KASHE-KASHEN MUTANE CIKIN FUSHI

 

Mun rigaya mun sani cewa mutum yana da karfi guda biyu: krafin sha'awa domin neman amfani da karfin fushi don tunkude cuta, hakan ya kasance bisa halitta dabbantaka da halittarsa ta mutum.

Sannan mutane cikin wannan karfi na fushi sun kasu zuwa matakai uku: wuce gona da iri da takaitawa da daidaito, wanda shi ne mataki na tsakatsaki, shi tsakaituwa falala ce gefayan biyu wato takaitawa da wuce gona da iri suna daga dabi'u marasa kyawu kamar yanda aka yi bayanin haka cikin ilimin Aklal da manyan litattafan Aklak na nazariya, kamar misalin Jami'ul Sa'adat da Almahajjatul Baida'u da sauran su, sai a koma can.

Amma bangaren takaitawa shi yana kasancewa ne ga wanda ya rasa karfin fushi ko kuma fushin ya raunana a wurinsa, ana kiran wannan mutumi da rago, ma'abocin ragwanta, baya yin fushi cikin abin da ya kamata ace yayi fushi kansa a shari'an ce da hankalce, lallai shi abin zargi ne, lallai shi yana daga wanda bai da kishi ya kasance rago da hankali da ma'abotansa suka yi Allah wadarai da shi, kamar yanda ubangiji matsarkaki ya zarge shi, lallai dukkanin wanda aka fusata shi sai ya zamanto bai fusata ba to shi jaki ne, kamar yanda wasu ke kiransa da mai tawayar mutumtaka da kamala, daga cikin kufaifayin hakan shi ne rashin kishin alfarmarsa, da wulakanta kansa da jurewa zalunci da danniya, da daukar kaskanci da kaskantuwa, da yin sassauci cikin al'amarin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna da alfasha da makamancin haka daga gurbatattun abubuwa, hakika Allah ya siffanta muminai da tsanantawa da kishi sai y ace:

{ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ }([1])،

Su masu tsanantawa ne kan kafirai.[1]

 

Azza wa Jalla ya ce:

 { (يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ جَاهِدِ الْكُفَّارَ وَالْمُنَافِقِينَ وَاغْلُظْ عَلَيْهِمْ }([2]).

Yakai Annabi ka yaki kafirai da munafukai ka kausasa kansu.[2]

 

Amma bangaren wuce gona da iri shi ne cewa wannan karfi na fushi ya zamanto yayi galaba kan mutum ta yanda zai rasa hankalinsa, ya kuma fitar da shi daga nutsuwarsa da addininsa da biyayyarsu, har ta kai ya rasa basirarsa da tunaninsa da zabinsa, sai ya kasance kamar misalin dabbobimasu kai bara mashaya jini, ba tare da rahama ba kuma tare da dukkanin kekasar zuciya da jafa'i, fushi a isdilahan ce yana iyakantuwa cikin wannan ma'ana, wannan shi ne abin da zamu bahasi kansa cikin wannan dan karamin littafi namu na gaggawa, daga wurin Allah mu ke neman dacewa da damdagatar


[1] Fatahu:29

[2] Attauba:73