sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Bakir (as)
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jawad Amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya faranta kwanakinku da murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Aliyu Ibn Musa Arrida amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Fatima Ma’asuma (a.s)
 • ZA A FARA DARASIN BAHASUL-KARIJUL-FIKHU NA ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Takwas ga watan Shawwal tunawa da ranar da Wahabiyawa suka ruguje kaburburan A’imma (a’s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da naku bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imamul Hassan
 • Mu’assatul Ihsan Alkairiya wacce take karkashin Majma’ul Tablig wal Irshad ta raba taimakon abinci a watan Ramdan Mai albarka
 • tashar tauraron dan Adam mai suna Anna'im zasu watsa laccar Assayid Alawi
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • Haihuwar Fatan Raunana Al'imamul Muntazar Mahadi (a.s).
 • MURNAR TUNAWA DA HAIHUWAR HASKEN GIDAN MUHAMMADU GUDA UKU
 • ALLAH YA GIRMMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM KAZIM A.S
 • LABARIN KAMUWAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI (H) DA CUTAR KORONA
 • MUHADARAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI KAN MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA AKA HAIFI FIYAYYEN HALITTU (S.A.W) DA IMAM SADIK A.S
 • FARA TARON BAJAKOLIN LITATTAFAI NA KASHASHE A JAMI’ATU ALU BAITI A.S
 • RANAR IMAMANCIN SAHIBUL-ASRI WAZ-ZAMAN A.S
 • Labarun da ba tsammani

  Muna ta’aziyya ga daukacin al’ummar musulmi kan shahadar imam Muhammad bakir amincin Allah ya tabbata gareshi

   

  Muna ta’aziyya ga daukacin al’ummar musulmi kan shahadar imam Muhammad bakir amincin Allah ya tabbata gareshi   

  Shahadar imam bakir (as)

  tareda kasantuwar imam bakir (as) ya nesantu gabaninsa kuma babansa imam sajjad (as) daga dukkanin abinda yake da dangantaka da hukuma, sai dai cewa ya kasance babbar barazana da ke baiwa hukumar umayyawa tsoro da yake cudanye da kishi da kiyayya da gaba, hakan ya shiga cikin sakafar da `ya`ya suka gada da iyaye daga mazajen daula, hakan ya faru sakamakon sun fahimci hatsarin ayyukan da imam bakir (as) yake kansu kasantuwarsa tushen wayewar muslunci ingantacce jagoran harkar kawo gyara cikin al’umma. Wacce take kunshe da girmama shi da mutunta shi, sai hukuma ta tashi tsaye da yin aiki don kawar da shi da halaka shi, ya zama manto sunyi amfani da makaminsu da suka saba amfani da shi suka halaka shi ta hanyar cusa masa guba lokacin mulkin hisham ibn abdul malik, wanda aka nakalto cewa shi wannan sarki hisham ya kasance yana da tsananta kiyayya da tsauri ga imam abu jafar Muhammad bakir (as) haka ma ga ahlil-baitinsa, riwaya bata ambaci bayani dalla-dalla ba kan yadda aka cusa masa gubar da yadda yayi shahadar.

  Duk dai yadda ta kasance lallai ba’arin wasu masadir sun ambaci dalilin mutuwarsa shine rashin lafiyar, dai-dai lokacin da wasu ba’arin masadir din kuma suka takaitu kan cewa imam bakir (as) yayi shahada sakamakon shayar da shi guba kamar yadda akaiwa babansa, sai dai cewa riwayar ba ta ambaci wanda ya sa masa gubar da hannunsa ba, wata riwayar kuma ta kawo cewa  hisham ibn abdul malik shine wanda ya sanya masa gubar, sai dai cewa kuma akwai wasu riwaya mai tsayi ta abu basir  daga baban Abdullah imam sadik (as) ya zo cikinta cewa dalilin da ya sanya hukuma ta himmatu da kisan imam bakir (as) shine sakamakon wani tsegumi da zaidu ibn Hassan ya kaiwa abdul-malik ibn marwan, cewa ya yayin da ya je wajensa yace masa: na zo wajenka daga wajen matsafi makaryaci wanda bai halasta ka kyale shi ba, kuma lallai yana tareda makamin manzon Allah da taobinsa da sulkensa da hatiminsa da sandarsa da gadonsa, jin wannan sai fushin abdul malik ya tashi saboda zaidu ya kai karar   imam bakir (as) cikin gadon manzon Allah (s.a.w) wajen alkali, sannan abdul malik ya aikawa imam da sirdi yayi da imam ya dora sirdi gareshi sai ya sauko yana kumbure , ya rayu kwanaki uku sannan ya yi sallama da wannan duniya ya koma zuwa ga karamcin ubangijinsa. Bayani ya gabata cewa lallai riwayar da take kawo labarin abubuwan da suka faru bata inaganta sai dai da kaddara faduwa da tahrifi sakamakon yanayin da riwaya ta samu kanta a zamanin hisham ibn abdul-malik.

  Daga cikin abin da yake nuni dagewar hisham kan kashe imam (as) shine cewa ya rubutawa gwamnansa na madina bayan ya bayyana imam tareda dansa sadik (as) da ya sanya musu guba cikin abinci ko abin sha sai dai kuma ba samu damar yin hakan ba.

  Wani mawaki yana cewa

  قال الشاعر :                     

  هلم بنا نبكي على باقر العلم                        سليل النبي المصطفى الأُمّي

  على لذّة العيش العفا بعد ما قضى                 شهيداً بلا ذنب أتاه ولا جرم

  له طول حزني ما حييت وحرقتي               ونوحي ولو أنّ البكا قد برى عظمي

  سقاه على رغم الوقى السمّ خفية                      هشام ردي الأب والجدّ والأُم

  عليه من الرحمن لعن مؤبّد                      بما سرّ من بغي وما سنّ من ظلم

  Ku taho mu yi kuka kan bakirul ilimi                           tsatson annabi zababbe ummi

  Kan dadin rayuwa ya gushe bayan ya bar duniya       yana shahidi ba tareda zunubi ba ko wani laifi

  Yana da tsawon bakin cikina matukar ina raye da konanata       da kukan bakin ciki da ace kuka ya fike kashina.

  Ya shayar da shi guba a boye duk da kasantuwa kariya      hisham mai lalataccen uba da kaka da uwa

  La’anar Allah madawwamiya kansa                          daga abinda ya sirranta daga zalunci da abinda ya sunnanta daga zalunci