sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Bakir (as)
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jawad Amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya faranta kwanakinku da murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Aliyu Ibn Musa Arrida amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Fatima Ma’asuma (a.s)
 • ZA A FARA DARASIN BAHASUL-KARIJUL-FIKHU NA ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Takwas ga watan Shawwal tunawa da ranar da Wahabiyawa suka ruguje kaburburan A’imma (a’s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da naku bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imamul Hassan
 • Mu’assatul Ihsan Alkairiya wacce take karkashin Majma’ul Tablig wal Irshad ta raba taimakon abinci a watan Ramdan Mai albarka
 • tashar tauraron dan Adam mai suna Anna'im zasu watsa laccar Assayid Alawi
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • Haihuwar Fatan Raunana Al'imamul Muntazar Mahadi (a.s).
 • MURNAR TUNAWA DA HAIHUWAR HASKEN GIDAN MUHAMMADU GUDA UKU
 • ALLAH YA GIRMMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM KAZIM A.S
 • LABARIN KAMUWAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI (H) DA CUTAR KORONA
 • MUHADARAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI KAN MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA AKA HAIFI FIYAYYEN HALITTU (S.A.W) DA IMAM SADIK A.S
 • FARA TARON BAJAKOLIN LITATTAFAI NA KASHASHE A JAMI’ATU ALU BAITI A.S
 • RANAR IMAMANCIN SAHIBUL-ASRI WAZ-ZAMAN A.S
 • Labarun da ba tsammani

  Muna mika ta’aziyya zuwa ga Sahibuz-zaman da daukacin al’ummar musulmai bisa tunawa da zagayowar ranar wafatin Sayyada Fatima Ma’asuma (a.s)


   

  Wani dan kamface dan tsokaci daga rayuwar Sayyada Ma’asuma (a.s)
  hakika ta fifita ta kuma shahara daga `ya`yan Imam Musa bn Jafar (a.s) wadanda yawansu yah aura mutuma talatin, cikin su akwai fitattun mutane biyu da suka fifita da ilimi da takawa sune Imam Rida (a.s) wanda ya gaji imamanci daga da nassi daga Allah da kuma nasabtawar manzonsa (s.a.w) sai kuma kanwarsa Sayyada Fatima Ma’asuma siddikataul sugra (a.s) hakika an haifeta cikin birnin Madina munawwara a farkon watan Zul ki’ida  hijira na da shekaru 173 kamar yanda aka rawaito, sannan ta yi wafati a birnin Qum goma ga watan Rabi’ul sani  hijira na shekaru 201 a loakcin da tanada shekaru 28.

  Hakika ta taso a karkashin Imani da takawa cikin gidan isma da tsarki, ta cimma wani matsayi wurin Allah matsarkaki har takai ga babanta Kazim (a.s) ya ce: babanki ya fansheki da ransa, ya maimaita hakan har karo uku cikin wata hikaya da yake bada labarin iliminta da hukuncin ta da hukuncin Allah daidai lokacin ko shekaru taklifi ba ta kai ba.

  Lallai ita ta kasance kamar misalin gwaggonta Sayyada Zainab (a.s) malamar da bata da malami, fahimtaciyya da wani bai fahimtar da it aba. Hakika ta kwankwasa kofofin ilimi da kwashi asalansa daga babanta Imam Kazim (a.s) da dan’uwanta Imam Rida (a.s) kofofin ilimi na budewa gabanta daga kowacce kofa guda kamar dai misalin kakanta Sarkin muminai Ali (a.s) inda yake cewa:

  علّمني رسول الله ألف باب من العلم ينفتح لي من كل باب ألف باب. 

  Manzon Allah ya sanar da ni kofa duba daga ilimi kuma kowacce kofa daga cikinsa tana bude mini kofa dubu.

   ma’ana da ilhama daga Allah, lallai shi yana daga kofar ilimi na wahayida yake biye da ilimin wahayi na musammam d aya kebantu da Annabawa, shi yana daga ilimin ladunni da yake kebance da ma’abootansa.

  Sayyada ma’asuma (a.s) ta kasance cikin yarintarta lokacin da wasu jama’a daga shi’a suka zo suna neman amsoshin tambayoyinsu sai suka kwanmkwasa kofar Imam (a.s) sai Ummu Rida tace musu baya gida ya fita wajen gari, sai lamari ya tsananta garesu suka shiga tunanin yaya zasu koma ba tare da samun amsoshin da suka kawo su ba, sai ta basu labarin cewa akwai wata karamar yarinya a cikin gidan, sai suka gabatarwa da Sayyada Ma’asuma (as) tambayoyinsu gareta sai ta basu amsa a rubuce, yayin da suke fitowa daga Madina sai suka hadu da Imam suka bashi labarin amsar da ta basu, sai Imam (a.s) y ace: ku bani in gani ya karba yay a duba sai ya ce: (babanta fansarta) ya fadi har sau uku, sannan ya ce hakika ta yi hukunci da hukuncin Allah a ma’anance.

  Lokacin da ta cika shekaru goma sai ya zamanto mahaifinta yayi shahada cikin fursun din dagutun zamaninsa Harun Rashid a ka binne shi cikin makabirul Kuraishi wacce a wannan zamani aka fi sanin ta da Kazimiyya mukaddasa.

  Sai yayanta Imam Rida (a.s) ya dauki nauyi kula da ita a kafadunsa.. kwanaki suka tafi har mulkin Abbasiyawa ya koma hannun Mamun wanda yayi bakin kokarinsa wajen dakusar da yunkurin Alawiyyawa wanda ya kasance yana kishiya da barazana ga sarakunan zalunci a lokuta daban-daban cikin garuruwan muslunci a wancan lokaci, sai Mamun sakamakon wasu dalilai kari kan wancan yunkuri ya tilastawa Imam Rida (a.s) karbar kujerar mai jiran gado bayansa, ya kuma yi masa baraza da idan yaki karba zai kasha sh, ya dauko shi daga madina ya dawo da shi birini Kurasan ba tare da son ransa domin ya kasance karkashin sanya idanunsa, Imam (a.s) ya karbi wannan mukami a zahirance tare da cewa ransa bai so, ya nufo garin Marwa, sakamakon wasu kebantattun dalilai Sayyada Ma’asuma (a.s) bata rako shi ba ta taho tare da shi cikin wannan tafiya mai tsananin wahala wacce babu komo cikinta.
  ya kasance ana buga misali cikin soyayya da kauna dake tsakanin yan’uwan juna da soyayyar da take tsakaninta da dan’uwanta kamar yanda ta kasance tsakanin `yan’uwan juna niyu shugaban Shahidai Husaini (a.s) da Zainab Kubra (a.s).

  Bayan shudewa lokaci cikin wannan rabuwa mai radadin gaske sai Sayyada Ma’asuma ta daura damara don rsikar dan’uwanta imaminta imamin zamaninta dominta ta kasance misalin gwaggonta Sayyada Zainab (a.s) cikin daukar mas’uliya da shelanta yakinta kan dawagitai da jabberai irinsu Mamun Abbasi, domin tonawa Abbasiyawa asiri kamar yanda gwaggonta Zainab (a.s) tayiwa Umayyawa da wadanda suka kasance irinsu daga azzalumai.

  Sayyada Ma’asuma (a.s) ta fito daga Madina cikin wannan hijira zuwa ga Allah da manzonsa tare da rakiyar mutane hudu da `yan’uwanta da wani adadi daga `ya`yansu da wasu adadi daga masoya da hadimai, ta kusanci wannan ayari da suka nufi Birnin Sawa cikin shaukin ganin Imamin zamaninta Imam Rida (a.s) sai dai cewa mutanen wannan gari sun kasance daga makiyan Ahlil-Baiti (as) suna da tsananin ta’asubbanci kan hukuma a wancan zamani, ai ayarin ta suka aka mamaye su da wani hari na babu zato babu tsammani daga fuskanin yaran Mamun makiya Ahlil-baiti.

  Cikin wannan hari na zalunci aka kasha dukkanin `yan’uwan Imam Rida (a.s) da yawancin mazajen da suke cikin ayarin, ance a wannan musiba mai radadi ya ta jawo dalilin wafatinta, wasu kuma sunce guba ce a da aka sanya mata tayi sanadiyar shahadarta, Sayyada Ma’asuma tayi rashin lafiya mai tsanani da hakan ya hanata cigaba da tafiya zuwa Marwa ta san cewa kuma ta dab da shiga birnin Qum, hakika tuntuni babanta da dan’uwanta sun bata labari cewa Qum cibiya ce ta shi’ar kakanninta tsarkaka sai kawai ta kuduri niyya tafiya can ta canja hanyarta daga hanyar Marwa zuwa birnin Qum mai tsarki, a rana ta 23 ga watan Rabi’u Awwal Sayyada Ma’asuma ta shiga birnin Qum mai tsarki.

  Hakika labarin shigowarta garin yayi matukar tasiri cikin zukata ta kai ga farin ciki da murna ya mamaye baki dayan sasannin birnin mutane suka fito don tarbarta da tarbar maukibinta mai cike da kwarjini babban malamin Hadisi Musa bn Kazraj Ash’ari yana masu jagoranci, lallai ya kasance daga manyan mutane a garin kumu daga ginshikan malaman shi’a, sai ya kama linzamin taguwar da take kai mutane suka kewayeta kamar yanda kwari suke kewaye kyandir mai haskakawa, Musa Ash’ari ya nemi ta sauka gidansa don ya kasance cikin hidimarta sai ta amsa bukatarsa ta sauka wani daki da bayan wafatinta ya shahara da sunan (Baitul Nur) wanda bai gushaba wurin ziyarar maziyarta daga masoyanta suna neman tabarruki da albarka numfashinta tsarkakka da ta shaka cikin gidan.

  Sayyada (a.s) ta wanzu cikin wannan gida tsawon kwanaki 17 tana fama tana jiyyar ciwo har sai da tayi wafati ta koma zuwa ga mahaliccinta a karshen mahallin bautarta, an raka jana’izarta ya zuwa makwancinta na karshe da yake Raudatu Babilanm Musa bn Kazraj ya gina kabarinta ya lullube shi da tabarma, a cikin karni na uku bayan hijira sai Zainab diyar Imam Muhammad Jawad (a.s) ta gina kubba kan kabarin aka binneta tare da ita kamar yanda aka binne mutane biyar tare da ita daga `ya`yan gidan annabta da mutum daga jikokin A’imma tsarkaka, kamar yanda aka ambaci hakan a manyan litattafai, sannan zaku iy samun iya ishara daga litattafai kamar (Shahdul Arwahu) da (Annajumul Mutanasira)

  Fadima diyar Imam Kazim (a.s) daga riwayoyi A’imma (a.s)            

  1 ـ قال الإمام الصادق  7: «ألا ان لله حرماً وهو مكّة ، ألا إنّ لرسول الله حرماً وهو المدينة ، ألا وان لأميرالمؤمنين حرماً وهو الكوفة ألا وان قم الكوفة الصغيرة ، ألا ان للجنة ثمانية أبواب ثلاثة منها إلى قم ، تقبض فيها امرأة من ولدي اسمها فاطمة بنت موسى ، وتدخل بشفاعتها شيعتي الجنة بأجمعهم »[3] .

  Imam Sadik (a.s) ya ce: ku saurara lallai Allah yanada wani harami wato Makka, ku saurara lallai manzon Allah yanada harami wato Madina, ku saurara lallai sarkin muminai yanada harami wato birnin Kufa, ku saurara lallai birnin Qum shine `yar karamar Kufa , lallai aljanna tanada kofofi takwas uku daga cikin zuwa Qum, za a krabi ran wata `ya mace daga `ya`yana sunanta Fadima diyar Musa, karkashin cetonta baki dayan shi’a zasu shiga aljanna.

  2 ـ قال الصادق  7«من زارها عارفاً بحقّها فله الجنة ».

  Imam Sadik (a.s) ya ce: duk wanda ya ziyarceta yana mai sanin hakkinta yanada aljanna.

  3 ـ قال الإمام الرضا 7«من زارها فله الجنة ، وفي رواية : كان كمن زارني »[4] .

  Imam Rida (as) ya ce: duk wanda ya ziyarceta yanada aljanna, a wata riwayar kuma ya kasance kamar wanda ya ziyarce ni

  Imam Jawad (a.s) yana cewa: duk wanda ya ziyarci gwaggona a birni Qum yanada aljanna.

  Dukkanin wadanan madaukakan riwayoyi suna labartar da girmanta da girmamar mukaminta wurin Allah da wurin mutane da kuma wurin Ahlil-baiti (as)