sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
 • Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
 • Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
 • Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
 • Shahadar Fatima Azzahra A.S
 • Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
 • Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Hassan Askari amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da wafatin Manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Rida (a.s
 • Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
 • Fara darasin Hauza a shekara 1442 tareda Assayid Adil-Alawi
 • Sirrin dawwama wani shiri ne daga Assayid Adil-Alawi da yake gudana cikin watan Muharram
 • Ganawar Samahatus Assayid Adil-Alawi da ba'arin `yan'uw adaga Hijaz
 • tsare-tsaren laccocin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Muharram Mai Alfarma shekara 1442
 • Bukukuwan kwanaki goma daga watan Muharram mai Alfarma shekara 1442
 • Watan Muharram Mai Alfarma shekara 1442 wata ne na bakin ciki da kuka
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Bakir (as)
 • sababun labare

  Labarun da ba tsammani

  Muna taya daukacin al’ummar musulmi ta’aziyyar tunawa da shahadar imam jawad (as)


  Muna taya daukacin al’ummar musulmi ta’aziyyar tunawa da shahadar imam jawad (as)  Bismillahi rahmanir Rahim

  Shahadar imam jawad amincin Allah ya kara tabbata gare shi

  Daga cikin abin ishara ga sabubban cin amfanin da halifan abbasiyawa mu’utasim da ya yi da ummu fadal matar imam jawad (as) da yadda ya zugata kan aikata kisan gillar ga imam jawad (as) shi ne abin da  aka rawaito daga tsananin kishinta zamanin mahaifinta da yadda ta shiga cikin rigimar kisan imam (as) saboda

  Abu nasar hamdani yana cewa: 

  «حدثتني حكيمة بنت محمّد بن عليّ بن موسى بن جعفر عمّة أبي محمد الحسن بن علي (عليهما السلام).

  Hakima `yar Muhammad ibn ali ibn musa ibn jafar gwaggwon baban Muhammad Hassan ibn ali (as) ta zantar da ni

  قالت: لمّا مات محمّد بن عليّ الرّضا (عليه السلام) أتيت زوجته اُم عيسى بنت المأمون فعزّيتها فوجدتها شديدة الحزن والجزع عليه تقتل نفسها بالبكاء والعويل، فخفت عليها ان تتصدّع مرارتها فبينما نحن في حديثه وكرمه ووصف خُلقه وما اعطاه الله تعالى من الشّرف والاخلاص ومَنَحَهُ من العزّ والكرامة، اذ قالت امّ عيسى: الا اخبرك عنه بشيء عجيب وأمر جليل فوق الوصف والمقدار؟ قلت: وما ذاك؟

  Tace: lokacin da Muhammad ibn ali rida (as) ya mutu na je wajen matarsa ummu isa `yar mamun sai nayi mata ta’aziyya sai na same ta tana cikin matsanancin bakin ciki da raki kan rasuwarsa tana neman halaka kanta da kuka a kansa, sai na ji mata tsoran kada rawancinta  ta tsage ya yinda muke cikin tattaunawa kansa da karamcinsa da siffanta halayensa da abin da  Allah madaukaki ya bashi daga girma da iklasi da abin da  ya yi masa kyauta daga daukaka da karama, sai kwatsam ummu isa tace: bana baki labarin wani abu mai ban mamaki mai girma da yake saman siffantawa ba da mikdari? Sai nace menene wannan abun?

  قالت: كنت أغار عليه كثيراً وأراقبه ابداً وربما يسمعني الكلام فاشكو ذلك الى أبي فيقول يابنيّة احتمليه فانّه بضعة من رسول الله (صلى الله عليه وآله)، فبينما انا جالسة ذات يوم اذ دخلت عليّ جارية فسلّمت، فقلت: من انت؟ فقالت: انا جارية من ولد عمّار بن ياسر وانا زوجة أبي جعفر محمّد بن عليّ الرضا (عليه السلام) زوجك.

  Na kasance ina kishi kansa mai yawa ina sanya masa ido ko yaushe sau da yawa yana jiyar da ni wani zance sai na kai kukan haka wajen babana sai ya ce yake `yar karamar `yata ki jure masa lallai shi tsokace daga manzon Allah (s.a.w) lokacin da na ke zaune wata rana kawai sai ga wata mata ta shigo wajena sai tayi sallama, sai nace wacece ke? Sai tace ni baiwa ce daga `ya`yan ammar yasir ni matar baban jafar ce muhammad ibn ali rida (as) mijinki.

  فدخلني من الغيرة ما لا اقدر على احتمال ذلك هممت ان اخرج واسيح في البلاد وكاد الشيطان ان يحملني على الإساءة اليها، فكظمت غيظي واحسنت رفدها وكسوتها، فلمّا خرجت من عندي المرأة نهضت ودخلت على أبي وأخبرته بالخبر وكان سكراناً لا يعقل. فقال: ياغلام عليّ بالسّيف، فاتى به، فركب وقال: والله لاقتلنّه فلمّا رايت ذلك قلت: انّا لله وانّا اليه راجعون، ما صنعت بنفسي وبزوجي وجعلت ألطم حرّ وجهي، فدخل عليه والدي وما زال يضربه بالسيف حتى قطعه.

  Sai wani irin kishi ya kamani wanda na kasa jure ma shi har na himmatu da na fita inyi yawo cikin gari, shaidan ya kusa sani in munana mata, sai na danne fushina na kyauatta mata na tufatar da ita, ya yin da ta fita daga wurina sai na tashi na je wajen babana na bashi labari a lokacin yana buge yana cikin maye baya cikin hankalinsa, sai ya ce ya kai wannan hadimi kawo mini takobi, sai ya kawo masa, sai ya hau abin hawa ya ce wallahi lallai sai na kashe shi, ya yin da na ga haka sai nace: inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un, me na aikatawa kaina da mijina, sai na kama dukan fuskata bai gushe ba yana sarnsa da takobi har sai da ya yi gunduwa-gunduwa da shi   

  ثم خرج من عنده وخرجت هاربة من خلفه فلم ارقد ليلتي فلمّا ارتفع النّهار اتيت أبي فقلت: اتدري ما صنعت البارحة؟ قال: وما صنعتُ؟ قلت: قتلتَ ابن الرّضا (عليه السلام)، فبرق عينه وغشي عليه ثم افاق بعد حين وقال: ويلك ما تقولين؟ قلت: نعم والله يا ابه دخلت عليه ولم تزل تضربه بالسّيف حتى قتلته، فاضطرب من ذلك اضطراباً شديداً وقال: عليّ بياسر الخادم فجاء ياسر.

  Sannan ya fito daga wajensa ni ma nafito ina gudu daga bayansa, banyi bacci ba wannan dare ya yin da gari ya waye rana ta `dago, sai naje wajen babana na ce masa kasan abin da  ka aikata kuwa jiya da daddare? Ya ce me na aikata? nace ka kashe `dan rida (as) sai idansa ya yi walkiya take ya suma sannan bayan `dan lokaci ya farfado ya ce: bominki me kike cewa ne? Sai nace; na’am wallahi ya babana kaje wajensa baka gushe ba kana ta saransa da takobi har sai da ka kashe shi, sai ya girgiza  daga hakan girgiza mai tsanani ya ce: ku zo mini da yasir hadimi sai yasir ya zo 

  فنظر اليه المأمون وقال: ويلك ما هذا الّذي تقول هذه ابنتي قال: صدقَتْ ياامير المؤمنين فضرب بيده على صدره وخدّه، وقال: انّا لله وانّا اليه راجعون هلكنا بالله وعطبنا وافتضحنا الى آخر الابد ويلك ياياسر فانظر ما الخبر والقصة عنه(عليه السلام)؟ وعجّل عليّ بالخبر فان نفسي تكاد ان تخرج السّاعة فخرج ياسر وانا ألطم حرّ وجهي، فما كان ياسر من ان رجع، فقال: البشرى ياامير المؤمنين. قال: لك البشرى فما عندك؟

  Sai mamun abbasi ya kalle shi ya ce: bominka me wannan `yar tawa take cewa ne, sai ya ce: gaskiya ta fada ya amirul muminina  sai ya doki kirjinsa da kuncinsa da hannunsa. ya ce: inna lillahi wa inna ilaihi raji’un mun halaka mun tozarta har abada, ya yasair jeka ka duba ka samu labarin da yake ciki ku gaggauta zo mini da labari. Lallai raina na neman fita a wannan lokaci, sai yasir ya fita ni kuma ina ta marin fuskata, yasir bai bata lokaci sai gashi ya dawo, ya ce ya mairul muminin bushara gareka, sai ya ce bushara gareka dame ka zo?

  قال ياسر: دخلت عليه فاذا هو جالس وعليه قميص ودواج وهو يستاك فسلّمت عليه وقلت: ياابن رسول الله اُحب أن تهب لي قميصك هذا اصلّي فيه واتبرك به، وانما اردت ان انظر اليه والى جسده هل به اثر السّيف فوالله كأنّه العاج الّذي مسّه صفرة ما به اثر. فبكى المأمون طويلاً وقال: ما بقى مع هذا شيء إنّ هذا لعبرة للأوّلين والآخرين.

  Yasir ya ce: na shiga wajensa sai na same shi a zaune yana sanye da riga tufafi kakkaura yana asuwaki sai nayi masa sallama na ce: ya `dan manzon Allah ina son ka bani rigar nan taka inyi salla da ita ina nemi tabarruki da ita, kadai dai nayi nufin in kalle shi in duba jikinsa shin ko akwai wata alamar saran takobi, wallahi kace hauran giwa ne wanda turare ya shafe shi babu wata alama a jikinsa, sai mamun ya fashe da kuka tsawon lokaci ya ce: babu abin da  ya ragewa wannan tabbas wannan abin lura da fadaka ne ga na farko da na karshe.

  وقال: ياياسر امّا ركوبي اليه واخذي السّيف ودخولي عليه فاني ذاكر له وخروجي عنه فلست اذكر شيئاً غيره ولا اذكر ايضاً انصرافي الى مجلسي فكيف كان امري وذهابي اليه، لعن الله هذه الابنة لعناً وبيلاً، تقدّم اليها وقل لها يقول لك ابوك والله لئن جئتني بعد هذا اليوم شكوت او خرجت بغير اذنه لانتقمنّ له منك.

  Mamun ya ce: ya yasir amma afka masa da nayi da dauko takobi da shiga ta wajensa lallai duk ina iya tunawa da fitowa ta daga wurinsa wa ba na iya tuna komai bayansu haka ma bana iya tuna dawowa ta majalisina yaya lamarina ya kasance da zuwana wajensa, Allah ya tsinewa wannan `ya tsinuwa mai yawa. Jeka ka ce mata babanki yana ce miki wallahi idan kika kara zuwa bayan wannan rana kika kawo kara ko kuma kika fito ba tare da izininsa ba lallai zan dau fansa kanki.

  ثم سر الى ابن الرّضا وابلغه عني السّلام واحمل اليه عشرين الف دينار وقدّم اليه الشهري الّذي ركبته البارحة، ثم أمر بعد ذلك الهاشميّين ان يدخلوا عليه بالسّلام ويسلّموا عليه. قال ياسر: فأمرت لهم بذلك ودخلت انا ايضاً معهم وسلّمت عليه وابلغت التّسليم ووضعت المال بين يديه وعرضت الشّهري عليه فنظر اليه ساعة ثم تبسّم.

  Sannan kaje wajen `dan imam rida ka isar mini da gaisuwa ka kai masa dinare dubu ishirin ka kai masa abin hawana da na hau jiya, sannnan ya umarci hashimawa su je wajensa da aminci suyi masa sallama, yasir ya ce: sai na umarce su da hakan sai ni naje tare da na yi masa sallama na isar da sallama na aje kudaden a gabansa na bijiro masa da abin hawan sai ya `dan kalle shi ya yi murmusi.

  فقال(عليه السلام): ياياسر هكذا كان العهد بيننا وبينه حتّى يهجم علي، اما علم ان لي ناصراً وحاجزاً يحجز بيني وبينه. فقلت: ياسيّدي ياابن رسول الله دع عنك هذا العتاب واصفح، والله وحق جدّك رسول الله (صلى الله عليه وآله) ما كان يعقل شيئاًمن امره وما علم اين هو من ارض الله وقد نذر لله نذراً صادقاً وحلف ان لا يسكر بعد ذلك ابداً، فان ذلك من حبائل الشّيطان، فاذا انت ياابن رسول الله اتيته فلا تذكر له شيئاً ولا تعاتبه على ما كان منه.

  Ya ce haka alkawari dama ya kasance tsakaninmu da shi da har zai kawo mana hari, ashe bai san cewa muna da mai taimako da ke katange tsakaninmu da shi ba, sai nace ya shugabana ya `dan manzon Allah ka bar wannan zargi kayi afuwa, wallahi na rantse da hakkin kakanka manzon Allah (s.a.w) bai kasance ya na gane komai ba daga lamarinsa bai ma san inda yake ba a kasar Allah hakika ya yi bakance bakance na gaskiya ya kuma ranste ba zai kara shan giya ba har abada bayan wannan, tabbas hakan na daga tarkunan shaidani, idan kai ya `dan manzon Allah kaje wajensa ka da ma ka ambaci komai ka da ka zarge shi bisa abin da  ya faru daga gare shi.

  فقال (عليه السلام): هكذا كان عزمي ورأيي والله، ثم دعا بثيابه ولبس ونهض وقام معه الناس اجمعون حتى دخل على المأمون فلمّا رآه قام اليه وضمّه الى صدره ورحّب به ولم يأذن لأحد في الدخول عليه ولم يزل يحدّثه ويستأمره، فلمّا انقضى ذلك قال أبو جعفر محمّد بن علي الرّضا (عليه السلام): «يا أمير المؤمنين»، قال: لبيّك وسعديك. قال: «لك عندي نصيحة فاقبلها».

  Sai imam (as) ya ce; shi ne abin da  dama nayi azamar yi shi ne kuma ra’ayi na wallahi, sai ya yi umarni a kawo masa kayansa ya sanya ya yunkura mutane suka tashi tare da shi baki daya ya tafi har sai da ya tuke wajen mamun ya yinda ya ganshi sai ya tashi ya jawo kirijinsa ya rungume shi ya yi maraba da lale da shi, baiwa kowa izinin shiga ba wajensa bai gushe ba yana tattauna da imam yana neman umarninsa, ya yinda ya kare sai baban jafar muhammad ibn aliyu rida ya ce: ya amirul muminina sai ya ce: labbaika wa sa’adaika, ina da wata nasiha da zan baka ka karbeta.

  قال المأمون: بالحمد والشكر فما ذاك ياابن رسول الله؟

  قال(عليه السلام): احبّ لك ان لا تخرج باللّيل فإني لا آمن عليك من هذا الخلق المنكوس وعندي عقد تحصّن به نفسك وتحرّز به من الشرور والبلايا والمكاره والآفات والعاهات، كما انقذني الله منك البارحة ولو لقيت به جيوش الرّوم والتّرك واجتمع عليك وعلى غلبتك اهل الأرض جميعاً ماتهيّأ لهم منك شيء بإذن الله الجبّار. وان احببت بعثت به اليك لتحترز به من جميع ما ذكرت لك. قال: نعم، فاكتب ذلك بخطّك وابعثه اليّ، قال: نعم.

  Sai mamun ya ce: tare da hamdala da godiya tana ina ya `dan manzon Allah? Sai imam ya ce: ina so maka kada ka fito da daddare lallai ni bana amintar maka daga wannan halittar nakasassa ina da wata laya da zaka iya kare kanka da ita ka yi tsari daga sharruka da bala’o’i da makirce-makirce da aibobi da cutuka, kamar yadda Allah ya tseratar da ni daga gareka daren jiya, da zak hadu da sojojin rumawa da turkawa da ita suka hadu kanka kan galaba kanka baki dayan mutane kasa ba zasu damar taba ka da komai da izinin Allah mai fin karfi. Idan kana so zan aiko maka da ita domin ka yi kariya da shi daga dukkanin abin da  na gaya maka, sai ya ce: na’am ka rubuta hakan da rubutunka ka aiko mini, ya ce: na’am.

  قال ياسر: فلمّا اصبح أبو جعفر (عليه السلام) بعث اليّ فدعاني فلمّا صرت اليه وجلست بين يديه دعا برقّ ظبي من ارض تهامة ثم كتب بخطّه هذا العقد.

  ثم قال(عليه السلام): ياياسر احمل هذا الى امير المومنين وقل له: حتى يصاغ له قصبة من فضّة منقوش عليها ما اذكره بعده فإذا اراد شدّه على عضده فليشدّه على عضده الأيمن وليتوضّأ وضوءاً حسناً سابغاً وليصل اربع ركعات يقرأ في كلّ ركعة: فاتحة الكتاب مرّة وسبع مرّات: آية الكرسي وسبع مرات: شهد الله وسبع مرّات والشمس وضحاها وسبع مرّات: واللّيل اذا يغشى وسبع مرّات: قل هو الله احد.

  Ya yinda baban jafar ya wayi gari sai ya aiko mini ya kirani ya yinda na je wajensa na zauna gabansa sai ya yi umarni da a zo masa da fatar barewa daga kasar tihama sannan ya rubuta wannan laya da hannunsa. sannan ya ce: ya yasir dauki wannan ka kaiwa amirul muminina ka ce masa a kera masa karan azurfa ya kasance an zana abin da  na rubuta bayansa idan yana son daura shi a dantsensa yan iya daurawa a dantsensa na dama ya yi alwala mai kyawu ya kyautata ya yi salla raka’a hudu cikin kowacce raka’a ya karanta fatiha kafa bakwai da wallaili iza yagsha kafa bakwai da kulhuwallahu ahad.

  فاذا فرغ منها فليشدّه على عضده الايمن عند الشّدائد والنوائب يسلم بحول الله وقوته من كلّ شيء يخافه ويحذره وينبغي ان لا يكون طلوع القمر في برج العقرب ولو انه غزى اهل الرّوم وملكهم لغلبهم باذن الله وبركة هذا الحرز.

  Idan ya gama ya daura a dantsensa na dama lokacin musibu masu tsanani da masu mayewa zai kubuta da karfin tsimin Allah da karfinsa daga dukkanin wani abu yake jin tsoro yake razana shiya kamata kada hudowar wata ya kasance cikin burujin akrabu, da zai yaki mutanen rum da mulkinsu da zai galaba kansu da izinin Allah da kuma albarkacinb wannan hirzi kariya.

  وروي انه لمّا سمع المأمون من أبي جعفر في أمر هذا الحرز هذه الصفات كلّها غزا اهل الرّوم فنصره الله تعالى عليهم ومنح منهم من المغنم ما شاء الله ولم يفارق هذا الحرز عند كلّ غزاة ومحاربة وكان ينصره الله عزوجلّ بفضله ويرزقه الفتح بمشيّته انَّه وليّ ذلك بحوله وقوته.

  An rawaito cewa lokacin da mamun yaji al’amarin wannan hirzi daga baban jafar da wadannan siffofi dukkaninsu ya yaki rum Allah madaukaki ya bashi nasara a kansu ya bashi ganima daga garesu masha Allah bai rabu da wannan hirzi ba cikin dukkanin yakoki  Allah nai girma da daukaka ya kasance yana bashi nasara albarkacinsa yana kuma azurata shi da fatahi da mashi’arsa lallai shi ma’abocin haka da tsiminsa da karfinsa.

  Malaman tarihi suna cewa tabbas ummu fadal ta aikata wannan aikin laifi nata kan hakkin imam jawad (as) lokacin da ta shayar da shi guba.

  Hakika an rawaito cewa: tabbas mu’utasim ya sa ai aikata masa wata dabara cikin kashe baban jafar (as) ya yi ishara zuwa ga `yar mamun matar imam da ta sanya masa guba saboda ya gano karkatarta da kaucewarta daga baban jafar (as) da tsananin kishinta kansa.. sai ta amsa masa ta sanya masa guba cikin inibi ta aje gabansa, ya yinda yaci daga gare shi sai tayi nadama ta fara kuka sai ya ce: me yasa ki kuka? Wallahi Allah zai jefeki da talauci da ba zai gyaru ba d bala’in dabai suturtuwa, sai ta mutu da wata cuta cikin mafi zurfafar gabbanta, ta kasance gurguwa dukiyar baki daya ta kare cikin neman magani har sai da ya kai ga tana neman taimako.

  Wannan sammu ya yi tasiri mai tsanani cikin imam jawad (as) har ya kai ga ya yi numfashinsa na karshe harshensa yana ta yin zikirin Allah madaukaki, hakika fitila mai bada haske ta mutu  daga imamanci da jagoranci na isma cikin muslunci.

  Hakika imam jawad (as) ya yi shahada a hannun dagutun zamaninsa mu’utasim abbasi hakika da mutuwa shafi daga shafuka sakon muslunci  ya nade wacce ta haskaka tunani ta daukaka hasumiyar ilimi da falala ta daga ta a ban kasa.

  Shirya jana’izarsa da binne shi:

  An shirya imam (as) an masa wanka gawa an anya shi cikin likkafaninsa wasik da mu’utasim sun gaggawa sunyi masa salla an dauki jikinsa mai girma  zuwa makabartar kuraishawa, hakika jama’a masu tarin yawa sun halarci jana’izarsa sun kewaye shi, wannan rtana ta kasance ranar da garin bagdaza bai taba shaida irin wannan rana ba dubban gomomi sunyiturmutsitsi cikin maukibin jimami da bakin ciki suna raira falalolin imam suna kiransa suna kuka, suna tuna asara mai girman gaske wacce aka jarrabci musulmi da ita cikin rashinsu ga imam jawad (as) aka hakawa tsarkakakken jikinsa kabari da yake manne da kabarin kakansa imam musa kazim (as) sai suka binne shi cikin wannan kabari hakika an binne kimomin mutumtaka tare da shi da misalan karamci.

  عن أبي جعفر المشهدي باسناده عن محمد بن رضيّة عن مؤدّب لأبي الحسن]الهادي(عليه السلام)[، قال: «انه كان بين يدي يوماً يقرأ في اللوح اذ رمى اللوح من يده وقام فزعاً وهو يقول: انا لله وانا اليه راجعون مضى والله أبي (عليه السلام) فقلت: من اين علمت هذا؟ فقال(عليه السلام): من اجلال الله وعظمته شيء لا أعهده.

  An karbo daga abu jafar mashhadi da sanadinsa daga muhammad ibn radiyyatu daga mu’addib ga abu hassan hadi (as) ya ce: lallai shi ya kasance a gabana wata rana yana karatu cikin wani allo kwatsam sai ya yarda allon daga hannunsa ya mike tsaye a gigice yana cewa: inna lillahi wa inna ilaihi raji’un wallahi babana (as) ya rasu daga in kasan haka? Sai (as) ya ce: daga girman Allah da azamarsa wani abu da ban saba da shi ba.  

  فقلت: وقد مضى، قال: دع عنك هذا ائذن لي ان ادخل البيت واخرج اليك واستعرضني بآي القرآن ان شئت اقل لك بحفظ، فدخل البيت فقمت ودخلت في طلبه اشفاقاً مني عليه وسألت عنه فقيل دخل هذا البيت وردّ الباب دونه وقال لي: لا تؤذن عليّ أحداً حتى أخرج عليكم.

  Sai nace: ya mutu, sai ya ce bar wannan kai mini izini in shiga gidan in fito wajenka ka bijiro mini da kowanne kur’ani idan ka so zan fada maka da hadda, sai ya shiga gidan na shiga cikin nemansa saboda tausayi daga gareni kansa nayi tambaya gameda shi  sai aka ce ya shiga gida ya dawo da kofa bayansa ya ce mini: ka da ka bar kowa ya shigo har sai na fito wajenku.

  فخرج(عليه السلام) الي متغيّراً وهو يقول: انا لله وانا اليه راجعون مضى والله أبي، فقلت: جعلت فداك، قد مضى فقال: نعم وتولّيت غسله وتكفينه وما كان ذلك لِيلَي منه غيري ثم قال لي: دع عنك واستعرضني آي القرآن ان شئت أفسر لك تحفظه»

  Sai ya fito (as) yana mai canjawa yana fadin: inna lillahi wa inna ilaihi raji’un babana ya rasu wallahi, sai nace: raina fansarka hakika ya tafi sai ya ce na’am na jibanci yi masa wankan gawa babu wanda zai iya masa hakan in banda ni sannan ya ce mini: bar wannan ka bijiro mini kowanne kur’ani idan kana so zan fassara maka zaka hadda ce shi,

  فقلت: الاعراف. فاستعاذ بالله من الشيطان الرجيم ثم قرأ (بسم الله الرحمن الرحيم * واذ نتقنا الجبل فوقهم كانّه ظلّة وظنوا انه واقع بهم ).

  Sai nace suaratul a’araf, sai ya fara neman tsarin Allah daga sharrin shaidan jefaffe sannan ya karanta bismillah* ya yinda muka daukaka dutse samansu sukai yakinin cewa zai afka musu.

  Shekarunsa da tarihin shahadarsa: lokacin da ya rasu yana wanda aka shayar da shi guba ya kasance yana da shekaru ishirin da biyar a sannan zance, shine mafi karamin cikin a’imma sha biyu (as) a cikin shekaru hakika ya yi rayuwarsa cikin tafarkin daukaka muslunci da musulmai da kiran mutane zuwa fa farfajiyar tauhidi da imani ta tsoran Allah.

  Ya yi shahada a shekara ta 220 ranar talata ishirin da tara ga watan zul ka’ada, wasu sunce a karshen darare biyar da suka rage a zul hijja wasu kuma sunce kwanaki shida da suka rage a zul hijja

  Amincin Allah ya tabbata gareka ranar da ka haifeka da ranar da aka rataya maka imamanci, ya yi jihadi cikin tafarkin ubangijinsa yana mai hakuri da dauriya da ranar da ka shahadantar da shi da ranar da za a tashe shi rayayye.