sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Bakir (as)
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jawad Amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya faranta kwanakinku da murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Aliyu Ibn Musa Arrida amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Fatima Ma’asuma (a.s)
 • ZA A FARA DARASIN BAHASUL-KARIJUL-FIKHU NA ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Takwas ga watan Shawwal tunawa da ranar da Wahabiyawa suka ruguje kaburburan A’imma (a’s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da naku bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imamul Hassan
 • Mu’assatul Ihsan Alkairiya wacce take karkashin Majma’ul Tablig wal Irshad ta raba taimakon abinci a watan Ramdan Mai albarka
 • tashar tauraron dan Adam mai suna Anna'im zasu watsa laccar Assayid Alawi
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • Haihuwar Fatan Raunana Al'imamul Muntazar Mahadi (a.s).
 • MURNAR TUNAWA DA HAIHUWAR HASKEN GIDAN MUHAMMADU GUDA UKU
 • ALLAH YA GIRMMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM KAZIM A.S
 • LABARIN KAMUWAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI (H) DA CUTAR KORONA
 • MUHADARAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI KAN MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA AKA HAIFI FIYAYYEN HALITTU (S.A.W) DA IMAM SADIK A.S
 • FARA TARON BAJAKOLIN LITATTAFAI NA KASHASHE A JAMI’ATU ALU BAITI A.S
 • RANAR IMAMANCIN SAHIBUL-ASRI WAZ-ZAMAN A.S
 • Muna `daga mafi tsarkaka da girma da hasken taya murna bisa zagayowar munasabar nasabta imam Ali (as) wasiyyin manzon Allah amincin Allah ya kara taabbata gareshi da iyalansa.

   

  Muna `daga mafi tsarkaka da girma da hasken taya murna bisa zagayowar munasabar nasabta imam Ali (as) wasiyyin manzon Allah amincin Allah ya kara taabbata gareshi da iyalansa.


  wani kamface daga littafin (idil gadir baina subut wal’isbat) tare da alkalamin sayyid adil alawi tasowa daga akidar muslunci ta gaskiya, ya zama wajibi kan dukkanin musulmi da musulma suyi bikin wannan rana tare da yin murna da wannan rana mai girma cikin yin ibada da neman kusancin Allah da yin salati da yin azumi da nuna godiya ga Allah matsarkaki da salati ga annabi da iyalansa, da tsinuwa kan makiyansu da masu inkarin falalolinsu da darajojinsu, kamar yadda muke biki da nuna farin ciki da ciyar da abinci da bada kyauta ga iyalai da abokai da masoya, muyi musanye farin ciki muyi tarayya cikin murna tsarkakka tare da mala’ikun sama, da taruwarsu cikin fadar Firdausi wacce maulanmu imaminmu rida (as) ya siffanta ta, mu raya idi tsakankaninmu da sumbata da runguma da gaisuwar wilaya, muna cikin farin ciki tare da bushara da abin da Allah ya bamu daga cikar addini da cika ni’ima wacce falolinta basu kidaituwa, mu ce godiya ta tabbata ga Allah da ya sanya mu daga cikin masu riko da wilayar amirul muminina ali (as) da imaman ahlul baiti tsarkaka.

  Yana daga cikin barabuwa mu ambaci cewa da yawa-yawan abubuwa da suke faruwa da afkuwa cikin muslunci kamar haihuwar annabi (s.a.w) lallai akwai sabani tsakanin musulmai cikin ainahin iyakantuwa afkuwarsa, bari dai muna samun sabani hatta cikin hukunce-hukunce fikihu, kai hatta cikin akidu da iyakokinta, sai dai cewa kawai muna samun ittifaki tsakanin dukkanin mazhabobin muslunci kan wadannan ranaku hudu (idukan musulmai) idin karamar sallah, idin babbar sallah, idin gadir, idin juma’a, juma’a karshen sati musulmai na taruwa suyi bikinta ta hanyar tsayar da sallar juma’a, kamar yadda suke murna idin karamar sallah farkon watan shawwal, da ranar idin babbar sallah goma ga zil hijj, babu sabani kan cewa lamarin gadir ya kasance a sha takwas ga zil hijja, sai a lura.

  Kamar yadda mai rabawa wanda akai tarayya cikinsa cikin wannan mas’ala ta iduka shi ne batun imamanci da tattaruwa daura da imami, cikin kowanne sati musulmai na haduwa na taruwa cikin sallar juma’a daura da limamansu (limaman jama’a da juma’a) domin su ji huduba da wa’azuzzuka da isarwa, kamar yadda asali isar da sako da cikarsa ya kasance cikin ranar gadir, da annabi bai aikata nasabta ali wasiyyinsa ba da kwata-kwata bai isar da sakonsa b, sai mutane suka tattaru daura da imaminsu cikin ranar gadir kamar yadda suke murna da biki cikin kowacce shekara domin raya wannan batu mai girma, haka ma mutane ke taruwa daura da limamansu cikin ranar idin babbar sallah da karamar sallah, sai a lura.

  Ka sani lallai sakafar mabiya mazhabar ahlul-baiti ta ginu kan rukunai jiga-jigai hudu:

  Cikakken tauhidi.

  2- annabata ta gaskiya.

  3-gadir mafi haskaka

  4- ashura wanzazziya.

  Na ukun yana tajalli cikinsa wilaya da imamanci ta gaskiy, kamar yadda na hudu bara’a daga barin makiya da shahada tana bayyanuwa cikinsa, na ukun na nufin wilaya kamar yadda na hudu yana tukewa zuwa ga shahada.

  Ga misalign irin wannan muke cewa (kadai dai ita ryuwa akida ce da jihadi) take da jin nauyi da sadaukarwa da fansarwa. Karshen maganarmu godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.