MUKAMI NA HUDU: ALAMOMIN FUSHI

 


shi fushi yana daga kulli tashkiki da yake da martabobi na sasannin ufuki da amudi daban-daban cikin tsanani da rauni, sai dai cewa kowacce martaba tana da tasirinta da alamiminta, daga cikin tasirinta cikin maratabar farko: shi ne sassauyawar launi, da tsananin tsawa cikin geffa, da fitar ayyuka daga tsaruwa da system, da raurawar motsi da Magana.

Sannan daya martabar: madarar na bayyana kan lebba idanu su yi jajawur fuskar mutum ta canja yayi muni, da fusatacce zai kalli fuskarsa a madubi da zai ji kunyar kansa, da fushinsa ya tausasa sabida tsananin jinin kunya da kunyata, sai dia cewa yana ganin kasan cikin waccan hali da yanayi bai son cewa ya munin badininsa yafi munin zahirinsa ba, kadai fuskarsa ta badini ta fara sai munin ya bayyana a zahrinsa, zahirinsa ya sauya sakamakon sauyawar badininsa, wannan shi ne kufaifayin da yake bayyana a jikin fusatacce.

Sannan karfin fushi yayi ta karuwa sai kufansa ya bayyana kan harshe, sai ka ga fusataccen naka ya fara zagi da furta munanan kalamai wadanda duk wani ma’boci hankali zai ji kunya daga jinsu, bari hatta shi kansa sai ya ji kunya abin da ya furta bayan tausasa da fita daga halin fushin da ya kasance, kai daga cikin mutane ma akwai wanda yake kafircewa Allah sa’ilin da yake cikin fushi_Allah ka tsaremu_sannan fushin ya cigaba da zabalbala ya bayyana kan gabbansa sai ka gay a fara kai duka da kai hari da keta kaya da jin rauni da kisa idan ya samu damar yin hakan ba tare da ya damu kan hatsarin hakan ba.

Idna wanda ya fusata kansa ya guje masa ko kuma ya subuce daga hannunsa sakamakon wani dalili, a wannan lokacin sai fushi ya dawo kansa kaga yana marin fuskarsa da kansa yana gudu kamar yand ayake cikin maye cikin dimauta, tama iya yiwuwa ya fadi kasa ya gaza tashi da mikewa sakamakon tsananin fushin, kai tana iya kaiwa ga kaga ya fadi sume, ko kuma ya bugi dabbobin d asuke kusa da shi ya kashe su, ko ka ganshi yana karya kayayyaki yana wurgi da kwanon abinci, yana farfasa akusai idna ya fusata kansu, kana iya samun yana aikin mahaukata sai ka same shi yana zagin dabbobi kai kace ma’abocin jaki, ko kuma yana zagin daskararrun abubuwa marasa rai kamar misalin mota , yana Magana da ita yana fadin har zuwa yasuhe zan cigaba da daurewa wahalhalunki da cutarwark, ta yiwu ka same shi yana dukanta, ta yiwu a lokacin wata dabba ta shure da kafa sai kaga ya rama, Allah ya tsaremu tare da ku daga wutar fushi da kufaifayinsa da da sabubbansa.