Masadik din bada’u cikin kissoshin Annabawa

 

44 ـ البحار بسنده عن أبي حمزة الثمالي عن أبي جعفر الإمام الباقر 7 قال : بينا داود على نبينا وآله وعليه السلام جالس وعنده شاب رثّ الهيئة يكثر الجلوس عنده ويطيل الصمت ، إذ أتاه ملک الموت فسلّم عليه ، وأحدّ ملک الموت النظر إلى الشاب ـ أي بالغ في النظر اليه ـ فقال داود على نبينا وآله وعليه السلام  : نظرت إلى هذا؟ فقال : نعم اني اُمرت بقبض روحه إلى سبعة أيّام في هذا الموضع ، فرحّمه داود فقال : يا شاب هل لک إمرأة ؟ قال : لا وما تزوّجت قطّ ، قال داود: فآت فلاناً ـ رجلاً كان عظيم القدر في بني اسرائيل ـ فقل له : إنّ داود يأمرک أن تزوجني إبنتک وتدخلها الليلة وخذ من النفقة ما تحتاج اليه ، وكن عندها، فاذا مضت سبعة أيّام فوافني في هذا الموضع ، فمضى الشاب برسالة داود على نبينا وآله وعليه السلام ، فزوّجه الرجل إبنته وأدخلوها عليه وأقام عندها سبعة أيام ، ثم وافى داود يوم الثامن ، فقال له داود: يا شاب كيف رأيت ما كنت فيه ؟ ما كنت في نعمة ولا سرور قطّ أعظم ممّا كنت فيه ، قال داود: اجلس فجلس وداود ينتظر أن يقبض روحه ، فلمّا طال قال : إنصرف إلى منزلک فكن مع أهلک ، فاذا كان يوم الثامن فوافني ههنا، فمضى الشاب ، ثم وافاه يوم الثامن وجلس عنده ، ثم انصرف أُسبوعاً آخر، ثم أتاه وجلس ، فجاء ملک الموت داود، فقال داود صلوات الله عليه : ألست حدّثتني بأنک اُمرت بقبض روح هذا الشاب إلى سبعة أيام ؟ قال : بلى ، فقال : قد مضت ثمانية وثمانية وثمانية ! قال : يا داود إن الله تعالى رحمه برحمتک له ، فأخّر في أجله ثلاثين سنة[1] .

 

Biharul-Anwar da isnadin sa daga Abu Hamza Assimali daga Abu Jafar Imam Bakir (as) ya ce: lokacin da Dauda amincin Allah ya tabbata ga Annabin mu da iyalan sa da shi yake zaune tare da akwai matashi da ke cikin shigar halin ban tausayi yana yawaita zama wajensa yana tsawaita shiru, sai kwatasam ga Mala’ikan mutuwa ya zo wajen sa sai yayi masa sallama, wannan Mala’ika ya kwafa idonsa kan wannan matashi yana ta kallon sa, sai Dauda (as) ya ce: kana kallon wannan ne? sai ya ce: na’am hakika an umarce ni da in dauki ransa nan da kwanaki bakwai a wannan wuri, sai Dauda yaji tausayin sa ya ce: ya kai matashi shin kana da mata? Sai ya ce: a’a ban taba aure ba, sai Dauda ya ce: kaje wajen wane babban mutum ne cikin Banu Isra’ila- kacce masa lallai Dauda yana uamrtarka ka aura mini diyarka akai ta dakina wannan daren sannan ka karbi kudin da kake wurin Dauda, ka kasan ce wurin amaryarka bayan kwana bakwai ka zo wurina, sannan ya je wurin Dauda rana ta takwas, sai Dauda ya ce masa: ya kai matashi yaya ka ga abin da ka kasan ce cikin sa? Ya ce ban taba kasancewa cikin wata ni’ima da farin ciki mafi girma daga abin da na kasan ce cikin sa ba, sai Dauda ya ce: zauna sai ya zuana yana jiran a dauki ransa, yayi lokaci ya nutsa sai ya ce: tashi ka tafi gida ka kasan ce tare da iyalinka, idan rana ta takwas ta kasan ce ka zo wurina nan, sai ya tafi, sannan ya zo ranar da takwas ya zauna wurin sa, sannan sati guda yak are, sannan ya kara zuwa ya zauna, sai Mala’ikan mutuwa ya zo wajen Dauda, sai Dauda (as) ya ce: ashe bakai ne kace mini an umarceka da daukar ran wannan matashin ba bayan kwana bakwai? Ya ce: eh, sai ya ce: kwanaki takwas sun shude wasu takwas kari sun kara wucewa hakama wasu takwas din! Sai ya ce: ya Dauda hakika Allah ta’ala yaji kansa da tausaya masa da kayi sai ya jinkirta ajalinsa zuwa shekaru talatin.  

45 ـ عن أبي عبدالله 7 قال : كان في بني اسرائيل نبي ، وعده الله أن ينصره إلى خمسة عشر ليلة ، فأخبر بذلک قومه فقالوا: والله إذا كان ليفعلن وليفعلن ، فأخّره الله الى خمسة عشر سنة ، وكان فيهم من عوده الله النصرة إلى خمس عشرة سنة ، فأخبر بذلک النبي قومه ، فقالوا: ما شاء الله، فعجّله الله لهم في خمس عشرة ليلة .

Na karbo daga Abu Abdullah (as) ya ce: wani Annabi ya kasan ce cikin Banu Isra’ila da Allah yayi masa alkawari da cewa zaio taimake shi ya zuwa darare goma sha biyar, sai gayawa mutanen sa sai suka ce: wallahi idan ya kasan ce zai aikata to ya aikata mu gani, sai Allah ya jinkirta masa ya zuwa shekara goma sha biyar, cikinsu akwai wanda ya kasan ce Allah ya sabar masa da taimako ya zuwa shekaru goma sha biyar, sai mutanen suka baiwa Annabin labarin hakan, sai Allah ya gaggauta musu cikin dare goma sha biyar.

Iana cewa: a gaba ta farko mutane sun kama yin tunanin kan kawukansu me zasu aikata ga duniyar su bayan wannan nasara ta kusa-kusa a zata zo bayan `yan kwanaki kadan, daidai lokacin da a gaba ta biyu sun fawwala al’amarin su ga Allah matsarkaki da irdar sa da mashi’ar sa, sai ya gaggauta musu taimakon sa kamar yanda ya zo cikin fadinsa madaukaki: 

 (الَّذينَ قالَ لَهُمُ النّاسُ إِنَّ النّاسَ قَدْ جَمَعُوا لَكُمْ فَاخْشَوْهُمْ فَزادَهُمْ إيماناً وَقالُوا حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكيلُ * فَانْقَلَبُوا بِنِعْمَةٍ مِنَ اللهِ وَفَضْلٍ لَمْ يَمْسَسْهُمْ سُوءٌ وَاتَّبَعُوا رِضْوانَ اللهِ وَاللهُ ذُو َفضْلٍ عَظيمٍ )[2] .

 Wadanda mutane suka ce musu lallai mutane sun tara rundunoni saboda ku ji tsoran su sai hakan ya kara musu Imani suka Allah ya isar mana kuma madalla da wakili shi, sai suka juya da ni’ima daga Allah da falala wani mummunan abu bai same sub a suka yardarm Allah Allah shi ne ma’abocin falala mai girma.

Natijar fadinsu (Allah mai isar mana ne madalla da wakili shi) cikin gaggawa Allah ya taimake su suka juya cikin ni’ima daga gare shi. Wani abu mara dadi bai shafe sub a, akwai misalin wannan al’amari cikin sahabban A’imma (as) lallai su sun basu labarin samun faraji da daular mutanen Allah salihai, sai diac ewa kuma sai suka je suka yada, sai hakan ya jawo jinkiri ya zuwa ga abin da yake cikin ilimin Allah matsarkaki, gaiba kubra ta kasan ce cikin lokaci mai nisa har ya kai ga mutane su kasan ce cikin tankade da rairaya da shiga cikin jarrabowowi kala-kala, babu wanda suka kan Imani daga gare su sai yan kadan, Allah ya tsaremu tare da ku ya tabbatar damu daku kan wilayar Ahlil-baiti duniyarmu da lahira, Amin rabbal Alamin.

46 ـ عن أبي بصير قال : قلت له : ألهذا الأمر أمر تريح اليه أبداننا وننتهي اليه ؟ قال : بلى ولكنّكم أذعتم فزاد الله فيه .

Daga Abu Basir yace: na ce masa: shin wannan al’amari yana da lokaci da jikkunan mu zasu huta mu huta da shi? Yace: eh sai dai cewa ku kun yada shi sai Allah ya kara lokacin yayewar sa.

Wannan shine abinda magabata nagargaru suka jarrabtu da shi daga yada sirrikan Ahlil-baiti Muhammad (as) da wannan ma’anar akwai wasu hadisan