sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Allah ya girmama ladan ku da na mu bisa musibar rashin Sarkin muminai Ali (as)
 • Tsare-tsaren shirin raya dararen lailatul kadari na watan Ramadan 1440 H
 • Muhadarorin watan Ramadan Assayid Adil-Alawi
 • An kammala zaman karanta ta’aziyar Imam Husaini (as) bisa zagayowar wafatin Sayyid Ali Alawi
 • Za a shirya zaman majalisin jimami har tsawon kwanaki uku bisa munasabar cika shekara talatin da bakwai da rasuwar Ayatullah Assayid Ali bn Husaini Alawi Allah ya jikan sa
 • Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala
 • Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi
 • Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar shigowa uku ga watan Sha’aban Ranar da aka haifi Imam Husaini a.s
 • Tsokaci dangane da zamanin Imam Alkazim (as
 • Ubangiji ya girmama ladanku da namu bisa wafatin Sayyada Zainab diyar Imam Ali bn Abu dalib (as)
 • Ubangiji ya faranta muku da haihuwar Imam Ali bn Abu dalib (as)
 • Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Aliyu bn Muhammad Hadi aminicnin Allah ya kara tabbata a gareshi
 • Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Bakir amincin Allah ya kara tabbata a gareshi
 • • Samahatus Sayyid Adil-Alawi zai gabatar da muhadara cikin Haramin Sayyida Ma'asuma a ranar mauludin Sayyada Fatima (as)
 • Allah ya girmama ladanmu da naku bisa tunawa da shahadar Siddikatul Kubra Fatima Zahara (as)
 • Hai’atu Ashura ta birnin Bagadaza zasu karbi bakunci Samahatus Sayyid Adi-Alawi
 • Samahatus Sayyid Adil-Alawi (h) ya tarbi maziyarta yan asalin kasar lubnan da suke zaune a kasas siwidin (Sweden
 • Ganawar samahatus Sayyid Adil-Alawi (h) tare da matasan kasar Labanun.
 • Ganawar samahatus Sayyid Adil-Alawi (h) tare da matasan kasar Labanun.
 • sababun labare

  Labarun da ba tsammani

  Ubangiji ya azurta kwanakinku cikin tunawa da ranar da aka aiko Annabi (s.a.w

  http://www.alawy.net/upload/3403.jpg

  Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

  Wasu `ya tsirarun abubuwa da ka gutsiro daga littafin (Sima`u Rasulil A`azam fil `Kur`an)

  Tareda da Alkalami sayyid Adil alawi

  Manzon mafi girma cikin motsin al`umma:

  Idan manzon mafi karamci ya fuskanci wahalhalu daga jama’arsa sakamakon jahiltarsa da jahiltar matsayinsa madaukaki cikin dukkanin marhaloli da daurori  wadanda harkar muslunci ta gifta ta, babu banbanci cikin kasantuwarta gabanin aiko annabi ko bayan aiko shi ko kuma kafin hijra ko bayanta lokacin da yake a raye ne ko bayan wafatinsa (s.a.w) lalle daga cikin abubuwan da suka biyo bayan wannan fakuwar saninsa ko ace gazawa ko kasawa wanda ya kai ga jahiltar girman matsayin annabin rahama da mutumtaka (s.a.w) da saninsa kamar yadda yake, musulmi sun koma baya sun ci baya daga girmansu mai tushe da wayewarsu ta mutumtaka wadda ta game duniya baki daya da falaloli da karamci da ilimi da fannoni, sai gaba da kiyayya da rigimgimun mazhabobi da kabilanci wanda suke da tushe na jahiliyar farko suka maye gurbi, sai ya zamanto karfinsu ya kau sun gaza samun nasara sun fadi jarrabawa a fagagen cigaba da gabata har ta kai ga bakin haure da karnukansu masu yi musu aiki daga sarakuna da shugabanni sun samu iko kan wuyayensu, sai suka kasance suna kwashe dukiyarsu  suna shan jinanansu suna ci da guminsu su koma su raya kasashensu, su rike ta matsayin taguwar da za ta kai su ga manufofinsu da bukatunsu da maslahohinsu da shirye-shiryensu na mallake raunana cikin duniya baki daya da kowanne irin yanayi ta kama.

  Babu wata al`umma da `daga ta kai ga gano martaba da matsayin manzo mafi girma a tsawon marhaloli da zamanunnuka da suka shude da gabata ballantana ace sun kai ga siffantuwa da dabi`unsa da sasanninsa da dabakokinsa, wajibi kan kowanne musulmi ya san yadda annabi (s.a.w) ya rayu  da kuma tarihinsa  mai cike da haske da ayoyin rahama da da tausayi da soyayya da `kauna lalle ya kamata ya san mu’ujizarsa dawwamammiya wato `kur’ani mai girma, kai ya kamata ace ya san sahabbansa wadanda sukai ma annabi (s.a.w) rakiya cikin halartuwarsa da tafiye-tafiyensa kai cikin dukkanin marhalolin rayuwarsa, sun kasance batattun da ya shiryar da su cikinsu  akwai kunne da yake kiyayewa wanda shi ne sarkin muminai Ali (as) lalle shi kamar yadda suka ce shi aya ne daga ayoyin annabta annabi (s.a.w) lalle shi ya kasance mu`ujiza ta biyu bayan kur’ani  mai girma wanda ke nuni zuwa ga gasgatar annabtarsa  da girman sakonsa ta yadda kimomi suka taso daga tarbiyarsa kamar misAlin sarkin muminai Ali (as).

  Mai karatu cikin rayuwar manzon rahama da sannu zai ga akwai wasu manyan mutane da suke kusa da manzon rahama kamar misAlin Ali (as) Abu zar gifari da Ammar ibn Yasir da Mikdadu kai hatta hadisi ya zo daga manzon Allah (s.a.w) yana cewa Salmanu daga cikinmu yake mu Ahlul–baiti. haka manzon rahama yana cewa lalle Allah yana shaukinsu lalle aljanna ma tana shaukinsu, kadai dai sun samu wannan daukaka mai girma sabon sanin da sukaiwa manzon Allah (s.a.w) da sanin a kamalarsa da kyawunsa basu taba yi masa jayayya ba kamar yadda wasu sukai cikin matsayarsa da hukuncinsa, su sun tsaya kyam tare da shi sakamakon karfafar imaninsu da shi  da kuma kasantuwarsa wajen shi bai Magana da son zuciya face abin da akai masa wahayi. Dayansu bai taba fadi kamar yadda wancan mutumin ya fadi lokacin da annabi (s.a.w) zai yi wafati da yace a kawo masa alkalami da tawada  da takarda domin ya rubuta musu wani abu da ba zasu bata a bayansa ba sai wannan mutum ya gane cewa annabi (s.a.w) yana ishara zuwa ga hadisin saklaini littafin Allah da tsatsonsa daga Ahlul-baiti wanda jagoransu ya kasance sarki muminai Ali (as) lalle manzon Allah (s.a.w)  ya furta wannan hadisi a wurare da daman gaske

  (إني تارک فيكم الثقلين كتاب الله وعترتي أهل بيتي ما ان تمسّكتم بهما لن تضلّوا بعدي أبداً وانهما لن يفترقا حتّى يردا عليّ الحوض

            Lalle ni mai barku muku nauyaya guda biyu ne littafin Allah da tsatsona Ahlul baiti matukar kun yi riko da su ba zaku taba bata ba bayana har abada lallai su biyun basu taba rabuwa da juna har sai sun gangaro wurina a tafki.

  Wannan ingantaccen hadisi ne mutawatiri daga dukkanin bangarori biyu shi’a da sunna. A wannan lokaci sai wani mutum ya cewa manzon Allah (s.a.w) wai wannan mutumin ya zautu baya cikin hankalinsa wa’iyazubillahi daga wannan mumuna kalami nasa. Ina wannan mutumin za a hada shi da Salmanu da misalsalinsa daga zababbun sahabban annabi (s.a.w) masu girman daraja yardadddun Allah.

  Babu shakka cikin kasantuwar nesantarwa da kusantarwa cikin matsayin manzon Allah (s.a.w) sun rukunantar da gurabe bayyanannu cikin mutanen da suka rayu da shi a kebance, haka da al`umma cikin gamewa duk wanda ya kasance mai adalci bai makantar da kansa cikin makauniyar biyayyar iyaye  sannan da kuma zargin mai zargi bai da meshi ba lalle zai fuskanci wannan abubuwa da muka fadi zai dauketa a matsayin sako da nauyi dake rataye a wuyansa.

  Sai ta banbanta wurinsa da yanayin amsar da ya samu da sakamako bisa akidu da ka`idoji ingantattu da suka samu ingancinsu kan hasken Kur’ani da Ahlul baiti amincin Allah ya kara tabbata gare shi.