sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Labarun da ba tsammani

MUNA TAYA DAUKACIN AL’UMMAR MUSULMI MURNA ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWAR WANDA AKA HAIFA CIKIN DAKIN KA’ABA ALIYU IBN ABI `DALIB(AS)


da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Hakika ingantaccen hadisi ya zo daga bangarori biyu na musulmi shi’a da sunna cewa wilayar sarkin muminai ali(as) itace mikakken  siradi, sannan duk wani mumini cikin dukkanin sallolinsa cikin dukkanin fatiha da yake karantawa yana neman Allah ya shiryar da shi tafarki madaidaici tafarkin wadanda akai ni’ima kansu daga annabawa da siddikai da shahidai  da salihai

 (وَمَنْ يُطِعِ اللّه‏َ وَالرَّسُولَ فَاُوْلَئِكَ مَعَ الَّذِينَ أ نْعَمَ اللّه‏ُ عَلَيْهِمْ مِنَ النَّبِيِّينَ وَالصِّدِّيقِينَ وَالشُّهَدَاءِ وَالصَّالِحِينَ وَحَسُنَ اُوْلَئِكَ رَفِيقاً)

 dukkanin wadanda sukayi biyayya ga Allah wadannan suna tareda wadanda Allah ya yi ni’ima garesu daga annabawa da siddikai da shahidai da salihai wadannan sun kyautata zama abokan tafiya.

Siradi yana misaltuwa cikin ibadar Allah lalle ita ibada tana daga cikin

abubuwan da ke gasgata siradi  

(وَأنِ اعْبُدُونِي هَذَا صِرَاطٌ مُسْتَقِيمٌ)

Ku bauta mini wannan shine hanyata mikakkiya

Kamar yadda ake kiran addinin muslunci da daidaitaccen addini mara karkata

(إنَّنِي هَدَانِي رَبِّي إلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ دِينا قِيَما مِلَّةَ إبْرَاهِيمَ حَنِيفا)

Lalle ni ubangijna ya shiryar dani tafarki madaidaici addinin `kimanatawa mai akidar Ibrahim mai karkata ga gaskiya

(وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الإسْلامِ دِينا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ)

Duk wanda ya nemi addini koma bayan muslunci har abada ba za a karba daga gareshi ba.

Da siraddi mikakke tafarki madaidaici bawa ke kaiwa zuwa ga arzzikin gida biyu:

«وَأنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيما فَاتَّبِعُوهُ».

Wannan shine tafrkina madaidaici ku bishi.

Bai buya ba cewa shi siradi ya kasu zuwa kashi biyu: siradin duniya da kuma siradin lahira  daya yana bayanin kan daya  sannan tsakaninsu akwai lazimci da juna  cikin ilimi da aiki.

Ankarbo daga mufaddal ibn umar ya ce: na tamabayi baban Abdullah(as) gameda siradi sai ya ce: shi siradi wata hanya ce zuwa ga sanin Allah girmansa ya daukaka, sannan shi sirsdin kasha biyu ne, siradin dake duniya da kuma siradin da yake lahira, amma siradin duniya to imami ne wannan siradi wanda shi biyayya gareshi wajibi ce duk wanda ya san shi cikin duniya ya yi koyi da shiriyarshi to zai wuce takan siradin wanda ya kasance shi gada ce ta jahannama a lahira, wanda kuma bai san shi ba a duniya to kafafuwansa zasu zame a kan siradi a lahira su halaka su fada jahannama. Imam sajjad(as) yana bayanin ainahin abinda ke gasgata siradi mafi cika madaidaici:

Lalle tsakanin Allah da hujjarsa babu hijabi, mune kofofin Allah, mune hanyar Allah mikakka , mune taskar  ilimin Allah,  muna tarjamar wahayin Allah mune rukunan tauhidinsa mune ma’ajiyar sirrinsa.

Ankarbo daga abu Hamza sumali, daga baban Abdullah(as) ya ce na tambayi imam kan fadin Allah mai girma da daukaka:  

«قَالَ هَذَا صِرَاطٌ عَلَيَّ مُسْتَقِيمٌ(،

Wannan shine tafarkina madaidaici.

Sai imam ya ce; wallah shine mizan da tafarki madaidaici.

Ankarbo daga baban Abdullah(as) cikin wani hadisi ya ce: sakin muminai ali(as) ya ce: hakika Allah mai’albarka madaukaki da ya so da ya bayyanawa bayinsa kansa, sai dai cewa ya sanya mu kofofinsa kuma hanyarsa da tafarkinsa da fuskar da ke zuwar masa daga gareta, duk wadanda suka janye daga wilayarmu  ko kuma suka fifita wasunmu a kanmu lalle zasu kasnce masu karkacewa daga barin siradi.

«وَإنَّكَ لَـتَدْعُوهُمْ إلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ * وَإنَّ الَّذِينَ لا يُؤْمِنُونَ بِالآخِرَةِ عَنِ الصِّرَاطِ لَـنَاكِبُونَ».

Lalle kai kana kiransu ya zuwa hanya mikakkiya*lalle wadanda basu Imani da lahira sun kasnce masu karkata daga hanya.

Duk wanda ya karkace daga hanya mikakka lalle shi yana cikin jahannama  yana maia zama cikinta tirr da makwanta. An karbo daga abu basir daga baban Abdullah(as) ya ce: siradinda iblis ke cewa:

(لأقعدنّ لهم الصراط المستقيم)،

Lalle ina zaune musu hanya mikakka.

Imam ali (as) ne wannan hanya da shaidan ke zaunewa shi sahaidan tun rana ta shida ya yi rantsuwa da girman Allah cewa sai ya batar da dukkanin mutane  baki daya face bayin Allah muklisai  kadan ne daga bayi muklisai , mutane sun ridda daga wilayar imam(as) jagoran addini zakin Allah  bayan wafatin manzon Allah(s.a.w) face wasu tsiraru daga cikinsu, hakika manzon Allah(s.a.w) gameda wilayar ali(as) ya ce: (na rantse da girman ubangijna lalle shi ne kofar Allah da ba a shiga face sai daga gareshi lalle shine hanyar Allah mikakka, lalle shine wanda za ai tambaya kan wilayarsa ranar kiyama, ya kara cewa jibrilu(as) ya zo wurina sai ya ce: in maka bushara ya muhammadu da abinda zaka keta a kan siradi? Ya ce sai nace masa eh, sai ya ce: zaka ketare da hasken Allah, shi kuma zai ketare da haskenka, lalle haskenka daga hasken Allah yake, ita kuma al’ummarka za ketare siradi d haskejn Allah, sannan shi hasken ali daga haskenka yake     

«وَمَنْ لَمْ يَجْعَلْ اللّه‏ُ لَهُ نُورا فَمَا لَهُ مِنْ نُورٍ».

Duk wanda Allah bai sanya masa haske ba to baida wani haske.

Ya ce: idan ranar kiyama ta kasance aka shimfida siradi a saman jahannama  babu mai ketare shi face wanda yake da passport(shaidar ketarewa) wanda shi wannan shaida ba wani abu bane da ya wue dai wilayar ali(as) saboda fadinsa madaukaki:

«وَقِفُوهُمْ إنَّهُمْ مَسْؤُولُونَ»

Ku dagatar dasu lalle su ababen tambaya ne.

Ma’ana kan wilayar ali(as) ya ce: idan Allah ya tattara mutanen farko da na karshe ranar kiyama aka kuma sanya siradi a kan gadar jahannama babu wanda zai ketare face wanda yake da bara’a da wilayar ali(as) sannan ya zo a hadisin waki’u abu sa’id yana cewa; ya manzon Allah(s.a.w)  menene ma’anar bara’ar ali (as) sai ya ce: babu arki sai Allah muhammdu manzon Allah ne ali kuma waliyin Allah ne.

Cikin wani hadisi mai tsawo yana cewa: lalle ubangija mai girma da daukaka ya yi rantsuwa da girmansa cewa babu wanda zai ketare siardi face wanda ke tareda bara’arka da wilayarka da wilayar imamai daga `ya`yanka. Haka ankarboa daga gareshi: idan ranar kiyama ta tsaya ali ibn abi dalib(as) zai zauna  a kan Firdausi wanda shi wani dutse ne  da ya ke saman aljanna  saman ala’arshin ubangijin talikai, daga sama koramu aljanna suke tsagewa su yayyadu cikin lambuna shi kuma yana zaune a kan kujera  daga wani haske mai gudana tsakanin  gabansa kuma ga tasnim, babu wani mutum da zai ketare siradi face treda shi akwai bara’a da wilayar imam ali(as) wilayar alinsa  msoyansa zsu shiga aljanna makiyansa kuma su shiga wuta.

Ankarbo daga baban Abdullah(as) : ( ya ubangijimu munyi Imani mun bi maulanmu waliyinmu ami shiryar damu mai kiranmu mai kira ga dukkanin al’umma ya zuwa hanyarka mikakka , hujjarka tafarkinka mai kira zuwa gareka bisa basira shi da wanda ya bishi tsarki ya tabbata ga Allah daga abinda suke tarayya gareshi da wilayarsa  da abinda suke kaucewa ta hanyar rikar wasu mafaka koma bayansa, Allah ka shaida cewa  imami  shiryayye mai shiryarwa shine ali sarkin muminai(as) wanda ka ambace shi cikin littafinka kace:     

«وَإنَّهُ فِي اُمِّ الكِتَابِ لَدَيْنَا لَعَلِيٌّ حَكِيمٌ»

Lalle shi cikin asalin littafi a wurinmu madaukaki ne mai hikima.

Bana masa tarayya da wani imami bana rikar wani mafaka koma bayansa.

Hakikar siradi hanya madaidaiciya mikakka da sirrinsa shine ali sarkin muminai da `ya`yansa  imamai ma’sumai  guda goma shadaya, wilayarsu na misalta wilayar annabi cika makin annabawa muhammadu lalle wilayarsu na misalta wilayarsa mafi girma, da wannan wilaya da tajallinta  da zahirinta  da sha’aninta  da yake isar da mutum zuwa ga arziki duniya da lahira. Imam sadik (as) yana cewa:  hanya mikakka sarkin muminai ali(as).

Sarkin muminai ali(as) ya ce cewa: ni ne hanya mikakka tsakanin aljanna da wuta. Sarkin muminai ali(as) ya ce:  ni ne mizani.

Amincin Allah ya tabbata ga hanya mikakka mizani marab tawaya har abada abidin, majibancinmu lamarinmu  arkin muminai sugaban wasiyyai ali ibn abi dalib(as) wanda Allah ya riki alkawali daga annabawa da salihai kan wilayarsa da wilayar `ya`yansa imamai  tsarkaka(as).

Muna taya al’umma musulmi murna zagayowar ranar haihuwarshi cikin ka’aba muna rikon Allah da ya datar da dukkanin musulmi  mazansu da mata  ya zuwa riko da wilayarsa da shiruyuwa da shiriyarsa da koyi da rayuwarsa wadda daidai take da rayuwar annabi Muhammad musdafa (s.a.w)  da  zababbun imamai daga `ya`yan Fatima zahara (as)  da kur’ani mai Magana hanya madaidaiciya ali(as).

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya mu cikin wadanda suke riko da nauyaya biyu littafinsa da tsatso tsarkaka  muhammadu da iyalansa(as)

Karshen kiranmu muna godiya ga Allah ubangiji talikai