sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Dawowar sayyid adil-alawi daga kasar siriya cikin shawaginsa da ya yi na tablig a watan safar

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Dukkanin godiya da yabawa sun tabbata ga Allah kamar yadda yake shi ahlin hakan ne kuma ya cancanci hakan, sayyid adil-alawi ya dawo daga shawaginsa na tablig na watan safar daga kasar siriya birnin damaskus bayan ya ya yi kwanaki shida jere a kasar sham wanda cikin wadannan kwanaki ya gabatar da laccoci goma sha hudu kan muslunci da akidu da akhlak da irfani.

1-tsawon darare goma bayan sallar magariba da isha’i cikin masallacin da yake cikin hubbaren saiida zainab amincin Allah ya kara tabbata gareta an gayyace gabatar da wadannan laccoci daga ofishin jagoran juyin juya hali na iran dake siriya ta hannun wakilinsa limamin juma’a samahatus sayyid taba’taba’i Allah ya dawwamar da girmansa, maudu’in laccar shi ne sharhin ziyarar arba’in

2-laccoci guda hudu a muhallin hauzar imam komaini ta dalibai maza da mata Allah ya tsarkake ruhinsa bayin sallolin azuhur da la’asar gayyatar ta fito daga jami’atul mustafa maudu’in laccar shi ne sharhin hadisin unwanu basari.

3-lacca ga jagoran tushukan jahadi cikin sham.

4-lacca ga mayaka daga garin halab cikin basira.

5-lacca ga muballigai cikin fagagen yaki

6-lacca ga malaman hauza.

7- lacca cikin makarantar muhassiniya babba da tsohuwa cikin taron malamai da gayyar yan sakafa daga gayyatar samahatus sayyid ayatollah abdullahi nazzam.

8- ganawa da tashar alwilaya ta tauraron dan adam.

Daukara hotunan tarihi da sannu za mu sauke lacocin da hotunan a sayit bayan zuwansu hannun mu kamar yadda samahatus sayyid ya kabo hadayoyi wadanda yayi wakafinsu ga gidan tarihin alawi sune :

1-kur’ani mai girma da sunan maularmu zainab amincin Allah yak ara tabbata gareta.

2-tutar maularmu sayyada zainab amincin Allah ya kara tabbata gareta  wanda ta kasance kafe a mukamin sayyada zainab a watannin muharram da safar.

3- ziyararta da ziyarar husaini amincin Allah ya tabbata garesu da ziyarar ashura.

4-wani yanki mai launin ja da sunan sayyada amicin Allah ya kara tabbata gareta.

 daga kuma na sayyada rukayya amincin Allah ya kara tabbata gareta.

1-labule kayatacce wand aya kasance shimfide kan kabarin maularmu sayyada rukayya `yar imam husaini amincin Allah ya tabbata garesu.

2-yanki guda hudu na rataye wanda ya kasance kan hubbaren sai dai wannan sayyid adail-alawi ya rike su don kansa da iyalansa don neman albarka da damantuwa sannan samahatus sayyid taba’taba’i ya bayarda wanu sulke da sunan jami’atul mustafa daga hauzatul imam komaini Allah yab tsarkake ruhinsa.

Daga karshe muna rokon Allah da ya baiwa kowa da kowa taufiki da dacewa dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai   


a