sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Bayanin sayyid Adil alawi akan mujalla na dorinnajafi


Da sunan Allah me rahama me jin kai

Gonar durrun najafi

Godiya ta tabbata ga Allah da ya koyar da dan adam abin da be sani ba, ya koya da shi sirri sannan ya rantse da abin rubutu da kuma abin da ake rubutu akai, sannan salitin Allah ya tabbata ga manzon tsira da kuma iyalan sa.

Wannan na daga cikin alamura bayyanannu

Mujalla (Durrun Najafi) na daga cikin gonannaki ma su kyau da ban sha’awa, domin duk lokacin da ka bude ko farta zaka shiga  za kaji  wani dadi, kana tafiya a tsakiyan bishiyoyi kana tsinkan yayan itacuwa, baa bin da zaka samu cikin wannan mujallar face wannan irin annashuwa, daga ban garori daban daban na wannan mujalla, wani abinda ya raba ta daga sauran mujja shine ilimin da akayi bayani a cikin ta da kuma wayar da kai ta ban garen al’adu, domin zakaga raayi daban daban domin basu rubutun wannan mujallar mutane daban dabanne, akwai larabawa da kuma ajami (wadan da ba larabawa ba), sai kuma ta bangaren yanki domin sun hada da wanda suka zo daga gabas da kuma yammacin duniya, sai kuma ta bangare ilimi da kuma siyasa, domin a cikin su akwai marajian taqlidi, da kuma malaman hauza.

Mun ya ba wa masu aiki kan wannan mujalla, kuma Muna fatan wannan mujallar zata kasance hanya na tarbiyyan ahlaq na gari, a kan wannan rayuwa da mukeyi na zamanin yanzu, sabida dukkanin yan adam sun kasance yan uwan junane (فكل الناس إمّا أخ لك في الدين أو نظير لك في الإنسانية) dan dam dan uwan kane ko ta addini ko kuma ta mutumta ka, qur’ani kuma na cewa ﴿وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعاً وَلا تَفَرَّقُوا﴾, sanna Allah ya sanya Alqur’ani da kuma iyalan gidan manzo hanyar tsira duk wanda ya bisu bazai taba bat aba.