MUKAMI NA GOMA: NASIHOHI DA KISSOSHI KAN DANNE FUSHI DA KUMA YIN HAKURI

 

قال أمير المؤمنين علي×: أولى النّاس بالعفو أقدرهم على العقوبة.

Sarkin muminai (a.s) ya ce: mafi cancantar yin afuwa daga mutane shi ne wanda yafi kowa samun dama da iko kan yin ukuba.

وقال × : إذا قدرت على عدوك فاجعل العفو عنه شكراً للقدرة عليه.

Amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: idan ka samu iko kan makiyinka to ka sanyi yi masa afuwa godiya kan ikon da kake da shi kansa.

وقال × : أقيلوا ذوي المروءات عثراتهم، فما يعثر منهم عاثر الا ويده بيد الله يرفعه.

Amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: ku zobaitar tubatuban ma'abota mutunci, wane mai zobaitarwa baita ba zobaitar da tuntube daga garesu face halin zobaitarwa hannunsa ya kasance kan hannun Allah yana daukaka shi.

Na farkon mayi mai hakuri daga hakurin da yayi, shi ne lallai mutane zasu kasance mataimakansa kan jahili.

Wani mutum ya cewa wanda yake zaginsa da ya ce masa da kai nake shi kuma sai ya bashi amsa da cewa kai nake kauwa da kai.

An ce daga al'adar mai karamci shi ne idan ya samu iko sai yayi gafara, idan ya ga zamewar kafa sai ya suturce.

Suka ce:baya daga cikin al'adar mutane masu daraja gaggauta fushi da daukar fansa.

An ce: duk wanda ya dau fansa hakika ya huce haushinsa, ya karbi hakkinsa, gode masa bai zama wajibi ba, ambatonsa ba zai zama abin yabo cikin mutane.

Larabawa suna cewa: shugabanci bai kasancewa tare da daukar fansa, abin da yake wajabta ga ma'abocin hankali idna Allah ya bashi dama shi ne ka da ya sanya yin ukuba ta zama siffarsa, idan ya zama dole a dauki fansar to ya tausayawa cikin daukar fansar ta shi, sai dai idan ya zama cikin tsayar da haddi daga haddodin Allah ta'ala ne.

Cikin ba'arin litattafai saukakku: lallai yawan afuwa yana kara tsahon rayuwa, asalinsa fadinsa madaukaki:

 (وأما ما ينفع الناس فيمكث في الأرض.

Amma abin da zai amfanar da mutane sai ya wanzu cikin kasa.

Hassan ya ce: mafificiyar riga da muatum ya sanya ta itace rigar hakuri, wallahi ita tafi kyawunta kanka daga bargon Hibaru.

Ana cewa shi mai hakuri shi ne lafiyayye, wawa ma'abocin miki ne.

Muhammad Ibn Ajlan yana cewa: babu wani abu mafi tsanani kan Shaidan daga malamin da yake tare da hakuri, idan yayi magana zai yi ta da ilimi, idan yayi shiru zai yi shi ne cikin hakuri, Shaidan yana cewa, shirunsa yafi tsanani gareni daga maganarsa.

Waka:

Idan ka kasance kana neman wata dabi'a koma bayan* dabi'ar daka dabi'antu kanta ba zaka samu nasara kan haka ba.

وعن الإمام علي بن الحسين × : أقرب ما يكون العبد من غضب الله إذا غضب.

An karbo daga Imam Aliyu Ibn Hassan (a.s) mafi kusa bawa ya kasance cikin azabar Allah shi ne lokacin da bawan yake fusata.

وقال رجل لرسول الله’ : أي شيء أشدّ؟ قال: غضب الله. قال فما يباعدني من غضب الله؟ قال أن لا تغضب.

Wani mutum ya tambayi Manzon Allah (s.a.w) wanne abu ne mafi tsanani? Sai ya ce masa: fushin Allah, sai ya ce to menene zai nesanta ni daga fushin Allah? Ya ce masa kada kayi fushi.

An ce duk wanda ya biyewa fushi ya tozarta basira.

Abu Atahiyatu ya rera waka cikinta yana cewa:

ولم أر في الأعداء حين اختبرتهم


 

عدّواً لعقل أمرءٍ أعدى من الغضب.


Cikin makiya lokacin da na jarraba su ban taba ganin makiyi ga hankali mafi kiyayya ba misalin fushi.

Ibn Mas'ud yana cewa: ya isa zama laifi ga mutum ace masa ka ji tsoran shi kuma sai ya fusata, ya ce: kaji da kanka.

An cewa Ib Mubarak: tattaro mana kyawawan dabi'u cikin kalma guda daya: ya ce watsi da fushi.

Malam Shu'ubi yana kaunar wannan baitin waka:

ليست الأحلام في حال الرضا


 

إنما الأحلام في حال الغضب
.

Hankali baya ga lokacin yarda*kadai ana gane hankali yayin fushi.

Ibn Sammak ya ce: wani bawa ya aikata laifi kan wata bakuraishiya, sai ta dauki bulala ta bi bayansa idan ta kusa zuwa daba da shi sai ta wurgar da bulalar tace: tsoran Allah baya kyale mutum ya huce fushinsa- shi ma'abocin takawa takawarsa tana hana shi daukar fansa da huce haushi sai hakan ya sanya shi yin hakuri da kau da kai.

Abu Zar ya cewa bawansa: menene ya sanya ka kora akuya zuwa ga ciyawar doki? Sai ya ce: ina son bata maka rai, sai ya ce: tabbas zan tattara fushi tare da lada, na `yantaka don neman yadar Allah ta'ala.

Wasu Yahudawa sun nemi izini shigowa wurin Manzon Allah (s.a.w) sai ya ce: baka ji abin da suka ce, sai ya ce: na fada: wa Alaikum.

Wani mutum ya zagi wani sai ya ce masa: ya kai wannan bawan Allah kada ka nutse cikin zaginmu ka bar gurbin sulhu mana, lallai ni ban yarda zage-zage ba tun ina karamin yaro, ba kuma zan aikata ba ina babba, lallai ni bana sakawa wanda ya sabawa Allah da wani abu fiye da ni in kiyaye `da'ar Allah ba cikin sa.

An hakaito daga Imam Sadik (a.s) cewa wani bawansa yana tsaye yana zubo masa ruwa kan hannunsa, sai butar ta fado daga hannun bawan sai ruwan ya fasu a kan fuskarsa, sai Jafar ya kalli wannan bawan cikin fushi sai bawan ya ce ya mai gidana: (da masu danne bacin ransu) sai ya ce masa na danne fushina, sai bawan ya ce: (da masu afuwa kan mutane) sai ya ce: nayi maka afuwa, sai ya ce (Allah ya na son masu kyautatawa) sai ya ce masa: jeka na `yanta don Allah ta’ala.

Ina cewa: na nakalto wannan kissa daga wurin malamanmu na Imamiya daga Imam Zainul Abidin da baiwarsa, babu mamaki idna haka ya maimaitu kan Imam Sadik (a.s) domin dukkaninsu haske ne gud adaya daga gidan Annabta da tsarkaka kuma su jagororin kyawawan dabi’u ne,

Sannan mutanenka wa’e sun nemi lika wata falala ga Umar da cewa ya bar fushi, kamar yanda ya zo cikin riwayoyinsu da cewa wai Ali (a.s) ya bar Amru Bin Wuddu Amirilokacin da ya zauna kan kirjinsa yana shirin yanke makogoronsa, sai Amru ya tofawa Imam miyau a fuska, sai Imam ya dan kyale shi zuwan kankani lokaci sannan ya dawo ya kashe shi saboda Allah, sai aka tambayi Imam kan dalili daga shi da kyale shi da yayi da farko sai ya ce: na daga shi ne domin in tsarkake abin da na yi domin Allah matsarkaki ka da ya zama cikin kisan akwai wani abu na kashin kaina.

Sai mutanen ka su ka nemi kirkiro wata falala da zasu kamantata da wannan falala ta Imam (a.s) domi a zamanin Mu’awiya da Banu Umayya an kirkiro hadisan karya masu tarin yawa da umarnin Mu’awiya cikin samarwa da wasu mutane falala da zata zama daidai da falalar Sarkin muminai Ali (a.s) sai dai cewa cikin ban takaici basu san cewa misalsalan wadannan falaloli na karya karyarsu da mummunan warinsu na bayyana karara ga wadanda zasu zo a bayansu kuma suka manta suka bar karairayin rubuce cikin litattafansu.

Ya zo cikin littafin Almustadraf fi Kulli Fannin Mustadrif juz 1 sh 418: an rawaito daga Umar bn Kaddab cewa ya ga wani yana cikin maye sai yayi kokarin kama shi domin ladabtar da shi, sai wnanan da yake cikin maye ya zagi Umar, sai ya Umar ya ja baya, sai aka tambaye shi aka ce ya Sarkin Muminai me yasa da ya zageka ka kyale shi ka ja baya, sai ya ce: na kyale shi saboda ya fusata ni, da na ladabtar da shi dana kasance na biyewa zuciya ta, bana son dukan musulmi bisa ta’assuabnci da fushin kaina.

Ina cewa: shin dama ana yiwa Allah `da’a ta hanyar saba masa, ta kaka zai halasta ga Halifa kuma Sarkin muminai ya kyale tsayar da haddi daga haddodin Allah, abin da ya zama wajibi shi ne matukar dai da gaske yake cikin abin da yake fada to sai ya dan jira ya huce haushin zagin da yayi masa sannan daga baya ya zartar da hukuncin Allah kan wannan mutumi da ya kama cikin maye yayi masa bulala tamanin, bawai ya ce zai ladabtar da shi.

Yanzu na tuna da wani abu da ya faru dani shekarun baya da suka shude, na kasance a birnin Madina Munawwara naje ziyara ne sai na shiga n akasdaya daga dakunan nazari da mudala’a na garin, daidai lokacin da nake jujjuya litattafai sai wani littafi ya bani sha’awa sai na bude shi haka cikin sauri sai cikin sa na ga an rubuta cewa Umar Ibn Kaddab bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) ya dauko kirare shi da wasu jama’a zuwa gidan Fatima Zahara (a.s) domin ya kona gidan da wadanda suke ciki, sai aka ce masa Fatima tana cikin gidan?! Sai ya ce ko da tana ciki… a daidai lokacin tana bayan kyauren gidan sai ya bugi kyauren da kafarsa sai awagarta ta karye tayi barin jinjirin da yake cikinta.

Sai na nunawa wanda yake kula da wurin wannan abu da na karanta ya kasance daga mutum mai dogon gemu da dangalallen wando, na tambaye shi ta yaya ya aikata haka, yayin da ya ga jumlar sai ya dimauce yayi shiru, daga baya ya ce zan tambayi malamai na dangane da hak.

A rana ta biyu sai na kara shi wannan dakin nazari domin inji amsar d aya samo daga malaman sa, sai ya ce mini Umar ya aikata haka domin raya sunnar Manzon Allah (s.a.w)?!! sai nayi mamaki matuka daga wannan Magana tasa nace masa ta kaka? Sai ya ce: saboda Ali ya bar sallar jam’I tsawon kwanaki uku, Manzon Allah ya ce duk wanda ya bar sallah tsahon kwanaki uku ku kona gidan sa a kansa!! Sai nace: ya subhanallah wannan uzuri naka yafi aikin muni ta kaka Manzon Allah da yake rahama da dalaci yayi umarni da kona gida kan mutanen cikin sa ba tare da da tambaya kan dalilin rashin zuwansu sallar ba da neman sanin dalili.

Kawai don baya halartar sallar jam’I sai a kona gidansa a kansa, shin dukkanin musulmi a wancan lokaci suna halartar sallar jam’I ko kuma idan bas u zo ba ana kona gidajensu a kansu, tarihi bai labarta mana Umar ya aikata hakan kan wani ba in banda gidan Fatima Zahara (a.s)?!!

Sannan ashe ba Annabi mafi girma ba shi ne rahama ga al’umma ba, ya kasance yana tsayuwa kan gidan Fatima (a.s) tsahon shekara a kowacce rana lokutan sallolin farilla yana cewa: amincin Allah ya kara tabbata gareku ya `yan gidan Annabta wadanda Allah ya tafiyar da datti daga garesu ya tsarkake su tsarkakewa, ishara zuwa ga wancan aya ta tsarki wacce ta sauko kan Fatima da babanta da mijinta da `yayanta Hassan da Husaini (a.s) ta yaya za kona wadannan tsarkaka da hujja kawai basa halartar sallar jam’I, tare da cewa siun kasance daga suna da sabani da wasu adadi daga masu rike da ragamar mulki sakamakon kwacen da akai musu na halifancin Ali (a.s) da gonar Fadak ta Fatima Zahara (a.s) sannan ta kaka zai kyale tsayar da haddi da ladabtarwa kan mashayin giya don gudun kada fushinsa yayi galaba kansa, amma kuma sai ya gaza kyale kona gidna Fatima Zahara har takai shi ga aikata abin da ya aikata, me ya sameku ne yaya kuke hukunci? Da sannu wadanda suka aikata kan iyalan muahammad zalunci zasu wancan majuya za su juya ranar da za a tashi kowanne mutane da jagoransu, misalin wadannan tabbatattun abubuwa iyayenmu da kakanninmu suka sani ba sai suka bi gaskiya suka taimake ta, kamar yanda ya kasance cikin farkawar muslunci ta wannan zamani matasa musulmi suna gano gaskiya sai fadaku su bi, ashe ba Allah mafi iya hukuncin daga masu hukunci ba