MUKAMI NA UKU: SABUBBAN FUSHI A WURIN MUTUM


Hakika sabubban suna da matukar yawa, sai dai kuma dukkanin suna karkarewa ya zuwa karkasuwa na biyuntuwa, ko dai su kasance al'amuran na halitta ko kuma lamurran yau da gobe.

Na farko yana daga cikin dabi'ar mutum ko kuma kamar yanda ake cewa cikin ilimin gado yana daga cikin kwayar halitta wacce take siffantuwa da fushi sai ya zamanto ya gaji babansa cikin fushinsa alal misali, kamar kuma yanda ya zo daga hadisai, hakika Kabila ya auri aljana shi kuma Habila ya Auri matar aljanna an halicceta daga asalin haske, duk wanda dabi'arsa ta kyawuntar zai siffantu da nutsuwa da tausasa da hakuri da danne fushi to ya kasance ne daga `ya`yan matar aljanna, duk wanda fushi da tsanani da kekasa da raurawa da damuwa suka kasance cikin sa, to shi ya kasance daga `ya`yan aljanar mata, kamar yanda ya kasance akwai riwayoyi gameda tabo d yunbu, lallai daga gareta akwai daga tabon wuta, haka ma akwai daga tabon aljanna da ni'ima, wannan duka yana komawa zuwa ga hukunci da kaddarar Allah, kamar yanda akai bayanin hakan a mahallinsa.

Sai dai cewa kuma wadannan riwayoyi ko da isnadinsu ya inganta, lallai su suna shiryarwa ne kan wadannan sabubba da dalilai na cikin gida, kadai su sun zo da fuskar tauyayyar illa da sababi da hukuntau, lallai ita tare da samuwar hanau ba ta iya wani tasiri, mutum zai iya samar da hanau da zai ti shamaki ya hana tasiri, kamar yanda yake cikin tabon tsiyata bko kuma `dan aljana, ko kuma ya kasance azurtacce dan matar aljanna, bari dai zama a iya tafiya kan fifituwa mafi falala, lallai mafi falalar ayyuka mafi wahalarsu.

Amma na biyu shi ne wanda ya kasance daga al’amuran da aka saba da su, shi yana kasancewa da la'akari da waje, kamar misalin zamantakewa da juna tare da wanda yake da dabi’ar saurin yin fushi, ko kuma wanda yake alfahari da daukar fansa da huce haushi, yake kuma la’akari da shi daga gwarzantaka da karfi da daukaka da karamci da mutumtaka da jarumtaka, sai ka same shi alal misali yana cewa: ni ne wanda bana hakuri bana jurewa wani abu daga wani mutum, duk wanda ya fada kalma daya zai amsa masa da guda goma, da dai makamantan haka daga abubuwan da suke shiryarwa kan rashin saisaituwar hankalinsa da hakurinsa, sannan abin ban mamaki daga gare shi shi ne ya na ambaton hakan a cikin mukamin alfahari da daukaka, duk wanda ya ji shi kyawuntar fushi yana zurfafa cikin zuciyarsa da son siffanta kansa da mutane, duk wanda zauna da mutane tsahon kwanaki arba’in zai zama misalinsu daga kuma garesu, zaka same su yana dabi’antuwa da irin dabi’arsu da halayensu da al’adunsu, sai ka samu fushi yana karfafa cikin sa da al’ada da abin da ya saba da shi.

Sannan duk sa’ilin da wutar fushi ta tsananta ta ruru sai kaga ta makantar da ma’abocinta ta kuma kurmantar da shi daga dukkanin wa’azi, ba zai dinga jin wa’azi ba bari dai wa’azin ma zai dinga kara masa fushi, yana kasuwa kadai yayin kunnuwar fitilar hankali, bakin hayaki yana hauhawa yayin tsanantuwar fushi ya zuwa kwakwalwa ya mamaye ma’adanan tunani, idna fushi ya kara karuwa da tunbatsa sai ya kai gay a mamaye hatta ma’adanan mariskai, sai idonsa yayi duhu ya zama baya gani baya ji, sai ka same a cikin rashin fadakuwa yana aikata abin da bai da kyakkyawan karshe, tama iya yiwu ya aikata laifi da ta’addanci, har al’amari ya kai ga ya mutu take sakamakon bugun zuciya ka bugun kwakwalwa, sai ya kasance cikin misalin hukuncin jirgin ruwa a tsakiyar teku  da yake hakin tomo da tumbatsa yayin tasowar iska da girgizarta, idna ya kasance ana fatan tsiran jirgi ta hanyar matukinsa da wadanda suke cikinta daga ma’abota hankali, sai dai cewa fusatacce jirgi ana debe fata daga gare shi, sakamakon kasantuwar matukin shi ne zuciya ita kuma babu wata dabara da ta rage mata yayin da fushi ya makantar da ita ya kurmantar da ita, shi baya ganin hakika baya sauraren gaskiya, shi ya kasance kamar dabba bari dai yafi dabba batan hanya_Allah ka tsare mu. Sabubban bisa kasa shi gida biyu ko dai su kasance daga wadanda aka al’adantu da su ko kuma na halitta, sabubban da malam Aklak suna ambata suna komawa garesu, sune: jiji da kai, alfahari, girman kai, yaudara, taurin kai, jayayya, barkwanci, izgilanci, aibatawa, husuma, tsananin kwadayi kan neman mukami da dukiya mai karewa, dukkaninsu miyagun halaye ne masu halakarwa, ba a iya kubuta daga fushi tare da wanzuwarsu, da farko dole ne a fara kawar da su domin kawar da fushin ya saukaka.[1]


[1] Jami’us Sa’adat: juz 1 sh 326