MUKAMI NA BIYU

 

Menene hakikanin fushi? Daga wanne abbubuwa yake kasantuwa, menene sinadaransa cikin samuwar cikin kwakwalwa da daga jinsi da fasali, ko kuma cikin samuwar ta zahiri da ake gani a waje daga mada da sura, wadanne abubuwa ne jijiyoyi na farko da dalilai na ciki dana waje da fushi ke kasantuwa daga garesu, sai ya tabbatu ciki fusatacce daga mace ko namiji?

Ka sani Allah ya karfafeka cikin duniya da lahira lallai Allah ya halicci dabba daga cikin akwai mutum, sannan lalacewa da mutuwa na bijiro masa da rashi dangananne, hakan na faruwa sakamakon dalilai da sabubba masu yawa, wani lokacin na cikin gida wani karon kuma daga waje, daga cikin ludufin ubangiji ya yiwa mutum kyauta daga abin da ya ni’ima kansa daga abin da zai bashi kariya daga lalacewa, da tunkude masa halaka ya zuwa lokacin da rubutaccen ajalinsa zai riskeshi, a wannan lokaci bai iya gabatarsa kankanin lokaci haka bai iya jinkirta masa, tambayar mu anan wadannan abubuwa ne wadannan sabubba da dalilai a waje da na cikin gida?

Amma dangane da sabubban cikin gida, lallai ubangiji ya halicci daga danshi da dumama, yayin da ya kasance kasantacce daga sinadaran farko gud ahudu: kasa, ruwa, wuta, iska, daga cikin abin da ya cudanya da su danshi da yake karkashin ruwa da kasa, sai kuma dumama da take kasan wuta da iska.

Sannan ya sanyab kishiyanta tsakanin danshi da dumama, kamar yanda hakan ke gudana kan dukkanin koma bayan Allah matsarkaki shi kadai ne bai da kishiya, amma ita duniya to lallai ita gida ce na kishiya da tanakudi da gogayya, duk sanda fari ya kasance to zaka samu baki yana kishiyantarsa, idna haske ya kasance zaka samu duhu, idan samuwa ta kasance to zaka gamu da rashintuwa.

Sannan abubuwa da suka lazimci dumama da suke warware danshi su busar da su su siracentar da su har sai yankunanta ya barbazu ya watsu ya zuwa hayaki da zai dinga hauhawa daga gareta, sannan mada ta canja zuwa energy da dumama. Wajibi ne asamu madadi ya kai ga danshi hakan ya tabbatu karkashin cimakar da take maye gurbi da dora abin da ya warware da kuma yi sirace da hayakantar da yankunanta, ba da ban hakan ba da dukkanin dabbobi sun lalace da mutum yam utu, saboda haka cimaka a abinci da kayayyakin sha suna dora abin da ya tawaya daga danshi wanda dumamar yanayi ya gurbata ya lalata shi ya canja shi zuwa hayaki da energy.

Allah ya halittarwa gangar jiki dabbobi nda mutane daga abin da ya ke dacewaq qda shi daga abinci da kayayyakin sham daga cimaka ta mada da zahiri, sannan ya halicci sha'awa cikin dabbobi saki babu kaidi da take biye da shi kan cin cimaka, tana kasancewa cikin hukuncin da aka fawwala shi gare shi domin gyara da dora abin da ya karya da toshe Baraka d ahuda da aka samu cikin sa, domin  hakan ya kasance mai kiyayewa da bada kariya daga hallaka da wannan sababi, sai mutum ya zama ya adontu da karfin sha'awa , domin jawo amfani don wanzar da nau'insa da tsatson `dan Adam a doran kasa da bashi kariya da hallaka ta cikin gida.

Amma sababin waje ga hallakar `dan Adam da dabbobi, lallai shi yana kasancewa da misalin takobi da makami da damka da sauran abubuwa masu hallakarwa da kisa na waje, kamar misalin kai hari ga wasu mutane, ya zama dole ne a samu wani karfi da kishi da zata motsa ta baiwa mutum kariya daga cikin badininsa domin ya tunkude abubuwan da zasu cutar da shi da hallaka shi, sai Allah ya halittar masa karfin fushi wanda ya kasance daga wuita, ya shuka shi cikin sa _ma'ana fushi ya zamanto daga cikin halitta da dabi'ar da take tattare cikin mutum, sai mutum ya wayi gari mai yin fushi, duk yanda yakai ga nufar wata manufa daga cikin manufofinsa sai wutar fushi ta ruru cikin sa al'amarin da yake kaiwa ga zabalbalar fushi cikin jinin zuciya da bazuwa cikin jijiyoyi, ya daga ya kai ga kololuwar jiki, kamar yanda wuta ke dagawa, kamar misalin ruwa da yake tafasa da zabalbala cikin tukunya, sannan ya fesu cikin fuska sai ka ga fuska da idonsa da fatarsa duk sun yi jajawur, domin su bada labarin abin da yake boye daga jajantuwar jini, kamar yanda kwalaba take hakaito launin abin da aka zuba cikinta.

Wannan duka fa yana kasancewa idan mutum ya fusata kan wanda yake kasa da shi, amma idan ya fusata kan wanda yake sama da shi kuma ya dbe tsammani daga samun damar daukar fansa da huce haushi da yake lazimtar fusata, to a wannan lokaci zaka same shi jini ya damke yak hana fushin bazuwa daga zahirin fata ya zuwa cikin zuciya, sai fushi ya koma iya bakin ciki, daga nan kuma sai launin ya koma ruwan dorawa, kamar yanda yake cikin zuciyar wanda yake cikin bakin ciki, sai ya zama ya kai komo tsakanin damka da mikewa cikin jini, sai fuska ta dinga kao koma ta dinga yin jajawur tana kuma komawa ruwan dorawa, raurawa da damuwa ta mamaye shi.

Shi fushi wani yanayi ne na mutum da yake haifar da vmostin ruhi da karfin fushi daga cikin gida zuwa waje domin galaba da tunkude cutuwa, mafararsa daga karfin sha'awar daukar fansa, ana kiransa kan bangaren wuce gona da iri cikin fsuhi, idan ya tsananta yana haifar da mummunan mosti da fita daga cikin hayyaci da daidaito, sakamakon hakan jijiyoyi da kwakwalwar mutum na cika da hayaki bakir kirin saai ya zamanto ya lullube hasken hankali ya kuma raunana motsin hasken, har takai ga mutum ya rasa daidaituwarsa da hayyacinsa da nutsuwarsa, saiu ka ga nasiha da wa'azi basa wani tasiri kan wanda ya shiga irin wannan hali, bari dai sai ya zama ma sun kara masa dagawa da jiji da kai, wa'azin ya zama ya kara masa tsanani da fusata (shi fushi bakin wuta ne da aka tsono shi daga wutar Allah rurarriya wacce take tsinkaya kan zukata, lallai ita tana tausasa cikin kasar fa'idoji kamar misalin tausasar garwashi cikin toka).

A wannan lokaci sai ya zama ko dai kishin addini da bashi kariya ya fito da wutar fushi sai ya kasance daga fushi domin Allah matsarkaki kamar yanda bayanin kan hakan zai zo a nan gaba, lallai misalin wannan fushi yana kasancewa fushi na haske, kadai dai ana kiransa da fushi majazan (jeka na yika).

Ko kuma dai ta'asubbancin jahiliya da son kai da fifita kai na shaidanci ya fito da wannan wuta mai zababbaka ya bayyanar da shi daga buya daga zukatan Jabberai, kai hatta misalin cikin tsakanin mata da miji, ta hade da jijiyoyi n shaidan tsinanne a inda yake cewa:

{خلقتني من نار وخلقته من طين}([1]).

Ka halicceni daga wuta shi kuma ka halicce shi daga tabo.[1]

 

Yayinda sinkiya ta kasance sababin shigewa cikin juna da hadewa, lallai Shaidan yana hallara cikin dukkanin fusatacce hallara mai tasiri ya shigar da shi cikin batar da shi da hallararsa sai mutum ya kasance Shaidani cikin zantukansa da ayyukansa, da abin da yake gangarowa daga gare shi daga kufaifayin fush, kamar yake yana daga sha'anin tabo tausasa da lausasa to haka ya kasance daga sha'anin wuta ta kasance mai zababbaka da ruruwa.

Sannan shi karfin fushi tana fuskantowa ne yayin tashinsa da dagowarsa ya zuwa tunkude abubuwa masu cutarwa idna ya kasance gabanin faruwarsu, ko kuma ya zuwa ga huce haushi da daukar fansa idna ya kasance bayan faruwarsu, wannan shi ne abin da ake kira da Gadabul nari(fushi na wuta) wanda ake amfani da shi kan kalmar fushi a hakika, kamar yand aka yi isdilahinsa cikin isdilahin Aklak da Ilmul Aklak.

        Shi fushi zuciya masaukarsa, ma'anarsa shi ne zababbakar jini domin neman daukar fansa da tukunde cutuwa da ababuwa masu takurawa gabanin faruwarsu, ko kuma ya zuwa huce haushi da kuma daukar fansa bayan afkuwar su, sannan shi daukar fansa da huce haushi sun kasance sakamakon wannan karfin na sha'awa, sannan cikin jin dadin yake bai samu tausasuw asai da shi.

[1] A'araf:12.