sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

jaridar sautul kazimaini221-222 watannin muharram mai alfarma da safar hijira tana da shekaru 1439 wacce tayi daidai da 2017 miladiya. Shin karbala bala'i ce! tare da sayyid Jafar Murtada amuli.

 

 

Amsa: lallai abin da ya zo cikin tambaya daga banbancin mahanga da mikekeniya tare da batun karbala ingantacce ne ba tare da kokwanto ba, lallai bai daga cikin maudu'in tuhuma ba a haddin kankin kansa, sai dai cewea zargi da tuhuma ya ratayu kadai kan takaitawa da jumudi kansa. Akwai mutumin da ya ke fahimtar karbalakan cewa ita batu ne na siyasa kawai a tarihance, ya zama dole ayi bayaninta filla-filla dalla-dalla tare da mikekeniya tare da ita da falsafarta karkashin  wannan mahanga da kallo, ya zama kan wannan fuska yayi la'akari da shi a matsayin fuskanta ta ilimi da tunani da tarihi da siyasa da harkar tsaro, ya ga cewa lallai al'amarin ya zama dole ya kasane dangantaka da ita ya zama da gwargwadon yadda mutum zai fa'idantu daga gareta  cikin wannan fuska, sannan akwai wanda ya ke mikekeniya tare da karbala ta fuskanin kaantuwa sha'a'ir abin da ya ke sanyawa a tuna da Allah da kuma aikin ibada , da tsayuwa kan raya wajibin bayyana bakin ciki da kunanar zuciya kan wadanda sukai shahada cikin karbala, da zurfafa alaka da ahlil baiti amincin Allah ya kara tabbata garesu karkashin hakan, saboda haka shi ya takaitu cikin jigon bala'I, cikin dukkanin halinsa da mabayyanansa, sannan gameda kiyaye waccan alaka ta imani da ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata garesu da zurfafata, muna cewa: lallai cikin abin da babu shakka cikinsa shi ne cewa wadannan fusake guda biyu tushe ne muhimmai matuka cikin wayewarmu ga bala'in karbala, baya daga kuskure himmatuwa da su da mai da hankali zuwa garesu sai dai cewa kuskure shi ne kallo na karo da juna cikin abin da ke tsakanin fusaken biyu, da lazimtuwa da dayansu da watsi da daya fuskar ta fuskanin wanda ya ke jingina kuskure garesu, wanda shi ne iyakance karabala cikin kebantar wadannan fusake guda biyu ta wata fuskar daban,

Hakikanin gaskiya shi ne lallai ya zama wajibi kanmu mu tsaya mu fuskanci karbala kan cewa ita muslunci ce baki dayansa tare da banbancin sha'anunnukansa da fagagensa, bai inganta a kayyade karbala ko iyakance cikin da wata kebantaciyar fuska ko wata zawiyya, cikin karbala akwai komai daga abin da rayukan masu neman gaskiya ke muradi, da dukkanin abin da hankulan ma'abota daidaito kan hanya ke sa'ayi domin samunsu a kan hanyar shiriya domin cikin karbala akidar muslunci take. Cikin shari'a take cikin da yawa-yawan fagagenta. Cikinta siyasisin muslunci suke. Cikin ma'anonin kur'ani suke, cikin tawilolin ayoyi suke, cikinta akwai kashim furen imamanci da annabta. Cikinta akwai wazifofin annabawa, da nasarorin wasiyyai, da nauyin da ya ke kansu da gyararrakinsu, cikinta tajallin ilimummuka imamai suke, cikinta darajojin isma da kayatattun karamominsu da sauran siffofi  cikin karabala wadanda suke gina mutumtakar mutum da msulunci aunanne.

Cikin karbala ake jawo tausayin zukata su taso su girma su kammalu, a banbance mai kyau daga mara kyau, cikin karbala akwai mahangar siyasa, cikinta akwai mafahuman akida.

Cikin karabala aka taka rawar siyasa da matsayar akida da akhlak da addini da mutumtaka, karbala bawai kawai wani abune da ya faru a tarihi ba ya wuce kamar saurarun abubuwa da suke faruwa irin na siayasa da tsaro ba kuma kawai bala'I da musiba ba bace kadai da za ta shude lokacinda da muke kaddamar ba'arin banbance aya da tsakuwa na tarihi kan sabubban faruwarta ba, da abin da ya bubbugo daga gareta, ko kuma lokacin da muka kammala bikin zaman makoki sai ta zama tarihi ta wuce. Ko lokacin da muka gama kuka sai ya zama an gama da it aba, ba kuma tsuran nishadin siyasa ce ba har idan muka tsinkaya kan wasu natijojinta na tunani ba zamu kara bukatuwa da it aba.

Kadai dai karbala wanda yak e misaltuwa da ita shi ne imam Husaini (as) wanda manzon Allah (s.a.w) kansa ke cewa: lallai Husaini shi ne fitilar shiriya kuma jirgin tsira. Lallai shi fitila ne da ya ke haska hanya ga batattu da rudaddu cikin mudu'ai mabanbanta na rudu da bata.

Lallai imam Husaini (as) shi ne hanyar  wadda da zaka bi ka'idar da zaka lazimceta don ka kai ga cimma burinka, ka samu bayani dalla-dalla karkashin ka'aida da kake rayuwa cikin sasaninta, ka fa'idantu daga tajallolinta cikin kowanne matsunai da wadancan sasanni suka tattaru kai, kada ka nutse cikin faifaicewa don kada ka bata daga barin ka'ida, ba zaka samu hasken shiriya ba da zaka shiriya da shi.

Lallai mu muna bukatuwa zuwa ga imam Husaini (as) saboda tsananin bukatuwarmu zuwa ga hasken shiriya cikin duhun dare mai kidimarwa.

Dukkanin hakan yana samu fuskantar cewa lallai karbala bawai tsuran wani abune na tarihi ba da ke fursunance cikin fursun din tsohon tarihi ba, a muke himmatuwa kan bincike kansa sannan mu ajiye natijojin bincikenmu cikin litattafai da mujalladai ba, da babu wani zai waiwaye kurar mantuwa ta lullube su a hijirce musu a kaurace musu face lokutan ziyartar ba'arin ustazan tsoffin tarihi cikin hauzozin addini ko cikin jami'o'i don bukatuwarsu zuwa ga nazarinsu.

Dukkanin wadannan abubuwa ya na samu mu fahimci lallai cewa abinda ya faru a karbala ba wai kadan tsuran labarin tarihi kamar ragowar labararrukan tarihi da ya suka gabata wadanda suke rubuce cikin litattafan tarihi suke ajiye cikin dakunan nazarin tarihi da kadai muke himmatuwa da yin bahasi kansu sannan mu ajiye sakamakon bahasinmu cikin litattafai da mujalladai wadanda babu mai kara waiwayarsu, kurar mantuwa ta lullube su. Su wayi gari ababen hijircewa da kauracewa, face lokutan da wasu ba’arin masana da malaman hauza suka waiwaye su don bukata, ko kuma cikin jami’o’i don bukatun karatun jami’a, ta yiwu ma wasu bangare daga masu son su rayu rayuwa da ta nesanta daga ambaton tarihin manya-manyan magabata su kau da kai daga wadannan litattafai su tsallake su.