MUKAMI NA BIYAR: TA YAYA ZAMU MAGAN CE MATSALAR FUSATA

 

Hakika malaman Aklak sun samu sabanin cikin yanda za a bi kawar da matsalar fushi baki daya daga asalinsa, wasu sunce: yi masa takumkumi daga asalinsa daga zuciya babu mai yiwuwa ba, saboda shi fushi yana daga dabi’ar da halitta mutum, kadia dai abu mai yiwuwa shi za a iya karya habbakarsa da tashinsa da raunanata ta har ya zamanto motsinsa bai tsananta ba, gaskiya kamar yanda shi ne ra’ayinmu sabanin wannan bayanai, saboda bayani kan kawar da fushi wanda hankali da shari’a ke zarginsa ba ta yabonsa, aboin da yake kasancewa da ishara daga hankali da shari’a, abin da ake kira da jarumta,  ko da kuw an kira shi da fushi na jeka na yika, shi fushi mara kyau abin zargi za a iya kawar da baki dayansa, don ba don haka ba da ya zama wajibi a same shi wurin Annabawa da wasiyyai wanda hakan ya gurbata.

Sannan kamar yanda yake cikin cututtuka da larurori na ganagar jiki samun lafiya da waraka na kasantuwa ta hanya guda biyu: wani lokacin kan kasancewa ta hanyar kare da riko da maganin kare kai, kamar misalin ya yanke sinadarai da jijiyon cututtukan da kaurace musu da guje musu, kamar misalin wanda yake nesanta kansa da wuraren iskar mai sanyi don kare kansa daga kamuwar da ciwon mura, wani lokacin kuma ta hanyar maganin lilitan zamani, yana kasancewa bayan kamuwa ta hanyar komawa ya zuwa ga likita da kebantacciyar hanyarsa da riko da kiyaye shan magani da waninsa, kamar yanda yake cikin tsohan ilimin likitanci da sabo na zamani.

Bai buy aba cewa kare kai daga kamuwa da ciwo shi ne mafi alheri daga yin magani, kuma shi ne amfi sauki daga shan magani, ta yiwu bibiyar likita na iya daukar lokaci da hadiye kudade masu yawa da sauransu.

Haka al’amarin yake cikin al’amuran Aklak da na ruhi da nafsu, kamar misalin miyagun dabi’u da munanan siffofi, wani lokacin kubuta daga garesu na kasancewa ta hanyar kare daga kamuwa da su da tunbuke jijiyo da sinadaransu domin kada su samu damar motsi da da ruruwa cikin mutum, wani karon kuma ta hanyar magan ce su da magani  cikin marhaloli uku: tsaftace zuciya, yi wa zuciya ado da kyawawan dabi’u, girmama, kamar amfani da magunguna daga kwayoyi da na ruwa da dai abin da yayi kama da haka cikin yiwa jiki magani, wadannan sune magunguna na Aklak da malaman Aklak suka kawo cikin litattafansu filla-filla da magan ce cutar fushi.

Amma kare kai daga kamuwa da fushi, lallai yana kasancewa ta hanyar tunbuke jijiyarsa da kawar da ita, hakan yana wajabta neman sanin sabubban fushi da dalilansa da farko, sannan mu nemi sanin ta wacce hanyar zamu kawar da su, mafi muhimmancin sabubba da masana ruhi da zukata da nufus wadanda sune ake kira da malaman Aklak daga Annabawa da wasiyyai da magadansu daga malamai nagargaru abin da zai zo a kasa:

1-girman kai da takabburanci.

2-alfahari da yinsa.

3-jiji da kai da ruduwa da kai.

4-ta’asubbanci da hanananci.

5-daga kai da son kai.

6-riya da jin kai

7-barkwanci da wasa da izgilanci.

8- wulakanci.

9-jayayya.

10-kishiyantar juna da yaudara.

11-tsananin kwadayi da buri kaN kudi da mukami.

Wadannan dukkaninsu suna daga miyagun dabi’u ababen zargi a hankalce da shari’a, da a iya kubuta daga fushi tare da wanzuwar wadannan sabubba da dalilai, ya zama dole a kawar da su da nesantar da su daga zukata da nufus cikin mukamin tsarkake zuciya da tsaftace wanda shi ne mafi girman jihadi, hakan na kasancewa ta hanyar samar da kishiyoyin junan munanan dabi’u, hakika kubuta daga baki na kasancewa ta hanyar samar da fari, kubuta daga duhu da samar da haske, ya kamata mu kashe girman kai mu kawar da shi ta hanyar tawali’u da kaskantar da kai ga Allah matarkaki madaukaki, haka kama a kawar cda alfahari da cin mutuncin mutane, ya kamata mu san cewa mutane daga uba da uwa daya suke, me zai san a dinga yin alfahari? Lallai `yayan Adamu daga nau’i gud adaya suke, dukkaninsu daga Adamu suke shi kuma Adamu daga turbaya yake, kadai banbanci da fifita na wurin Allah ta hanyar tsoran sa da ilimi mai amfani da aiki nagari da jihadi cikin tafarkin Allah

 

{ إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ }

Hakika mafi karamcinku wurin Allah shi ne mafi tsoran Allah cikinku.[1]

 

{ يَرْفَعِ اللَّهُ الَّذِينَ آَمَنُوا مِنْكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَاتٍ}

Allah ya daukaka darajojin wadanda suka yi Imani daga cikinku da wadanda suke da ilimi.[2]

 

{وَفَضَّلَ اللَّهُ الْمُجَاهِدِينَ عَلَى الْقَاعِدِينَ أَجْرًا عَظِيمًا}

Allah ya fifita masu jidadi kan wadanda suka zauna gida da lada mai girma.[3]

 

Saboda haka alfahari cikin duniya da lahira yana kasancewa da falaloli da darajoji, bawai yawan dukiya da matsayi da mukamai da nasabobi ba.

Amma jiji da kai da riya ana kawar da su ne da abin da yake kishiyar su daga dabi’u, ka san cewa duk abind ayake gareka daga falala daga Allah yake (wannan yana daga falalar ubangiji na) domin ya ga yaya zaka gode masa ka bauta masa, ka da ka danganta hakan zuwa ga kanka don kada ka rudu ka kayatu da shi, ka da ka yiwa Allah shirka cikin bautarsa, wadannan mutane da kake son ka burge wai su waye su mene ne su? Shin ba misalinka suke b? ashe ba mutuwa ce alkawarnsu ba, ashe ba Allah ne mai gani ba kuma mai iko kan komai ba kuma hannunsa ramar komai take ba?!

Me ya kawo yin riya Sannan kada dagawa da aikata laifi ta kama ka, lallai karshen masu aikata zunubi matukar basu tubaba shi ne kunyata da tozarta da wuta, sannan me ya kawo yin ta’asubbanci da hananancin jahiliya ga dangi da kabila ko kuma kungiya ko mutanenku da dai abin da yayi kama da haka?

Shin dukkanin wannan abubuwa bai kama da bautar gumaka ba wanda yake cin karo da mukamin bautar ubangiji shi kadai matsarkaki madaukaki? Sannan yana cin karo da ruhin shari’a da wahayin sama?...

Sannan me ya kawo dagawa da cin mutuncin wasu, kana ganin kyawun kanka kamar Dawisu, ya isar maka ka kalli aibobinka, kamar yanda Dawisu yake ganin munin kafafuwansa hakan sai kashe dagawarsa, sannan duniya gida ne gada ce kuma kayan aro ne da aka ara maka, ko dai dausayi daga dausayoyin aljanna ko kuma dai rami daga ramukan wuta.

Ya kai wanda ya shagaltu da duniyarsa***hakika dogon buri ya rudar da shi.

 Ya kai wanda ya zo wa duniya babu zato babu tsammani***shi kabari akwatun aiki ne.

Amma shi wasa da barkwanci yana tafiya da haske da kwarjini da ruwan fuska, haka wargi da izgilanci da kansa da kan wasu, kawar da hakan yana kasancewa da shagaltuwa ayyukan addini da suke mamaye addini, da shagaltuwa da mas’auliyar zamantakewa da dangi, ana kawar da wargi da wasa da neman ilimi da fanni da sakafa da falaloli da Aklak kyawawa da aiki tukuru domin neman rayuwa ko kuma ga arzikin lahira, amma izgilanci kan wasu to ana kawar da shi da karamci da dena cutar da su da kuma kare kai daga hana wasu su yi maka izgilanci.

Amma wulakanci da tozartuwa ma’ana wasu su tozarta ka ko kuma ka wulakanta su, lallai kawar da shi na kasancewa daga nesantar munanan halaye, da kuma kare kai daga jin radadin jawabin sauran mutane da zafafan kalmomi.

Amma yaudara, to kawar da wannan matsala na kasancewa ne da cika alkawari, amma kwadayi shi ana kawar da shi ne da kana’a wadatar zuci wanda shi ne taskarsa wanda baya karewa, da wadatuwa da kai da kamewa, da kare ruwan fuska, da ka da ta kai yana mika hannunsa yana neman taimako daga gare shi, ya kauracewa hakan don kare mutuncin kansa da karamar iyalansa da daukaka daga kaskanci roko da neman taimako.

Bai buy aba cewa dukkanin wadannan miyagun dabi’u da wasunsu da ake bukatar magani da kare kai daga garesu, kamar misalin mai wasan motsa jikin cikin daga abubuwa masu nauyi, kamar yanda yake bukatar lokaci mai tsaho da har zai zame musu jiki da bazai iya rabuwa da it aba, idan miyagun dabi’u suka nesantu daga gareta to lallai zuciya ta tsarkaka ta tsaftatu, hakika dukkanin wanda ya tsarkaketa ya rabauta, wanda ya kazantar da ita ya tabe.

Sannan duk wanda ya kubuta daga wadannan miyagun dabi’u ta hanyar kalubalanntar su da kishiyoyi, kamar misalin kashe wuta da ruwa, lallai zai kubuta daga abin da yake haifuwa daga gareta kamar misalin fushi lallai shi fushi ya samu ne daga haramun daga wadannan cutukan, musammam ma lokacin cudanyar ba’arinsu ga ba’ari, duk wani `dan zina da haramun yana samuwa ne daga jiji da kai da takabburanci, daga dagawa da alfahari, daga son kai da kwadayi da abin da yayi kama da haka!!

Mamaki dukkanin mamaki lallai daga mafi tsananin dalilai da sabubba fushi wurin mutane shi ne kiran da mutane fushi mai muni da cewa jarumta ne da karamci da abin da yayi kama da haka sakamakon wautarsu da jahilcinsu, lallai Shaidan yana hallara yayin da aka fusata kamar yanda Shaidan ya gayawa Annabi Nuhu (a.s) don ya ci gallar matsaya cikin amfaninsa daga ya halaka wanda yayi fushi da batar da shi domin ya sanya shi ya aikata miyagun ayyuka da zunbai yayi galaba kansa, lallai Iblis bai rantse da Izzar Allah ba.    

{ وَلَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ * إِلَّا عِبَادَكَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِينَ}

Na rantse sai na batar da su baki dayansu*sai dai bayinka daga cikinsu wadanda ka tsarkake.

Sannan idan yaji wani mummunan fushi daga manyan sai ya dauki hakan matsayin jarumta da izza sakamakon wasiwasin Shaidan, da hakan ya nufi ya cudanya da su sai ya kutsa ta cikin fushinsu.

Manzon Allah (s.a.w) ya bada labara kan zargin fushi wanda yake kasancewa don kai ba don Allah ba face fushin baffansa Hamza, wanda ya kasance sababin shiriyarsa duk da kasancewarsa fushin don wanin Allah.

Sabida haka abin da yawancin mutane suke siffanta da fushi da karamci da izza da jarumtaka tsabagen jahilci ne, sakamakon ciwon zuciya da nakasar hankali, daga cikin abin da yake shiryarwa kan cewa fushi na daga rauni da raunin nafsu baya daga jarumta wanda shi ne fushi tsakatsaki, shi ne nuna kishi da fushi kan alfarmar abubuwa masu daraja kamar addinin da iyalanka  da duk abin da ya kasance don Allah matsarkaki, abin da yake shaida kan haka shi ne mara lafiya yafi saurin fushi daga lafiyayye, kamar yanda mace tafi saurin fusata daga namiji, haka ma karamin yaro daga babba, da jahili daga malami, da mai miyagun dabi’u daga mai kyawawa, haka daga bagidaje daga wayayye, haka dai.

Ya zo cikin hadisi mai daraja: jarumi bashi ne mai karfi ba, jarumi shi ne wanda yake iya mallakar zuciyarsa yayinda yake cikin fushi.

yanda yake kasancewa a fagen kokawa, karfaffa shi ne wanda yake galaba kan zuciyarsa, ma’ana ragamar kansa ta kasance a hannunsa yayin fushi, baya zalunci baya zaluntar mutane baya ketare iyaka, baya ta’addanci kan mutane, bai barna kan dukiyar mutane, sai a lura.


[1] Hujrat:13

[2] Mujadala:11

[3] Nisa:95