Batu na biyar: bada'u kan hasken kur'ani da hadisan Ahlil-baiti

 


littafin Allah tsatson shiriya daga Ahlil-baiti:

kur'ani mai girma:

Allama Majalisi cikin Biharul-Anwar cikin bada'u da nasaku ya kawo ayoyi da suke shiryarwa kansu, kamar misalin fadin sa madaukaki cikin suratu Bakara:

 (ما نَنْسَخْ مِنْ آيَةٍ أَوْنُنْسِها نَأْتِ بِخَيْرٍ مِنْها أَوْمِثْلِها أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللهَ عَلى كُلِّ شَيْءٍ قَديرٌ)[1] .

 Bamu shafe daga wata ay aba ko mu manatar da ita face mun zo da mafi alheri da ita ko misalin ta ashe baku san cewa lallai Allah yana da iko kan komai ba.

 

2 ـ المائدة : (وَقالَتِ الْيَهُودُ يَدُ اللهِ مَغْلُولَةٌ غُلَّتْ أَيْديهِمْ وَلُعِنُوا بِما قالُوا بَلْ يَداهُ مَبْسُوطَتانِ يُنْفِقُ كَيْفَ يَشاءُ)[2]  .

 Yahudawa sun ce hannun Allah daddaure yake hannayen su daddaure an kuma tsine musu sakamakon abin da suka fada bari dai shi hannayen sa bude suke yana ciyarwa yanda ya so, Suratu Ma'ida

3 ـ الانعام : (هُوَ الَّذüي خَلَقَكُمْ مِنْ طيüنٍ ثُمَّ قَضى أَجَلاً وَأَجَلٌ مُسَمًّى عِنْدَهُ ثُمَّ أَنْتُمْ تَمْتَرُونَ )[3] .

 Shi ne wanda ya halicce ku daga yunbu sannan ya hukunta ajali da kuma ajali ambatacce wurin sa sannan ku kuna jayayya.

4 ـ الرعد: (لِكُلِّ أَجَلٍ كِتابٌ * يَمْحُوا اللهُ ما يَشاءُ وَيُثْبِتُ وَعِنْدَهُ أُمُّ الْكِتابِ )[4] .

 Ga kowanne ajali akwai littafi* yana shafe abin da ya so ya kuma tabbatar kuma wurin sa uwar littafi yake.

Madaukakan hadisai

Sannan Allama Majalisi cikin babin ya kawo riwayoyi saba'in zamu yi ishara zuwa jumla daga cikin su domin takaitawa, mai san fadadawa sai ya koma asalin littafin.

1 ـ قال الإمام الصادق  7«ما عظّم الله عزوجل بمثل البداء»[5] .

 Imam Sadik (a.s) ya ce: bat aba girmama Allah Azza wa Jalla ba da misalin bada'u.

2 ـ عن الباقر أو الصادق  8: «ما عبد الله عزوجل بشيء مثل البداء».

An karbo daga Imam Bakir ko Sadik (a.s): ba a bautawa Allah Azza wa Jalla da wani abu misalin bada'u.

Iana cewa: hakika wanda yayi imani da Allah yake ganin girman sa da girmama shi, to bai girmama shi ba da misalin imanin sa da bada'u ba, lallai shi bai bauta masa da wata bauta ba misalin imanin sa da bada'u, hakika lazimin sa imani da hukuncin Allah da kaddarar sa da sallama masa, da tawakkali da shi da mika al'amari gare shi, dukkanin haka ya ta'allaka ne da aikin zuciya da imani na akida da tunani wanda yake da dangantaka da ruhin mutum abadi, sannan kuma ya kasan ce mafi falalar ibada.

Amma imani da bada'u dacacce da hankali wanda imani da shi yake wajabta samun kusanci da Allah matsarkaki ta'ala: 

3 ـ قال الإمام الصادق  7: «إنّ لله علمين : علم مكنون مخزون لا يعلمه إلّا هو، من ذلک يكون البداء. وعلم علّمه ملائكته ورسله وأنبيائه ونحن نعلمه » 

Imam Sadik (a.s) ya ce: Allah yana da ilimummuka guda biyu: ilmul maknun taskatacce babu wanda ya san shi sai shi kansa, daga nan bada'u yake kasancewa, da kuma ilimin da ya sanar da Mala'iku da manzannin sa da annabawan sa kuma mu ma mun san shi.

Da misalin wannan ma'ana akwai wata riwaya da take shiryarwa kan tushen ilimummukan A'imma tsarkaka kamar yanda take shiryarwa kan bada'u

4 ـ عن أبي عبدالله 7 قال : «إنّ الله تبارک وتعالى قال لنبيه : (فَتَوَلَّ عَنْهُمْ فَما أَنْتَ بِمَلُومٍ )[6]  أراد أن يعذب أهل الأرض ، ثم بدا لله فنزلت الرحمة فقال : ذكّر يا محمد فان الذكرى تنفع المؤمنين ، فرجعت من قابل ـ أي في السنة القادمة جئت الإمام وباطل ـ قال : فقال أبو عبدالله 7: إنّ لله علمين : علم عنده لم يطلع عليه أحداً من خلقه ، وعلم نبذه إلى ملائكته ورسله ، فما نبذه إلى ملائكته ، فقد انتهى الينا ـ أي ذلک العلم عندنا، فانهم معدن وعيبة علم الله عزوجل ـ».ـ فقلت لأبي عبدالله 7: «جعلت فداک إني حدثت أصحابنا أي بما حدثتني في العام الماضي من البداء، إلّا انهم استفسروا عن ذلک ؟ وانه كيف يكون ؟ فقالوا: بدا لله ما لم يكن في علمه ، فهذا يلزمه الجهل على الله وهو محال

An karbo daga Abu Abdullah (a.s) ya ce: hakika Allah tabaraka wa ta'ala ya cewa Annabin sa: (ka juya ga barin su kai ba abin zargi ba ne) ya nufi ya azabtar da mutanen kasa sai ya bayyana gare shi sai ya saukar da rahama ya ce: ya Muhammad ka tunatar lallai tunatarwa tana amfanar da muminai, sai na dawo bayan shekara guda na je wajen Imam (a.s) ya ce: sai Abu Abdullah (a.s) ya ce: lallai Allah yana da ilimummuka biyu: akwai ilimin da yake wurin sa da bai tsinkayar da wani daga halittun sa ba kansa, da kuma ilimin da ya wurga shi zuwa ga Mala'ikun sa, hakika mu ma ya iso garemu, lallai su A'imma ma'adar ilimin Allah ne Azza wa Jalla, sai na cewa da Abu Abdullah raina fansarka lallai ni na zantar da sahabban mu daga abin ya bani labari shekarar da ta gabata dangane da bada'u sai dai cewa kuma sun nei Karin bayani kan haka  da cewa ta kaka yake kasancewa? Sai suka ce: ya bayyana ga Allah abin da bai kasan ce ba cikin ilimin sa ba, wannan yana lazimta jahilci kan Allah wanda kuma hakan bamai yiwuwa bane kansa korarre daga Allah.

5 ـ عن سدير قال : سأل حمران أبا جعفر 7 عن قوله تعالى : (عالِمُ الْغَيْبِ فَلا يُظْهِرُ عَلى غَيْبِهِ أَحَداً) فقال له أبو جعفر 7: «الا من ارتضى من رسول فانه يسلک من بين يديه ومن خلفه رصداً» وكان والله بما مقدّر من شيء ويقضيه في علمه ، فذلک يا حمران علم موقوف عنده ، اليه فيه المشيئة فيقضيه إذا أراد ويبدو له فيه فلا يمضيه ، فأمّا العلم الذي يقدّره الله ويقضيه ويمضيه ، فهو العلم الذي انتهى إلى رسول الله 6 ثم إلينا.

An karbo daga Sudairu ya ce: Himranu ya tambayi Abu Jafar (a.s) kan fadin sa madaukaki: (masanin gaibu baya bayyanar da gaibunsa ga kowa) sai Abu Jafar (a.s) ya ce masa: (face wadanda ya yarda dasu daga manzo lallai yana shigar da tsakanin gaban sa da bayansa masu gadi) Allah ya kasan ce bisa abin da ya kaddara daga wani abu ya hukunta shi cikin ilimin sa, wadancananka ya Himrana ilimi da ya tsayu wurin sa, gare shi cikin sa mashi'a take sai ya hukunta shi idan ya so ya bayyana gare shi baya zartar da shi, amma ilimin da yake kaddara shi  ya hukunta shi ya zartar da shi shi ne ilimin da ya uke ga manzon Allah (s.a.w) sannan ya karaso garemu.

6 ـ عن الفضيل قال : سمعت أبا جعفر 7 يقول : «العلم علمان : علم عند الله مخزون لم يطلع عليه أحد من خلقه ، وعلم علّمه ملائكته ورسله ، فأمّا ما علّم ملائكته ورسله فانه سيكون لا يكذّب نفسه ولا ملائكته ولا رسله ، وعلم عنده مخزون يقدّم فيه ما يشاء ويؤخّر ما يشاء ويثبت ما يشاء[7] .

Na karbo daga Fudailu ya ce: naji Abu Jafar (a.s) yana cewa ilimi kasha biyu ne: ilimin wurin Allah da ya taskace shi gare shi bai tsinkayar da wani daga halittun sa kansa ba, da kuma ilimin da ya sanar da Mala'ikun sa da manzanninsa, ilimi da yake taskace wurin sa yana gabatar abin da ya so cikin sa yana kuma jinkirta abin da ya so.  

7 ـ قال الإمام الصادق  7«من زعم ان الله عزوجل يبدو له في شيء لم يعلمه أمس فأبرأوا منه ».

Imam Sadik (a.s) ya ce: duk wanda yake raya cewa Allah Azza wa Jalla wani abu ya bayyana gare shi da a jiya bai san shi to barrantu daga wannan mutumin.

Wannan korarren bada'u ne wanda yake wajabta kafirci da bata, sai su barranta daga wanda yake fadin sa.

8 ـ عيون أخبار الرضا بسنده عن النوفلي يقول : قال الرضا 7 لسليمان المروزي في مجلس عده المأمون بين الإمام الرضا والعلماء: ما أنكرت من البداء يا سليمان ، والله عزوجل يقول : (أَ وَلا يَذْكُرُ الاِْنْسانُ أَنّا خَلَقْناهُ مِنْ قَبْلُ وَلَمْ يَکُ شَيْئاًويقول عزوجل :(وَهُوَ الَّذي يَبْدَوُا الْخَلْقَ ثُمَّ يُعيدُهُ ) ويقول : (بَديعُ السماواتِ وَالارض ) ويقول عزوجل :(ويزيدُ في الخَلقِ ما يَشاء) ويقول : (وَبَدء خَلقَ الانسان مِن طين ) ويقول عزوجل : (وَآخَرُونَ مُرْجَوْنَ لاَِمْرِ اللهِ إِمّا يُعَذِّبُهُمْ وَإِمّا يَتُوبُ عَلَيْهِمْ)ويقول عزوجل :(وَما يُعَمَّرُ مِنْ مُعَمَّرٍ وَلايُنْقَصُ مِنْ عُمُرِهِ إِلّا في كِتابٍ).

Daga Uyunu Akbarul Rida da isnadin sa daga Naufali yana cewa: Rida (a.s) ya cewa Sulaiman Almaruzi cikin majalisin da Mamun Abbasi ya shirya tsakanin Imam Rida da sauran malamai: me kayi inkari daga bada'u ya Sulaiman, Allah Azza wa Jalla yana cewa: (ashe mutum ba zai tuna cewa mun halicce shi daga gabani ba alhalin shi bai kasan ce komai ba) haka yana cewa: (shi ne wanda ya fara halitta sannan ya dawo da ita) yana cewa (makagin sammai da kasa) yana cewa (kuma yana kara abin da ya so cikin halitta) yana cewa (ya fari halitta daga yunbu) yana cewa (kuma da wasu da aka jinkirta su ga al'amarin Allah ko dai ya azabtar da su ko kuma ya karbi tubansu) yana cewa (ba a rayar daga wanda ake rayawa kuma ba za a tauye daga rayuwar sa ba face cikin littafi)   

قال سليمان : هل رويت فيه عن آبائک شيئاً؟ قال : نعم رويت عن أبي عبدالله 7انّه قال : لله عزوجل علماً مخزوناً مكنوناً لا يعلمه إلّا هو، من ذلک يكون البداء، وعلماً علّمه ملائكته ورسله ، فالعلماء من أهل بيت نبيّک يعلمونه .

Sai Sulaiman ya ce: shin ka rawaito wani abu cikin sa daga babannin ka? Sai ya ce: na'am na rawaito daga babana Abu Abdullah (a.s) cewa shi ya ce: Allah Azza wa Jalla yana da wani taskace boye babu wanda ya san wannan ilimi sai shi kadai, daga cikin wannan ilimi akwai bada'u, da kuma wani ilimi da ya sanar da Mala'iku da Manzanni shi, malamai daga Ahlil-baiti sun san wannan ilimi.

قال سليمان : أحبّ أن تنزعه من كتاب الله عزوجل . قال : قول الله عزوجل لنبيّه : (فَتوَلَّ عَنهُم فَما أنتَ بِملوم ) أراد إهلاكهم ثم بدا فقال : (وَذَكِّرْ فَإِنَّ الذِّكْرَى تَنفَعُ الْمُؤْمِنِينَ)[8] .

Sai Sulaiman ya ce: ana son ka ciro shi daga littafin Allah Azza wa Jalla, ya ce fadin sa Azza wa Jalla ga Annabin sa: (ka juya baya daga barin su kai ba abin zargi bane) ya nufi halakar da su sannan ya bayyana gare shi sai ya ce: (ka tunatar lallai tunatarwa tana amfanar da muminai) 

قال سليمان : زدني جعلت فداک .

Sai Sulaiman ya ce raina fansarka kara mini.

قال الرضا 7: لقد أخبرني أبي عن آبائه ان رسول الله 6 قال : ان الله عزوجل أوحى إلى نبي من أنبيائه أن أخبر فلان الملک إني متوفيه إلى كذا وكذا، فأتاه ذلک النبي فأخبره فدعا الله الملک ، وهو على سريره حتى سقط من السرير، وقال : يا ربّ أجلني حتى يشب طفلي ، وأقضى أمري ، فأوحى الله عزوجل إلى ذلک النبي ان أتت فلان الملک ، فأعلمه إلى قد أنست أجله ، وزدت في عمره خمس عشرة سنة ، فقال ذلک النبي يا رب إنک لتعلم اني لم أكذب قطّ ، فأوحى الله عزوجل إليه ، إنّما أنت عبد مأمور، فابلغه ذلک والله لا يسأل عمّا يفعل

Sai Rida (a.s) ya ce:  hakika babana da ga babannin say a bani labari cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce: lallai Allah Azza wa Jalla yayi wahayi ya zuwa wani Annabi daga Annabawan sa da cewa ka gaya sarki wani lallai ni zan karbi ransa zuwa kaza da kaza, sai wannan Annabi ya je wurin wannan basarake ya bashi labari  sai Allah ya kira shi alhalin yana kan gado sai ya fado daga kan gadon, ya ce: ya ubangiji ka jinkirta mini har `dana ya zama saurayi, ka hukunta al'amarina, sai Allah yayi wahayi ga wannan Annabi kaje wajen wannan Sarki ka gaya masa hakika an mantar da ajalin sa na kara masa shekara goma sha biyar, sai wannan Annabi ya ce ya ubangiji ka san cewa ni fa ban taba karya, sai Allah Azza wa Jalla yayi wahayi gare shi, kadai dai kai bawa ne da aka umarce shi, ka je ka isar da haka ba a tambayar Allah abin da yake aikatawa.

ثم التفت إلى سليمان فقال له : احسبک ضاهيت اليهود في هذا الباب ، قال  : أعوذ بالله من ذلک ، وما قالت اليهود؟ قال : قالت اليهود: (يَدُ اللّهِ مَغْلُولَةٌ)[9]

Sannan ya juya zuwa ga Sulaiman ya ce masa: ina zatonka kayi kama da Yahudawa cikin wannan babin, ya ce: ina neman tsarin Allahdaga haka, me Yahudawa suka ce? Sun ce: (hannun Allah daure yake)

يعنون إنّ الله قد فرغ من الأمر فليس يحدث شيئاً، فقال الله عزوجل : (غُلَّتْ أَيْدِيهِمْ وَلُعِنُواْ بِمَا قَالُواْ)[10]  ولقد سمعت قوماً سألوا أبي موسى بن جعفرعن البداء، فقال : وما ينكر الناس من البداء، وان يقف الله قوماً يرجئهم لأمره .

Suna nufin Allah y agama al'amari ba zai kara farar da wani abu, sai Allah Azza wa Jalla ya ce: (hannayen su ne daddaure an kuma tsine musu sakamakon abin da suka fada) hakika naji wasu mutane sun tambayi babana Musa bn Jafar (a.s) dangane da bada'u, sai ya ce: me mutane suke inkari daga bada'u, Allah ya dagatar da wasu mutne ya jinkirta su ga al'amarin sa.

قال سليمان : ألا تخبرني عن (إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ)[11]  في أي شيء

أنزلت ؟ قال : يا سليمان ليلة القدر يقدّر الله عزوجل فيها ما يكون من السنة إلى السنة في حياة أو موت أو خير أو شرّ أو رزق ، فما قدّره في تلک الليلة فهو من المحتوم .

Sai Sulaiman ya ce: ba zaka bani labarin daga (hakika mun saukar da shi cikin lailatul kadari) cikin wanne abu aka saukar? Ya ce: ya Sulaiman a lailatul kadari Allah Azza wa Jalla yake kaddara abin da zai kasan ce cikin shekara daga rayuwa da mutuwa da alheri da sharri ko arziki, abin da Allah ya kaddara shi cikin wannan dare yana daga tabbatacce yankakke.

قال سليمان : الان قد فهمت جعلت فداک فزدني قال : يا سليمان إنّ من الأُمور أُموراً موقوفة عند الله تبارک وتعالى يقدم منها ما يشاء ويؤخر ما يشاء، يا سليمان إنّ علياً 7 كان يقول : العلم علمان : فعلم علّمه الله ملائكته ورسله ، فما علّمه ملائكته ورسله فانه يكون ولا يكذّب نفسه ولا ملائكته ولا رسله ، ويمحو ويثبت ما يشاء.

Sulaiman ya ce: yanzu na fahimta raina fansarka ka kara mini, ya ce: ya Sulaiman lallai daga al'amura akwai tsayayyu wurin Allah tabaraka w ata'ala yana gabatar abin da ya so cikinsu yana kuma jinkirta wanda ya so, ya Sulaiman hakika Ali (a.s) ya kasan ce yana cewa: shi ilimi biyu n: ilimin da Allah ya sanar da Mala'ikun sa da manzannin sa, abin da ya sanar da Mala'iku da manzanni lallai zai kasan ce shi baya karya ta kansa ba kuma ya karyata Mala'ikun sa da manzannin sa, yana shafe abin da ya so ya tabbatar da abin da ya so.

قال سليمان للمأمون : يا أميرالمؤمنين لا أنكر بعد يومي هذا البداء، ولا اكذّب به إن شاء الله.

Sulaiman ya cewa Mamun: ya sarkin muminai bayan wannan ranar bazan kara inkarin bada'u ba, ba zan kara karyata shi ba da yardar Allah.

Allama Majalisi cikin bayanin hadisin ya ce: ta yiwu kafa dalilin sa (a.s) da farko da ayoyi ya kasan ce domin kawar da nesantar da abin da yake ginanne kan bada'u daga Allah ta'ala da ya farar da abu kaza da a bai kasan ce ba, ya canja abin da ya rigaya ya kasan ce, bawai kan abin da Yahudawa suka fad aba da wanda yayi kama da su: lallai Allah ya aikata abin da ya aikata, ya kaddara abin da ya kaddara cikin farkon al'amari, ba kuma ya canja komai daga halittar sako hukuncin s, lallai Allah yana da wani littafi yana shafe abin da ya rigaya ya tabbata a cikin sa, bisa abin da bincike kansa zai zo nan gaba, hakika bayaninsa ya gabata cikin wannan Risala sai ka koma ka bibiya.

Ya kawo ba'arin abin da yake shiryarwa kan nasaki, ko dai kan nazari da misali bisa kama d ajuna tsakanin bada'u da nasaki cikin kasantuwar dayan su canjawar al'amarin taklifi ne, dayan kuma canjawa al'amarin kasantattu ne da halitta, ko kuma dai abin nufi anan ya game nasaki

9 ـ عن أميرالمؤمنين  7 إنّه قال : لو لا آية في كتاب الله لأخبرتكم بما كان وبما يكون وبما هو كائن إلى يوم القيامة ، وهي هذه الآية : يمحو الله ما يشاء ويثبت وعنده امّ الكتاب .

Na ankarbo daga sarkin muminai (a.s) ya ce: ba da ban wata aya cikin littafin Allah ba dana baku labarin abin da ya kasan ce da wanda zai kasan ce da kuma wanda yake kasantacce har zuwa ranar kiyama, ita ce wannan aya: Allah yana shafe abin da ya so yana tabbatar da wanda ya so gare shi uwar littafi yake.

10 ـ تفسير علي بن ابراهيم القمي في قوله تعالى : (وَقالَتِ الْيَهُودُ يَدُ اللهِ مَغْلُولَةٌ غُلَّتْ أَيْديهِمْ وَلُعِنُوا بِما قالُوا بَلْ يَداهُ مَبْسُوطَتانِ )[12]  قال : قالوا: قد فرغ الله

من الأمر، لا يحدث الله غير ما قدّره في التقدير الأوّل ، فردّ الله عليه فقال : (بَلْ يَداهُ مَبْسُوطَتانِ يُنْفِقُ كَيْفَ يَشاءُ)[13]  أي يقدّم ويؤخّر ويزيد وينقص ، وله البداء والمشيئة .

Daga tafsirin Aliyu bn Ibrahim Qummi cikin fadin sa ta'ala: (Yahudawa sun ce hannun Allah daure yake hannayensu ne daddaure an tsine musu sakamakon abin da suka fada bari dai hannayen sa bude suke) ya ce: sun ce: hakika Allah ya gama al'amari babu wani abu kuma da zai fafar sabanin abin da ya kaddara cikin kaddarawa ta farko, sai yayi musu martani ya ce: (bari dai hannayen sa shimfide suke yana ciyarwa yanda ya so) ma'ana yana gabatarwa yana jinkirtawa yana karawa yana tauyewa, kuma yana da bada'u da mashi'a.

Ka sani abin da ake nufi daga hannaye biyu bawai biyun kirga ba, bari dai kinaya ce kan kamalar karfi da mubalaga da kurewa cikin siffanta ni'ima, kamar yanda mai magana yake cewa: bani hannu cikin wannan al'amari, bai nufin hannu na zahiri, bari dai yana nufin mubalaga cikin kore karfi da iko cikin al'amarin, ta yiwu ace: abin da ake nufi da waccan ni'imar duniya d ani'imar lahira.

11 ـ تفسير القمي في قوله : (هُوَ الَّذي خَلَقَكُمْ مِنْ طينٍ ثُمَّ قَضى أَجَلاً وَأَجَلٌ مُسَمًّى عِنْدَهُ ثُمَّ أَنْتُمْ تَمْتَرُونَ )[14]  عن أبي عبدالله 7 قال : الأجل المقضي هو

المحتوم الذي قضاه الله وحتمه ، والمسمّى هو الذي فيه البداء يقدّم ما يشاء ويؤخّر ما يشاء والمحتوم ليس فيه تقديم ولا تأخير.

وحدثني ياسر عن الرضا 7 قال : ما بعث الله نبياً إلّا بتحريم الخمر وان يقرّ له بالبداء، أن يفعل الله ما يشاء.

Tafsirul Qummi cikin fadin sa ta'ala: (shi ne wanda ya halicceku sannan ya hukunta ajali da kuma ajali ambatacce wurin sa sannan kuna jayayya) daga Abu Abdullah (a.s) ya ce: hukuntaccen Ajali shi ne yankakke wanda Allah ya hukunta shi ya tabbatar da shi, Almusamma shi ne ajalin da a cikin sa akwai bada'u yana gabatarwa yana jinkirtawa abin da ya so, amma hattamamme cikin sa babu gabatarwa da jinkirtawa. Yasir ya zantar da ni daga Rida (a.s) ya ce: Allah bai aiko wani Annabi ba face da haramta giya da kuma yi ikirari da bada'u, Allah yana aikata abin da ya s.

12 ـ تفسير القمي عن محمد بن الفضيل عن أبيه عن أبي جعفر 7 قال : قلت له جعلت فداک بلغنا إنّ لآل جعفر راية ، ولآل العباس رايتين ، فهل انتهى اليک من علم ذلک شيء؟ قال : أمّا آل جعفر فليس بشيء ولا إلى شيء، واما آل العباس فان لهم ملكاً مبطئاً يقرّبون فيه البعيد ويباعدون فيه القريب ، وسلطانهم عسر ليس فيه يسر، حتى إذا آمنوا مكر الله وآمنوا عقابه صيح منهم صيحة ، لا يبقى لهم مال يجمعهم ولا رجال يمنعهم ، وهو قول الله: (حَتّى إِذا أَخَذَتِ الاْرْضُ زُخْرُفَها وَازَّيَّنَتْالآية.

Tafsirul Qummi daga Muhammad bn Fudailu daga babansa daga Abu Jafar (a.s) na ce masa raina fansarka mun samu labari cewa Alu Jafar suna da tuta, Alu Abbas suna da tutoci biyu, shin ka sami wannan labari? Sai ya ce: amma Alu basa bakin komai ba kuma zuwa komai suke ba, amma Alu Abbas lallai su suna da mulki mai tsayi cikin sa suna kusanto da na nesa suna nesanta na kusa, mulkinsu tsanani babu sauki cikin sa , har lokacin da suka ji sun lamintu daga makircin Allah da ukubar sa sai ai musu wata tsawa da kara babu wata dukiya da suke tarawa da mutane da suke karesu da zasu ragu su wanzu, shi ne fadin Allah (har lokacin da idan  kasa ta riki zinariyarta ta kayatu)

قلت : جعلت فداک فمتى يكون ذلک ؟ قال : أما إنّه لم يوقّت لنا فيه وقت ، ولكن اذا حدّثناكم بشيء فكان كما نقول ـ فان وجود المعلول بوجود علته التامة من وجود المقتضى وعدم المانع ، فنخبركم بتمام العلة باذن من الله سبحانه فيكون ما نقوله لكم ـ فقولوا: صدق الله ورسوله ، وان كان بخلاف ذلک ـ حيث نذكر لكم العلّة الناقصة بذكر المقتضى من دون ذكر المانع فكان الواقع بخلاف ما أخبركم لوجود المانع فلم تتمّ العلّة ، فلا يقع المعلول فقولوا ـ: صدق الله ورسوله ، تؤجروا مرتين ـ لقبولكم القول الأول بذكر المقتضي وحسب ، وما لم يتحقق المقتضي بوجود المانع الذي لم تطلّعوا عليه ـ.

ولكن إذا اشتدّت الحاجة والفاقة ، وانكر الناس بعضهم بعضاً، فعند ذلک توقّعوا هذا الأمر صباحاً ومساءاً.

قلت : جعلت فداک الحاجة والفاقة قد عرفناهما، فما إنكار الناس بعضهم بعضاً؟ قال : يأتي الرجل أخاه في حاجة فيلقاه بغير الوجه الذي كان يلقاه فيه ، ويكلّمه بغير الكلام الذي كان يكلّمه[15] .

Sai na ce raina fansarka to yaushe ne hakan zai faru? Sai ya ce: amma yanda lamarin yake bai iyakan ce mana lokaci ba cikin sa, sai dai cewa idan muka baku labarin wani abu sai ya kasan ce to kuce Allah yayi gaskiya- sakamakon samuwar sababin sa faruwarsa da rashin shingen da zai hana afkuwar. idan kuma muka baku labarin wani abu sai bai kasan ce- sakamakon mun ambaci illa nakisa da kawo muktadi amma bamu gaya muku cewa akwai mani'u hanau shinge da zai ratso bay a hana afkuwar ma'aluli ba- to shima kuce Allah da manzonsa sunyi gaskiya, lallai zaku samu lada karo biyu sakamakon yardarku kan maganar farko da mabaton hukuntau kadai, kuma matukar hukuntau bai tabbatar da rashin samuwar hanau wanda baku iya tsinkayar sa ba.

Sai dai cewa kuyi tsammanin wannan al'amari safiya da maraice.

Sai na ce: raina fansarka tsananin bukata da talauci mun san su, amma me ya kawo inkarin ba'arin mutane ga ba'arin su? Ya ce: mutum zai jewa dan'uwansa cikin bukata sai ya hadu da shi da sabanin fuskar da ya saba haduwa da shi, sai yayi masa magana da sabanin maganar da ya kasan ce yana yi masa. 

13 ـ تفسير القمي في قوله تعالى : (لِكُلِّ أَجَلٍ كِتابٌ * يَمْحُوا اللهُ ما يَشاءُ وَيُثْبِتُ وَعِنْدَهُ أُمُّ الْكِتابِ)[16]  عن أبي عبدالله 7 قال : إذا كان ليلة القدر نزلت

الملائكة والروح والكتبة إلى سماء الدنيا، فيكتبون ما يكون من قضاء الله تعالى في تلک السنة ، فاذا أراد الله أن يقدّم شيئاً أو يؤخره أو ينقص شيئاً، أمر الملک أن يمحو ما يشاء، ثم أثبت الذي أراد.

قلت : وكل شيء هو عند الله مثبت في كتاب ؟ قال : نعم ، قلت : فأيّ شيء يكون‌بعده ؟ قال : سبحان الله ثم يحدث الله أيضاً ما يشاء تبارک وتعالى .

Tafsirul Qummi cikin fadin sa: (kowanne ajali yanada littafi* Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar da wanda ya so wurin sa uwar littafi yake) na karbo daga Abu Abdullah (a.s) ya ce: idan lailatu kadri ta kasan ce sai Mala'iku su sauko da Ruhu da marubuta ya zuwa saman duniya, sai rubuta abin da zai kasan ce daga hukuncin Allah ta'ala cikin wancan shekara,, idan Allah ya nufi ya gabatar da wani abu ko jinkirta shi ko tauye wani abu sai ya umarci Mala'ika ya shafe abin da ya so ya tabbatar da abin da ya nufa.

Sai na ce: kowanne abu a wajen tabbace yake cikin littafi? Ya ce: na'am na ce: mene ne zai kasan ce daga bayansa? Ya ce: tsarki ya tabbatar masa sannan ya farar da abin da ya so tabaraka wa ta'ala.

14 ـ تفسير القمي في قوله تعالى : (وَما يُعَمَّرُ مِنْ مُعَمَّرٍ وَلا يُنْقَصُ مِنْ عُمُرِهِ إِلّا في كِتابٍ )[17]  يعني يكتب في كتاب ، وهو ردّ على من ينكر البداء.

Tafsirul Qummi cikin fadin sa madaukaki: (da kuma abin da yake rayawa daga abin da yake rayawa baya tauyewa daga shekarunsa face yana cikin littafi) ma'ana yana rubuta shi cikin littafi, wannan raddi kan wanda yayi inkarin bada'u. 

15 ـ تفسير القمي (فِيها يُفرَق ) في ليلة القدر (كُلُّ أمرٍ حَكيم ) أي يقدّر الله كل أمر من الحق ومن الباطل ، وما يكون في تلک السنة ، وله فيه البداء والمشيئة يقدّم ما يشاء ويؤخر ما يشاء من الآجال والأرزاق والبلايا والأعراض والأمراض ، ويزيد فيها ما يشاء وينقص ما يشاء ويلقيه رسول الله 6 أميرالمؤمنين  7، ويلقيه أميرالمؤمنين  7 إلى الأئمّة  : حتى ينتهي ذلک إلى صاحب الزمان عجّل الله فرجه ، ويشترط له في البداء والمشيئة والتقديم والتأخير، قال : حدثني بذلک أبي عن ابن أبي عمير، عن عبدالله بن مسكان ، عن أبي جعفر وأبي عبدالله وأبي الحسن صلوات الله عليهم[18] . 

Tafsirul Qummi (cikin sa ake rarrabe) ma'ana cikin lailatul Kadri(duk wani al'amari na hikima) ama'ana Allah yana kaddara duk wani al'amari daga gaskiya da bata, da abin da zai kasan ce a cikin shekara, cikin sa yana da bada'u da mashi'a yana gabatar da abin da ya so ya jinkirta wanda ya so daga ajali da arziki da bala'o'i da abubuwa masu bijirowa da cututtuka, yana kara abin da ya so cikin say a tauye wanda ya so yana mika ga Manzon sa (s.a.w) da sarkin muminai (a.s) da A'imma (a.s) har ya tuke zuwa ga Sahibul Zaman Allah ya gaggauta bayyanar sa, yana shardan masa bada'u da mashi'a da gabata da jinkirta, ya ce:babana ya zantar dani haka daga Ibn AbI Umairu daga Abdullahi bn Muskan daga Abu Jafar da Abu Hassan amincin Allah ya tabbata a gare su.

16 ـ امالي الطوسي بسنده عن محمد قال : سئل أبو جعفر 7 عن ليلة القدر، فقال : تنزّل فيها الملائكة والكتبة إلى سماء الدنيا، فيكتبون ما هو كائن في أمر السنة ، وما يصيب العباد فيها، قال : وأمر موقوف لله تعالى فيه المشيئة ، يقدّم منه ما يشاء ويؤخر ما يشاء وهو قوله تعالى : (يَمْحُوا اللهُ ما يَشاءُ وَيُثْبِتُ وَعِنْدَهُ أُمُّ الْكِتابِ )[19] .

Amali Dusi da isnadin sa daga Muhammad ya ce: ya tambayi Abu Jafar (a.s) dangane da lailatul kadari, sai ya ce: cikin sa Mala'iku suna sassauka da marubuta ya zuwa saman duniya, sai rubuta abin da zai kasan ce cikin al'amarin shekara, da abin da zai samu bayi cikin ta, ya ce: al'amarin ya tsayu ne kan Allah ta'ala cikin sa akwai mashi'a, yana gabatar abin da ya so daga gare shi yana jinkirta wanda ya so, shi ne fadin sa ta'ala: (Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar wanda ya so wurin sa uwar littafi yake)  

17 ـ علل الشرائع بسنده عن أبي جعفر الباقر 7: إنّ الله عزّوجل عرض على آدم أسماء الأنبياء وأثارهم قال : فمرّ بآدم إسم داود النبي ، فاذا عمره في العالم أربعون سنة فقال آدم : يا رب ما أقلّ عمر داود وما أكثر عمري ! يا رب إن أنا زدت داود من عمري ثلاثين سنة أثبت ذلک له ؟ قال : نعم يا آدم ، قال : فإني قد زدته من عمري ثلاثين سنة ، فانفذ ذلک له ، وأثبتها له عندک وإطرحها من عمري ، قال أبو جعفر 7: فأثبت الله عزوجل لداود من عمره ثلاثين سنة ، وكانت عند الله مثبتة ، فذلک قول الله عزوجل : (يَمْحُوا اللهُ ما يَشاءُ وَيُثْبِتُ وَعِنْدَهُ أُمُّ الْكِتابِ )[20] ، قال : فمحى الله ما كان عنده مثبتاً لآدم وأثبت لداود ما لم يكن عنده مثبتاً،

A'ilalul shara'i da isnadin sa daga Abu Jafar Albakir (a.s): hakika Allah Azza wa Jalla ya bijiro da sunaye da kufaifayin su kan Adam ya ce: sai Adam ya wuce ta kan sunan Annabi Dauda sai ga shekarun sa a duniya Arba'in sai Adam ya ce: ya ubangiji me yafi karanta daga shekarun Dauda mae yafi yawa daga shekaruna! Ya ubangiji idan ni na karu da shekaru talatin daga shekaruna to ka kara hakan ga Dauda, ka tabbatar masa da ita wurin k aka cire su daga nawa shekarun, sun kasan ce tabbatattu wurin Allah, haka zalika fadin Allah Azza wa Jalla (Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar da abin da ya so wurin sa uwar littafi yake) ya ce: sai Allah ya shafe abin da ya kasan ce ga Adam ya tabbatar da su ga Dauda daga abin da bai kasan ce tabbace gare shi ba.

قال : فمضى عمر آدم فهبط ملک الموت لقبض روحه ، فقال له آدم : يا ملک الموت إنّه قد بقي من عمري ثلاثون سنة ! فقال له ملک الموت : يا آدم ألم تجعلها لابنک داود النبي وطرحتها من عمرک حين عرض عليک أسماء الأنبياء من ذريتک ، وقد عرضت عليک أعمارهم وأنت يومئذ بوادي الدخيا؟ قال له آدم : وما أذكر هذا، قال : فقال له ملک الموت : يا آدم لا تجحد، ألم تسأل الله عزوجل أن يثبتها لداود ويمحوها من عمرک ؟ فأثبتها لداود في الزبور، ومحاها من عمرک في الذكر قال آدم : حتّى أعلم ذلک .

Ya ce: sai shekarun Adam suka tafi suka shuda Mala'ikan mutuwa ya sauka domin karbar ransa, sai Adam ya ce masa: ya Mala'ikan mutuwa akwai shekaru talatin da suka rage mini ai! Sai Mala'ikan mutuwa ya ce masa: ya Adamu ashe bakai kyautar su ga `danka Annabi Dauda ka cire su daga lissafin shekaruka ba lokacin da aka bijiro maka da sunayen Annabawa daga zuriyar ka, da shekarun rayuwar su a lokacin kana kwazazzabon Dukiya, sai Adam ya ce masa: ni bana iya tuna wannan, ya ce, sai Mala'ikan mutuwa ya ce masa: ya Adam kada kayi jayayya, ashe ba kaine ka roki Allah Azza wa Jalla da ya tabbatar da shekaru talatin daga cikin shekarun ka ga Dauda ya goge daga gareka? Sai ya tabbatar da su ga Dauda cikin Zabura, ya goge daga shekarunka cikin Ambato sai Adam ya ce: har sai na gano haka. 

قال أبو جعفر 7: وكان آدم صادقاً لم يذكر ولم يجحد، فمن ذلک اليوم أمر الله تبارک وتعالى العباد أو يكتبوا بينهم إذا تداينوا وتعاملوا إلى أجل مسمى ، لنسيان آدم وجحوده ما جعل على نفسه .

Abu jafar (a.s) ya ce: Adamu yana da gaskiya bai tuna ba bai kuma yi jayayya ba, daga wannan rana Allah tabaraka wa ta'ala ya umarci bayinsa su dinga rubutu tsakanin su idan sun kulla bashi ko wata mu'amala zuwa wani ambataccen ajali, sakamakon mantuwar Adam da jayayyar da yayi kan abin da ya sanya shi da kansa.

Ina cewa: hakika Allah yayi umarni da haka cikin kur'ani mai girma cikin karshen suratu Bakara cikin mafi tsayin ayar kur'ani mai girma.

18 ـ توحيد الصدوق بسنده عن أبي عبدالله 7 أنه قال في قوله عزوجل  : (وَقالَتِ الْيَهُودُ يَدُ اللهِ مَغْلُولَةٌ ) لم يعنوا إنّه هكذا، ولكنّهم قالوا: قد فرغ من الأمر فلا يزيد ولا ينقص ، فقال الله جل جلاله تكذيباً لقولهم : (غُلَّتْ أَيْديهِمْ وَلُعِنُوا بِما قالُوا بَلْ يَداهُ مَبْسُوطَتانِ يُنْفِقُ كَيْفَ يَشاءُ)[21]  ألم تسمع الله عزوجل يقول : (يَمْحُوا للهُ ما يَشاءُ وَيُثْبِتُ وَعِنْدَهُ أُمُّ الْكِتابِ )[22] .

Attauhidul Saduk da isnadin sa daga Abu Abdullah (a.s) cewa cikin fadin sa Azza wa Jalla (Yahudawa sun ce hannun Allah daure yake) ya ce: basu nufi cewa haka yake ba, sai dai sun ce: Allah y agama al'amari ba zai kara bazai tauye ba, sai Allah girmansa ya girmama don karyata fadin su ya ce: (hannayen su suke daddaure an la'an ce su sakamakon abin da suka fada bari hannayen sa shimfide suke yana ciyarwa yanda ya so) ashe baka ji fadin Allah Azza wa Jalla ba (Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar da wanda ya so wurin sa uwar littafi yake)

19 ـ التوحيد بسنده عن أبي عبدالله 7 قال : ما بعث الله عزوجل نبياً حتى يأخذ عليه ثلاث خصال : الاقرار بالعبودية ، وخلع الانداد، وإنّ الله يقدم ما يشاء ويؤخر ما يشاء.

Attauhid da isnadin sa daga Abu Abdullah (a.s) ya ce: Allah Azza wa Jalla bai aiko wani Annabi ba har sai ya riki abubuwa uku kansa: ikirari da bauta, kore masa kishiyoyi, da kuma cewa Allah yana gabatar da abin da ya so ya jinkirta wanda ya so.

20 ـ أيضاً التوحيد باسناده قال : سمعت أبا عبدالله 7 يقول : ما تنبأ نبيّ قط حتى يقرّ لله تعالى بخمس : البداء والمشيئة ، والسجود، والعبودية ، والطاعة .

Haka dai daga Attauhid da isnadin sa ya ce: naji Abu Abdullah (a.s) yana cewa: Allah bai baiwa wani Annabi annabta ba har sai tabbatarwa da Allah abubuwa biyar: bada'u, mashi'a, sujjada, bauta, `da'a.

21 ـ بصائر الدرجات باسناده عن أبي عبدالله 7 قال : إنّ الله تبارک وتعالى قال لنبيه (فَتَوَلَّ عَنْهُمْ فَما أَنْتَ بِمَلُومٍ)  أراد أن يعذّب أهل الأرض ، ثم بدا لله فنزلت الرحمة فقال : (ذكر يا محمد فان الذكرى تنفع المؤمنين (فرجعت من قابل ـ أي رزية في السنة القابلة ـ فقلت لأبي عبدالله 7: جعلت فداک اني حدّثت أصحابنا، فقالوا: بدا لله مالم يكون في علمه ؟ قال : فقال أبو عبدالله 7 : ان لله علمين : علم عنده لم يطلع عليه أحد من خلقه ، وعلم نبذه إلى الملائكة ورسله فما نبذه إلى ملائكته فقد انتهى إلينا.

Basa'irul darajat da isnadin sa daga Abu Abdullah (a.s) ya ce: hakika Allah tabaraka wa ta'ala ya cewa Annabin sa: (ka juya ga barin su kai baa bin zargi bane) da hakan ya nufi yiwa mutanen kasa azaba, sannan ya yi bada'u sai rahama ta sauka ya ce: (ya Muhammad ka tunatar ita tunatarwa tana amfanar muminai, sai bayan shekara guda na dawo na cewa baban Abdullah (a.s) raina fansarka hakika ni na zantar da mutanen mu sai suka ce: ya bayyana ga Allah abin da bai kasan ce cikin ilimin sa ba? Sai ya ce: Allah yana da ilimu biyu: ilimin da yake wurin sa da bai tsinkayar da kowa shi ba daga halittunsa, da kuma ilimin da sanar da wasu daga Mala'ikun sa hakika ya karaso wurin mu.

Cikin hamishi gefan shafuka cikin bayanin hadisin ya ce: ta yiwu sun fadi haka ne kan misalin neman fahimta da sigar inkari, ko kuma sun ce: lallai lazimin abin da ka bada labari daga ayoyin biyu shi ne cewa ya bayyana ga Allah abin da da bai kasan ce cikin ilimin sa ba, wannan sabanin abin da shi'a suka tafi kai ne, yayin da Abu Basir ya ga wannan inkari da mamaki daga mutanen sa abokan sa, sai bijirar da hakan ga Imam (a.s) shi kuma ya bashi amsa da cewa bai ya lazimta hakan saboda Allah yana da ilimi nau'i biyu ne, ilimin da ya kebantu da shi bai tsinkayar da wani shi ba cikin sa akwai bada'u, yana gabatar abin da ya so ya kuma jinkirta wanda ya so, ya tabbatar da wand aya so, ya shafe wanda ya so, kan abin da maslaha amfanonin abubuwan suke hukuntawa tare da iliminsa cikin azal da gabatarwa da jinkirtawa, da goge shi da tabbatarwa.

Sannan Allama majalisi (ks) ya nakalto riwayoyi da suke zama misdaki da yake shairyarwa kan bada'u na hankali, ma'ana yana kawo kissoshi da hikayoyin Annabawa da Mala'iku da mutane ta yaya suke bada labarin abu sannan ya canja da wani abu daban, kamar misali yam utu bayan kwanaki bakwai sai kuma shekarun sa us mika zuwa talatin kamar yanda ya zo cikin kissar Annabi Dauda (a.s) ko kuma taimakon wani Annabi daga Banu Isra'ila bayan kwanaki goma sha biyar sai ya jinkirta shi zuwa shekaru goma sha biyar, haka akasi, da kuma kissar Annabi Hizkilu da Sha'aya da wasun su, ka koma ka bibiyar a can littafin.

22 ـ المحاسن بسنده عن الفضيل قال : سمعت أبا جعفر 7 يقول : العلم علمان : علم عند الله مخزون لم يطلع عليه أحداً من خلقه ، وعلم علّمه ملائكته ورسله ، فأمّا ما علّم ملائكته ورسله ، فإنّه سيكون لا يكذّب نفسه ، ولا ملائكته ولا رسله، وعلم عنده مخزون يقدّم فيه ما يشاء، ويؤخّر ما يشاء، ويثبت ما يشاء.

Almahasin da isnadin sa daga Fudailu ya ce: na ji Abu Jafar (a.s) yana cewa: ilimi biyu ne: ilimin da yake taskace wurin Allah bai tsinkayar da kowa ba kansa daga halittun sa, da ilimin da ya sanar da Mala'iku da Manzannin sa shi, amma wanda ya sanar da Mala'iku da manzannin sa shi, lallai zai kasan ce baya karya ta kansa kuma baya karyata Mala'ikun sa da Manzannin sa, ilimin da yake taskace wurin sa cikin sa yana gabatar da wanda ya so ya jinkirta wanda ya so, ya tabbatar da wanda ya zo.

23 ـ وعنه  7 في هذه الآية (يَمْحُو اللّهُ مَا يَشَاء وَيُثْبِتُ)[25]  قال : فقال : وهو

يمحو الله إلّا ما كان ، وهل يثبت إلّا ما لم يكن ؟

Daga gare shi (a.s) cikin wannan aya (Allah ya shafe abin da ya so ya tabbatar da wanda ya so) ya ce: sai ya ce: shi ne Alah yana goge face abin da ya kasan ce, kuma shi yana tabbatarwa face abin da bai kasan ce ba?

24 ـ عن مرازم بن حكيم قال : سمعنا أباعبدالله 7 يقول : ما تنبّأ نبي قطّ حتى يقرّ لله تعالى بخمس : بالبداء والمشيئة والسجود، والعبودية ، والطاعة .

Daga Mazarimu bn Hakim ya ce: mun ji Abu Abdulla (a.s) yana cewa: wani Annabi bai zama Annabi face yayi wa Allah ikirari da abubuwa biyar: bada'u, mashi'a, sujjada, bauta, `da'a.

Ina cewa: misalin wannan hadisai masu daraja ana fa'idantuwa daga da cewa akwai tabbatattun abubuwa asalin annabta ko kuma gamammiya annabt-kamar yanda yake isdilahi cikin Ilmul Kalam-duk wani Annabi tun daga Adamu har zuwa cikamakin Annabawa, sunyi ikirari da bada'u, bari ya sanya ikirari da shi matsayin sharadin basu annabta, wannan shi ne alkawarin da Allah ya rika daga gare su, duk al'ummomin Annabawa sun kasan ce suna imani da bada'u face al'ummar cika makin Annabawa, hakika kungiya tseratatta daga mabiya A'imma tsarkaka sunyi imani da bada'u, kan haka makiya sun bata musu suna, babu cutuwa cikin haka matukar gaskiya tana bayyane tare da dawwamar kan gaskiya zuwa gaskiya cikin gaskiya , ka fara sanin gaskiya zaka san ahalinta shin akwai wani abu bayan gaskiya in banda bata?

25 ـ عن الريان قال : سمعت الرضا 7 يقول : ما بعث الله نبيّاً قطّ إلّا بتحريم الخمر، وأن يقرّ له بالبداء.

Daga Rayyan ya ce: naji Rida (a.s) yana cewa: Allah bai aiko wani Annabi kwata-kwata face da haramta giya da kuma yi masa ikirari da bada'u.

26 ـ وعن مالک الجهني قال : سمعت أبا عبدالله 7 يقول : لو يعلم الناس ما في القول بالبداء من الأجر ما فتروا عن الكلام فيه .

An karbo daga Malik Ajjuhni ya ce: na ji Abu Abdullah (a.s) yana cewa: da mutane sun san abin da yake cikin imani da bada'u daga lada da basu kagi magana cikin sa ba.

Ina cewa: sakamakon abin da yake cikin sa daga laziman akida da suluki daga imani da hukuncin Allah da kaddara da sallamawa al'amarin Allah da tawakkali da shi da fawwala lamari gare shi, wadannan mukamai ne na masana Allaha Arifai da masu suluki zuwa ga Allah matsarkaki.

27 ـ عن أبي عبدالله 7 في قوله (ثُمَّ قَضَى أَجَلا وَأَجَلٌ مُّسمًّى عِندَهُ)[26]  قال  :

الأجل الذي غير مسمّى موقوف يقدم ما شاء ويؤخر منه ما شاء، وأمّا الأجل المسمّى فهو الذي ينزل ممّا يريد أن يكون من ليلة القدر إلى مثلها من قابل ، فذلک قول الله: (فَإِذَا جَاء أَجَلُهُمْ لاَ يَسْتَأْخِرُونَ سَاعَةً وَلاَ يَسْتَقْدِمُونَ)[27] .

An karbo daga Abu Abdullah (a.s) cikin fadin sa: (sannan ya hukunta ajali da kuma ajali ambatacce wurin sa) ya ce: ajalin da yake wanda ba ambatacce bba ya tsayu kan Allah yana gabatar da abin da ya so ya jinkirta wanda ya so, amma ambataccen ajali shi ne wanda yake saukar da abin da ya so abin da yake nufa ya kasan ce daga lailatul kadari ya zuwa misalin shekara mai zagayowa, hakan ne fadin Allah (idan ajalin su ya zo bas a jinkirtawa sa'a guda baku sa gabatar sa) 

28 ـ عن حمران عن أبي عبدالله 7 قال : سألته عن قول الله: (ثُمَّ قَضَى أَجَلا وَأَجَلٌ مُّسمًّى عِندَهُ) قال : المسمّى ما سمّي لملک الموت في تلک الليلة وهو الذي قال الله: (فَإِذَا جَاء أَجَلُهُمْ لاَ يَسْتَأْخِرُونَ سَاعَةً وَلاَ يَسْتَقْدِمُونَ) وهو الذي سمّى لملک الموت في ليلة القدر، والآخر له فيه المشيّة ان شإقدّمه وان شاء أخّره

Daga Himrana daga Abu Abdullah (a.s) na tambaye shi dangane da fadin Allah: (sannan ya hukunta ambataccen ajali wurin sa) ya ce: almusamma shi ne wanda aka gayawa Mala'ikan mutuwa a wancan dare shi ne fadin Allah (idan ajalinsu ya zo basa jinkirta masa sa'a guda kuma basa gabata) shi ne wanda aka gayawa Mala'ikan mutuwa a lailatul kadari, dayan kuma cikin akwai mashi'a idan ya so ya gabatar da shi idan ya so ya jinkirta shi.

Ina cewa: hakika bangarorin shi'a da sunna sun ambaci nau'ion ajalin biyu: ratayayyen ajali da ake kira da (ajalul mu'allak) da yankakken ajali (ajalil mahtum) na farkon yana cikin lauhul mahawu wal isbat, shi yana karbar canji shi ne wanda yake canjawa sakamakon ayyukan mutum daga sadaka da sadar da zumunci da `da'a da addu'a da biyayyar iyaye da abin da yayi kama da haka, addu'a tana tunkude bala'I yankakke, sai ya kasan ce tayi tasiri cikin karuwar arziki da shekaru, kamar yanda idan ya zama akasi sai sakamakon ya kasan ce akasi, duk wanda ya yanke zumuncinsa Allah zai rage shekarunsa, haka idna ya aikata zina Allah ya tsaremu- Allah zai karanta arzikin sa, haka dai kamar yanda ya zo cikin jumlar ingantattun hadisai daga bangarori biyu-sunna da shi'a-wannan yana daga abin da ba a inkarin sa, shi ne asalin bada'u na hankali shar'antacce wanda ba a bautawa Allah da wani abu ba misalin sa.

Amma ajali yankakke shi rubutacce ne cikin uwar littafi yana daga ilmul maknun daga tsantsar tabbatattu.

Ya zuwa wannan ma'ana ne ishara ta zo cikin wannan hadisi mai daraja:

29 ـ عن حمران قال : سألت أبا عبدالله 7 عن قول الله: (ثُمَّ قَضَى أَجَلا وَأَجَلٌ مُّسمًّى عِندَهُ)قال : فقال : هما أجلان : أجل موقوف ـ أي معلق كالحكم التعليقي في السجون من قبل القضاة على الجناة ـ يصنع الله ما يشاء، وأجل محتوم .

Daga Himrana ya ce: na tambayi Abu Abdullah (a.s) daga fadin Allah (sannan ya hukunta ajali da kuma ajali ambatacce a wurin sa) ya ce: sai ya ce: ajali ne guda biyu: tsayayye-ma'ana ratayayye kamar ratayayyen hukunci cikin fursuna daga fuskanin alkalai kan masu laifi-yana aikata abin da ya so, da kuma ajali yankakke mahtumi.

Cikin wannan ma'ana akwai wasu riwayoyin cikin babin sai ka koma can.

30 ـ عن حمّاد عن الإمام الصادق  7 في قول الله: (يَدُ اللّهِ مَغْلُولَةٌ)[28]

يعنون قد فرغ ممّا هو كائن لعنوا بما قالوا قال الله عزوجل (بَلْ يَدَاهُ مَبْسُوطَتَانِ)[29] .

Daga Hammad daga Imam Sadik (a.s) cikin fadin sa Allah (hannayen Allah dabaibaye suke da dauri) suna nufin an gama daga abin da yake mai kasantuwa, an tsine musu saboda abin da suka fada, Allah Azza wa Jalla ya ce: (bari dai hannayensa shimfide suke).

Cikin wannan ma'ana ita ma akwai wasu riwayoyin sai ka koma can. 

31 ـ عن زرارة عن أبي جعفر 7 قال : كان علي بن الحسين  8 يقول : لو لا آية في كتاب الله لحدّثتكم بما يكون إلى يوم القيامة ، فقلت : أيّة آية ؟ قال : قول الله:(يَمْحُو اللّهُ مَا يَشَاء وَيُثْبِتُ وَعِندَهُ أُمُّ الْكِتَابِ)[30] .

Daga Zurara daga Abu Jafar (a.s) ya ce: Aliyu bn Husaini (a.s) ya kasan ce yana cewa ba da ban wata aya cikin littafin Allah da na zantar muku da abin da zai kasan ce har zuwa tashin kiyama, sai na ce: wacce ay ace? Sai ya ce: fadin Allah: (Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar kuma wurin sa uwar littafi yake)

Ina cewa: cikin wannan ma'ana akwai wasu riwayoyin cikin babin, kamar yanda sarkin muminai Ali (a.s) ya fada, sai ka koma can.

32 ـ عن الفضل بن بشار عن أبي جعفر 7 قال : إنّ الله لم يدع شيئاً كان أو يكون إلّا كتبه في كتاب فهو موضوع بين يديه ينظر اليه فما شاء منه قدّم ، وما شاء منه أخّر، وما شاء منه محا، وما شاء منه كان ، وما لم يشأ لم يكن .

Daga Fadlu bn Bashar daga Abu Jafar (a.s) ya ce: hakika Allah bai bar wani da ya kasan ce ba ko zai kasan ce face sai da ya rubuta shi cikin littafi sanyayye tsakanin gabansa yana duba shi duk abin da ya so daga cikin sa sai ya gabatar da shi, ya kuma jinkirta wand aya so, ya shafe abin da ya so, abin da ya so ya kasan ce, abin da kuma bai so bai kasancewa.

Ina cewa: ga dukkanin wata duniya daga duniyoyin cikin kauslul nuzuli da su'udi yanada kebantacce yaransa, lallai cikin wannan duniyar tamu dunyar dabi'a karshen duniyoyi cikin kausul nuzuli, na farko kausul su'udi kadai dai yaransa shi ne mada (material) hayuli-da sur, ma'ana yaran jikkuna riskakku da mariskai biyar na zahiri, tana dibar bigire cikin samuwa tare da la'akarin sasannin ta guda uku: tsayi da fadi da zurfi, abar hankalta da mariskan badini biyar, kamar yanda ake suranta haka cikin kwakwalwa daga hissi da akai tarayya cikin sa-karfi na bindanasiya, da hafiza mai hiyali mai tasarrufi da hankalta.

Sai dai kuma yaran duniyar da take gabanin duniyar mu wacce ake kira da duniyar masal, duniyar mu ta kasan ce inuwa gare ta, lallai ita duniyar surori ce, yaranta luggar haske da marasa gangar jiki. Da wannan ne zaka san littafin da aka ambata cikin hadisi, littafi d amuke suranta shi cikin duniyar mu ta zahiri a bayyane, shi yayi kama ne da inuwa ga littafin duniyar hankali da marasa jiki, haka dai har al'amari ya kai ga littafin da yake gaban Allah matarkaki, lallai shi –kamar yanda yake bayyana daga riwayoyi masu daraja-kadai dai shi daga Mala'ika yake shi haske ne cikin haske, Allah yana shiryar da wanda ya zuwa ga hasken sa da abin da ya so, kamar yanda shi lauhu fuskar mulki ce, haka ma alkalamin kudura, kadai shi Mala'ika ne da dukkanin wannan daga duniyoyin haske, su sun fita daga tasawwuran mutane da tunanin su, sai dai cewa Allah daga ludufin sa kan bayin say a sanya masa kwatankwaci da tanka cikin duniyar dabi'a, lallai shi digo ne daga teku, dukkanin abin da yake cikin digo  daga mahiyya da zati da siffofi, lallai haka ma cikin teku mai tuma da igiyar ruwa da habbaka, tsarki ya tabbatar masa daga abin da suke siffantawa, bama yin kage kan ubangijin mu, kadai muna fawwala al'amari gare shi, babu abin da aka baku daga ilimi face cikin cokali, a saman duk wani ma'abocin sani akwai wanda ya fishi sani, kace ubangiji ka kara mini ilimi ka riskar dani da salihai , karshen maganar mu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai

33 ـ عن حمران قال : سألت أبا عبدالله 7(يَمْحُو اللّهُ مَا يَشَاء وَيُثْبِتُ وَعِندَهُ أُمُّ الْكِتَابِ) فقال : يا حمران إنه إذا كان ليلة القدر ونزلت الملائكة الكتبة إلى السماء الدنيا فيكتبون ما يقضي في تلک السنة من أمر فاذا أراد الله أن يقدّم شيئاً أو يؤخره أو ينقص منه أو يزيد، أمر الملک فمحا ما شاء، ثم أثبت الذي أراد. قال : فقلت له عند ذلک ، فكلّ شيء يكون فهو عند الله في كتاب ؟ قال : نعم فقلت : فيكون بيده بعده ؟ قال : سبحان الله ثم يحدث الله أيضاً ما شاء تبارک وتعالى .

Daga Himrana ya ce: na tambayi Abu Abdullah (a.s) (Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar da abin da ya so wurin sa uwar littafi yake) sai ya ce: ya Himrana lallai idan lailatul kadari ya kasan ce Mala'iku suka sassauko da kuma marubuta ya zuwa saman duniya sai rubuta abin da ya hukunta cikin wancan shekara daga al'amarin Allah idan ya nufa sai gabatar da abu ko ya jinkirta shi, ko ya rage daga gare shi ko ya kara, ya umarci Mala'ika ya goge abin da ya so, sannan ya tabbatar da wand aya nufa, ya ce: a wannan lokaci sai na ce masa: duk wani abu da yake kasancewa to yana rubuce cikin littafi a wurin Allah? Ya ce: na'am, sai na ce: sai ya kasan ce hannunsa bayansa? Ya ce: tsarki ya tabbatar masa sannan ya farar abin da ya so tabaraka wa ta'ala.

34 ـ عن الفضيل بن يسار عن أبي عبدالله 7 قال : انّ الله كتب كتاباً فيه ما كان وما هو كائن فوضعه بين يديه ، فما شاء منه قدّم ، وما شاء منه أخّر، وما شاء منه محا، وما شاء منه أثبت ، وما شاء منه كان ، وما لم يشأ منه لم يكن .

Daga Fudailu bn yasar daga baban Abdullah (a.s) ya ce: hakika Allah ya rubuta littafi cikin sa abin da ya kasan ce da wanda zai kasan ce da kasantacce sai ya sanya shi gabansa, abin da ya so sai gabatar da shi, ya jinkirta da wanda ya so, wanda kuma bai so ba zai kasan ce ba.

35 ـ عن الفضيل قال : سمعت أباجعفر 7 يقول : من الأُمور أُمور محتومة جائية لا محالة ، ومن الأُمور أُمور موقوفة عند الله يقدّم منها ما يشاء، ويمحو منها ما يشاء، ويثبت منها ما يشاء، لم يطلع على ذلک أحداً ـ يعني الموقوفة ـ فامّا ما جائت به الرسل فهي طائفة لا يكذّب نفسه ، ولا نبيّه ولا ملائكته[31] .

Na karbo daga Fudailu ya ce: naji Abu Jafar (a.s) yana cewa:  daga al'amura akwai al'amura tabbatattu yankakku da za su babu makawa, daga al'amura akwai wadanda suka tsayu wurin Allah yana gabatar da abin da ya so daga gare su yana kuma goge abin da ya so, yana tabbatar da abin da ya so, bai tsinkayar da wani kan haka ba,   amma abin da manzanni suka zo da shi to wasu jimilla adadi ne da basa karyata kansu.

36 ـ عن أبي حمزة الثمالي قال : قال أبو جعفر وأبو عبدالله 8: يا أبا حمزة إنّ حدّثناک بأمر أنّه يجيء من هاهنا فجاء من هاهنا، فان الله يصنع ما يشاء، وان حدّثناک اليوم بحديث وحدّثناک غداً بخلافه ، فان الله يمحو ما يشاء ويثبت.

An karbo daga Abu Hamza Assimali ya ce: Abu jafar ko Abu Abdullah (a.s) ya ce: ya Abu Hamza idan muka zantar daku da wani al'amari cewa zai zo daga nan sai ya zo daga nan, lallai shi Allah yana aikata abin da ya so, idan yau muka gaya muku wani labari sai gobe muka gaya muku sabanin sa, lallai Allah yana goge abin da ya so ya tabbatar abin da ya so. 

37 ـ عن عمرو بن الحمق قال : دخلت على أميرالؤمنين  7 حين ضرب على قرنه فقال لي : يا عمرو إنّي مفارقكم ثم قال : سنة السبعين فيها بلاء ـ قالها ثلاثاً ـ فقلت : فهل بعد البلاء رخاء؟ فلم يجبني وأُغمي عليه ، فبكت اُمّ كلثوم ، فأفاق فقال : يا اُمّ كلثوم لا تؤذيني فانک لو قدترين ما أرى لم تبک ، إنّ الملائكة في السموات السبع بعضهم خلف بعض ، والنبيون خلفهم ، وهذا محمد 6 آخذ بيدي يقول : إنطلق يا عليّ فما أمامک خير لک ممّا أنت فيه ، فقلت بأبي أنت واُمي ، قلت إلى السبعين بلاء، فهل بعد السبعين رخاء؟ فقال : نعم يا عمرو وإنّ بعد البلاء رخاءً، ويمحو الله ما يشاء ويثبت وعنده اُمّ الكتاب.

An karbo daga Amru bn Hamak ya ce: na shiga wurin sarkin muminai Ali (a.s) lokacin da sare shi akansa sai ya ce mini: ya Amru lallai ni mai bankwana daku ne sannan ya ce: shekaru cikin bala'i- ya fadi haka har sau uku-sai na ce: shin bayan bala'i akwai sauki? Sai bai amsa mini mana sannan ya suma, sai Ummu Kulsum ta fashe da kuka, sannan ya farfado ya ce: ya Ummu Kulsum kada ki takura mini lallai da kina gani abin da nake gani da bakiyi kuka ba, hakika Mala'iku cikin sammai bakwai ba'arin su bayan ba'ari da Annabawa bayan su ga Muhammad (s.a.w) yana rike da hannuna yana cewa taho ya Ali abin da yake gabanka yafi alheri gareka daga abin da kake cikin sa, sai na ce babana da babata fansarka, na ce ya zuwa bala'i saba'in shin akwai sauki saba'in? sai ya ce:  ya Amru lallai bayan bala'I akwai sauki, Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar kuma wurin sa uwar littafi yake.

38 ـ قال : أبو حمزة : فقلت لأبي جعفر 7: إنّ علياً 7 كان يقول : إلى السبعين بلاء وبعد السبعين رخاء، فقد مضت السبعين ولم يروا رخاءاً، فقال لي أبو جعفر 7: يا ثابت إن الله كان قد وقّت هذا الأمر في السبعين ، فلمّا قتل الحسين إشتدّ غضب الله على أهل الأرض ، فأخره إلى أربعين ومأة سنة ، فحدّثنا كم فاذعتم الحديث ، وكشفتم قناع السرّ، فأخره الله ولم يجعل لذلک عندنا وقتاً، ثم قال : يمحو الله ما يشاء ويثبت وعنده أُمّ الكتاب .

Ya ce: ya Abu Hamza: sai na cewa Abu Jafar (a.s) lallai Aliyu (a.s) ya kasan ce yana cewa: ya zuwa bala'i saba'in akwai sauki saba'in, hakika bala'i ya wuce amma bamu ga sauki ba, sai Abu Jafar (a.s) ya ce ya Sabit hakika Allah ya kasan ce ya sanya wannan al'amari lokaci cikin saba'in, yayin da aka kashe Husaini (a.s) sai fushin sa ya tsananta kan mutanen kasa, sai ya jinkirta shi ya zuwa araba'in da dari, sau nawa ne muka zantar sai kuka yada zan cen, kuka yaye rufin sirri, sai Allah ya jinkirtar bai sanya mana lokaci ga hakan ba, sannan ya ce: Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar da abin da ya so kuma wurin sa uwar littafi yake.

39 ـ عن إبن سنان عن أبي عبدالله 7 يقول : إن الله يقدّم ما يشاء ويؤخر ما يشاء، ويمحو ما يشاء ويثبت ما يشاء وعنده اُمّ الكتاب وقال : فكلّ أمر يريده الله فهو في علمه قبل أن يصنعه ، ليس يبدو له إلّا وقد كان في علمه ـ وهذا هو البداء المعقول والمشروع والحق ـ إن الله لا يبدو له من جهل .

Daga Ibn Sinan daga Abu Abdullah (a.s) yana cewa: lallai Allah yana gabatar da abin da ya so ya jinkirta wanda ya so, ya goge abin da ya so ya tabbatar da wanda ya so wurin sa uwar littafi take, ya ce: duk abin da yake so to lallai shi yana cikin ilimin sa gabanin kagar sa, babu abin da yake bayyana gare shi face ya rigaya ya kasan ce cikin iliminsa-wannan shi ne bada'u na hankali da shari'a da gaskiya-hakika Allah babu abin da yake bayyana gare shi daga jahilci.

Ina cewa: wannan shi ne bada'u gurbatacce na bata wanda akewa shi'a kagen sa, ku duba kuga yanda A'immar mu suke inkarin haka, kamar yanda suke bayani filla-filla da cewa abin da ake nufi daga bada'u da abin da yake cikin sa daga gaskiya, ka lura ka san gaskiya ka san ahalinta, kamar yanda ka fara sanin bata zaka san ahalinsa, shin bayan gaskiya akwai wani abu ba bata ba, ka karanta wannan hadisi tare da ni ka duda yanda A'imma Ma'asumai suka bayyana fuskar gaskiya cikin bada'u na ibada wanda yake bubbugowa daga imani da kudurar Allah mudlaka, kamar yanda yake zantar da girman mutum a halinsa, lallai shi ubangiji mai iko ne kan komai, yana aikata bainda ya so yanda ya so, lallai yana da lauhul mahawu wal isbat, ya sanyawa mutum dauri bayyananne cikin kaddara makomar sa, da cewa shi ubangiji yana gogewa yana kuma tabbatarwa daga abin da yake cikin allo daga ayyukan mutum nagari ko marasa kyawu, lallai shi mutum idan cewa an kaddara masa mutuwa da ajali ratayayye, haka zalika an kaddara masa wata kaddarar da cewa idan yayi addu'a ya roki ubangijin sa to zai goge abin da aka rubuta kansa daga ratayayyen hukunci, misalinsa misalin jirgin kasa kan titinsa da tsallakawa daga tasha kaza zuwa wancan tashar inda ya nufa, lallai sh mutum yana tsallake jirgin rayuwar sa daga tashar ratayayyen ajali cikin aminci hart ya kai ya tuke ya karkare ya zuwa tabbataccen ajali na karshe, kamar yanda bayanin haka ya gabata.

40 ـ عن أبي عبدالله 7 سئل عن قول الله: (يَمْحُو اللّهُ مَا يَشَاء وَيُثْبِتُ وَعِندَهُ أُمُّ الْكِتَابِ)[32] قال : إن ذلک الكتاب كتاب يمحو الله ما يشاء ويثبت ، فمن ذلک الذي يردّ الدعاء القضاء، وذلک الدعاء مكتوب عليه : الذي يردّ به القضاء، حتى إذا صار إلى أم الكتاب لم يغن الدعاء فيه شيئاً.

Daga Abu Abdullah (a.s) an tambaye shi dangane da fadin Allah (Allaha yana shafe abin da ya so ya tabbatar kuma wurin sa uwar littafi yake) ya ce: wancan littafin ne littafin yana shafe abin da ya so ya tabbatar, daga nan ne addu'a take canja kaddara, wancan addu' an rubuta kansa: yana canja kaddara, har idan ya kasan ce ya kai ga uwar littafi babu wata addu'a da zata canja komai cikin sa.

Ina cewa: shi ne abin da fadin Allah ya shiryarwa zuwa gare shi: (idan ajalin su ya zo basa gabatar sa sa'a guda ba kuma sa jinkirtawa) addu'a bata amfanar da komai idan ajalin ya gangara ga matakin mahtumi yankakke, idan kuma cikin lauhul mahawu wal isbat ne to zai iya canjawa addu'a tayi tasirinta da dage mutuwar, amma idan ya kai ga lauhul mahfuz to fa komai yak are magana ta kare babu wani abu daga ayyuka da zai tasiri.

41 ـ عن جعفر بن محمد 8 عن أبيه  7 قال : قال رسول الله 6: إن المرء ليصل رحمه وما بقي من عمره الّا ثلاث سنين ، فيمدّها الله إلى ثلاث وثلاثين سنة ، وان المرء ليقطع رحمه وقد بقي من عمره ثلاث وثلاثون سنة ، فيقصّرها الله إلى ثلاث سنين أو أدنى .

قال الحسين : وكان جعفر يتلو هذه الآية : ) (يَمْحُو اللّهُ مَا يَشَاء وَيُثْبِتُ وَعِندَهُ أُمُّ الْكِتَابِ.

An karbo daga Jafar bn Muhammad (a.s) daga babannin sa (a.s) ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya ce: hakika mutum yana sadar zumuncin sa a daidai lokacin da babu abin da ya rage masa sai shekaru uku, sai Allah ya mikar da su zuwa shekaru talatin da uku, sannan mutum yana yanke zumuncin sa a daidai lokacin yake da ragowar shekaru talatin da uku a rayuwa da zai yi su, sai Allah ya rage su zuwa shekaru uku koma kasa da haka.

Sai Husaini ya ce: Jafar ya kasan ce yana karanta wannan aya: (Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar da wanda ya so kuma wurin sa uwar littafi yake)

42 ـ وفي قصة اليهودي والنبي الأكرم  6 ـ كما سيأتي ـ وانه قال اليهودي السام عليک ، فأجابه النبي وعليک من دون ان يردّ سلامه ، إذ لم يسلّم بل قال (السّام عليک) والسام هو الموت ، وأخبر النبي إنّه حية سوداء تقتله بعضة في قفاه ، إلّا انه بعد الاحتطاب ، لم يمت اليهودي فأمره النبي أن يضع الحطب ، فرأى حية أسوداً في جوف الحطب عاضّ على عود، فسأل النبي اليهودي ماذا فعل حتى دفع عنه البلاء والموت ؟ فقال كان لي كعكتان أكلت واحدة وتصدّقت بالأُخرى على مسكين .

فقال رسول الله 6: بها دفع الله عنه ، وقال : إنّ الصدقة تدفع ميتة السوء عن الانسان .

Ya zo cikin kissar bayahude da Annabi mafi karamci (s.a.w) kamar yanda zai zo- cewa wannan bayahude ya ce Samu Alaika: sai Annabi ya amsa da wa'alaika ba tare da ya cika masa sallama ba, domin wannan ba yahude bai yi sallama cewa yayi (samu Alaika) wanda yana nufin mutuwa, sai Annabi ya ce bakin kumurci ne zai kashe ta hanyar saran keyar sa, sai dai cewa bayan tattara kirare wannan bayahude bai mutum sai Annabi ya bashi umarni da ya sauke wannan ita ce yana saukewa sai ya ga bakin kumurci cikin kiraren ta ciji kan wani ita ce, sai manzon Allah (s.a.w) ya tambaye shi me ya aikata da har aka tunkude masa wannan bala'i ?sai ya ce inada cincin guda biyu sai naci daya nayi sadaka da guda daya na baiwa wani mabukaci.

Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: da wannan sadakar da ya yi ne Allah ya tunkude masa wannan bala'in, ya ce: hakika sadaka tana tunkude wa mutum mummunar mutuwa.

Ina cewa: cikin wannan hadisi mai daraja akwai ma'anoni, daga ciki: abin da ya ta'allaka da maudu'in da muke ciki daga bada'u, daga lauhul mahawu wal isbat, lallai mutum yana da ikon da karama wurin Allah da zai iya canja abin da aka rubuta mai kyau ne ko mara kyau, hakika Allah baya canja halin mutane har sai sun tashi da kansu sun canja, ka lura.

Daga ciki: lallai wannan al'amari ba ta'allaka da iya musulmi ba da muminai ba bari dai yana gudana hatta kan kafirai da Yahudawa da Nasara, kai kace yana kallon janibin mutumtaka ne, ko bautantaka da ubangijintaka, Allah ne masanin hakikanin al'amura.

43 ـ وأخيراً وليس بآخر: عن سليمان الطلحي قال : قلت لأبي جعفر 7 : أخبرني عمّا أخبرک به الرسل عن ربّها، وأنهت ذلک إلى قومها أيكون لله البداء فيه ؟ أمّا إنّي لا أقول لک : إنّه يفعل ، ولكن إن شاء فعل .

Daga karshe wanda ba ita ce maganar karshe ba: an karbo daga Sulaimani Addalahi ya ce: na cewa Abu Jafar (a.s) bani labarin dangane da abin da manzanni suka baka labari daga ubangijin su, suka hana haka ga al'ummar su shin bada yana kasancewa ga Allah? Ni bazan ce gaya maka, hakika shi yana yi idan ya so yayi.

Ina cewa: wannan sune jumlar daga abin da aka rawaito daga hadisai masu daraja da aka rawaito su daga A'immatu Ahlil-bai (a.s) lallai su t fuskanin isnadi akwai ingantattu da wadanda ake la'akari da su kamar yanda akwai muwassak da da'ifi, sai dai cewa ta fuskar jimillar su suna kasancewa mutawatirai a ma'anan ce ko ijmali sai ya zamanto sun fa'idantar da yakini da ilimi, amma ta fuskar abin da suke shiryarwa zuwa gare shi lallai suna shiryarwa zuwa ga hakikanin bada'u daga makarantar Ahlil-baiti (a.s) lallai su ma'abota kebantaccen isdilahi ne, duk wanda ya ketare shi ya tsallake zai fada cikin fagarniya da jahilci, sannan ya kagi karya kan mabiyan su da shi'ar su, ya tuhume su da karkacewa da bata.

Domin Karin fa'ida zamu yi ishara zuwa ga wasu jimillar daban da suke shiryawa kan bada'u na hankali karkashin afkuwar masadik da aka rawaito cikin rayuwar Annabi (s.a.w) mafi karfin dalili kan yiwuwar abu shi ne afkuwar sa, Allah ne abin neman taimako kuma shi ne mai shiryarwa zuwa tafarkin shiriya.