sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Allah ya faranta kwanakinku da murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Aliyu Ibn Musa Arrida amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Fatima Ma’asuma (a.s)
 • ZA A FARA DARASIN BAHASUL-KARIJUL-FIKHU NA ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Takwas ga watan Shawwal tunawa da ranar da Wahabiyawa suka ruguje kaburburan A’imma (a’s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da naku bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imamul Hassan
 • Mu’assatul Ihsan Alkairiya wacce take karkashin Majma’ul Tablig wal Irshad ta raba taimakon abinci a watan Ramdan Mai albarka
 • tashar tauraron dan Adam mai suna Anna'im zasu watsa laccar Assayid Alawi
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • Haihuwar Fatan Raunana Al'imamul Muntazar Mahadi (a.s).
 • MURNAR TUNAWA DA HAIHUWAR HASKEN GIDAN MUHAMMADU GUDA UKU
 • ALLAH YA GIRMMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM KAZIM A.S
 • LABARIN KAMUWAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI (H) DA CUTAR KORONA
 • MUHADARAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI KAN MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA AKA HAIFI FIYAYYEN HALITTU (S.A.W) DA IMAM SADIK A.S
 • FARA TARON BAJAKOLIN LITATTAFAI NA KASHASHE A JAMI’ATU ALU BAITI A.S
 • RANAR IMAMANCIN SAHIBUL-ASRI WAZ-ZAMAN A.S
 • ALLAH YA GIRMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM HASSAN ASKARI A.S
 • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
 • Labarun da ba tsammani

  MUNA TAYAN BAKI DAYAN MUSULMI MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA AKA HAIFI UBA GA `YANTATTU ABU ABDULLAH HUSAINI IBN ALI (AS)

   

  MUNA TAYAN  BAKI DAYAN MUSULMI  MURNAR  ZAGAYOWAR RANAR DA AKA HAIFI UBA GA `YANTATTU ABU ABDULLAH HUSAINI IBN ALI (AS)                                    DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

  SIRRI DAGA SIRRIKAN UBA GA `YANTATTU(AS)-TAREDA ALKALAMIN SAYYID ADIL ALAWI(H)

  Allah matsarkakin sarki  cikin littafinsa mai girma yana cewa:

  (اللهُ نُورُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ مَثَلُ نُورِهِ كَمِشْكَاةٍ فِيهَا مِصْبَاحٌ) .

  Allah shine hasken sammai da kasa misalin haskensa kamar taga wadda cikin akwai fitila.

  Manzon Allah muhammadul almusadafa(s.a.w) yace: anyi rubutu a daman al’arshi da koren launi (wanda shi koren launi launi ne na ma’arifa) an rubuta husaini shi ne fitilar shiriya jirgin tsira.

  An karbo daga husaini ibn ali(as) yace: na je wajen manzon Allah(s.a.w)  daidai lokacin da yake tareda ubayyu ibn ka’ab sai yace mini; sannu da zuwa lale da kai ya baban Abdullah ya adon sammai da kassai. Sai ubayyu ibn ka’ab yace masa ta kaka wani mutum zai kasance ya manzon Allah(s.a.w) adon sammai da kassai bayan kai, sai yace: na rantse da wanda ya da gaskiaya annabi lallai husaini ibn ali a sama ya fi girma cikin kasa, lallai rubutacce ne daga daman al’arshin Allah cewa: husaini shine fitilar shiriya jirgin tsira jagoran alheri da albarka ba tareda rauni ba, shine daukakar alfahari da lallai shi kogin ilimi makil, lallai Allah mai girmma da daukaka ya sanya zuriya tsarkakka cikin tsatsonsa  mai albarka tsarkakakke, hakika ya lakanta addu’o’I da wani mutum ba zai yi su ba face Allah ya tasheshi tareda shi. Zai kuma kasance mai cetonsa ranar kiyama  zai kuma yaye mas damuwarsa  ya biya masa  basukansa  ya saukake al’amarinsa ya bayyanar masa hanyarsa ya karfafeshi kan makiyinsa ba kuma zaim keta msa alfarmasa ba, sai ubayyu ibn ka’ab yace: wadannane addu’o’I ne ya anzon Allah(s.a.w) ? sai yace: yayinda ka kamala sallah kana tsugune sai kace: (ya Allah lallai ni ina rokonka don matsayin kalmarka da matsugunan al’a’arshinka da mazauna sammanka da annabwanka da manzanninka ka amsa mini lallai tsanani ya risknei daga lamrina  ina rokonka kayi salati ga muhammadu da iyalansa  ka sanya sauki daga abinda ya tsananta daga lamarina) lallai Allah mai girma da daukaka zai saukaka lamarinka zai buda kirjinka  zai lakanta maka Kalmar shahada lokacin da ranka zai fita ka bar duniya.

  Wannan hadisi mai albarka  yanada tsayi akwai ambaton sunaye imamai daga `ya`yan imam husaini(as) da addu’o’insu sai ka nenmi cikakken hadisin.

  Ya zo cikin kasa’is husainiyya na ayatollah jafar tusturi(rd) lallai an rubuta yabon husaini(as) da begensa a daman al’arshi

  (إنّ الحسین مصباح الهدی وسفینة النجاة)

  Lallai husaini fitilar shiriya ne jirgin tsira.

  Sai Allah ya bashi daga mafi girman halittunsa, daman al’arshinsa mai girma da wannan kyautar ubangiji  da karamar kyakkyawa wadda ta kasance daga kebantattun karamominsa tana yanayi mabanbanta sakamakon kebantar da ar’arshi take da shi daga sauran halittu.

  Sabaoda muke cewa:

  Da farko dai Allah ya baiwa imam husaini(as) inuwar ar’ashinsa domin ya sanya msa msa wani wuri da zai zauna cikinsa ranar kiyama tareda maziyartansa  da wanda sukai masa kuka  sai ya aiko musu matayensu  daga aljanna su zo su zabi majalisinsa  da zancensa

  Na biyu: lallai yayi masa kyauta da daman al’arshinsa  sai ya sanya shi matabbata gareshi cikin barzahunsa, lallai shi daga daman al’arshinsa yake hango mafadarsa da wanda ya shigo cikinsa.

  Na uku: ya kallon maziyartansa  da msu yi mas kuka zai nema musu gafara zai kuma tattuana da su zai roki kakansa da babansa da su nema musu gafara, tsakaninka da Allah shin kana ganin wanda annabi da yalansa tsarkaka suka nema masa gafara anya kuwa wani zai ragu ya wanzu gareshi ace an masa azaba da shi ranar kiyama?

  Na hudu: Allah ya bashi wani mahalli a saman al’arshi domin tattaunawa da maziyartansa, hakika ya zao cikin ba’arin kasha-kashen ziyararsa cewa zai kasance daga masu zance da Allah a saman al’arshinsa, lallai ala’arshi majalisin tattauna da maziyartansa, inuwarsa ga wanda zai tattauna da shi, sannan saman al’arshinsa mahallin tattaunawa da Allah.

  Na biyar: lallai Allah ya bashi inuwowin al’arshi wadda ta yankwane ta kwansare  sakamakon zubda jininsa ta yi kuma kuka kan hakan.

  Na shida: hakika ya bashi kwatankwacin al’arshi daga sinfofin mala’iku dake kewaye da kabarinsa  da yin dawafi.

  Na bakwai: akwai yanayi da matsayin da ya shallake wannan kai kace Allah y aba shi dukkanin al’arshin kacoka, domin idan ya kasance shi da  `dan’uwansa hassan almujtaba(as) sune adon al’arshin Allah to kowanne irin abu da kyawunsa da adonsa ake saninsa, da al’arshi za tai Magana da ta ce: lallai ni daga husaini nake, ita al’arshi samuwarta husaini sonta husaini hakan ya isar.

  Amma gameda abubuwan da suka kebantu da mahallin imam husaini(as) cikin barzahu lalli shi daga daman al’arshi yake hango wanda ya fada da wanda ya shiga ciki daga yake hango rundunarsa daga nan yake kalon maziyartansa shi yafi kowa saninsu da sunayensu da sunayen iyayensu da darajojinsu kowannensu  da matsayinsu wajen Allah, lallai shi yana kallon wanda yake masa kuka sai ya nemar masa gafara ya kuma roki babansa ali ibn abi dalib(as) ya nema msa gafara, ya kai mai yin kuka da mai sanya ai kuka saboda musiba da shahadar husaini shugaban shahidai  saboda musibar da ta samu ahlin gidansa da cin mutucin matansa da iyalansa da maida su fursunan yaki  da ka san abinda ubangiji ya tanadar maka daga lada kan yin hakan da farin cikinka ya shallake rakinka musamman cikin kebantuwar  muhalllin taruwa ranar kiyama. Ya zo cikin riwayoyi cewa: lallai imam yana da wan majalisi kebantacce da ke da wata kebanta shine cewa ahlin wannan majalisi daga masu kuka kan husaini da maziyartansa zasu ka sance masu debe haso da hira tareda husaini suna cikin aminci yayinda zamansu a wajensa za a kawo musu matayensu daga aljanna , lallai mu muna shaukinku sai kau da kai daga tafiya aljanna su zabi cigaba da hira da masoyinsu shugabansu majibancinsu  shugaban shahidai  uba ga `yantattu imam husaini(as) lallai majalisinsa a wannan lokaci yana cikin aljanna, sannan shi yanada wani matsaya ranar tashin bayi da ya kebantu da shi da yake wajabta girgizar dukkanin wanda aka tattaro Fatima (as) za ta gigice ta dinga shashshaka da kuka lokacin da zata ganshi ya taso babu kai a gangar jikinsa jijiyoyinsa suna kwararar da jini, bayanin hakan dalla-dalla yana muhallinsa kadai dai nayi ishara a jumlace kan  sirrika da abubuwan da suka kebanta da husaini (as) raina fansarsa. Cikin littafin mai suna(imam husaini fi arshillah) da (adwa’u ala sharh ziyaratu Ashura)  da (maktalul imam husaini. As) da (min malakuti nahdatu husainiyya) da (makalat fi imam husain.AS)  da (riyadul arifin fi ziyaratu Ashura) dukkaninsu an buga kuma an sanya su a sayit  haka cikin mausu’atul kubra risalatul islamiyya.

  Sai a koma a neme su. Daga karshe muna odiaya ga Allah ubangijin talikai