sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • TUNAWA DA HAIHUWAR IMAM ALIYU BN MUHAMMAD ALHADI A.S
 • ALLAH YA AZURTAKU DA FARIN CIKI DA ZAGAYOWAR BABBAN IDI IDUL GADEER
 • HUBBAREN IMAM RIDA SUN GAYYACI ASSAYID ADIL-ALAWI LACCA
 • TUNAWA DA SHAHADAR IMAM MUHAMMAD JAWAD MUTUM NA TARA DAGA IMAMAI (AS)
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Nufus Aliyu bn Musa Arrida (as)
 • Makalar Idin Nairuz a muslunci ta fito tareda Alkalamin Assayid Adil-Alawi
 • Makalar Hubbun Nisa’i fi Hadisun Nabawi ta fito- tare da Alkamalin Assayid Adil-Alawi
 • Makalar Annaji Bashar Mau’udul Muntazar ta fito tareda Alkalamin Assayid Adil-
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam
 • Makalar duba li mushatulArba’in tareda Alkalamin Assayid Adil-Alawi
 • Asalamu alaikum na kasance mai yawan sha’awa
 • Mujallar Sautul Kazimaini mai fitowa wata-wata ta kara fito adadi 231/232
 • kissoshin bayin Allah Salihai nagargaru tare da Assayid Adil-Alawi (h)
 • Allah ya girmama ladan ku da na mu bisa musibar rashin Sarkin muminai Ali (as)
 • Tsare-tsaren shirin raya dararen lailatul kadari na watan Ramadan 1440 H
 • Muhadarorin watan Ramadan Assayid Adil-Alawi
 • An kammala zaman karanta ta’aziyar Imam Husaini (as) bisa zagayowar wafatin Sayyid Ali Alawi
 • Za a shirya zaman majalisin jimami har tsawon kwanaki uku bisa munasabar cika shekara talatin da bakwai da rasuwar Ayatullah Assayid Ali bn Husaini Alawi Allah ya jikan sa
 • Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala
 • Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi
 • Labarun da ba tsammani

  maulidin imam zainul abidin


  Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

  A ranar biyar ga watan Sha’aban shekara ta talatin da takwas ta hijirar Ma’aiki (s.a.w.a) matar Imam Husaini (a.s) ta haifi danta mai albarka.

  Lokacin da aka isar da wannan labari mai dadi ga Amirul Muminina Ali bn Abi Talib (a.s), sai ya yi sujada don nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki, daga nan kuma sai ya sa masa suna Aliyu. Shi dai wannan jariri da aka haifa shi ne Allah Ya kaddara zai ba shi matsayi na Imamanci, don kuwa shi ne Imami na hudu na daga Imaman gidan Manzon Allah (s.a.w.a) bayan kakansa Imam Ali (a.s) da baffansa Imam Hasan al-Mujtaba da kuma babansa Imam Husaini (a.s), kamar yadda Allah din ya kaddara dukkan sauran Imamai (a.s) za su kasance ne daga tsatsonsa mai albarka.

  Wannan batu kuwa ba wai kirkiransa muka yi ba, face dai magana ce daga Manzon Allah (s.a.w.a), don kuwa an ruwaito Imam Husain bn Ali (a.s) yana cewa: Wata rana na tafi wajen kakana Manzon Allah (s.a.w.a), sai ya zaunar da ni akan cinyarsa, ya ce min: ‘Hakika Allah Ya zaba daga tsatsonka, Ya Husain, Imamai tara, na taransu kuwa shi ne Ka’im dinsu, dukkansu kuwa matsayinsu guda ne a wajen Allah([i])”.

  Haka nan an ruwaito daga Ibn Abbas (r.a) yana cewa: Na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Ni da Ali da Hasan da Husaini da kuma tara daga Husaini tsarkaka ne kuma ma’asumai (wadanda ba sa sabo)([ii])”.

  Har ila yau Ahmad ya ruwaito daga Masruk cewa: Wata rana muna zaune tare da Abdullah bn Mas’ud yana karantar da mu Alkur’ani, sai wani mutum ya ce masa: Ya Abdallah! Shin kun taba tambayar Manzon Allah (s.a.w.a) kuwa kan halifofi nawa wannan al’umma za ta samu? Sai Abdullah ya ce masa: ‘Ba wani mutum da ya tambaye ni tun daga lokacin da na iso daga Iraki kafinka’. Daga nan sai ya ce: Na’am, lalle mun tambayi Manzon Allah (s.a.w.a) kuma ya gaya mana cewa: Su goma sha biyu ne tamkar zababbun Bani Isra’ila([iii])”.

  An kuma ruwaito daga Abdullah bn Ja’afar al-Tayyar cewa: ‘Na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Ni na fi cancanta a wajen muminai daga kawukansu, sai kuma dan’uwana Ali, wanda ya fi cancanta a wajen muminai daga kawukansu, idan ya yi shahada sai dana Hasan, shi ya fi cancanta a wajen muminai daga kawukansu, sai dana Husaini, shi ya fi cancanta a wajen muminai daga kawukansu, idan ya yi shahada sai dansa Ali, shi ya fi cancanta a wajen muminai daga kawukansu….([iv])”.

   

   

  ([i]).Yanabi’ul Mawadda na al-Balkhi al-Kanduzi, juzu’i  na 2, shafi na 105.

  ([ii]). Kamar na sama da Bihar al-Anwar, juzu’i na 36, shafi na 243 da kuma Kifayat al-Athar , shafi na 19.

  ([iii]). Musnad Ahmad, juzu’i na 1, shafi na 398, da kuma sauran ruwayoyi masu yawa da suke cikin Sahih Bukhari, juzu’i na 9, shafi na 81, da Sahih Muslim, juzu’i na 6, shafi na 4 da Bihar al-Anwar, juzu’i na 36, shafi na 230.

  ([iv]). Ikmalluddin wa Itmam al-Ni’ima na al-Saduk, shafi na 157 da al-Khisal, juzu’i na 2, shafi na 77 da kuma Uyun Akhbar al-Ridha, shafi na 28.