sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Labarun da ba tsammani

Tunawa da zaluncin da akaiwa Faɗima Zahara amincin Allah ya tabbata gareta wacce itace farko wacce ta fara riskar manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata gareshi tare da-alkalamin sayyid Adil-Alawi

daga amali mufid isnadinsa ya ce: yayin da wafatin ya halartowa annabi (s.a.w) ya fashe da kuka har sai da hawaye ya jike gemunsa, sai aka tambaye shi aka ce ya manzon Allah (s.a.w) mene ne ya sanyaka kuka? Sai ya ce: ina kuka ne saboda zuriya da abin da ashararan cikin al’ummata zasu aikata kansu bayan wafatina, kai kace ina ganin `yata Faɗima gabana an zalunceta bayana tana halin kira ya babana ya babana, babu wani daga cikin al’ummata da yake kai mata `dauki, sai Faɗima ta ji wannan magana sai ta fashe da kuka, sai manzon Allah ya ce: kada kiyi kuka yake `yar karamar `yata, sai tace bana kuka kan abin da za a aikata kaina bayanka sai dai cewa ina kuka ne kan rabuwa da kai ya manzon Allah, kiyi bushara yake `yar Muhammad cikin gaggawa zaki riskeni, lallai ke ce ta farkon wacce zata fara riskata.

Lallai wannan maɗaukaki hadisi yana nuni kan zaluncin da akaiwa Ahlil-baiti kamar yadda yake nuni zuwa ga cewa kadai dai wanda zai zaluncesu yana daga mafi sharrin al’umma bayansa, lallai su sun juya bayansu duniya ta rude su, sun sayar da lahirarsu da mafi ƙaskantar farashi, sai sukai hasara biyu hasarar duniya da lahira lallai wancananka shine hasara mabayyaniya.

Hakama ya nuni kan halascin kuka kan musibar da ta afku kan Ahlil-baiti (as) sannan ya nuna zuwa ga keɓantacciyar daraja daga keɓantattun darajojin sayyada Zahara (as) lallai itace ta farkon wacce zata fara riskar manzon Allah (s.a.w) a gidan lahira daga Ahlin gidansa. Ya zo cikin  littafin bihar daga littafin dala’ailul imama na muhammadu bn jariri ɗabari dan imamiyya:

عن أبي المفضّل الشيباني ، عن محمّد بن هاشم ، عن أحمد بن محمّد البرقي ، عن أحمد بن محمّد بن عيسى بسنده عن أبي بصير عن أبي عبد الله 7 قال : «ولدت فاطمة في جمادي الآخرة اليوم العشرين منها سنة خمس وأربعين من مولد النّبي  6، فأقامت بمكّة ثمان سنين وبالمدينة عشر سنين ، وبعد وفاة أبيها خمساً وسبعين يوماً، وقبضت في جمادي الآخرة يوم الثلاثاء لثلاث خلون منه سنة إحدى عشرة من الهجرة »[1

Daga Mufaddal shaibani daga Muhammad bn Hashim daga Ahmad bn Muhammad Albaraki daga Ahmad bn Muhammad bn Isa da isnadinsa daga Abu basiru daga Abu Abdullah (as) ya ce: ana haifi Faɗima ishirin ga watan jimada akhar shekara arba’in da biyar da haihuwar annabi (s.a.w) sai ta zauna a makka shekaru takwas a madina kuma shekaru goma, sannan ta rayu bayan babanta kwanaki saba’in, Allah ya karɓi ranta ranar talata uku ga watan jimada akhar hijira nada shekaru goma sha daya

A wani hadisin kuma ta rayu a bayansa kwanaki casa’in da biyar shi’ar masu karamci cikin wannan zamani suna tattara dukkanin zantuka biyu cikin tsayar da taron bikin makokin shahadarta suna raya uku daga sha ukun jimada ula da kuma kwanakin ukun farkon jimada sani.

Allah ya saka musu da alheri lallai raya makoki yana daga ibadun Allah  

ومن يعظّم شعائر الله فانّها من تقوى القلوب .

Duk wanda ya raya ibadun Allah lallai ita tana daga takawar zuciya.

Domin neman Karin bayani zaku iya komawa abin da samahatus sayyid Adil-Alawi (h) ya rubuta  mai taken kasa’isus faɗimiyya ala dau’il saklaini.