sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Labarun da ba tsammani

MUNA TAYA DAUKACIN AL'UMMAR MUSULMI MURNAR HAIHUWAR SAYYADA FATIMA MA'ASUMA AMINCIN ALLAH YA TABBATA GARETA

 

 

MUNA TAYA  AL'UMMAR MUSULMI MURNAR HAIHUWAR SAYYADA FATIMA MA’ASUMA AMINCIN Allah ya tabbata garetaTsokaci kan rayuwar sayyada Fatima ma’asuma (as) tareda alkalamin samahatus asyyid adil alawi

Hakika sayyada fatima ma’asuma ta shahara ta kuma fifita cikin `ya`yan imam musa alkazim ibn jafar (as) wanda adadin `ya`yansa suka haura talatin, fitattu biyu daga `ya`yansa sune: imam aliyu rida (as) wanda ya gaji mahaifinsa alkazim (as) da nassi daga Allah mai giram da daukaka da kuma nasabtawa daga manzonsa (s.a.w) imam rida ya yi shahada a garin kurasan ta hanyar shan gubar da sarkin abbasiyawa mamun (l.a) an kuma binne imam rida (as) cikin wannan gari.

An haifi Fatima ma’asuma  a garin madinatu munawarra a farkon watan zul’ka’ada hijira na da shekaru 173 ta kuma bar duniya a birnin qum mai tsarki a goma ga watan rabi’u sani hijira na da shekaru 201 lokacin tanada shekaru 28 a duniya  

ta taso ta girma cikin imani da takawa cikin gidan isma da tsarki ta kuma samu wani matsayi da sha’ani daga matsaye a wurin Allah har sai da ya kai ga mahaifinta kansa na fansarta da ransa ya fada karo uku cikin wata hikaya da yake bada labari gameda ilimin sayyada ma’asuma (as) da hikimarta daga hikimomin da Allah ya bata a wannan lokaci ba ta ma kai shekarun takalifi ba na shari’a.

hakika fatima ma’asuma (as) ta kasance kamar gwaggwanta sayyada Zainab ma’ana malamar da bata da malami fahimtatta wadda wani bai fahimtar da ita ba, ta kwankwasa kofofin ilimi ta debe asalansa daga babanta imam musa alkazim (as) haka daga `dan’uwanta  imam rida (as) daga kowacce kofa kofofi na budewa gareta kamar misalin kakanta sarkin muminai aliyu ibn abi dalib (as) lallai yana daga kofofin ilimin Allah da suke biyo ilimin wahayi da ya kebantu da annabawa. Lallai iliminta yana daga ilimin ladunni da ya kebantu da ahalinsa.

Sayyada Fatima ma’asuma (as) ta kasance cikin shekaru hudu na  rayuwarta lokacin da wasu jama’a daga shi’ar babanta suka zo suna neman amsar tambayoyin addini, sai suka kwankwasa kofar imam musa alkazim (as) sai babar imam rida (as) ta ce musu ya fita wajen madina ba ya nan, sai al’amari ya tsananta garesu ta yaya za su koma garuruwansu ba tareda samun amsoshsin tambayarsu ba, sai babar rida (as) ta basu labari da cewa akwai sayyada Fatima ma’asuma (as) cikin gida, sai suka nemi zini shiga cikin gidan suka gabatarwa sayyada Fatima ma’asuma (as) tambayoyinsu saboda su suna da yakini kan cewa kananan yaran da ke cikin wannan gida tsarkakku ne basu kazantuwa kuma garwashin wuta ne da bai takuwa lallai kuma sun sha ilimi matukar sha, sai ta basu amsa a rubuce, sa’ilin fitowarsu daga madina sai sukai kacibus da imaminsu suka bashi labari kan amsar da ta basu, sai imam kazim (as) ya ce: ku bani amsoshin sai ya karba ya duba  sai karo uku ya ce:  (babanta fansarta) sannan ya ce: lallai ita hikma ce daga hikimomin Allah – an nakalto wannan kissa a ma’anance.

Ya yinda takai shekaru goma mahaifinta imam kazim (as) ya yi wafati a gidan kason harun rashid dagutun zamaninsa an binne imam alkazim (as) a makabartun kuraishawa wadda akafi sani da sunan kazimiyya tsarkakka.

 imam rida (as) ya dauki nauyin kulawa da ita, kwanaki suka shuda mulki ya koma hannun mamun abbasi, mamun ya nufi kashe wutar yunkuri da juyin- juya halin kishiyantar hukumomi azzalumai da alawiyya ke kokarin samarwa lokaci zuwa lokaci a geffan garuruwan muslunci a wannan zamani, da kuma wasu dalilai da suka tilasa imam rida (as) karba da yarda da nadinsa a matsayin mai jiran gado bayan sarki mamu, idan kuma yaki yarda da karbar wannan matsayi mamun zai kashe shi, sarki mamun ya kira imam rida (as) zuwa helkwatarsa garin marwa da ke kurasan domin imam (as) ya kasance karkashin ikonsa da kulawarsa, sai imam (as) cikin tilashi da rashin zabi ya karbi wannan nadin matsayi na mai jiran gado alhalin zuciyarsa ba ta so, ya taso ya nufi garin marwa, sai dai cewa sakamakon wasu kebantatun dalilai sayyada Fatima ma’asuma (as) ba ta raka dan’uwanta imam rida (as) zuwa marwa cikinn wannan safara ta shi mai tsananin wahala wadda babu jada baya daga gareta,

Hakika soyayya da kauna tsakanin imam rida (as) da kanwarsa sayyada Fatima ma’asuma ta kasance a bar buga misali, kamar yadda ta kasance tsakanin imam hassan da `dan’uwansa imam husaini (as)  da kanwarsu zainabul kubra (as).

Bayan shudewar wani lokaci cikin wannan rabuwa mai radadi, sai sayyada Fatima ma’asuma (as) ta yanke shawarar riskar imamin zamaninta imam rida (as) domin ta zamanto kamar gwaggwonta sayyada Zainab (as) cikin daukar nauyi  da shelanta yakar dagutai da jabberai misalin mamun abbasi, domin kuma ta tona asirin abbasiyawa kamar sayyada Zainab (as) ta tonawa azzaluman sarakunan umayyawa gabaninta .

Sayyada Fatima ma’asuma (as) ta fito daga madina tana tareda mutane hudu daga `yan’uwannta da wani adadi daga `ya`yansu da hadimai da wasu adadi daga masoya cikin wannan hijira da tayi zuwa ga Allah da manzonsa, sai dai cewa wannan ayari da suke cike da shaukin ganin waliyinsu masoyinsu sunyi kacibus da wasu mahara daga garin sawa da mutanen garin sun kasance makiya ahlul-baiti masu tsananin ta’asuubanci kan abbasiyawa suka afka musu wadanda su wannan mahara fadar sarki mamun ce ta tana d su don akwao cikas ga wannan safara.

Cikin wannan hari ne aka kashe dukkanin `yan’uwan imam rida (as) da mafi yawan mazajen da ke cikin wannan ayari na Fatima ma’asuma, sakamakon wannan wannan ta’addanci mai sanya radadi ance an sanyawa Fatima ma’asuma (as) guba  da ya kai ta da yin rashin lafiya mai tsanani wadda ta kai ga ta gaza cigaba da yin tafiyar zuwa garin marwa, ta riski cewa ita tana kusa da shiga garin qum mai tsarki, dama babanta da`dan’uwanta tuntuni sun bata labari cewa garin qum cibiya ce muhimmiya daga cibiyoyin shi’a  kakanninta tsarkaka, sai ta yanke shawarar shiga garin qum sai ayarin suka sauya hanyarsu zuwa hanyar qum, cikin rana ta 23 daga rabi’u auwal  a shaekara ta 201 ga hijira Fatima ma’asuma ta shiga birnin qum mai tsarki, labarin shigarta birnin qum ya haifar da kebantacce tasiri mai girma cikin zukatan ahalin garin, farin ciki da murna suka mamaye baki dayan sasannin garin qum, mutane masu tarin yawa suka fito tarbarta cikin maukubi mai girma da kwarjini, malamin hadisi mai girma musa ibn kazraj ash’ari yana ja musu  gaba ya kasance cikin manyan mutane da manyan malamai masana hadisi sai musa ibn kazraj ya kama akalar taguwar Sayyad ma’asuma (as) mutane suka kewaye inda take tsaye kamar yarda kawaron malam buda mana littafi filfilo (butter fly) ke kewaye hasken kyandir.

 musa ash’ari ya nemi sauka gidansa don shirya mata liyafa, sai ta amsa bukatarsa ta sauka daki wanda aka saninsa bayan wafatinta da (baitur nur ) har yanzu wannan gida bai gushe ba  masoya masu ziyara suna  ziyartarsa suna neman tabarruki da numfashinta tsarkakka.

Sayyada Fatima ma’asuma ta wanzu cikin wannan daki har tsawon kwana goma sha bakwai tana fama da ciwo har zuwa lokacin da ta ce ga gidanku ta koma ga Allah, an raka gawarta tsarkakka cikin jimami  ya zuwa makwancinta da ke dausayin babilan.

A karni na uku `yar Zainab `yar imam jawad an binneta ta tareda da ita kan kabarinta akwai kubba, kamar yadda aka binne mutum biyar daga `ya`yan gidan annabta biyu kuma daga jikokin imamai tsarkaka, kamar yadda aka ambaci hakan cikin littafai da sukai bayani filla-filla na kuma yi ishara cikin littafai na biyu wato (shahida arwahu) da (annujumul mutanasira)  kana iya komawa don neman karion bayani.

Fatima diyar imam kazim cikin riwayoyin imamai ma’asumai ::   

ـ قال الإمام الصادق  7: «ألا ان لله حرماً وهو مكّة ، ألا إنّ لرسول الله حرماً وهو المدينة ، ألا وان لأميرالمؤمنين حرماً وهو الكوفة ألا وان قم الكوفة الصغيرة ، ألا ان للجنة ثمانية أبواب ثلاثة منها إلى قم ، تقبض فيها امرأة من ولدي اسمها فاطمة بنت موسى ، وتدخل بشفاعتها شيعتي الجنة بأجمعهم

 Imam sadik (as) ya ce: ku saurara lallai Allah yanada wani harami wanda shi ne garin makka, lallai manzon Allah yanada wani harami wanda shi ne garin madina, sannan ku saurara lallai sarkin muminai ali yanada wani harami wanda shi ne birnin kufa ku saurara lallai qum shi ne karamar kufa, ku saurara lallai aljanna tanada kofofi takwas uku cikinsu sun tuke ga birnin qum, za a karbi ran wata mata  daga `ya`yana sunanta  Fatima diyar musa alkazim `yan shi’ata za su shiga aljanna da cetonta baki dayansu.

ـ قال الصادق  7: «من زارها عارفاً بحقّها فله الجنة

Imam sadik (as) ya ce: duk wanda ya ziyarceta yana mai sanin hakkinta yanada aljanna.

 . 3ـ قال الإمام الرضا 7: «من زارها فله الجنة ، وفي رواية : كان كمن زارني »

Imam rida (as) ya ce: duk wanda ya ziyarci kabarin gwaggona daidai yake da wanda ya ziyarce ni.

ـ قال الإمام الجواد 7: «من زار قبر عمتي بقم فله الجنة. »

Imam jawad (as) yan cewa: duk wanda ya ziyarci kabarin gwaggona a birnin qum yanada aljanna.

Dukkaniin wadannan hadisai suna bada labarin irin girmanta da girmamar mukaminta madaukaki a wajen mahalicci da wajen halittu da ahlul-baiti.