sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Bakir (as)
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jawad Amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya faranta kwanakinku da murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Aliyu Ibn Musa Arrida amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Fatima Ma’asuma (a.s)
 • ZA A FARA DARASIN BAHASUL-KARIJUL-FIKHU NA ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Takwas ga watan Shawwal tunawa da ranar da Wahabiyawa suka ruguje kaburburan A’imma (a’s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da naku bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imamul Hassan
 • Mu’assatul Ihsan Alkairiya wacce take karkashin Majma’ul Tablig wal Irshad ta raba taimakon abinci a watan Ramdan Mai albarka
 • tashar tauraron dan Adam mai suna Anna'im zasu watsa laccar Assayid Alawi
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref

 • Haihuwar Fatan Raunana Al'imamul Muntazar Mahadi (a.s).
 • MURNAR TUNAWA DA HAIHUWAR HASKEN GIDAN MUHAMMADU GUDA UKU
 • ALLAH YA GIRMMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM KAZIM A.S
 • LABARIN KAMUWAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI (H) DA CUTAR KORONA
 • MUHADARAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI KAN MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA AKA HAIFI FIYAYYEN HALITTU (S.A.W) DA IMAM SADIK A.S
 • FARA TARON BAJAKOLIN LITATTAFAI NA KASHASHE A JAMI’ATU ALU BAITI A.S
 • RANAR IMAMANCIN SAHIBUL-ASRI WAZ-ZAMAN A.S
 • bahasul karij bahasi kan kiran sallah da ikama

  Cigaba kan darasinmu da ya gabata kan hukuncin kiran  sallah da tada ikama hakika jiga jigan malamai sun sassaba kan wannan mas`ala, daga cikinsu akwai wadanda suka tafi kan cewa mustahabbi ce mai karfi kamar yadda wannan ra’ayi shi yafi shahara hatta malam mawallafi (ks) kan haka ya tafi yana mai cewa hakika wasu malamai sun tafi kan wajabci sai dai cewa bamu san mai wannan ra’ayi ba, wasu kuma daga malaman fikihu sun tafi kan cewa wajabcin kiran sallah da tada ikama ya kebanta da sallolin magariba da asubahi kamar yadda aka aka hakaito daga malam ibn akilu ummani: amma ita ikama hakika tana zama wajibi cikin salloli biyar na yau da gobe, wasu kuma daga cikin malamai sun kebantar da wajabcin ikama kadai cikin sallolin jam’I kai sun sanya yin ikama matsayin sharadin ingancin sallar jam’I, kamar manyan shehunai suka hakaitar wato ibn barraj da ibn Hamza da abi salahu alhalabi , wasu kuma sun sanya kiran sallah da ikama matsayin sharadi cikin samuwar mutane  da dai wasunsu daga ra’ayoyin malamai.

  Mai littafin almadarik sayyid amili (ks) yana cewa: hakika dukkanin mutane sunyi ittifaki kan kasantuwar shar’antar kiran sallah da ikama cikin salloli biyarn na wajibi.

   Cikin littafin alhada’ik ya ce: babu kokwanto kan kiran allah da ikama cikin jumlar masallata maza da mata sallar jam’I ce ko ta daidaiko.

  Cikin littafin mustanad ya ce: babu shakka cikin kasantuwar kiran sallah da ikama da bukatar yinsu ga dukkanin sallaolin yau da gobe biyar na wajibi kai daga ckinsu ma harda sallar juma’a  maza da mata cikin sallar daidaiko da ta jam’I ramuwa da saukewa a halin tafiya ko kuma cikin gari bari ma dais hi kiran sallah da ikama na daga sallamamme lamari wajen musulmi, sai abinda Magana za ta zo kansa daga baya.

  Abinda ya shahara daga malamai magabata da wadanda suka zo daga baya  da wadanda suke daga bayansu  da wadanda muke cikin zamani daya tareda su shine kasantuwar kiran sallah da ikama a matsayin mustahabbi, sai dai cewa ansamu daga littafin jamal da sharhinsa  haka daga littafin mukni’atu da nihaya da mabsud da wasila haka daga littfin ahkamul nisa’I na malaminmu mufid (ks) kan cewa suna wajabta kan maza a sallar jama’I, an samu daga alkadi ibn barraj danganta wannan ra’ayi ga akasarin malamai , haka daga littafan algunya da alkafi  da al’isbahi da cewa wajibi ne cikin sallar jam’I babu banbanci cikin kasantuwar masallatan maza ko mata su basu kayyade su da ksantuwarsu maza ba. An hakaito daga shaik mufid (ks) wanda nassin Magana ya kasnce kamar haka: duk sanda kayi sallar jam’I ba tareda kiran sallah ba da ikama to hakika baka samu falalar sallar jam’in ba  da ma sallar da ta gabata. Ma’ana sallarka tayi ta inganta babu bukatar ramuwa, an samu daga jamal sayyid ibn akilu da ibn junaidu kan cewa sun tafi kan wajibcini ikama cikin kowacce sallah amma kiran sallah to shi wajabcinsa ya kebantu da sallolin magariba da asubahi, an samu daga ibn Junaid wanda ya gabaci wanda muka ambata a tarihi cewa wajabcin ikama ya takaitu kan sallar magariba da isha’I ga maza banda mata , amma maganar mawaallafi sayyid yazdi (ks) cewa babu matsala cikin karfafuwar rijnjayarta  ba tareda kaidi ba to menene abinda yake nufi da rijnayar bisa la’akari da duniyar tabbatar da hukunci cikin kanakin kan umarni, ko kuma dai bisa la’akari da duniyar tabbatar da hukunci kan mukallafai da dalilan lafazi  daga nassoshi  da riwayoyi, idan ya kasance na farko wato duniyar tabbatar hukunci a kankin kansa  dacewar abin nufi daga rinjayarta  shine karfafa a duniyar tabbatuwa ba tareda kaidi ba ma’ana dalab din ya ratayu da da ita da maslaha da milak ma tsanani da yake kusanta daga maslaha mai lazimta wajibci bisa salloli da yanayi da daidaiku, to gaskiya hakan har ya zuwan yanzu bai tabbatu ba, domin dalab din ya ratayu da su biyu ne bisa yadda halaye suke da sallolin kamar yadda haka zahirin riwayoyi ya yi ishara kai, idon kuma ya kasance ana nufin duniyar isbat ma’ana duniyar shar’anta hkunce hukunce kan mukallafai da kuma kasantuwar dalili kan rinjayar yana karfafa  sakamakon wasu adadin dalilai kan rinjayar duk da cewa ma’auni ya banbanta cikin duniyoyin biyu bisa banbantar daidaikunsu  da yanayi da kuma sallolin, to ma’anar ba zata nesanta ba kamar yadda hakan zai bayyana cikin riwayoyi da zasu daga baya cikin wannan mukami, saboda haka  sai a lura.

   Ya kai mai karatu ka sani cewa ita wannan mas’ala ta kiran sallah da ikama ma’asala ce da malamai ke da sabani cikinta kuma tushen sabanin ya samo asali daga riwayoyi da aka rawaito cikin wannan babi, saboda haka ya zama tisa mu bijiro da su mu warware karo da juna da ya afku cikin riwayoyi, Magana za ta kasance cikin mukami biyu: na farko shine ikama, na biyu kuma shine: kiran sallah.

  Amma na farko wato ikama: hakika yawancin malamai sun tafi kan cewa mustahabbi ce ba tareda wani kaidi ba kamar yadda wannan ra’ayi shine mafi karfafa a wajen mawallafi sayyid yazdi wanda wasu jumla daga nassoshi ke nuni ya zuwa hakan, wadanda nassoshi sun nuna karfafar mustahabbancin ikama cikin ba’arin salloli hakama sunyi nuni da rashin mustahabbancin cikin wasu ba’arin sallalin. Haka sababi ya ksance cikin bayani filla filla kan wannan mas’ala .

  Daga cikin riwayoyi da suka zo kan wannan mas’ala akwai ingantacciyar riwayar halabi.

  An karbo daga mohd ibn husaini da isnadinsa daga husaini ibn sa’id daga yahaya alhalabi: daga baban Abdullah (as) ya ce: idan ka kira sallah ka tada ikama a daji sahu biyu daga mala’iku za suyi sallah a bayanka, idan kuma ikama kayi kadai ba tareda  kiran sallah ba to sahu daya rak daga mala’iku za suyi sallah a bayanka.

  Haka ma daga cikin riwayoyin akwai ingantacciyar  riwayar ubaidullah ibn ali alhalabi.

  Daga ciki akwai ingantacciyar mohd ibn muslim ya ce: baban Abdullah(as) ya ce:  lalle kai idan ka kira sallah ka tada ikama lalle sahu biyu daga mala’iku za su sallata a bayanka, idan kuma ka tada ikama ba tareda kiran sallah ba to sahu guda day arak zasu sallata bayanka.

  Da wasu daga irien ieren wadannan hadisai  amsu tarin yawa da suke da wannan ma’ana.

  Amma bangare na biyu daga riwyoyin shine riwayar da aka rawaito daga baban Abdullah(as) daga babansa(as) cewa shi ya kasance idan zai yisallah shi kadai a gida sai ya tada ikama ba tareda yayi kiran sallah ba.[1]

  Daga cikin riwayoyin ingantacciyar riwayar Abdullah ibn sinani.

  Ankarbo daga baban Abdullah(as) ya ce: idan ka kebantu a gidanka to ikama guda daya ta isar maka ba tareda kayi kiran sallah ba[2]

  Fuskar kafa dalili:  da wadannan riwayoyi na bangaren farko da ke nuni kan cewa hakika hukunci  sahun  mala’iku  a bayan  wanda ya tada ikama ya takaitu da ikama ba tareda kiran sallah ba shi ne mafi karfafa dalili kan rashin wajabcin kiran sallah, saboda ta yaya mala’iku za su yi sallah a bayan wanda sallarsa ba ta inganta ba.

  Sai dai cewa mai ya sa kuma daga riwayar ke nuni da cewa wanda bai kirayi sallah wata martaba mai girma ta tsallake shi- hakika shi ta hanyar barin kiran sallah ya rasa sahu guda kammalalle daga mala’iku, lalle babu shakka sallar mala’iku a bayansa yana daga cikin abinda zai kara kamalar sallarsa da kammaluwarta da kusanta ubangiji wanda girmansa ya girmama.

  Kamar yadda zahirin bangare na biyu daga riwayoyin daga abinda aka samu imami yana aikatawa  daga sunna shne cewa lalle shi imam jafar(as) ya kasance yana sallah a gida da ikama kadai ba tareda kiran sallah ba, kamar yadda imam (as) ya bayyana halascin takaituwa da ikama guda day aba tareda kiraitar sallah ba idan ya kasance yana sallah shi kadai ba cikin jam’I ba.

  Shin daga bangarori biyu daga riwayoyin na nuni da cewa wannan hukunci ya kebantu da wanda yake sallah shi kadai ba sallar jam’I ba.

  Bai buya cewa akwai bangare na uku da hudu daga riwayoyi da suke fa’idantar da wajabci, sai dai cewa wanda suke kafa dalili da cewa wani lokaci hakan na kebantar sallar jam’I  wani lokacin kuma na kebantuwa da sallolin asubahi da magariba, to hakan na nuna cewa an samu karo da juna cikin bangarori biyu da bangare guda ke nuni da wajabci daya bangaen kuma na karshe ke nuni kan rashin wajabcin.

  Bayanin haka: amma sallar jam’I, hakika sun kafa dalili kan wajabcin kiran sallah cikinta da wasu jumla daga riwayoyi  daga ciki riwayar abu basir daga daya daga cikin imamai(as) ya ce: na tambayi imam shin kiran sallah guda daya na isarwa sai ya ce idan kai sallah cikin jam’I babu abinda ke gudana face kiran sallah da ikama.[3]

  Daga cikin riwayoyin akwai muwassakatu ammar.

  Ankarbo daga mohd ibn yakub ibn mohd ibn yahaya ibn ahmad ibn hassan daga amru ibn sa’id daga ammar  daga baban Abdullah (as) cikin hadisi: ya ce: an tambaye shi kan mutum da ya kira sallah yayi ikama domin yayi sallah shi kadai sai kuma wani mutum ya zo y ace masa muyi sallah tare, shin ya halasta garesu suyi sallah da karan sallah da ikamar dana farko yayi ? sai imam ya ce: a’a sai dai cewa zai yi kiran sallah ya tada ikama[4]

  Sayyid ku’I(ks) yana cewa hakika shaik ya rawaici wannan riwaya daga hanyoyi uku dukkaninsu ingantattu.[5]

  Daga cikin riwayoyin akwai ingantacciayr Abdullah ibn Sinan.

  Daga mohd ibn hassan daga fadalatu ibn ayyub daga Abdullah ibn sinani daga baban Abdullah(as) ya ce: zai bakanta maka idan ka halwa a gidanka kayi ikama guda ba tareda kiratar sallah ba, kamar yadda yadda ma’anar haka ya gabata cewa shine rashin wadatuwa matukar bai kebantu a gidansa ba ma’ana idan yayi sallah cikin jam’I , kamar yadda wannan shine ma’anar riwayar ubaidullah alhalabi, hadisin na sila da cigaba insha’Allah  

  [1] Wasa’il babi 5 daga babukan kiran sallah da ikama hadisi 6 da na 4

  [2] Wasa’il babi 5 daga babukan kiran sallah da ikama hadisi 6 da na 4

  [3] Wasa’il babi na biyu daga babukan kiran sallah da ikama hadisi na 1

  [4] Wasa’il babi na bakwai daga babukan kiran salah da ikama hadisi 1

  [5] Kafi juz 3 sh 304/13. Alfakihu juz 1 sh 258. Tahzib juz 2 sh 277/1101