sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
 • Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
 • Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
 • Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
 • Shahadar Fatima Azzahra A.S
 • Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
 • Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Hassan Askari amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da wafatin Manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Rida (a.s
 • Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
 • Fara darasin Hauza a shekara 1442 tareda Assayid Adil-Alawi
 • Sirrin dawwama wani shiri ne daga Assayid Adil-Alawi da yake gudana cikin watan Muharram
 • Ganawar Samahatus Assayid Adil-Alawi da ba'arin `yan'uw adaga Hijaz
 • tsare-tsaren laccocin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Muharram Mai Alfarma shekara 1442
 • Bukukuwan kwanaki goma daga watan Muharram mai Alfarma shekara 1442
 • Watan Muharram Mai Alfarma shekara 1442 wata ne na bakin ciki da kuka
 • sababun labare

  Taron cibiyoyi masu da kula ziyarar arba’in

  Taron cibiyoyi masu da kula ziyarar arba’in


  taron cibiyoyi da suke kula da ziyarar arba’in

  Cibiyar warisul anbiya ta shirya taro don karatu na musammam kan motsar da harkar husainiyyya wannan mu’assasa da muka ambata a sama tana karkashin kulawar mu’asassar kabarin imam husaini (as) tsarkakakke

  Wannan taro ya kasance a ranar alhamis wanda yayi daidai da 19/12/1395 hijra tafiyar rana (shamsiyya) wanda yayi daidai ga (9/3/217) miladiyya taron ya kasance a dakin taron na warisul anbiya cikin birnin qum mai tsarki.

  Bayan karatun kur’ani mai hikima sai shugaban mu’asassa shaik rafid tamimi ya dan bayyana wasu kalmomi da suka tattaro abubuwa kamar haka:

  Takaitaccen bayani kan bangarorin mu’assasa da ayyukanta.

  Nuna majigi don bayyanarwa mahalarta ayyukan mu’asassa ta yaddda sun samu damar buga rubutuka 45 daga ayyukan husainiyya, sannan sun samu nasarar shirya taruka 32 haka sun shirya mu’utamar karo hudu, bugu da kari sun shirya daurori har guda bakwai domin ilmantarwa da sakafantarwa.

   Hakama sun kawo da Ambato muhimman hadafin taron wadanda sune:

  Bada dama ga wasu da budewar kirji, sadar da zumunci tsakanin cibiyoyi da mu’assosi da suke kula da ziyarar arba’in.

  Sanin ayyukan da nishadodi da wadannan cibiyoyi a fagen hidimtawa ziyarar arba’in

  Magance matsaloli da kalubale da cikin bikin taron ziyarar araba’in gwargwadon iko.

  Kai kawo don shirya mu’utamar na kasashe daban daban a cikin garin karbala tsarkakka.

  Samarda wasu masu sadar da alaka masu cin gashin kansu ga cibiyoyin da ke kula da ziyarar arba’in.

  Bayan bayani daga shugaban mu’assasa sai kuma daya daga cikin membobinta ya ta shi ya fara bayani wato ayatollah sayyid adil alawi (h) yana mai nuni zuwa ga muhimmancin mu’assasa da ke hidima kan ziyarar arba’in, yana mai la’akari da cewa yin hakan  hidimtawa imam husaini (as) ne da kuma cewa lallai iata hidima da aiki nagari sun shardantu da tsarkake niyya da rike amana.

  Bayan y agama sai wakilin mu’assar ahlul baiti shaik Muhammad hassuni ya yi huduba ya na mai karfafa larura amfani da da wannan ziyara ta arvba’in cikin fagen isar da sako kamar yadda ya karfafa larura kan mai da hankali da Karin haske kan gwagwarmayar safar (1397/1977) ta yadda gwamnatin zalunci da kama karya ta saddam ta hana zuwa ziyarar arba’in da ake tatttaki a kafa sai shi’a sukai watsi da wannan hani na gwamnatin kama karya suka kwarara kan hanya suna tattakin arba’in lamarin da yakai ga kama wasunsu da zabtar da su da kasha wani adadi daga cikinsu, kamar ya karfafa muhimmancin cigaba da shirya zaman a daurori da su kebanci wannan ziyara. Da kuma samar da lajana da za ta tattaro wakilan cibiyoyi masu hidima ga ziyarar arba’in shaik mas’ud  haji Ibrahim  wakilin taron arba’in da mas’ul din sakafa  cikin jahohi da kungiyoyi da suke hidimtawa cikin taron arba’in ya bayyana ayyukansu a takaice ya kuma yi bayani da karaffa larurar datarwa cikin al’adu tsakankanin al’ummar iraki da al’ummar iran da kuma amfani da kafofin sadarwa  wajen yada sakafar ziyarar arba’in.

  Sannan dokta Muhammad sa’id ya wakilci cibiyar bincike da dandakewa cikin lamarin hajji da ziayara ta yadda ya gabatr da ayyukansu kamar yadda yayi bayani gabobin karfinsu da rauni cikin wannan ziyara ya kuma ba da sharawa yadda za a magance su.

  Haka sayyid ali rida husaini ya wakilci mu’asssasar majma’u ahlul baiti alami (as) yayi takaitacce bayanin ayyukansu ya kuma gabatar da shawara da a gayara gabobin raunin da ake samu a kowacce shekara  bayan ziyarar arba’in domin samun dmar cimma manufar da ake son cimma cikin wannan ziyara

  Sai kuma wakilin jami’atul almustafa shaik husaini muradi daulat abadi shima ya tashi ya gabatr da takaitaccen bayani kan ayyukan jami’ar ya kuma bayyana cewa karkashin wannan ziayara an samu damar tattaro dukkanin shubuhohi da kuma bugar kirji don magance su, kamar yadda akayi aikin tarjama muhimman ilimai  da yaruka daban-daban , haka yayi ishara kan shirya taro kasa da kasa mai take (fadaka) da aka yi cikin tsarin wake wanda da anayinsa iya mahallai bai kai ga kasa da kasa ta yadda yanzu kusan kasashe 80 suka yi tarayya

  Bayan shi sai wakiltar masallacin jamkaran shugaban dukkanin alakoki wato sayyid mahadi hashimi shima ya tashi ya gabatar da bayanin kan tarayyar da ayyukan maukibobi, ya kuma bada shawara kan samar da lajana ta kwararru cikin ayyuakn ziyarar araba’in.

  Sai kuma wakilin hubbaren sayyida ma’asuma kuma mai taimakawa cikin ayyukan sakafar hubbaren wato shaik safar fallahi shima ya tashi ya bayyana ayyuaknsu cikin maukibin husainiya.

  Hakika wannan babban taro ya tattaro manya manyan malaman hauza daga cikinsu akwai: samahatul sayyid jawad shaharistani wakilin ayatollah al’uzma sayyida sisatani (dz) da kuma shugaban ofishin ayatollah sayyid hakim taba-taba’I wato dansa sayyid riyad hakim(dz) hakama wakilin ofishin ayatollah shaik safi gulfaigani (dz) ya halarta, sai kua wakilin ayatollah shaik Muhammad lankalrani da wakilin ayatollah shaik mulim dawari da wakilin allama shaik Muhammad rida mamakani, da said Muhammad taki tabataba’I, allama sayyid ali mar’ashi, allama shaik sa’aid barujudi, allama shaik mahadi baharani, allama abdul husaini muhaddis, allama sayyid jawad shibar da wasunsu daga malaman hauza da manya manyan mazajen ilimi.

  Taron ya fitar da shawarwari da wasiyyoyi kamar haka:

  Samar da rabida da zat tattaro cibiyoyi da suke aiki a ziyarar araba’in.

  Shirya zaman daurori ga wadannan cibiyoyi.

  Shirya taron mu’utamar  na kasashe da ya kebanci wannan lamari a cikin garin karbala.

  Yin aiki domin kusanto da al’adun ingantattu tsakanin mutanen iraki da iran.

  Amfani da kafofin sadarwa cikin yada sakafar ziyarar arba’in.

  Aiki domin tsaruwa dawwamamme tsakanin mas’ulan irakawa da na iraniyawa.

  Maida hankali cikin gyara da daidaita gabobin rauni  kowacce shekara bayan kammala ziyarar arba’in.

  Amfanuwa da wannan ziyara wajen tablig da isar da sakon ahlul baiti(as) da yada sakafar addini husainiyya