sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Allah ya faranta kwanakinku da murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Aliyu Ibn Musa Arrida amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Fatima Ma’asuma (a.s)
 • ZA A FARA DARASIN BAHASUL-KARIJUL-FIKHU NA ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Takwas ga watan Shawwal tunawa da ranar da Wahabiyawa suka ruguje kaburburan A’imma (a’s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da naku bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imamul Hassan
 • Mu’assatul Ihsan Alkairiya wacce take karkashin Majma’ul Tablig wal Irshad ta raba taimakon abinci a watan Ramdan Mai albarka
 • tashar tauraron dan Adam mai suna Anna'im zasu watsa laccar Assayid Alawi
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • Haihuwar Fatan Raunana Al'imamul Muntazar Mahadi (a.s).
 • MURNAR TUNAWA DA HAIHUWAR HASKEN GIDAN MUHAMMADU GUDA UKU
 • ALLAH YA GIRMMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM KAZIM A.S
 • LABARIN KAMUWAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI (H) DA CUTAR KORONA
 • MUHADARAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI KAN MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA AKA HAIFI FIYAYYEN HALITTU (S.A.W) DA IMAM SADIK A.S
 • FARA TARON BAJAKOLIN LITATTAFAI NA KASHASHE A JAMI’ATU ALU BAITI A.S
 • RANAR IMAMANCIN SAHIBUL-ASRI WAZ-ZAMAN A.S
 • ALLAH YA GIRMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM HASSAN ASKARI A.S
 • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
 • Labarun da ba tsammani

  Muna yiwa sahibuz- zaman ta’aziyar shahadar kakansa imamul Aliyu Alhadi amincin Allah ya kara tabbata gareshi
  Muna daga mafi zafin ta’aziyya zuwa ga shugabanmu majibancin lamarinmu sahibuz-zaman ( ruhina fansar kurar takun kafarsa) cikin wafatin kakansa imamul Aliyu bn Muhammad Alhadi amincin Allah ya kara tabbata garesu kamar yadda muke kara kai ta’aziya zuwa ga mukamin manzon Allah (s.a.w) da iyalan gidansa masu karamci tsarkaka hakama zuwa ga malaman al’ummar musulmai baki daya.

   

  Matsayinsa A ilimi amincin Allah ya kara tabbata gareshi:

  Hakika dukkanin manya-manyan malaman tarihi da sira sun yi ijmma’I kan cewa lallai imam (as) ya kasance alami da ba a iya kusantarsa daga tsakanin alaman manyan malamai zamaninsa, hakika Shaik dusi ya ambatar masa cikin littafinsa mai suna (Rijalul dusi) Almajiransa dalibai dari da tamanin da biyar da marawaitan hadisi wanda suka rawaita daga wurinsa daga gareshi.

  Imam (as) ya kasance makoma marja’i ma’abota ilimi da fikihu da shari’a, litattafan riwaya da hadisi da munazarori da fikihu da tafsiri da misalsalansu sun cika da abinda aka karbo daga gareshi sun kimsu da ilimansa da ma’arifofinsa.

    
   daga hukuncinsa amincin Allah ya kara tabbata gareshi.

  Daga maganganun da hikimomin imam Aliyul Alhadi (as)

  ● قال الإمام الهادي (عليه السلام): من اتقى الله يتقى ومن أطاع الله يطاع ومن أطاع الخالق لم يبال سخط المخلوقين ومن أسخط الخالق فلييقن أن يحل به سخط المخلوقين.

  Imam hadi (as) ya ce: duk wanda ya ji tsoran Allah shima za aji tsoransa, duk wanda ya yiwa Allah da’a shima za ai masa da’a, duk wanda ya yiwa Allah biyayya  ba zai damu yi da fushin mutane ba, amma wanda ya fusata Allah to ya samu yakini da cewa fusatar mutane zata sauka kansa.  
  ● قال الإمام الهادي (عليه السلام): إن الله لا يوصف إلا بما وصف به نفسه وأنى يوصف الذي تعجز الحواس أن تدركه والأوهام أن تناله والخطرات أن تحده والأبصار عن الإحاطة به نأى في قربه وقرب في نأيه كيف الكيف بغير أن يقال كيف وأين الأين بلا أن يقال أين هو منقطع الكيفية والأينية الواحد الأحد جل جلاله وتقدست أسماؤه.

  Imam hadi (as) yace: lallai Allah ba a siffanta shi face da abinda ya siffanta kansa da shi, ta yaya za a siffanta wanda marisakai suka gaza riskarsa, wahamai suka gaza samunsa, darsawa ta kasa iyakance shi, idanuwa suka gaza kewaya da shi, ya nesantu cikin kusantuwarsa ya kusantu cikin nesantarsa, shi ya kayyafantar da kaifa ba tareda da ace kaifa da fadin ina aina ba tareda fadin yana in aba me yankakkiyar kaifiya da ainiyya daya makadaici girmansa ya girmama sunayensa sun tsarkaka.
  ● قال الإمام الهادي (عليه السلام): الشاكر أسعد بالشكر منه بالنعمة التي أوجبت الشكر لأن النعم متاع والشكر نعم وعقبى

  Imam hadi (as) yace: mai godiya shi ya azutar da yin godiya daga gareshi da ni’imar da ta wajabta yin godiya saboda ita ni’ima dadi ce godiya kuma ni’ima ce da kyakkyawan akiba.