MUKAMI NA SHIDA CIKIN HAKURI DA DAURIYA

 

Babu shakka cewa hakuri mafi falala yana daga danne fushi _da kuma yin juriya wanda shi ne kallafawa kai yin hakuri da jurewa hakan cikin wahala da tsanani yayin da aka fusata mutum, sai dai cewa kuma idan mutum ya sabawa kansa yin hakan har ta kai ga danne fushi ya wayi gari ya zame masa jiki da al'ada ta yanda ba zai iya rabuwa da shi kuma cikin sauki zai danne fushi idan wani ya fusata shi, wannan shi ne abin da ake kira da hakuri, shi (tahalummi) kallafawa kai yin hakuri masdari ne shi kuma (Ahulmu) hakuri ismul masdar ne, wanda daga masdari din yaka samuwa, wanda shi ne hakuri dai da aka saba da shi yau da gobe wanda yake shiryarwa zuwa ga kamalar hankali da galabarsa da ikonsa kan fushi, shi hakuri shi ne Sarki kan fushi shike iko kansa bawai fushi ke iko kansa ba, shi hakuri nutsuwar nafsu ne da yake hana faruwa fushi kuma shi kishiyarsa ne a hakikan ce, kamar yandadanne fushi yake kishiya kan fushi.

Farkon hakuri shi ne kallafawa kai yinsa da kuma danne fushi, sai dia cewa kuma hakan na jawo wahala da tsanani, wannan ma'ana tana gudana cikin dukkanin siffofin Aklak ababen yabawa yababbu, kuyi tawali'u kuyi tawali'u, share fagen shiga tawali'u da zuhudu shi ne kallafawa kai yin hakan, ku nemi sani ku nemi sani, share fagen ilimi shi ne kallafawa kai neman sani, kamar yanda Manzon Allah (s.a.w) yayi ishara zuwa ga hakaya ce: 

: إنّما العلم بالتعلم والحلم بالتحلّم , ومن يتجّوى الخير يعطه, ومن يتوقّى الشر يوقه.

Kadai dai ilimi yana samuwa ne ta hanyar kallafawa kai neman sa hakuri na samu ta hanyar kallafawa kai yinsa, duk wanda ya…. Alheri za a bashi, duk wanda ya nemi kare kansa daga sharri zai samu kariya daga barinsa.

 

Hanyar samun hakuri shi ne kallafawa kai yinsa, hanyar samun ilimi kallafawa kai nemansa, an karbo daga gare shi (a.s) fadinsa:

اطلبوا العلم واطلبوا مع العلم السكينة والحلم , ليّنوا لمن تتعلمون منه , ولاتكونوا من جبارة العلماء , فيغلب جهلكم حلمكم.

Ku nemi ilimi ku neme shi tare da nutsuwa da hakuri, ku lausasa ga wanda kuke neman ilimi daga gare shi, ka da ku kasance daga Jabberan malamai, sai jahilcinku yayi galaba kan hakurinku.

 

Sai yayi ishara ya zuwa cewa yin jabberanci yana dgaa sabubban fushi_ kamar yanda bayani ya gabata, lallai shi jabberanci yana motsa fushi, yana kuma hana yin hakuri da lausasa da afuwa.

Sabubban yin fushi suna kasancewa kan kasuwa ta biyunta: ko dai halitta ko kuma bisa al'amura da aka al'adantu kansu, sannan wadanan abubuwa guda biyu suna komawa ga abin da malaman Aklak suka ambata, wanda sune: jiji da kai, alfahari, yaudara, jayayya, izgilanci da suaransu, sannan baki dayansu suna daga miyagun dabi'u masu halakarwa, babu hanya kubuta daga fushi tare da wanzuwa tare da su, wajibi a kawar da su domin kawar da fushi ya saukaka.

قال أمر المؤمنين ×: إن لم تكن حليماً فتحلّم , فإنّه قلّ من تشبّه بقوم الا أوشك أن يكون منهم .

Sarkin muminai Ali (a.s) ya ce: idan ba kai bamai hakuri bane to ka kallafawa kanka yinsa, lallai ya karanta mutum yayi kaman ceceniya da mutane face ya ksa kasancewa daga cikinsu.

 وقال×:خير الحلم التحلّم ,من لم يتحلم لم يحلم , من تحلّم حلم.

Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: mafi alherin hakuri kallafawa kai yinsa, duk wanda bai kallafawa kansa yin hakuri to fa ba zai iya yin hakuri, duk wanda ya kallafawa kansa yin hakuri zai yi hakuri.

 وقال الصادق ×:إذا لم تكن حليماً فتحلّم.

Imam Sadik (a.s) ya ce: idan ba kasance ma'abocin yin hakuri to ka kallafawa kanka yin hakuri.

Ma'ana idna a dabi'arka baka iya yin hakuri to ka tilastawa kanka yinsa, ka bayyanar da danne fushi ka yaki zuciyarka kan yin hakan har sai ya zama dabi'arka da zata saukaka maka yin hakuri, tare da cewa cikin hakan akwai tsanani da wahala sai dai cewa kuma akwai lada mai yawa, lallai mafi falalar ayyuka sune mafi tsananinsu, kad aka gafala, a wannan lokaci idan kasan banbanci tsakanin danne fushi da kallafawa kai yin hakuri to babu laifi mu yi ishara zuwa ga kowannensu daga abin da ya zo daga riwayoyi masu daraja tare da kiyaye takaitawa ba tare da tsawaitawa ba.