MUKAMI NA GOMA SHA UKU:

 

Masadik din aiki cikin motsin fushi:

Duk Abinda muka ambata ya kasance cikin magan ce fushi ta hanyar ilimi da hikima ta nazari, amma masadik din aiki don kubuta daga motsin da tashin fushi da ninkuwarsa mai munu da kufaifayin masu halakarwa, hakika ba'arin masadil sun zo cikin daga riwayoyi masu daraja, kamar yanda masana halayyar `dan Adam suka ambaci wasu masadik din na daban da za a kashe ruruwar wutar fushi, lallai sababinsa daga zafi yake, sannan musabbabin zafin shi ne motsi, sannan zama da kwanciya yana janyo yankewar motsi.  

قال رسول الله’: إن الغضب جمرة تتوقد في القلب, ألم ترى إنتفاخ أوداجه, وحمُرة عينه, فإذا وجد أحدكم من ذلك شيئاً, فإن كان قائماً فليجلس, وان كان جالساً فلينم, فإن لم يزل ذلك فليتوضأ بالماء البارد, وليغتسل فان النار لا يطفيها الاّ الماء.

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: hakika fushi garwashi ne da yake ruruwa cikin zuciya, ashe baka ganin kunburar jijiyoyin mafusaci ba, da yanda idanuwan sa suke jajawur, idan dayanku ya samu kansa cikin wannan hali, idan ya kasance a tsaye to ya zauna, idan ya kasance a zaune to ya kwanta, idan duk da haka fushin bai gushe ba to yayi alwala, ya yi wanka da ruwan sanyi lallai ita wuta babu abinda yake kashe ta sai ruwa.

قال رسول الله’: يا علي لا تغضب, فإذا غضبت فاقعد, وتفكر في قدرة الرّب على العباد وحلمه عنهم, واذا قيل لك:اتقّ الله فانبذ غضبك وراجع حلمك.

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ya Ali kada kayi fushi, idan ka fusata ka zauna, kayi tunani cikin ikon ubangiji kan bayinsa da hakurinsa daga barinsu, idan an ce maka, kaji tsoran Allah to ka yi watsi da fushinka ka dawo da hakurinka.

قال الامام الباقر عليه السلام: إيمّا رجل غضب وهو قائم فليجلس, فأنه سيذهب عنه رجز الشيطان, وإن كان جالساً فليقم...

Imam Bakir (a.s) ya ce: duk mutumin da yayi fushi alhalin yana tsaye to ya zauna, lallai da sannu dattin Shaidan zai tafi daga barinsa, idan ya zaune ya mike…

قال أمير المؤمنين علي عليه السلام: أيما رجل غضب وهو قائم فليلزم الأرض من فوره, فانه يذهب رجز الشيطان.

Sarkin muminai Ali (a.s) ya ce: duk sanda wani mutum yayi fushi yana tsaye take ya zauna kan kasa, lallai hakan na tafiyar da kazantar Shaidan.

عن ابي ذر ان رسول الله’ قال:إذا غضب أحدكم وهو قائم فليجلس, فأن ذهب عنه الغضب والاّ فليضطجع.

An karbo daga Abu Zar cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce: idan dayanku ya fusata alhalin yana tsaye to ya zauna idan fushin bai tafi daga gare shi ya kwanta.

Na uku: (Alwadu'u) alwala: da ma'anarta ta lugga da wasalin fataha kan harafin wawun, shi ne wanke fuska da hannuwa, ko kuma da ma'anar isdilahi wanda shi ne bayani kan wanke fuska da hannuwa biyu da shafar kafafuwa tare da niyyar neman kusancin Allah.

قال رسول الله’ إذا غضب أحدكم فليتوضأ بالماء البارد, فإن الغضب من النار.

وفي رواية:(إنّ الغضب من الشيطان, وإنّ الشيطان خلق من النّار, وإنما يطفي النار الماء, فإذا غضب أحدكم فليتوضأ).

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: idan dayanku yayi fushi yayi alwala da ruwna sanyi, lallai shi fushi daga wuta yake.

A wata riwayar kuma: lallai shi fushi daga Shaidan yake, lallai shi Shaidan an halicce shi daga wuta, kuma ana kashe wuta da ruwa ne, idan dayanku yayi fushi to ya daura alwala.

Na hudu: yin sujjada domin Allah matsarkaki

قال أبو سعيد الخدري: قال النبي’:(ألا إنّ الغضب جمرة في قلب ابن آدم, ألا ترون إلى حمرة عينيه, وانتفاخ أوداجه, فمن وجد من ذلك شيئاً, فليلصق خدّه في الأرض).

Abu Sa'id Kudri ya ce: Annabi (s.a.w) ya ce: (ku saurara shi fa fushi garwashin wuta cikin zuciyar `dan Adam, ashe bakwa ganin yanda idanunsa suke jajawur, da yanda jijiyonsa suke kumbura, duk wanda ya ga daya daga haka, to ya manna kuncin da kasa).

Ya zo cikin littafin Mahajjatul Baida juz 5 sh 308: kai ka ce wannan ishara ce zuwa ga sujjada yana mika mafi daukakar gabbai ya zuwa mafi kaskantar mahalli wato turbaya domin domin ka dandanawa zuciya kaskanci ka cire mata izza da girman kai da shi ne sababi da ya jawo fushi.

Na biyar: tunatarwa da tausasawa da lausasawa, an ce wani mutumi ya kasance gabani yana fusata sai fushinsa ya tsananta, sai ya rubuta takardu uku, sai ya baiwa kowanne mutum guda takarda daya, ya cewa na farko: idan na fusata ka bani wannan takarda, ya cewa dana biyu idan fushina ya yayi sanyi ka bani wannan takarda, ya cewa na uku idan fushina ya tafi ka bani wannan takarda.

Sai wata rana fushinsa ya tsananta, sai aka bashi takardar farko, sai gashi cikinta an rubuta: me ya saka wannan fushi, kai ba ubangiji bane kai mutum ne kadai, ya kusa sashenka ya cinye sashenka, sai fushinsa ya sanyaya, sai aka bashi ta biyu, sai gashi cikinta an rubuta (ka tausayawa wanda yake cikin sa kasa wanda yake sama zai tausaya maka), sannan aka bashi ta uku sai gashi cikinta an rubuta: ka rike mutane da hakkin Allah, lallai babu abinda zai gyara su face haka, ma'ana ka da ka jingine aiki da tsayar da iyakokin shari'a.

Na shida: shiru da kame baki:

قال امير المؤمنين عليه السلام: داووا الغضب بالصّمت, والشهوة بالعقل.

Sarkin muminai (a.s) ya ce: ku magan ce fushi da yin shiru, ku magan ce sha'awa da hankali.

Lallai daga cikin dabi'ar da halayyar sha'awa shi ne tana kara fajirci da fasikanci, lallai ita sha'awa tana daga cutar da take wahalar samun magani face wanda ya amintu daga maganinta babu abinda yake juya ragamar sha'awa sai hankali, lallai yana nufin danne nafsul ammara da daidaita ta da tsarkake ta, shi hankali shi ne maganin sha'awa, kamar yanda shiru da kame baki ya kasance maganin cutar fushi.

Na bakwai: shafar jikin wanda kake danganta da shi:

قال الامام الباقر×:(.. وإيمّا رجل غضب على ذي رحم فليدن منه, فيلمسّه, فإنّ الرحّم إذا مسكت سكنت.

Imam Bakir (a.s) ya ce: (duk sa'ilin da wani mutumi ya fusata kan dan'uwansa to ya matsa kusa da shi ya shafa jikinsa, lallai yan'uwantaka idan aka kama ta tana tausasa.

Wannan yana shiryarwa zuwa ga dangatakar halittu ba'arinsu ya zuwa ba'ari a duniyar halittu, lallai shari'a cikin hukunce-hukuncen ta da kundinta tana yaye wani bangare daga wannan hakika, kamar yanda akwai alaka da dangantaka tsakanin duniyar halittu da duniyar shari'a, bari dai dukkanin biyun abu ne guda daya da yake da sasanni biyu, kamar misalin kwabo da yake da fuska biyu, sai a lura sosai.