sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Labarun da ba tsammani

Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Bakir amincin Allah ya kara tabbata a gareshi


 

Amincin Allah ya kara tabbata ga annabi da iyalan gidansa tsarkaka.

Shaik Mufid cikin littafinsa Al'irshad ya rawaito daga Imam Bakir (as) yace:
"دخلت على جابر بن عبد الله رحمة الله عليه، فسلّمت عليه، فردّ عليّ السّلام، ثم قال لي: من أنت؟ وذلك بعد ما كفّ بصره؛
فقلت: محمد بن علي بن الحسين.
فقال: يا بني أدن مني، فدنوت منه، فقبّل يدي، ثم أهوي إلي رجلي يقبّلها، فتنحّيت عنه.


 


Na shiga wajen Jabir bn Abdullah Ansari Allah yayi masa rahama, sai na yi masa sallama  sai ya amsa sallama ta, sannan yace: wanene kai? Hakan ya faru ne bayan ya makance idonsa baya gan, sai nace: ni ne Muhammad bn Ali bn Husaini.


Sai yace: ya `dana matso kusa dani mana, sai matso, sai ya sumabci hannuna sai ya durkusa zai sumbaci kafafuna, sai na matsa na ja gefe daga gareshi.
ثم قال لي: إن رسول الله [صلى الله عليه وآله وسلم] يقرئك السلام.


Sannan yace mini: hakika manzon Allah (s.a.w) yana gaisheka.

فقلت: وعلى رسول الله السلام ورحمة الله وبركاته، وكيف ذلك يا جابر؟

فقال: كنت معه (ص) ذات يوم، فقال لي: يا جابر لعلك أن تبقي حتى تلقي رجلاً من ولدي يقال له محمد بن علي بن الحسين يهب الله له النور والحكمة فأقرئه مني السلام."


Sai nace: nima ina gaishe da manzon Allah, nace kaka haka ta faru ya Jabir?

Sai yace: wata rana ina tareda manzon Allah (s.a.w) sai yace mini ya Jabir me yiwuwa zaka wanzu kayi tsayin rai har kaga wani daga `ya`yana ana kiransa Muhammad bn Ali bn Husaini Allah ya bashi haske da hikima ka gaida mini da shi.