa zuwa ga Mala’iku masu rubutu cikin lauhul da tsinkaya kansa.

Daga ciki akwai cewa: shi ne wadannan hadisai su kasan ce yayi bakin ciki daga muminai da masu jiran faraji waliyyan Allah da galabar gaskiya da ahalinta, kamar yanda aka rawaito kissar Nuhu amincin Allah ya tabbata ga annabin mu da iyalansa da shi lokacin da aka bashi labarin halakar mutanen sa, sannan aka jinkirta hakan, kamar yanda aka rawaito cikin farajin Ahlil-baiti (a.s) da galabar su saboda su da ace sun baaiwa shi’ancu labari cikin farkon ibtila’in su da mamayar masu sabani da su da tsananin jarrabawar su da cewa ba za a samu faraji sai bayan shekara dubu da shi’an su sun debe tsammani daga addini, sai dai cewa su sun baiwa shi’ansu labarin gaggautar bayyanar faraji, tama yiwu sun gaya musu cewa zai iya yiwuwa  a samu faraji cikin wani zamani kusa-kusa domin su samu tabbatuwa kan addini, su samu ladan tsimayin faraji, kamar yanda ya gabata cikin hadisin Sarkin muminai (a.s) kamar yand zai zo cikin Risalar mu da izinin Allah ta’ala    

1 ـ روى الكليني باسناده عن علي بن يقطين قال : قال لي أبو الحسن  7 : الشيعة تربّي بالأماني منذ مائتي سنة ، قال : وقال يقطين لابنه علي بن يقطين : ما بالنا قيل لنا فكان ، وقيل لكم فلم يكن ؟ قال : فقال له علي : ان الذين قيل لنا ولكم كان من مخرج واحد، غير إنّ أمركم حضر فاعطيتم محضة ، فكان كما قيل لكم ، وأن أمرنا لم يحضر فعلّلنا بالأماني ، فلو قيل لنا: ان هذا الأمر لا يكون إلّا إلى مائتي سنة أو ثلاث مأة سنة لقست القلوب ، ولرجع عامة الناس عن الاسلام ، ولكن قالوا: ما أسرعه وما أقربه ، تأليفاً لقلوب الناس وتقريباً للفرج ، وقوله : قيل لنا أي في خلافة العباسية ـ وكان من شيعتهم ـ أو في دولة آل يقطين ، وقيل لكم أي في أمر القائم وظهور فرج الشيعة .

Ya rawaito da isnadin sa daga Aliyu bn Yakdinu ya ce: Abu Hassan ya gaya mini cewa: hakika shi’a sun tao cikin burace-burace tun kusan shekaru dari biyu  ya ce: sai Yakdinu ya cewa dansa Aliyu bn Yakdinu ya zamu yi an gaya muku ta faru an gaya mana ba ta faru ba? Sai Aliyu y ace masa: abin da aka gaya mana mu daku mafitar sa guda day ace, lallai al’amarinmu bai hallara sai muka sanya rai da burace burace, da za a gaya mana, wannan al’amari ba zai kasantu ba sai bayan shekaru dari biyu ko shekaru dari uku da zukata sun kekashe, da galibin mutane sun juyawa muslunci baya, sai dai cewa sun ce: me yafi gaggauta da shim ae yafi kusa da shi, domin su tattaro zukata da kusanto da faraji, fadin sa an ce mana yana nufin a zamani halifancin Abbasiyawa-ya kasan ce daga `yan shi’ar su- ma’ana cikin daular Yakdinu, an ce muku cikin al’amarin Imamul Hujja da bayyanar farajin shi’a,

2 ـ وروى أيضاً عن الحسين بن محمد بسنده عن الفضيل بن يسار عن أبي جعفر 7 قال : قلت لهذا الأمر وقت ؟ أي لظهور صاحب الزمان  7 المهدي القائم من آل محمد : فقال : كذب الوقاتون كذب الوقاتون ، كذب الوقاتون ، إنّ موسى على نبينا وآله وعليه السلام ـ لمّا خرج وافداً إلى ربّه واعدهم ثلاثين يوماً، فلمّا زاد الله إلى الثلاثين عشراً قال قومه : قد أخلفنا موسى فصنعوا ما صنعوا، فاذا حدّثناكم الحديث فجاء على ما حدّثناكم فقولوا: صدق الله، واذا حدّثناكم الحديث فجاء على خلاف ما حدّثناكم به ، فقولوا: صدق الله ـ أيضاً ـ تؤجروا مرتين .

An rawaito daga Husain ibn Muhammad da isnadin sa daga Fudailu bn Yasar daga babansa daga baban Jafar (a.s) ya ce: n ace shin wannan al’amari kuwa yana da lokaci? Ma’ana bayyanar Imam Mahadi (af) sai ya ce: masu sanya masa lokaci sunyi karya masu sanya lokaci sunyi karya, hakika Musa amincin Allah ya kara tabbata ga Annabin mu da iyalansa da shi-lokacin da ya fito yana mai nufar ubangijin sa yayi banu Isra’ila alkawarin kwanaki talatin, yayin da ya kara kwana goma kai sai mutanen sa suka ce ka Musa ya saba alkawari suka aikata abin da suka aikata, idan muka baku labari sai lamarin ya zo kamar yanda muka gaya muku to kuce Allah yayi gaskiy, idan kuma muka gaya muku sai al’amarin yazo sabanin abin da muka gaya muku to anan ma kuce Allah yayi gaskiya zaku samu lada karo biyu.

Ina cewa: wannan shi ne ma’anar bada’u dacacce da hankali wand ashi’a suka tafi kansa biye ga A’immar su (a.s) lallai su sun tarbiyantar da su da ladubban Allah, da su gasgata abin da Allah ya afkar da abin da masu gaskiya suka fada Imamai Ma’asumai daga iyalan Muhammad (s.a.w) lallai al’amarin su daga al’amarin Annabawa Ulul Azmi daga manzannin sa yake, idan har Musa ya bada labari da dare talatin sannan ya kara goma sai yayi bada’I ga Allah ma’ana abin da ya buya gare su ya bayyana kansu sakamakon hikimar jarrabawa da ibtila’i, da hikimar Allah wacce babu wanda ya santa sais hi da kuma masu zurfafar ilimi, sai dai cewa mutanen Musa basu yi Imani da bada’u sun bada sun kafirta sun koma da fushin Allah.

Wannan na daga banbanci daga girmamar al’ummar Muhammad da suke Imani da bada’u da kuma al’ummar Musa wadanda suka kafircewa abin da Annabin su ya basu labara sabani haka ya bayyana, duk wanda bai Imani da bada’u ya kasan ce kan batan Yahudawa daga al’ummar Musa (a.s).

Sannan Allama Majalisi ya ce: da sannu da yawa daga hadisai kan wannan za si cikin kitabul nubuwwa, musammam ma cikin babukan kissoshin Nuhu da Musa da Sha’aya tsira da aminci su kara tabbata kan annabin mu da iyalan sa da s, hakama zai zo ciki kitabul gaiba, bada labarin su kan abin da sabani sa zai bayyana a zahiri daga fuskanin dunkulallun maganganu da masu kaman ceceniya da juna wadanda suke gangarowa daga gare su da hukuncin hikima, sannan bayanin su da tafsirin su ya zo daga baya.

Fadinsu: abu kaza zai faru a lokaci kaza, idan ya kasan ce kaza maanar sa kaza, ko kuma idan abu kaza da yake cin karo da shi bai faru ba, ko kuma idan basu kawo sharadi kaza ba, kamar yanda suka fada cikin nasaki gabanin aiki, hakika mun yi Karin bayani cikin babin zabahi Isma’ail amincin Allah ya kara tabbata ga annabin mu da iyalan sa da shi.

Ma’anar fadinsu (ba a bautawa Allah da wani abu misalin bada’u ba) shi ne cewa Imani da bada’u yana daga mafi girman ibadoji na zuciya sakamakon wahalar sa da kawo da bijirar wasiwasin shaidan da yake kansa, sakamakon kasantuwar sa ikirari da cewa halitta da al’amari na hannun ubangiji, wannan yaa daga kamalar tauhidi, ko kuma ma’anar sa lallai shi yana daga mafi girmamar sabubbba da abubuwan da suke jawo hankali zuwa ga bautar ubangiji madaukaki kamar yanda ka sani.

Haka zalika fadin su (ba a girmama Allah da wani abu misalin bada’u ba) wannan yana karbar fuska biyu, duk da cewa ta farko cikin sa tafi bayyana. 

Amma fadin Imam Sadik (a.s)     

الإمام الصادق  7: (لو علم الناس ما في القول بالبداء من الأجر، ما فتروا عن الكلام فيه )

da mutane sun san ladan da yake cikin Imani da bada’u da jikinsu bai yi sanyi ba cikin Magana kansa.

Sakamakon abin da ya gabata daga akasarin maslahohin bayi da suka doru kan Imani da bada’u, domin da ace sun yi Imani da cewa dukkanin abin da aka kaddara tun azal ya zama dole ya afku, da bas u yi addu’a sun roki Allah komai ba cikin bukatun su, da basu yi masa magiya ba da basu kaskantar da kansu gabansa ba, da basu ji tsoran sa, da basu yi fata zuwa gare shi ba, da makamancin wannan daga abin da Mukai ishara zuwa gare shi.

Amma batun cewa wadannan al’amura suna daga jumlar sabubban kaddara cikin azal al’amarin yana faruwa tare da su bawai babu su, hakan yana daga abin da hankulan galibin muatne basu iya kaiwa gare su, sai ya bayyana cewa shi wannan lauhul da tsinkayar su da abin da zai faru cikin sa daga mahawu da isbat ya gyara musu komai-anan maganar sa ta zo karshe Allah ya daukaka matsayin sa.

Wannan sune jumlar maganganu da kalmomin malaman shi’a daga magabata dana bayansu da kumla daga dalilan su da suke shiryarwa kan afkuwar bada’a, lallai wajibi ayi Imani da shi, lallai shi yana daga kamalar tauhidi da kuma Imani da ikon Allah mudlaki da ilimin sa sarmadi.

A jumlace ya bayyana, baki dayan mutane al’umma bayan al’umma sun yi ittifaki kan cewa Allah masani ne kan abin da yaake gudana daga abubuwan da suke faruwa har abada gabanin halittar halittun sa, da sannu zai cigaba da kasancewa masani lallai kuma babu canji cikin ilimin sa, Azza wa Jalla, kowanne abu samamme cikin ilimin sa da samuwar sa ta ilimi, babu sauyi cikin iradar sa, kadai dai sauyi na tsakanin su cikin warware ishkalin mai gangara kan canji da bada’u cikin nassoshin da aka rawaito cikin makarantar Ahlil-baiti (a.s) da cewa da wacce ma’ana za a danganta shi zuwa ga Allah cikin fadin mu (bada lillahi kaza) abu kaza ya bayyana ga Allah, cikin warware ishkalin suna hanyoyi.

1-daga cikin su: shi ne ya kasan ce abind ake nufi daga bada’u shi ne samuwar wani abu da iliminsa ba ta’allaka da shi ba a aikace, shi ilimi bayani ne kan hallarar ma’alum ga zati mai riska masaniya, idan aka samu samammu a waje muka kiransu da hallarar su gaban Allah matsarkaki da sanin Allah kansu da ilimi na aiki, lokacin batan su sai mu kira su da rashin hallara da samun ilimi na aikace, daga fuskanin saliba bi intifa’u maudu’I, lallai maudu’in ilimi na aikaceda ilimi na hallare shi ne samuwar samammu cikin duniyar waje, yayin da aka rasa maudu’I sai ya kasan ce rashin ilimi a aikac, bawai Allah bai san su ba mudlakan, wannan rashi na aiki bai lazimta tasirantuwar zatin Allah, kamar misalin wanda ya fassara shi da gurbataccen bada’u, kadai bayan zanuwa muna fadi, domin babu zanantuwa cikin zatin Allah, domin shi zanuwa baya shiga cikin hakikar ilimi, bai kuma kasan ce masa lazimi ko mai daidaita da ilimi.

Abin da Kulaini ya rawaito yana ishara zuwa ga wannan fuska ta bada’u na hankali:

في الكافي بسنده عن الحسين بن محمد عن معلى بن محمد قال : سئل العالم ـ الإمام الكاظم  7 كيف علم الله؟ قال عَلَم وشاء وأراد وقدّر وقضا وأمضى . فأمضى ما قضا، وقضا ما قدّر، وقدّر ما أراد، فبعلمه كانت المشيئة ، وبمشيته كانت الإرادة ، وبإرادته كان التقدير، وبتقديره كان القضاء، وبقضائه كان الإمضاء، والعلم متقدّم المشيئة ، والمشيئة ثانيةٌ والارادة ثالثة ، والتقدير واقع على القضاء بالامضاء، فللّه تبارک وتعالى البداء فيما علم متى شاء، وفيما أراد لتقدير الأشياء، فاذا وقع القضاء بالامضاء، فلا بداء، فالعلم من العلوم قبل كونه ، والمشيئة في المشيء قبل عينه ، والارادة في المراد قبل قيامه ، والتقدير لهذه المعلومات قبل تفصيلها وتوصيلها عياناً ووقتاً، والقضاء بالامضاء هو المبرم من المفعولات ذوات الأجسام المدركات بالحواس من ذي لون وريح ووزن وكيل ، وما دبّ ودرج من إنس وجن وسباع وغير ذلک ، ممّا يدرک بالحواس ، ولله تعالى فيه البداء مما لا عين له ـأي ليس له وجود خارجي بل له وجود علمي في علم الله سبحانه ـ فإذا وقع العين المفهوم ـأي ماله مفهوم ووجود ذهني ـ والمدرک فلا بداء، والله يفعل ما يشاء، فبالعلم علم الأشياء قبل كونها، وبالمشيئة عرف صفاتها وحدودها وإنشاءها قبل إظهارها، وبالارادة ميّز أنفسها في ألوانها وصفاتها، وبالتقدير قدّر أقواتها، وعرف أوّلها وآخرها، وبالقضاء أبان للناس أماكنها ودلّهم عليها، وبالإمضاء شرح عللها، وأبان أمرها، وذلک تقدير العزيز العليم[4] .

 ya zo cikin Alkafi da isnadinsa daga Husain ibn Muhammad daga Mu’alla bn Muhammad ya ce: ya tambayi malamin gidan iyalan Muhammad –Imam Alkazim (a.s) ta yaya Allah ya sani? Sai ya ce: ya sani ya so ya nufa ya kaddara ya hukunta ya zartar, ya zartar da abin da ya hukunta, ya hukunta abin da ya kaddara, ya kaddara abin da ya nufa, da ilimin sa mashi’a ta kasan ce, da mashi’arsa irada ta kasan ce, da iradarsa kaddara ta kasantu, da kaddararsa hukunci ya kasantu, da hukuncin sa zartarwa ta kasantu, ilimi ya gabaci mashi’a, ita mashi’a ita ce ta biyu, irada kuma ta uku, kaddara yana afkawa kan hukunci da zartarwa, Allah yana da bada’u cikin abin da ya sani duk sanda ya so cikin abin da ya sa kaddara abubuwa , idan bada ya afku da zartarwa to babu bada’u shi ilimi yana daga ilimummuka gabanin kasantuwar sa, mashi’a cikin abin da ya so kafin ainahin sa, irada cikin abin da ya nufa gabanin tsayuwar sa, da kaddara wadannan abubuwa gabanin faifaice su, da sadar da su a waje da lokaci hukunci da zartar da shi yana daga tabbatacce daga ayyukan ma’abota jikkuna masu riska da mariskai daga ma’abota launi da kamshi da nauyi da awo, daga abin da ya gudana ya hau daga mutane da aljannu da dabbobin daji da makamantan su, daga abubuwan da ake riska da mariskai , Allah ta’ala yana bada’u cikinsu daga cikin abin da bai da samuwar waje kadai dai yana samuwa ta ilimi cikin ilimin sa matsarkakiidan abin da yake da samuwa ta kwakwale ya afku abin da ake riska, to babu bada'u cikin sa- shi Allah ya aikata abin da ya so, da ilimi ya san abubuwa gabanin kasantuwar su, da mashi’ar sa ya san siffofin su da iyakokin da kagar su gabanin bayyana su, da iradar say a mayyaze kawukan su daga launukan su da siffofin su, ya san farkon su da karshen su, da kaddara ya kaddara abincin su, da hukuncin say a bayyanawa mutane wuraren su ya shiryar da su zuwa gare su, da zartarwar sa ya sharhanta illolin su, ya bayyana al’amarin su, wadancananka shi ne kaddararwa mabuwayi masani.

Muhamma Rafi’u bn Mumin cikin sharhinsa kan madaukakin hadisi yana cewa: hakika abubuwa guda bakwai da aka ambace cikin wannan hadisi baki dayansu suna gudana ne cikin kasantattu daga kasa da sama daga ma’abota jikkuna bawai cikin ma’abota ruhi kadai ba kai hatta halittar farko.

Sai dai idan ace ya kawo jikkuna bisa misali ne, domin lallai abubuwan bakwai suna gudana cikin masau dauke da ruhi da yanayin la’akari.

Assayidul Rafi’u ya ce: zahiri daga tambayar mai tambaya cewa yaya ya san Allah? Shin ilimin Allah ya jingina zuwa ga hallarar waje da shuhudi cikin lokacin sag a samamme na gundari da misdaki na waje, ko kuma cikin samamme na gundari, kamar yanda yake cikin sanin mu ga ma’alumat na waje, ko kuma ilimin sa ya jingina zuwa ga zati magabaci kan halittar abubuwa.

Sai ya bada amsa: da cewa ilimin sa magabaci ne kan samuwar halittattu da martabobi, ya ce: ya so ya nufa ya kaddara ya hukunta ya zartar, wadannan martabobi shida suna sassabawa cikin ma’nonin su:

1-ilimi: shi ne abin da da shi abu yake yake bayyane ya yaye.

2- mashi’a: duban halayen da ake kwadayi cikin su da cikin mu suke wajabta mana karkata, koma bayan mashi’ar sa ta’ala matsarkaki, sakamakon daukakar sa daga siffantuwa da siffa ta kari kan zatin sa.

3- irada: motsar sabubba zuwa ga fuskanin sa da motsin nafsu cikin, sababin iradar sa matsarkaki.

4- kaddara: iyakan cewa da ayyanawa iyakoki da lokuta.

5- hukuntawa: shi ne wajabtawa.

6- zartarwa: samarwa-lallai abu mai yiwuwa yana tsayuwa da waninsa idan ya wajaba- da samuwar mai hukuntawa da rashin mai hanawa, idan ya samu sai ya wajaba, matukar bai wajaba ba zai samu ba, samuwar halittu bayan sanin sa matsarkaki da wannan martabobi. Da fadin sa: (sai ya zartar da abin da ya hukunta) ma’ana sai ya samar da abin da ya wajabta-ai da samuwar cikakkiyar illar sa, ya kuma wajabta abin da a kaddara, ya kaddara abin da ya nufa, yayin da bayanin sa (a.s) ya kai zuwa wannan gabar, sai ya sabi bayani karo na biyu daga faraway da fuska mafi bayyana, ya ce: (da ilimin sa mashi’a ta kasan ce) har zuwa dai karshen hadisin.

Sannan ma’anar bada’u dacacce da hankali cikin ba’arin martabobi, a wani lokacin wurin amawa wani lokacin kuma ga kebantattu kasawa. Amma gamagarin mutane to su wurin su: hakika cikin samuwar abin da ake zato a al’adan ce dorarre shi ne ya kai ga samuwar wani abu, kamar misalin wutar Namarudu- kan abin da ya tuke gare shi daga abin da yake a al’adan ce mukaddima ne zuwa ga samuwar wancan abun da ake zaton tabbatuwar kaddara cikin halaye bakwai da bibiyar sag a sauran su, idan wani abu ya samu sai a gano tabbatuwar dukkanin su, ta yiwu wani lokacin a samu sabawa al’ada-kamar yanda aka fada kan mu’ujiza daga abin da yake cikinta daga keta al’ada-bata bin tsarin mukaddimar da aka saba da ita ga samuwa zuwa ga samuwa-kamar misalin kunan wuta bari dai sai ta kasan ce sanyi da aminci ga Ibrahim (a.s) a wannan lokaci ana cewa (ya bayyana ga mahalicci makagi sha’anin sa ya girmama wuta mai kuna a al’adan ce ta zama canja ta zama lambu wadatacce sanyi da aminci).

Amma ma’anar bada’u wurin gamagari a wannan lokaci shi ne Allah matsarkaki ya kasan ce magudanar al’ada cikin fagen samar da abu sakamakon maslaha, ya kuma tsara ba’arin wasu mukaddimomin samuwar sa, sai dia cewa sabubban samuwa basu cika ba sakamakon canja maslaha, wannan misalin illa nakisa tauyayya tare da samuwar mai hukuntawa da farko tare da samuwa mai hanawa shamaki bayanta, al’adar wuta dai tare da samuwar mai hukuntawa shi ne ta kasan ce mai kuna da konewa sai dai kuma samuwar shamaki ya hana tabbatuwar wannan mai hukuncin kamar misalin samuwar kirare domin rura wuta, shamaki mai hanawa cikin kissar Ibrahim shi ne ta’allakar iradar Allah da cewa wuta ta kasan ce sanyi da aminci sakamakon maslahar hakan da take dawo wag a bayi.

Amma kasawa kebantattun mutane cikin bada’u na hankalisuna cewa Allah madaukaki ya ce:

 (وَإِنْ مِنْ شَيْءٍ إِلّا عِنْدَنا خَزائِنُهُ وَما نُنَزِّلُهُ إِلّا بِقَدَرٍ مَعْلُومٍ )[5]

Babu wani abu face wurin mu taskokin sa suke bama saukar da shi face da wani mikdari sananne.

 (اللهُ الَّذي خَلَقَ سَبْعَ سَماواتٍ وَمِنَ الاْرْضِ مِثْلَهُنَّ يَتَنَزَّلُ الاْمْرُ بَيْنَهُنَّ لِتَعْلَمُوا أَنَّ اللهَ عَلى كُلِّ شَيْءٍ قَديرٌ وَأَنَّ اللهَ قَدْ أَحاطَ بِكُلِّ شَيْءٍ عِلْماً)[6] .

Allah wanda ya halicci sammai bakwai da kuma daga kasa misalin su al’amari yana sassauka tsakankanin su domin kusan cewa lallai Allah yana da da iko kan komai kuma lallai Allah ya kewaya da ilimi kan komai.

Ya zo cikin Kamus (tanazzala) ma’anar sa sauka a sannu-sannu sai ya zamanto Kenan saukar sa ta kasan ce gwargwadon martabobin da aka ambata cikin hadisi, ba a inkarin la’akari da suna su kasan ce ga ilimi bisa wancan la’akari –duk da cewa dukkanin su suna shiga karkashin mafhumin ilimi da hakikar sa guda daya-  ta fuskanin mudlakin yaywa da bayyana ana kiransa da (ilimi) mudlaki da ya tattaro nau'ukan ma'lumat babu banbanci cikin abin da ya cancanci  kwarara samuwa daga samuwa mudlaka kansa wacce kwararar samuwa ba ta dogara kan abin da bai cancanci samuwar aikace ba ta waje cikin hikimar s- da abin da bai cancanci samuwa sakamakon rashin maslaha aikace cikin sa- saboda haka ilimin sa mudlaki kulli yana game duk mafhuman guda biyu  daga samuwar ilimi da zahiri. Ta fuskanin kasancewar shi wani nau'i ne na yayewa ta farko-shi ne abin da yake cancantar samuwa sabida maslaha cikin samuwar sa, ana kiran sa da (mashi'a) amma ta fuskanin abin da yake dacewa da nau'in farko daga fasalinsa da iyakoki ana kiransa da (irada) sannan ta fuskar yayewa da abin da ya dace da zamani da bigire ana kiransa da (kaddarawa) kan wannan kiyasi ne sauran la'akari wadanda yake da su daga bangaren kansa a wani lokaci, a wata fuskar kuma cudanyarsa daban, yana kasacewa ga la'akari bakwai wadanda ake kiransu da halaye bakwai mabayyanan samuwa daga ma'abota ruhi tsantsa da ma'bota jikkuna, cikin su hukuncin mai sauka daga mai gudanarwa mai hikima da mulkin sa ya buwaya yana tabbata, haka al'amri ke mikuwa cikin kausul nuzuli ya zuwa tukewa ga zartarwar Allah wacce babu makawa daga gare shi.

Wannan misalin litattafai da Risaloli sarakunan duniya idan sarki ya buga hatimi ya zartar to babu makawa ga gudanar hukuncin sa, domin baya dacewa da sha'anin mulkin sa ya janye, lallai yin hakan yana nuni ya zuwa rashin nazarin maudu'in kammalallen nazari sai abin da yake duniyar muliki da shuhudi ya kasan ce yana kaman ceceniya da abin da yake duniya mala'iku da gaibu, da mikuwa zuwa ga haddi.  

Zartarwa da babu makawa daga gare shi ya shardantu da rashin shafe abin da yake tabbace cikin lauhul mahfuz da saukar da wani hukuncin daban da yake shafe hukuncin farko, yake yaye bayanin sabubban daga bangaren bawa wadanda Allah ya sanya su sabubba ya zuwa sababin wani hukuncin daban sanyayya da izinin Allah, kamar misalin sababin sadar da zumunci da yanke shi cikin karuwar shekaru da tawayar su.

Sauka ta biyu wacce ake kira da bada'u a urfin shari'a-wannan isdilahi na shari'a yana nuni ya zuwa bada'u na hankali-lallai kuma yana kama bada'un lugga ta fuskanin canja abin da ya kasan ce yana aikata shi, da wannan ne aka kira shi bada'u, an dauko shi daga gamammiyar ma'anar sa ta lugga wacce take nufin bayyana ya zuwa ma'anar shari'a kebantatta da abin da ya ta'allaka da lauhul mahawu wal isbat da kuma saukar hukunci biyu daga tsantsar ilimi kulli da ilimi huduri na aikace, wanda ya ta'allaka da samamme na waje, ma'anar isdilahin shari'a kan bada'u ba it ace ta bada'u na lugga ba, domin yana bayyana ne daga jahilci da nadama, Allah ya daukaka daga haka daukaka mai girma, ya tsarkaka daga abin da suke siffantawa, saboda haka shi bada'un Allah daga ilimin sa azali yake wanda jahilci bai cufanya da shi, shi tabbataccen baya canjawa.

Daga ciki: shi danganta bada'u ga Allah madaukaki kadai dai ya kasan ce kan yanayin jinginawa majazi ba hakika ba, (bawai da ma'anar abin da yake cikin kalma ba) a bayyane yake cewa babin majazi cikin isnadi da jingina da kuma cikin hikima mayalwaciya kamar yanda yake cikin ilmul ma'ani wal bayan, Karin bayanin hakan: shi isnadi tsakanin musnad da musnad ilaihi cikin ilmul bayan, sune mubtada da kabar cikin ilimin nahawu, maudu'I da mahmuli cikin ilimul mandik, wani lokacin yana kasancewa hakika kamar yanda ake cewa (ruwa ya gudana) Allah ya tsurar da dankali, wani lokacin kuma yana kasancewa majazi kamar yand ake fada : indararo ya kwarara, da kaka ta tsirar da dankali, lallai shi yana daga istimali amfani na mazaji sakamakon alaka da dangantaka da samuwar Karina shaida da take shiryarwa zuwa ga haka mafi gamewa da ya kasan ce ace iya  shaida ta lafazi ko ta hankali ko ta magana ko hali.

Idan ya kasan ce zahiri daga fi'ilin bada'u da ya sadu da lamun jarra kamar fadin mu (bada lahu) da yake da ma'anar faruwa abin da da bai kasan ce ba, to lallai wannan ma'ana yanke tana lazimtar jahilci gabatacce, a irin wannan lokaci misalin wannan ma'ana amfani da ita kan Allah ya haramta a hankalce, idan hakan ya zo a hadisai masu daraja ko ayoyi masu girma to wajibi ayi tawilin su da bayyana su da yanayin da ya dace da hankali domin a kawar wa da jahilci daga Allah, idan ka danganta masa abin da yake lazimmta jahilciu bisa zahirin kalma ko jumla to wajibi a yi tawilinsa ya zuwa abin da baya cin karo da ilimin sa azali zati, baya kuma lazimta masa canji, da wani bayani: ita shaidar hankali cikin hana al'amarin kan dora isnadi kan majazi ko kalma kan majazi bata takaitu bata yi kasa da sauran shaidun lafazi da na hali dana mukami da suke shiryarwa kan amfani na majazi cikin isnadi ko kalma cikin hikima kan zahiri daga ayoyi ko riwayoyi.

Idan ya kasan ce zahirin ayoyi da riwayoyi yana cin karo da hukuncin hankali to ya zama dole ayi tawilinsa a yi tafsiri cikin sa, sakamakon rashin cin karo tsakanin hankali da hukunci shari'a, idan cikin kur'ani wani ya zo da zahirin san a farko yana nuni zuwa ga jikkanta Allah matsarkaki kamar misalin fadin sa madaukaki:

 (وَجَاء رَبُّکَ) (اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ) (وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاضِرَةٌ * إِلَى رَبِّهَا نَاظِرَةٌ)

(kuma ubangijinka ya zo) (ya harde kan al'arshi) (kuma fusake a wannan rana suna haske suna kallon ubangijinsu).

Basyan tabbatuwa koruwar jikkanta mudalakan daga Allah wanda ya wadatu da zatin sa, kuma lallai shi samuwar sa wajibi ce ga zatin sa, jikkanta na lazimta rakkabuwa da bukatuwa da talauta, wannan na daga ayoyin imkani.

A wannan lokaci ya zama dole muyi tawilin zahirin da abin da ya dace abubuwan da hankali ya tabbatar, alal misali hannun Allah saman hannun su da ya zo a aya, na nufin ikon Allah na saman ikon su, wannan shi ne abin da baki dayan malaman muslunci suka tafi akai face wasu yan tsiraru daga `yan Zahiriya da Hanbalawa a wannan zamanin na mu kuma sune `yan Salafiyya.

A wannan lokaci cikin abin da muke kai idan daba'u ya zamanto zahiri na komawa ga jahilci, ya zama dole ayi tawilin haka, lallai shi daga majazi cikin isnadi ko kalma yake, a wannan lokaci ba za ai mafani da bada'u kan ma'anar sa ta hakika kamar yanda mutane suke amfani da ita, bari za ai amfani da ma'anar sa ta majazi kamar misalin mahawu wal isbat cikin Allah matsarkaki ta'ala.

Kari kan haka hakika nya zo cikin hadisai ingantattu da bayani karara da cewa bada'u bai kasan ce daga jahilci ko nadama ko canja irada ba, bayan wannan da wancan ta kaka zai inganta da abokan rigimar shi'a su yi kage kansu da abin da suka barranta kansu da shi suke kuma inkarin sa da mafi tsananin inkari.

Daga ciki: lallai abin da ake nufi daga bada'u shi ne bayyanarwa da yanayin istimali na majazi, sai dia cewa kan tsarin majazi cikin kalma ba cikin isnadi, kamar yanda ya kasan ce a fuskar da ta gabata, shi ne ma'anar (sanarwa) sai ya bayyana ga Allah ma'ana ya sanar da wanin sa abin da bai sani ba daga abin da yake wurin sa, wannan amsa ta dace da abin da ya zo cikin bada'u cikin imamancin imamai biyu Musa bn Jafar Alkazim (a.s) da mutuwar dan uwansa Isma'il, da kuma Imam Hassan Askari mutuwar dan'uwansa Assayid Muhammad amincin Allah ya tabbata a gare shi.

Hakika tattara daga tsakanin wadancan riwayoyi masu tarin yawa yana shiryarwa kan cewa mutuwar Isma'il da Abu Jafar Assayid Muhammad shi ne sababin dagewar wahamin kasantuwar su imamai bayan mahaifinsu, lallai su biyun sun girmi Musa Alkazim da Hassan Askari (a.s) abin da yake a bayyane daga akida bisa abin da ya jewa mutane cikin hadisai shi ne cewa imamanci yana kasancewa ga babban `da bayan kowanne imami.

Sai Imam Alkazim (a.s) yayi ishara kan cewa Allah ya karbi ran Isma'il gabanin sa domin da hakan ya san cewa bashi ne imami bayana ba, hadisai sun shiryar kan cewa abin da ake nufi da bada'u shi ne (sanarwa) wannan amfani na majaziu cikin kalma ne kamar yanda ake cewa Zaidu zaki ne, ma'ana sadauki ne.

Takaice magana: bada'u gurbatacce kamar yanda makiya shi'a suke karantawa yana jawom kafirci da bata sakamakon ma'anar da yake dauke da ita daga tabbatar jahilci da nadama ga Allah matsarkaki, daga sauyawar ilimin sa da sabuntuwar iradar sa, da samuwar muradai guda biyu dangane da Allah masu kishiyantar juna, wannan dukkanin gurbace yake, daga nan sakamakon misalin wannan ishkali wasu sukai inkarin asalin samuwar bada'u

Sai dai cewa abin da ya zo a hadisai Ahlil-baiti: kadai yana da ma'anar bayyanuwa bayan buya sakamakon maslaha da take komawa ga bayi, babu kokwanto cikin samuwar bada'u na hankali da ake danganta shi ga Allah ta'ala cikin hadisai da aka rawaito daga Ahlil-baiti, bari dai an kirga haka cikin ba'arin wasu hadisai da cewa yana daga alamomin imani, cikin wasu ba'arin kuma da cewa: ba a bautawa Allah da wani abu misalin bada'u, sabida haka imani da bada'u ya kasan ce daga jumlar akidun mazhaba duk da cewa bai kasan ce daga laruran sa ba wadanda inkarin su yake wajabta kafirci.

Idan muka nufi tabbatar da bada'u daga hanyoyin da bana hadisai ba da gurbatattun ababen gujewa masu tarin yawa sun gangara kansa, sai dai cewa tabbatar da shi da hadisai kadai yana kasancewa bayan kallon hadisai da suka a cikin mukamin, lallai su kamar kur'ani sashen su yana fassara sashe, bayan tattara ma'ana tsakanin su, kuma ka da ya kasan ce yana sabawa ko kore hukuncin hankali, lallai muna fadar sa muna kuma imani da shi, kadai cikin sa an shardanta rashin cin karo da zahirai da hukuncin hankali- kamar yanda yake cikin ilimin Usulul fikhu-bisa abin da ya tabbata ciikin muhallin sa hakika bautuwa da zahiri da zato da hanyoyi  tare da cin karo da hukuncin Allah baya inganta mudlakan, ya zama dole a yi tawilin zahiri a wannan lokaci kamar yanda gabata cikin hukunce-hukuncen shari'a na fikihu ballantana bautuwa da zahiri cikin akida.

A ba'arin wasu hadisai ya zo: hakika Allah ya bai tana bada'u daga wani abu face abin da da ma can ya kasan ce cikin ilimin sa, cikin ba'arin wasu kuma: hakika Allah ta'ala yana da ilimi biyu: ilimul maknun baya sanar da bayin sa shi, sai kuma ilimi wanda ba maknun ba da yake sanar da shi ga ba'arin wasu bayin sa kamar annabawa, da wanin haka daga bayanai da suke shiryarwa kan danganta bada'u zuwa ga Allah matsarkaki, sai dai cewa bai lazimta ya kasan ce amfani da shi da ma'anar sa ta hakika, bai lazimtuwa da tabbatacciyar ma'anar sa canjawar ilimin azali ko jahilci da nadama, ko kuma sabunta irada azaliya, ko haduwar irada biyu masu karo da juna dangane ga zuwa ga Allah ta'ala, bari dai sabunta da mahawu da isbat kamar yanda ya gabata kadai dai suna cikin abubuwan da ya rigaya ya sani bawai cikin ilimin sa ba, shi ma'alumi abin da ya sani shi ne abin da ilimin sa azali ya ta'allaka da shi daga ayyukan bayi.

Cikin wata jumlar daban: abin da aka fa'idantu daga jimillar wandancan hadisai shi ne cewa abubuwan da suka rataya da umarninnikan da hanunnukan shari'a kamar sallah da shan giya daga ayyukan mukallafai sun tace cikin fuskar hukunce-hukuncen shari'a, da ma'anar cewa ubangiji yana nufin amfani da mukamin sa tsantsa cikin umarnin sa da hanin sa don bautar da bayinsa, bari dai sakamakon abin da yake cikin su daga maslaha da barna, cikin su akwai fuskar halitta da kasanta dake hukunta kebantaccen tasiri da kufai, alal misali zina da matar aure idan ya kasan ce haramun a shari'an ce to a duniyar halitta da kasanta yana hukunta yankewar arziki  da tauye rayuwa.

Wannan ma'ana tana gasgata cikin dukkanin hukuncin shari'a duk wani aiki daga ayyukan bayi da suka ta'allaka da umarni ko hani kadai yana da fuska biyu, fuskar hukuncin shari'a wand ayake ratayuwa da uamarni ko hanin ubangiji, fuskar halitta, shi ne bangaren da yake hukunta kufaifayin waje, abin da ya zo daga addu'a da ziyarori yana shiryarwa zuwa ga haka cikin siffanta zunubai, kamar yanda ya zo cikin du'au Kumaili da daren Arafat, 

اللّهم أغفرلي الذنوب التي تغيّر النعم وتهتک العصم ، وتنزل البلاء وتغيّر الهواء، وتمنع قطر السماء.

Ya Allah ka gafarta mini zunuban da suke canja ni'ima suke keta Katanga, suke saukar da bala'i, suke canja iska, suke hana sama digar da ruwa.

Da dai makamantan haka.

Kamar yanda hakika duk wani aiki da ayyuka bayi yana da dangantaka biyu: dangantakar sa da bawa t fuskanin kasantuwar aikin karkashin zabin bawa mai gangarowa daga iradar sa kamar yanda wannan shi ne zabi daga maganar zabi tsakanin jabar da tafwidi, sai dangantakar sa da mahalicci ta'ala, shi ne sanya lada kan abin da yayi umarni da aikata shi, kamar ladan sallah, da ukuba kan abin da ya hana aikatawa, kamar ukubar shan giya, babu banbanci cikin kasantuwar sa daga abin da ake bada lada ko wanda ake yin ukuba duniya ko ta lahira, kamar misalin rage tsahon rayuwa ga ba'arin wasu masu sabo misalin yanke sadar da zumunci da sabawa iyaye, ko kuma samun Karin arziki ga ba'arin wasu ayyukan `da'a kamar sadar da zumunci da kosar da mayunwaci da tufatar da matsaraici da sauran su.

Abin da ake fadi cikin rayuwar mutanen karshen zamani cewa za ta karkare tsakanin shekaru sittin zuwa saba'in, hakan bai kasantuwa karkashin illa tamma, bari dai yana kan hukuntau da illa nakisa, kadai dai hakan yana tasiri ba da ban samuwar shamaki hanau ba, kidan an ce shekarun Zaidu saba'in, idan ya sadar da zumuncin sa zasu zama tamanin, hakan bai daga abin da yake kawo sauyi da canji cikin ilimin Allah azali ko kuma haduwar kishiyoyin juna biyu ko tabbatar da jahilci ko nadama ga Allah matsarkaki madaukaki.

Abubuwan biyu duka sun kasan ce da sanyawar Allah matsarkaki, kamar yanda ya sanya cikin umarnin sa da hanin sa ta fuskar shari'a da bautarwa, da kuma fuskanin rattabuwar kufaifayin dabi'a da halitta kamar samun lada da ukuba kan ayyukan bayi, da wannan duban ne fuskoki da martabobi ke kasancewa ga kowanne guda daga wadancan ayyuka cikin mika da bijira, suna sassabawa cikin sunayen su bisa lakari da kuma fuskoki.

Ta yiwu ga kowanne daya daga wadancan fuskoki da martabobi ya zamanto yana da wata hakika kiyayya cikin zarafi da mazubin mazubai, ta yiwu ya kasan ce abin da ya zo daga Alluna cikin hadisai da ayoyi kamar misalin Allon (uwar littafi) da na (hukunci da kaddara) da (mahawu wal isbat) da (lauhul mahfuz) ishara ce zuwa ga wadancan addu'o'i tare da abin da yake cikin su daga zarafin su daga fuskar sabawa cikin fuskokin martabobi.

Alal misali fuskar shari'a ga ayyuka daga yanayin kasantuwar su umartattu da hanannu suna kasancewa kiyayyu cikin uwar littafi da fuskar kasancewa gare su daga kasantuwar shekaru Zaidu da yake aikata aiki kaza shekaru talatin da kuma shekarun mai aikata aiki kaza tsahon shekaru sittin wanda ake kidaya hakan daga kufaifayin halitta da kasanta da suka doru kan wadancan ayyukan kaddararru, kadai dais u kiyayyu ne cikin lauhul kada'I wal kadar.

Amma ta fuska wacce take bayani kan ta'allakuwar kowanne kufai kan mai tasiri kansa, daga ccewa wane da zai aikata aiki kaza da ya kasan ce kaza, da kuma ya aikata aiki kaza da zai shafe masa kufai kaza, sai ya tabbatar masa da kufai kaza, kadai dai haka kiyayye ne cikin lauhul mahawu wal isbat, haka ma fuskokin uku kiyayyun ne cikin (lauhul mahfuz) wadannan alluna sai su sanya alamomi ga ishara zuwa ga martabobin ilimin sa madaukaki ta'ala, kamar yanda abin da yake cikin ba'arin hadisai daga martabobin ilimi guda shida suke karfafa hakan kamar yanda ya gabata. Ko kuma bayani da cewa lallai shi Allah ta'ala yana da ilimi guda biyu ne, ilmul maknun da wanda da wanin sa, ko kuma cewa: babu wani anui da bayyanar masa face dai abin da ya rigaya ya kasan ce cikin ilimin sa mumkini.

Zai iya yiwuwa allunan su kasan ce ishara ne zuwa ga martabobin ilimin Allah matsarkaki domin daukaka mukamin mulkin sa da ikon sa mudlaki, kuma shi hannun sa bude yake yana aikata abin da ya so cikin abin da ya so, yana shafe abin da ya so ya tabbatar da wanda ya so wurin sa uwar littafi take.

Jumlar abin da muka ambata: lallai bada'u da ya zo cikin hadisai ma'anar sa a bayyane take bayanin zurfafa duba da nazari cikin su lallai shi yana daga al'amari na hankali yana daga cikin dunkular tauhidi da zurfafar imani,  da tattarar tsakanin jimilar su ba tare da wani kokwanto ba da ishkali, duk wani mai kawo ishkali kodai jahili da bai fahimci ma'anar bada'u ba wanda aka bijiro da shi a makarantar Ahlil-baiti (a.s) ko kuma munafuki cikin zuciyar akwai ciwo Allah ya kara masa ciwo, babu tsimi babu dabara sai ga Allah madaukaki mai girma.